Showing 93001 words to 96000 words out of 132766 words

Chapter 32 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87963

nata, yashiga ya motsata son ranshi sai da yagaji don kansa yasaketa.
Gaba d'aya jikinta rawa yake ta sulale k'asa da6ss.......yana wicked smile ya durk'usa gabanta saida yaja iska yana wani lumsashe idanu, yace _wow! What's a perfect game I like it's baby_
Haleesa d'ago idanunta da suka canza colour zuwa red har ta bud'e baki za ta yi magana da sauri yadaura yatsanshi bisa lips d'inta _shhh......don't say anything baby_ ke fa ki ka tsokanoni don na mayarda Martani ae ba laifi bane kinga ki tashi sahunki a likkafa mu koma parlour kada aunty Juwairiyya ta yi tsanmani ko.......sai kawai hadiye sauran kalamansa ya kashe mata ido, cike da jin haushi Haleesa ta mik'e luuuuu.......jiri yadebe ta tafi za ta fad'i Habeeb yataro ta yadaura bakinshi dai-dai kunnenta yace _take it easy my hot baby it's just a pretending_
Yana k'arasa magana yasaketa Yajuya cikin parlour
Haleesa tasauke ajiyar yafi a kirga saida tad'auki tsawon _6 minutes_ tana jinyar dafin da Habeeb ya zuba mata, jikinta a sanyaye tak'arasa parlour, tana murmushi yak'e tanemi kujera ta zauna duk yawancin firar aunty Juwairiyya ce take yi _11:00pm_ tana bugawa aunty Juwairiyya ta mik'e ta dube Habeeb tace my in-law sai da safe "Toh.... aunty Allah ya tashe mu lafiya
Ameen tafad'a had'e da juyawa tanufi bedroom d'in Haleesa da sauri Haleesa ta bi bayanta har tana had'awa da tuntu6e Habeeb ya bi ta da murmushin mugunta har tafara haura stairs yadakatar da ita ta yadda aunty za ta ji abunda zai fad'a yace _baby in kin raka aunty bedroom ki zo ki had'a min coffee in yaso sai kidawo ki taya aunty kwana_
A tsorace Haleesa tajuya suka had'a ido ya yi mata signal..............


Jeeddah Aliyu🌹

[10:46AM, 04/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [03/12 9:03 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```84```

~~Haleesa ta yi k'ayatace murmushi ta kad'a kwayar idonta a yangance tanufi wurin Habeeb kamar za ta shige k'irjinshi, sai kawai tanufi gefen bed ta zauna tana yi masa dariya.
" Habeeb ya yi murmushi had'e da ya mutsa sumar kansa da baya-baya yafad'a bisa bed ya runtse idanunshi, lek'a fuskarshi Haleesa ta yi tana mai cigaba da dariya, cikin tsokana tace _hey Mr pretender whats is wrong"?_
Ya mirgino yadawo saitin fuskarta kallon ido cikin ido yake mata ya ja iska yace kina nufi ko yau pretending d'in ne yakawo ki d'akina"?
''Kaima kasan in bayan shi ba abunda zai kawo ni d'akinka
Cije lips d'inshi ya yi yana kallonta a yatsine da sauri ta d'auke fuskarta da barin kallonshi.
Shiru sukayi ba Wanda yak'ara tankawa d'an uwanshi Haleesa tajuya ta sace kallonshi ya yi pillow da hannayenshi idanunshi a rufe ruf kamar mai bacci, kasa d'auke fuskarta ta yi akansa tashiga nazari kyakyawa fuskarsa ta yi ajiyar zuciya a kasalance ta mik'e tanufi gefenshi ta kwanta, tana mamaki d'abi'un Habeeb bata ta6a ganin mutum mai abubuwan mamaki irinshi ba ta yi nisa a tunaninshi batansan lokacin da ya matso daf da ita sai jin ta ta yi cikin jikinshi, cikin kunnenta ya rad'a mata bai kamata ki dinga wahalarda zuciyarki da tunanina bayan gani kusa da ke yak'arasa magana had'e da hura mata iskan bakinshi a kunne.
