Showing 6001 words to 9000 words out of 132766 words
kasan duk lokacin da naga babylove mantawa nakeyi da komai_
Mtsss...salman yaja tsoki yace wannan kuma matsalarka ce ni ba abunda yahad'ani da wannan shirme naka, don haka ka ajiye shi a gefe mu yi abunda yake gaban mu.
Hannu Haleesa, Habeeb yarik'o yace _babylove fad'a min sunan da kike so asakawa shagonmu?_
Kallon amma kai shashasha ne salman yake watsawa Habeeb, yayin da Haleesa ta wangale baki tana dariya daga bisani tace ```Ni da yaya Habeeb ```
Habeeb ya tintsire da dariya Haleesa na taya shi, cikin tafarfasa zuciya salman yaja dogon tsoki, ya mik'e had'e da ficewa daga gidan domin yana tunani Habeeb ya zauce.
Salman bai tabbatar da Habeeb ya zauce ba sai a washe gari da yaci karo da k'aton _symbol_ a kafe a gefen shagon su an rubuta ```NI DA YAYA HABEEB TAILORING CENTER ``` salman ya yi tsaye had'e da tsurawa sunan ido kawai yasaki murmushi yak'ara sa shiga shagon batare da kalle Habeeb ba yanufi wurin tela sa yayinda Habeeb yayi tsuru-tsuru da ido daga bisani ya mik'e yanufi wurin salman yadafa kafad'arsa ya marairaice murya yace kayi hank'uri salman nasan suna da na sanyawa shagon nan baiyi maka dad'i ba amma Dan Allah kayi hank'ur karka yi fushi da ni.
Salman yasaki murmushi yarik'o hannu Habeeb, yace daina bani hank'uri Habeeb duk abunda kake so nima ina sonshi saidai son da kake nunawa Haleesa yayi yawa da za ka d'auki shawara na da nace karage ko da d'an k'ank'ani ne.
Habeeb ya6ata fuska daga bisani yace son Haleesa _Allah ne yad'ora min bani na d'orawa kaina ba_
Salman ya girgiza kai batare da yace komai ba domin yasan har abada Habeeb ba zai ta6a d'aukar shawara sa.
Sannu-sannu shagon su Habeeb yadinga han6aka suna samu _customers_ sosai gani yadda suke samu kud'i yasa suka yanke shawara neman _admission_ a _polytechnic_ cikin yarda Allah suka samu adadafe suka, kamalla _diploma_ sun sha gwagwarmaya neman aiki amma basu samu ba dole suka hank'ura suka cigaba da d'ikin su na tela, watakila nan Allah yanufi abincin su yake.
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu🌹
[24/08 8:51 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [24/08 7:35 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```10```
```BAYAN SHEKARA BIYAR ```
Haleesa tana aji hudu a sakandire{secondary school} ta zama 'yan mata kyauta yak'ara fitowa, soyayya suke zubawa ita da Habeeb tafitar hankali, a lokacin akayi bikin aure juwairiyya da mijinta mas'ud kasance wa masa'ud yana aiki a karkashen wani shaharare _company_ a Lagos da ke sarafa shinkafa mai suna _majeed's parboiled Rice Limited_ shiyasa ana kamalla bikinsu masa'ud yadauki matarsa suka lula Lagos.
Mal Usman da mal Audu suka tsayarda lokacin bikin Haleesa da Habeeb zarar Haleesa ta kamalla _secondary school_ za'ayi bikin aure su da yake Habeeb basida karfin siyen fili kuma har yayi gini mal Usman ya zaunarda d'an uwansa mal Audu yafad'a masa ya yanke shawarar su raba gida nasu kashi biyu kowane yad'auki nasa kaso domin Habeeb da salman su fara gini matsuguni da za su zauna da iyalinsu, mal Audu ya yi na'am da shawarar d'an uwansa wannan shine dalilin da yasa suka ra6a gida tuni Habeeb da salman suka fara gini dai-dai na talaka mai k'arami k'arfi.
```CIGABAN LABARI ```
_A washe gari_
Haleesa da zainab sun dawo daga _school_ da yake makaranta nasu bashida nisa sosai da gida da k'afa suke takowa, tafiya suke suna fira kamar yadda suka sa6a Zainab ta kalli Haleesa tace ina fatar yau ba za ki biya shagon su yaya Habeeb ba"?
A yatsine Haleesa take kallon zainab daga bisani tace mutuwa za'a fasa ko Hisabi"?
Humm....ba Wanda za'a fasa Zainab tafad'a kaitsaye.
To kidaina wahalar da kanki ta hanyar tambaya na.
Amma gaskiya ina tausaya miki saboda in yaya salman ya d'ank'eki sai kin yabawa aya zak'inta.
