Showing 99001 words to 102000 words out of 132766 words

Chapter 34 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87973

you express my feelings 4 u I'll tell you how much I love you.
Yak'ara pecking nata a goshi ya gangaro akan pink lips d'inta nan ma yasake mata peck har ya mik'e tsaye ko me yatuna oho! Yak'ara durk'usawa yarik'on hannunta yaciro Biro daga aljihun coat d'inshi ya rubuta mata *I LOVE YOU* a tafin hannu a hankali ya mayarda hannunta ya ajiye yafita da sauri.
_12:00pm_
Haleesa da Hannah suka tashi daga bacci a gaugauce suka shirya Aderwale ya yi dropping d'insu Airport kafin flight d'insu yatashi suna zaune Haleesa ta lura da rubutu Biro a hannunta ta k'urawa rubutun ido duk yadda ta kai da so ta karanta rubutu ta kasa saboda a wajen wanka bata lura da rubutun ba ya wanke sai dishi-dishi kawai take gani a haka jirginsu yad'aga sai Abuja.
Sai misali k'arfe _1:30pm_ Habeeb yafito daga meeting bayan sunyi sallah shi da Mus'ab a cikin office d'inshi Mus'ab ya dube shi yace zuwa yanzu mutane ka sun tsofa a Abuja.
Cike da mamaki had'e da fad'uwar gaba yace su wa kenan"?
Haleesa da Hannah mana"
Saura kiris Numfashin Habeeb yafita daga gangar jikinsa yarasa Kalmar da zai furtawa Mus'ab sai faman had'a gume yake........

Jeeddah Aliyu🌹
[10:31PM, 08/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [08/12 1:45 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```88```

_ina mai mik'a sak'on ban hak'uri a gareku reader's pg d'in da nayi post jiya bashi bane original pg da yakamata na turo muku Pg d'in ne suka d'an rikitarda ni amma Dan Allah Ku yi hak'uri Ku sake karanta pg 87 zan yi post d'inshi tare da pg 88_


~~Gaba d'aya Habeeb yafita hayyacinsa sai yakai karshen bango yadawo farko bango yana yarfe hannaye kamar Wanda ruwan zafi suka k'ona.
"A d'age Mus'ab yake kallonshi yana murmushi mugunta sai kawai ya d'auke fuskarshi yaciro phone d'inshi gaban aljihun rigarsa ya kira Hannah yana zuba mata kalaman soyayya, yayi kamar bai fahincin halin da Habeeb yake ciki ba.
"Habeeb yarasa idan zai sa kansa jin yake yi kamar duniya ta juya masa baya me yasa leesa za ta yi min haka"?
Me yasa saida ta bari zuciyata tayi niyar fallasa mata sirrin da ke cikinta za ta gujeni domin nasan saboda ni leesa ta koma Abuja yau.
Da sauri yadauko phone d'inshi ya yi dialling number ta ga mamakinsa wayar na ringing ba'a d'aga ba da yacigaba da kira sai ya ji wayar a rufe ya ja iska da k'arfi jikinsa yadauki rawa kamar mai jin sanyi.
Cikin tafarfasa zuciya ya maka wayar a bango ta tararatsi sai kace wayar ce tayi masa laifi.
"Why leesa tell me why do this to me"?
Yak'arasa magana cikin shouting had'e da dukan desk, yasoma watsi da files d'in da ke zube akan desk da sauri Mus'ab ya katse wayar da yake yi da Hannah.
Yanufi wajen Habeeb yarik'onshi da k'arfi kanka d'aya kuwa Lamido"?
Ko kasha kwaya ne ko angaya maka soyayya hauka ne"?
"Habeeb ya ja iska had'e da ya mutsa gashin kanshi manyan idanu nan, nashi suka k'ara firfitowa basu da banbancin da na magge da sauri Mus'ab yadauke idanunshi da barin kallonshi, yace kai ni daina kallona da wad'annan masifafin idanun naka masu firgita mutum gaba d'aya kafara tsorata ni.
matsalarka kenan Lamido komai da zafi ka ke daukarsa zo ka zauna mu yi magana zan nemo maka solution yanzu nan.