"Da sauri ta lumshe idanu, Habeeb yak'ara matso da ita cikin jikinshi ya hard'e k'afafunshi cikin nata yasaka hannaye shi ya layyace gadon bayanta fuskokinsu na facing d'in juna duk abunda yake yi idanunshi suna rufe kasa motsi Haleesa ta yi sai fama zazzare ido kawai take yi numfashinta na fita da k'arfi, ta k'urawa Habeeb ido a zuciyata tace ina ma ace da yaya Habeeb d'inta take kwance ba da wannan arrogant d'in ba mutumi da ya furta mata cewa sha'awarta yake yi ba sonta yake ba tabbata duk ranarda ya yi nasara cima burinshi akanta zai goge babinta ne a zuciyarshi, tausayin kanta yakamata hawaye suka zubo mata saboda tuni ta fahimce cewa ta fad'a tarkon so Habeeb Lamido tacigaba da kallonshi, yayinda Habeeb bai masan tanayi ba saboda tuni bacci ya yi awo gaba da shi ta ja karan hancinshi ta lumshe idonta a haka bacci mai dad'i ya yi nasara d'auke ta.
*************************
_11:00am_
Haleesa da Habeeb na zaune a dining table suna taking breakfast cikin kulawa Habeeb ya dube Haleesa, yace k'arfe nawa flight d'insu aunty Juwairiyya zai tashi"?
Saida Haleesa ta hadiye chips d'in da take tauna tace _11:30am_ Habeeb ya gyad'a kai suna gama breakfast suka nufi parlour inda aunty Juwairiyya take jiransu su kaita airport, kafin su wuce da ita airport nasiha ta yi musu sosai basu baro airport ba saida suka ga tashin jirginsu.
"tun akan hanyar su na dawowa gida Haleesa ta daure fuska Habeeb ya dube ta ya yi murmushi yad'age gira sama yana kallonta hannunta yarik'o cikin zafin rai ta firzge hannunta, a yatsine tace aunty Juwairiyya ta tafi daga yanzu ba wani sauran pretending, the game is over.
"Habeeb yak'ara fad'ad'a murmushinsa ya wani kad'a kai batare da yace da ita uffan ba har suka isa gida Bala na yi parking
tun kafin ya bud'e mata k'ofa ta bud'ewa kanta da sauri tanufi cikin gida.
Habeeb yafito daga cikin mota ya yi mik'a ya bi Haleesa da mayen kallo a baiyane ya furta _the game is not over baby this is just the beginning_
Bala ya matso daf da shi ya yi k'asa da murya kamar munafuki yace "boss wannan wane irin game ne jikina yabani wasan zai yi dad'i kuma na tabbata Kaine winner.
"Da mugun mamaki Habeeb ya kalli Bala daga bisani yadafa kafad'arsa suka jera suna tafiya a hankali Habeeb ya ja iska yace nima ina ji a jikina ni ne winner amma basan how long wasan zai dauka kafin nayi winning.
''Bala ya washe hak'ora yace karka damu da tsawon lokacin da wasan zai dauka abu mafi mahimmancin ka yi nasara cinye wasan amma boss wannan wane irin wasa ne"? Bala yak'arasa magana yana dariya.
''Habeeb ya galla masa harara yadak'i kafad'asa yace na tsani shissshigi Bala.
Murmushi Bala ya yi yace "yes boss.
"Direct Haleesa ta wuce bedroom d'inta ta qargame k'ofa, tun daga lokacin suka koma 'yar gidan jiya za ta girka masa abinci ta jejjera akan dining table ta shigewarta d'akin ta murza key.
idan Habeeb yaga dama yaci ranar da yaji baya ra'ayi ci yabar mata kayanta a haka suka share _1 week_ suna gida d'aya amma kowanesu rayuwarsa yake yi.
_10:00pm_
Habeeb yana kwance a bedroom d'inshi abun duniya yataro ya yi masa yawa, tunanin Haleesa na azabtarda ruhinshi da yarufe ido ita yake gani, ba abunda yake buk'ata irin ya ji d'umi jikinta da sanyaye k'amshinta kamar Wanda aka mintsina da sauri yasauko daga kan bed yanufi part d'inta.