''Da kyar Habeeb ya amince ya zauna sai huci yake, kamar Wanda ya yi wrestling Mus'ab ya bud'e fridge yadauko coke na gwagwani ya balle, ya mik'awa Habeeb da k'arfi yafizge gwagwani daga hannun Mus'ab yakafa kai saida ya shanye coke d'in tass....Ya matse gwagwanin cikin tafin hannunshi.
"Mus'ab ya girgiza kai yace ni ina mamaki wannan fushi na menene"?
"Akan wane dalilin leesa za ta koma abuja without my permission"? kasan irin zafi da quna da zuciyata take mun a lokacin da ka ke sanarda ni leesa, ta koma abuja shin ko kasan saura kiris heart attack ya kamani"?
"Mus'ab kacuce ni me yasa ka zuba min desire tablet a drink na kusance leesa da k'arfi"? gashinan a garin wannan iskanci naka ka janyo min leesa ta yi fushi da ni.
Mus'ab ya ja tsaki yace to ae ni taimaka maka nayi na nema maka hanyar da za ka kawarda sha'awarka akanta, to yanzu kuma menene abun damuwa just forget about her my friend mu cigaba da tsara yadda contract d'in nan zai tashi karka manta kai ka ke cewa money is everything, so za ka iya magance wannan matsala da ke tsakaninka da leesa da k'udi yak'arasa magana yana dariyar shak'iyanci.
"mugun kallo Habeeb ya watsawa Mus'ab karka fad'a min maganar banza Mus'ab duk ba wannan shishshigin naka bane yajanyo leesa tayi fushi infact ina ruwanka da sha'awarta da nakeyi ko kai ne ka biyan mun sadakin aurenta"?
"Omg! Wai kai Lamido wane irin masifafen mutum ne huh!"? Abunda ka keso ne nayi maka kai fa kace baka sonta sha'awarta ka keyi to don tayi fushi da kai shine me"?
''Habeeb kamar zai fashe da kuka yace Mus'ab "I'm in love with her wallahi Mus'ab ina sonta inason leesa tankar numfashina.
Mus'ab ya yi ajiyar zuciya yace d'an iska kawai da kana sonta uban waye yace kadinga wulaqantata"? Yanzu kuma it's her turn abun ya juyo kanka, ba lallai bane leesa ta amince da soyayyarka ba.
"Da mugun mamaki Habeeb yake kallon Mus'ab daga bisani ya ja tsaki, ina tsanmani Mus'ab ka manta da waye Habeeb Lamido shiyasa har ka ke tunani leesa bara ta amince da soyayyata ba.
Tabe baki Mus'ab ya yi shikenan Lamido in kana gani kamar wannan zafin kan naka zai sa leesa ta amince da kai ga filin ga mai doki, tun kafin tafiya tayi nisa kafara sauke fushinka akan phone zuwa gaba leesa tana 6ata maka rai wuta za ka cillawa company nan.
"Harara Habeeb ya galla masa ya ja tsaki ya kwashe sauran phone's dinshi da ke zube akan desk yanufi k'ofar fita, Mus'ab ya kyalkyale da dariya yace d'an rainin wayyo, yadauka masa briefcase d'inshi wance garin watsi da files ya had'a da ita ya Mara masa baya yana dariya a k'ofar fita ya had'u da Bala yace Bala please ka saka a gyarawa Lamido office dinshi kasame mu a parking space.
"Cike da mamaki Bala yace maigida Mus'ab lafiya kuwa saboda naga boss yafita cikin mugun fushi yanzu nan ya wanke sister Lora da mahaukacin mari.
"Mus'ab ya zaro ido muryarsa na rawa yace Lamido ya mari sister Lora to me tayi mishi da ya mare ta"?
Bala ya karkace kai yafara kwararowa Mus'ab sharhi dai-dai babbar k'ofar fita ya zo wuce wa yaci karo da Sister Lora by mistake ta goge hannunshi shine fa ware yatsunsa akan kumatunta, ina tsanmani sai taje hospital saboda ta maru ba kad'an ba.
'Mus'ab ya yi dariya yace to BBC shige ka aiwatarda da aikin da nasaka ka.
********************
_ABUJA_
duk kiran da Habeeb yake yi wa Haleesa tana sane tak'i picking da taga ya matsa da kira sai tayi switch off d'in wayarta tanaso tagano har yanzu Habeeb Lamido yana nan akan bakarshi na cewa sha'awarta yake yi ba sonta yake ba ko kuma yanzu yafara sonta ne.
"Don kawai ta musgunawa zuciyarsa yasa ta matsawa Hannah tanemo mu su ticket suka dawo Abuja yau a maimakon sai gobe za su dawo.
Saida dare yayi Haleesa ta zo kwanciya tarena kanta saboda kasa bacci sai juyi take, ta mik'e a sa6ule tanufi part d'in Habeeb, ta kwanta akan katafare Bed d'inshi, can! Idanunta suka hasko Mata d'an k'aramin frame mai d'auke da pic d'in Habeeb da salma akan bedside kishi taji yakamata da k'arfi tafizgo frame d'in ta jefa shi jikin bango ya tararatsi.
"Kawai sai tasa kuka tana magana ita kadai kamar, mai ta6in hankali me yasa ba za ka soni ba yaya Habeeb"?
Ni ina sonka koda baka sona kuma zan cigaba da sonka har zuwa karshen rayuwata.
"A da na dauka daga kan margayi yaya Habeeb bara k'ara son wani D'a namiji ashe abun ba haka bane da kyar tasamu bacci yadauke ta.

```HABEEB```

Asuban fari Habeeb ya tashi yana gama sallah yacigaba da trying number Haleesa, still wayar a kashe yadafe kai zuciyarshi na soya yaja tsaki yafi a kirga.
"Haushin Haleesa yakama shi yafara zance zuci har ni leesa za ta wulaqanta in kirata tak'i picking daga k'arshe ta rufe wayarta don kawai ta fahimce na kamo da sonta sai na nuna mata cewa mace bata yi mun wulaqancin.

_10:00am_
A hankali Habeeb yake taka staircase sanye yake da black colour suit, hannaye shi na zube cikin aljihu wandonshi fuskar nan tashi a murtuk'e.
''Ya hango Mus'ab da Bala zaune akan dining table suna breakfast kallo d'aya yayi musu yadauke fuska.
Mus'ab yace Lamido ka zo ka yi breakfast harara Habeeb ya galla masa, tsawon zamanka da ni kata6a gani nayi breakfast a irin wannan lokacin"?
Uhm.....Mus'ab yafad'a had'e da tabe baki yacigaba da cin abincinsa.
A yatsine Habeeb ya dube Bala yace Bala ka yi sauri ka gama ka kaini airport.
"Cikin Tsananin mamaki Mus'ab ya ajiye fork d'in hannunshi me za ka je yi a airport Lamido"?
"Abuja zan tafi yafad'a kaitsaye yanufi 1 seater ya zauna yayi crossing legs, da alama yau 'yan rashin mutuncin sun motsa.
Mus'ab ya mik'e had'e da ture kujera yanufi wajen Habeeb me ka ke shiri aikatawa Lamido"?
"Habeeb ya ja iska can! K'asan mak'oshi yace bara iya jure rashinta ba Mus'ab koda ba zan ganta ba atlast ko muryata ce naji na tabbata jin muryarta kadai zai sa nasami kwanciyar hankali yak'arasa magana kamar zai yi kuka.
"Mus'ab ya zauna bisa hannun kujera da Habeeb yake kai yadafa kafad'arsa bai kamata akan wannan abun kad'aga hankalinka ba leesa matarka ce kamata ya yi ka lalla6ata Ku gyara zaman aurenku ka jinginar da wannan zafin kan naka domin yana d'aya daga cikin abunda yake hanaka jin dad'i rayuwa.
"Katuna manzon Allah{s,a,w} yahane mu da fushi don haka Lamido ka yi wa kanka fad'a karage fushi domin ba abunda fushi yake haifarwa face danasani.
"Karka manta daga kai har leesa kun aure junanku ne batare da kuna son juna ba Haleesa akwai Wanda takeso mutuwa ce ta raba su kaga kenan mafi mahimmancin kafara cusa mata soyayarka ka goge kiyayyarka daga zuciyarta domin ka cutarda ita ba kad'an ba.