Yana murd'a handle ya ji k'ofar d'akinta a rufe ya yi tsaye kamar zai kurma ihu tsawon lokacin yadauka yana safa da marwa can! Idea tafad'o mishi da sauri yafice sai gashi yadawo rik'e da mopper da k'arfi yafara dukan kujerin parlour da mopper hannnushi yature d'an k'aramin glass madauke da flower da ke ajiye akan center table yafad'o yadak'i tiles ya tararatse.
''Haleesa na kwance har bacci yafara d'aukarta taji k'arar fashewar glass, ta zabura da k'arfi ta diro daga kan bed tanufi parlour da gudu tun kafin tak'arasa ta hango Habeeb yana watse da pillowcases na kujeri gaba d'aya ya hargitsa mata parlour a rikice tak'arasa wurinshi, muryarta na rawa tace lafiya yaya Habeeb"?
Banza yayi da ita yacigaba da watsi da kaya rik'e mai hannnu ta yi yadakatar da abunda yake yi, yana sauke numfashi, wai yaya Habeeb me ka ke nema ne duk ka bi ka rikita min parlour"?
"Habeeb ya karkace kai yafara tsara Haleesa ta hanyar cewa _ina zaune a dining area na ga wani abu mai bindi ya rugu da gudu yashigo parlournki shine na biyo shi da mopper yashige k'ark'ashin kujeri_
Zo ki ta ya ni mu fiddo shi Haleesa ta zaro ido cikin sark'ewar halshe tace ni fa ban fahimce abunda ka ke nufi ba"?
Habeeb yadafe goshi yace ina wannan abin mai tsawo yana da dogon bindi ya ma sunanshi yashiga tunani kamar da gaske karaf Haleesa tace bera
Habeeb ya yi shiru yana kallonta ya girgiza Kai yace No....ba bera bane ae bera baya cizo koh"?
''Haleesa ta gyad'a kai to ko k'adangare ne yaya Habeeb"?
Haleesa tafad'a da alama tafara tsorata shiru Habeeb yana nazari maganarta daga bisani yace k'adangare kai bashi bane domin shima baya cizo wannan abu mai tsawo jikinshi yana da tsantsi, za ki tuna suna wannan abu da na ta6a siyowa Imaan na roba a Canada har yabaki tsoro"?
tun kafin Habeeb yak'arasa magana Haleesa tadaka mahaukacin tsalle ta chukuikuye shi jikinta na rawa tace yaya...Habeeb....Maciji
Wicked smile Habeeb ya yi yace eh! Maciji ne nima na yi matuk'ar mamaki yadda aka yi yashigo parlounki.
"Haleesa tafashe da kuka tak'ara qanqame Habeeb kamar za ta shage k'irjinshi Dan Allah yaya Habeeb kafita da ni gidanan wallahi tsoro nakeji.
Kinga me ye kuma abun tsoro tun da ba'a bedroom d'inki yake ba yanzu yadda za'ayi ki shage bedroom ki qargame kamar yadda ki ka saba gobe da safe zan kira securities su fito da shi.
Cikin shashshek'ar kuka Haleesa take girgiza kai bara iya ba yaya Habeeb, zai iya shiga har bedroom ni dai ka fita da ni.
Habeeb ya fakace idonta ya yi mata gwalo yace saidai in za ki je part d'ina mu tafi amma ni basan inda zan kai ki ba.
Kuka yaci k'arfinta takasa furta komai sai faman d'aga kai ta ke yi cike da farin ciki Habeeb yadauke ta cak......da kyar ta amince yasauke ta bisa gado Habeeb ya dube fuskarta ya ga yadda ta kwa6e da hawaye had'e da majina, tausayinta ya yi mugun kamashi ya mik'a hannu bisa mirror ya yago tissue ya goge mata fuska yace kwanta ki cigaba da baccinki.
Girgiza kai ta yi ta rik'e mishi hannu gam yayi k'asa da murya ki kwanta ba abunda zai same ki bathroom zan shiga bara d'auki dogon lokacin ba zan fito kinji"?
Uhm!...uhm...ni dai mu tafi tare zaro ido Habeeb ya yi yace a ina za mu tafi"?
Bathroom tafad'a cikin murya kuka, komawa Habeeb ya yi zauna kusa da ita yace na fasa zuwa bathroom d'in saboda bara yarda ki bini ciki ki k'are min kallo.
Da sauri Haleesa ta matsa tashige cikin jikinshi, a hankali yake bubbuga bayanta har yasamu tadaina kuka ya ja mata pillow ta kwanta cike da nishad'i Habeeb ya kwanta kusa da ita ya rungumeta tsanm.
**********************
_washe gari_
Habeeb da Haleesa suna zaune a parlour Habeeb ya yi pillow da cinyoyinta, ita kuma sai faman damuk'a mishi gashi take yi idanunshi na lumshe yace ke! har yanzu ba'a gama Kitso bane"?
"Turo baki ta yi sumarka yacika tsantsi da yawa da na kitsa sai ya warware, ayya kuwa yaya Habeeb ba relaxer ka ke sakawa ba"?
Tsaki ya ja ya mintsine ta a gefen cinya angaya miki ni d'an daudu ne da zan sakawa suma na relaxer"?
Uhm..!ka ga bawan Allah maida wuk'a ni bance maka d'an dauda ba kawai dai naga kai d'an gayu ne tak'arasa, magana tana lek'on fuskarshi.
Habeeb ya yatsine fuska yace gayanci na bai kai can ba kinji koh magge"?
Tashiga ture masa kai daga cinyoyinta d'aga mun daga jiki tun bara ka daina kira na da magge ba ni dama dole ce tasani zama a part d'inka.
Ke fa ki ka ce sunanki magge"
Yaushe nace da kai sunana magge"?
Kafin yabata amsa phone d'inshi ya yi ringing Haleesa ta mik'a hannu bisa center table tadauko masa, kamar ba zai d'aga kiran ba sai da yagama Jan ajinsa sannan yad'aga _Hello Maryam ya akayi ne"?_
Rass...rass...gaban Haleesa yafad'i da ta tuna wacece Maryam a wurin Habeeb nan take wani irin kishi ya turnuk'e ta har Habeeb yagama waya batasan inda kanta yake ba saida taji yana mata tafiyar tsotsa a gefen cinyarta, buge mishi hannu tayi kamar daga sama ta ji muryarshi yana cewa Maryam ce ta kirani wai gobe za ta turo driver yad'auki Imaan ta je musu hutu.
"Ajiyar zuciya Haleesa ta yi tace uhm...
Tun daga wannan lokacin shak'uwa mai k'arfi yashiga tsakanin Habeeb da Haleesa yau Habeeb yashirya zai tafi Lagos, kuka Haleesa tasa mishi bara ta iya zama ita kadai ba saida yakira Hannah a waya ta turo masa yarinye Housemaid d'in madam Hindu ta tayata zama saboda Hannah exam take yi Haleesa tana tsaye a palour tana matsar hawaye Habeeb yafito rataye da briefcase d'inshi gani tana kuka yasa jikin Habeeb ya yi sanyi ya rungumeta yana rarrashinta kidaina kuka bara wuce _1 week_ ba zan dawo kinji"?
Yak'arasa magana had'e da d'ago fuskarta ya tsotsi lips d'inta na k'asa wani irin quncin ya ziyarce zuciyarta tana tunani yadda za ta share tsawon sati d'aya batare da Habeeb ba.
Cikin muryar kuka tace ni ban damu da kowane lokacin za ka dauka ba ka dawo ba babban damuwa na yadda za ka tafi kabarni da maciji a cikin gidanan.
Tsaki Habeeb ya ja cike da takaici yake kallonta da ya dauka kukan da take yi saboda zai tafi yabarta ne har yafara murna ita ma tafara jin abunda yakeji a game da ita shiyasa ma yake d'aga mata k'afa kafin ya ga iya gudun ruwanta, ashe ita abun ba haka bane a wurinta.
Kukan Haleesa ya tsananta Habeeb ya galla mata harara cikin zafin rai yace, maciji ya kashe ki kafin in dawo yaciro bundle na 'yan N1000 ya jefa mata bisa kujera yafice da sauri saboda jin yake yi kamar zuciyarsa za ta tarwatse.