"Habeeb yayi ajiyar zuciya yace shiyasa nakeso tafiya abuja yau d'inan na sanarda ita irin son da nake mata.
''Lamido bai kamata ka tafi abuja yau ba kamata gobe ne tafiyar mu Japan"? Kuma wannan tafiya dole sai da tare kai ka yi hak'uri har Allah yadawo da mu lafiya zuwa wannan lokacin leesa ta huce Mus'ab yacigaba da rarrashin Habeeb had'e da yi masa dad'in baki har yayi nasara hanashi tafiya.
***********************
_3 day's later_

Haleesa tana kwance akan 3 seater Hannah tayi sallama tashigo a gajiye tafad'a bisa kujera washh....matar yaya Habeeb wallahi na kwaso gajiya, akwai abinci a gidanan"?
"Haleesa ta mik'e zaune ta tabe baki ki kira yarinye ta kawo miki.
Bayan Hannah tagama cin abincin ta zuge zip d'in handbag d'inta tafito da invitation card ta mik'awa Haleesa ga invitation d'in auren yaya Sageer d'a wurin Aunty Mami a Sokoto za'ayi bikin
''A kasalance Haleesa ta kar6i invitation d'in ta duba ta ajiye a gefenta, yaushe za Ku tafi ne"?
"Maybe ranar Wednesday saboda mom tace tafiyar mota za mu yi kada mutum yaje yarasa mota da zai dinga fita da shi ko za ki je ne"?
Ajiyar zuciya Haleesa tayi cikin sanyi murya tace zan je ko zan rage wannan zaman kadaici da zaman tunanin mutume da bai da mu da ni ba tak'arasa magana hawaye na zuba akan fuskarta.
"Hannah ta mik'e tadawo kusa da ita ta zauna, kina nufi har yanzu ba wani canji Haleesa ta girgiza kai cikin muryar kuka ta kwashe yadda suka yi da Habeeb tafad'awa Hannah saboda ta yarda da Hannah d'ari bisa d'ari.
''Cike da takaici Hannah ta ja tsaki narasa gane yaya Habeeb wane irin shu'umin mutum ne"? In banda wulaqancin da rainin hankali don baya sonki sha'awarki yake bai kamata yafito fili ya fad'a miki ba.
"Ae gwara da ya gayamin matsayina a zuciyarshi kinga yanzu nasan cewa jikina yakeso ba ni ba amma zahirin gaskiya Hannah d'an uwanki yayi min illah domin zuciyata tayi nisa a sonshi sai nakeji kamar banta6a son wani d'a namiji ba sai akanshi.
Hannah ta rungume Haleesa tafara rarrashinta ta hanyar furta mata kalamai masu dad'i har tayi nasara shawo kanta tadaina kuka shawara da zan baki duk lokacin da ya zo miki da buk'atarshi ki bashi had'in kai da haka za ki kama shi duk abunda yakeso ki dinga yi mishi kada ki ta6a nuna masa kema kina sonshi ki nuna masa kawai biyayyar aure ce tasa kike masa abunda yakeso koda dutse ne a k'irjinshi ba zuciya ba dole wata rana yabaki gurbi a zuciyarsa.
''yanzu Ki tashi ki had'a kayanki mutafi gidan mom tunda jibi ne tafiya domin banga amfani zaman nan da ki ke yi ba.

_8:00pm_

Madam Hindu na zaune a katafare parlournta tana waya da Habeeb tana gamawa tafara kwallawa kira Haleesa da sauri Haleesa tafito daga d'akin Hannah.
''Gani mom!
Yanzu nan nagama waya da mijinki yace mini baki fad'a masa za ki je sokoto ba don haka ki kira shi a waya kinemi izzinshi duk da nasan ba zai hanaki ba.
"A sanyaye Haleesa tajuya ta koma d'akin ta kwanta kusa da Hannah tace Hannah kinji wata sabuwa"?
"Inji 'yan caca meke faruwa ne? Hannah tafad'a had'e da kallon fuskar Haleesa.
"Wannan kiran da mom tayi Min wai tayi waya da yaya Habeeb yace da ita ban fad'a masa ba zan bi Ku sokoto ba wai na kira shi na nemi izzinishi.
''Hannah ta ja tsaki wallahi mom ita ke k'arawa yaya Habeeb girman kai me ye na wani cewa sai kin nemi izzinishi mtww...tak'ara Jan tsaki.
''Haleesa tace ni babban tashin hankalina tun lokacin da muka dawo daga Lagos na rufe wayana.
"Ki daure kawai Haleesa ki kira shi kada mom ta fahimce akwai rashin jintuwa a tsakaninku.
"Ajiyar zuciya Haleesa tayi ta mik'e tadauko wayarta ta koma ta kwanta, tajuya wajen Hannah tace Hannah, ina masifar son yayanki
"Dariya Hannah tayi tace don't worry ta hannun dama na shima insha Allah wata rana sai ya zubarda hawaye akan sonki.
"Haleesa ta girgiza kai tace kuka fa ki ka ce Hannah wannan shu'umin ne zai yi min kuka"? Ke dai bara in kira shi ki ji yadda za ta kaya a tsakaninmu gabanta na fad'uwa tayi dialling numbershi..........

Jeeddah Aliyu🌹
[10:02PM, 09/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [09/12 4:55 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```89```

~~Wayar tayi ringing har ta tsinke bai d'aga ba Haleesa ta ja tsaki tace Hannah kinga halin yayanki koh"? Yanzu nan mom tak'are waya da shi amma ni gashi na kira shi yak'i picking.
"Yi masa uziri ki K'ara kira watakil yana ja miki class ne kinsan yayana mai tsada ne tak'arasa magana tana dariya tabe baki Haleesa tayi tace hum.....ae naga alama tak'ara danna kiran number Habeeb still har ta tsinke bai yi picking, 3 misscall Haleesa tayi mishi ranta abace ta ajiye wayar a gefenta.
"Share shi kawai anjima ki k'ara kira idan bai dauka ba ruwanshi kedai ba kinsan kin kirashi wulaqancin shine yahanashi d'auka.
"Ajiyar zuciya Haleesa tayi narasa me nayi wa yaya Habeeb ya tsaneni haka"? kwanakin da suka gabata yaya Habeeb yana bani kulawa, a koda yaushe za ki tararda mu manne da juna cikin d'an k'ank'ani lokacin yayi nasara raba zuciyata da soyayyar margayi yaya Habeeb.
''A lokacin har tunani nake ko yafara sona ne ashe, tunanina ne kawai yabani haka.
Hannnayen Haleesa Hannah tarik'o cikin sigar rarrashi tace Haleesa nasan abunda yaya Habeeb yake miki Sam baya kyautawa amma Dan Allah ki yi hak'uri ki cigaba da kai kukanki wurin Allah, sannu Allah zai kawo miki karshe wannan matsala kafin mu kwanta bacci ki daure ki k'ara kiranshi.
"Batare da Haleesa tace da Hannah komai ba ta miyar da hankalinta wurin film d'in da suke kallo.

_1 hour later_
Haleesa please ki K'ara kiran yaya Habeeb wallahi banaso mu yi tafiya nan batare da ke ba.
"Huh....Hannah kema kinsan ko na kira bara dauka ba amma tun da kin matsa bara na kira ta call had'e da k'ara wayar a kunne.

```JAPAN```

"A lokacin da Habeeb yagama da waya da mom yasaka phone's d'inshi a changing yafita zuwa haraban hotel d'in sukayi masauki shiyasa time d'in da Haleesa ta kirashi bai d'aga ba saboda baya kusa da wayan.
A yanzu kuma koda kiranta yashigo wayanshi har ya kwanta bacci saboda a can dare yayi sosai ringing d'in wayarshi ne yata yarda shi.
"Tsaki ya ja idanunshi a rufe ya mik'a hannu akan bedside yana lalla6e wayar, har yayi nasara gane wayar da ke ringing mamaki yake yadda bacci yadauke shi batare da yayi switch off d'in phone's d'inshi ba.
"Niyarsa da yadauko wayar yayi switch off, da kyar ya bud'e idanunshi sakamako bacci da yake ji sosai a rikice yak'arasa ware idanu, _leesa omg! I can't believe it leesa is call me_
"Hannunshi na makyaryata yayi received yakara a kunnenshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login