Haleesa ta yi sororo baki sake ta bi bayanshi da kallo dama tasan har abada Habeeb Lamido bara ta6a sonta ba ko 'yar wannan shak'uwa da tashiga tsakaninsu, duk lokacin da ya bud'e bakinshi saidai yace tana burgeshi tana bashi sha'awa, ita kuma ta tsani jin wad'annan kalamai daga bakinshi saboda ta kai k'ololuwa a sonshi tak'ara fashewa da kuka ta kwasa da gudu tashige bedroom d'inshi..........

Jeeddah Aliyu🌹
[10:36AM, 07/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [06/12 8:22 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```86```

~~Jikin Haleesa yad'auki rawa takasa furta uffan, haka ya ba wa Habeeb dama yak'ara matsowa da ita k'irjinshi, ya ware idanunshi yana mata kallo mai cike da sinadarin so" very slowly yafurta _you're looking so beautiful today leesa_
"Takaici had'e da k'unar zuciya suka lullu6e Haleesa dama iya wad'annan kalamai ne Habeeb zai furta mata shine ya tsaya yana 6ata mata lokacin batasan lokacin da ta ture hannaye shi daga kafad'arta tajuya cikin zafin nama yarik'o hannunta, batare da tajuyo ba ta yi tsaye cak ya matsa kusa da ita ta baya ya yi hugging d'inta yatura kanshi a gefen wuyanta, ya ja iska yace _hey! Are you feeling shy_
''Ta kad'a kwayar idonta tace of course not ta yi yunk'urin kwacewa ya hanata ta hanyar k'ara qanqameta, leesa kina mun wulaqancin ko don kin fahimcin nafara damuwa da ke shiyasa ki ka za6i hanyar da za ki dinga musgunawa zuciyata koh"?
''Haleesa ta yi murmushi, banida amsar wannan tambayar taka amma zan iya cewa ka taimaka kasake ni kada Hannah tafito taganmu haka tak'arasa magana kamar zai ta yi kuka.
"So what's don Hannah taganmu a haka ae ba haramun mu ka aikata ba
Ba haramu bane amma gaskiya da kunya.
Ya yi ajiyar zuciya me ye abun kunya anan abunda yafi wannan zan iya miki a gabanta.
"Zaro ido Haleesa ta yi a tsorace tace meke nan"?
Juyo da fuskarta ya yi yace kamar wannan ya had'e bakinshi da nata daga bisani yasaketa yana dariya k'asa-kasa
Hmm.....da kuwa ka kasance marar kunya lamba d'aya dariya Habeeb yake yi sosai da kyar yasaketa tafice da sauri har tana had'awa da gudu ya bita da kallo yana Shafa sumar kanshi.
"Tana shiga bedroom ta tararda Hannah zaune a gaban dressing mirror tana make-up, ta cikin mirror suka had'a ido princess Hannah sai yanzu aka ga damar tashi daga bacci"?
Huh......matar yaya Habeeb hope kin nemi gaban mijinki"?
''Shiru Haleesa tayi bata tanka ta ba sai kawai tad'auki phone d'inta tana game.
Hannah tasaka kayanta ta dube Haleesa tashi mu tafi koh"?
"Batare da Haleesa tayi magana ba ta zari mayafinta, suka fice a parlour suka tararda Habeeb Lamido yana aiki a system.
''Good morning bros!
"Morning Autar mom ina za'a tafi haka naganki da 'katuwar handbag"?
''Market za mu shiga babyn aunty Juwairiyya za mu yi wa shopping.
"Hmm......ba wani shopping da za Ku je kedai kifito fili ki ce za Ku tafi yawon rabon ido a kasuwa.
''Allah yaya Habeeb shopping za mu je kuma ma bara mu dad'e ba koh Haleesa"?
Sai lokacin haleesa ta dube su sai kawai ta gyad'a kai Habeeb ya dubeta ya tabe baki akwai take away akan dining table....kafin Yak'ara sa magana Hannah tanufi dining area da sauri sai gata dawo da Leda fara mai tambari _Royal kitchen_ tafito da robubin take away guda hudu ta mik'awa Haleesa guda biyu.
Haleesa tazari guda d'aya ina plate Hannah"?
Ba bu buk'atar plate Haleesa haka ma za ki iya ci ko kinmanta ne sauri mu ke yi Hannah tafad'a had'e da bud'e robar soyayye chips had'e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login