Haleesa ta ja tsoki mtsss wallahi ba Wanda ya isa yahanani zuwa, gani hasken zuciyata tak'arasa magana tana wani murgud'a baki murmushi zainab tayi had'e da cewa Allah ya kai lafiya amma inaso Kisani duk tsuntsu da ya kira ruwa shi, ruwa kan d'oka kafin Haleesa tabata amsa wata tsadadiya mota kirar _Range Rover elegance 2016_ wance tsawon rayuwa Haleesa bata ta6a ganin irin ta ba _driver_ motar ya fatsala musu ruwan kwatami da ke gefen hanya tun daga fuskar Haleesa har izuwa farin Hijab d'inta yalalace da ruwan kwatami, Haleesa tabi jikinta da kallo tsanani bacin rai yarufe ta musanman da tad'aga kai ta hango mai motar bashida niyar tsayawa, zuciyarta tak'ara tafarfasa, saida _driver_ motar yayi nisa kad'an da su sai kuma yayi _reverse_ yadawo daf da su ya tsaya, da yake gilasai motar _tented_ ne basu iya hango Wanda ke ciki balle k'ofar motar akayi wani mutum gajere yafito yana sanya da riga da wando bak'i da fara da _fencing cap_ bak'a kallo d'aya Haleesa tayi ma kayan jikinsa tagano _uniform_ ne da ke nuna shi driver ne bashi ne ainihi mai motar ba.
_driver_ yace Dan Allah kuyi hank'uri banganku bane.
Zuciyar Haleesa na tafarfasa idanuta sunyi jajir tace da yake kai makaho ne ae dole kace baka ganmu ba kuma don tsabar wulak'anci da reni wayo shine saida kaga dama sannan kafito ka bamu hank'uri
Haba baiwa Allah nace kuyi hank'uri wallahi ba da sanina na watsa muku ruwan nan.
Zainab ta rik'o hannu Haleesa tace _please Haleesa tun da yabamu hank'uri ki kyale shi yayi tafiyarsa mana.
A harzuk'e Haleesa ta buge hannu zainab tace hank'uri sa na banza da wofi ko kina nufi hank'uri sa zai cire min wannan wari kwatami da nakeyi ko kuma zai wanke mini kayana"?
Karar bud'e k'ofar mota ne yaja hankalinsu gaba d'aya suka mayarda ganinsu, wurin motar k'afafu sanye da _black cover shoe_ suka fara fitowa daga cikin motar sai kyalli da d'aukar ido suke yi da sauri driven yanufi k'ofar mota yarik'e had'e cewa _I'm sorry boss yarinya ce tafiye kafuwa na bata hank'uri amma taki ta hak'ura_
Sai ganin sukayi an turo driver da k'arfi gangar jikinsa tafito daga cikin mota sanye yake da _suit dark green colour_ kwayar idonsa lullube cikin _black shade_ kyakyawan matashi saurayi Wanda shekaru sa na haihuwa ba za su haura 37-38 fari tass da shi sumar kansa bak'a wulik, fuskarsa a murtuk'e yanufi wurin Haleesa tuni jikinta yad'auki rawa domin tayi masifar tsorata da gani wannan _guy_ yana isa daf da ita yad'aga kyakyawa hannusa ya sharara mata tagwaye mari, saida ta zube k'asa tsawon rayuwata ba'a ta6a mari ta ba shiyasa ta rud'e matuk'a.
cikin _husky voice_ yafara magana _you Animal who do you think you are?_
Da har za'a baki hank'uri kina cewa ba za ki hak'uri ba to sai kiyi abunda za ki iya banza kawai 'yar iska 'yar talakawa.
Tsanani tsoro had'e da firgici sukayi nasara lullube Haleesa tad'ago baki bud'e tana kallon wannan saurayi.
Tsawa yadaka mata ta hanyar cewa tadaina kallona dan uban ki
A tsorace Haleesa ta sada kai k'asa yayinda saurayin yaja tsoki yajuya yanufi motarsa _drivernsa_ ya bud'e masa k'ofa ya yayinda driver zagaye da gudu ya zauna a driver _sit_ yaja mota da k'arfi..
Jeeddah Aliyu🌹
[24/08 8:37 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```11```
Suka halba kan titi Zainab tabisu da kallo daga bisani tadawo da ganita akan Haleesa, wance ke zaune da6ass a k'asa tadafe kumatu ta ita ba kuka takeyi ba, kuma batada niyar tashi tsaye da sauri Zainab ta girgiza ta had'e kiran sunanta Haleesa ki tashi mu tafi gida Allah sai saka miki wannan zalunci da akayi miki.
Har zainab tadasa aya a zanceta Haleesa na kallonta, abunda yayi matuk'ar rana Zainab kenan, da kyar ta iya mik'e wa tsaye ta kwasa da gudu tanufi shagon su yaya Habeeb, a firgici tafad'a shagon sai faman sauke take yaya Habeeb yadaka mata tsawa ke! Lafiya za ki shigo mana shago a hargitsi"?
Cikin sark'ewa halshe zainab tace yaya Habeeb Haleesa tun kafin tak'arasa Yaya Habeeb ya mik'e tsaye jikinsa na rawa yace me yasami Haleesa"?
wani mutum ne mai siffar larabawa direba sa ya watsa mana ruwan kwatami don kawai Haleesa tayi magana shine, mutume mai siffa larabawa yafito daga mota yadinga wanka mata mari saida tayi suman zaune, yanzu haka tana chan gefe hanya ko motsi bata yi.
Cikin tsanani tashin hankali, yaya Habeeb ya kwasa da gudu yafita daga shagon yayin da yaya, salman da saura yaran shagon suka Mara masa, baya yadda zainab tabarta haka yaya Habeeb yatarda dafe da kumatu, a rikice ya zube gabanta yad'ago fuskarta nan take yak'ara rud'ewa sakamako gani idanu ta sunyi kwacin jini ga kuma yatsu Mai siffa larabawa sunyi radau-radau sun kwanta a kumatu ta, Haleesa nagani yaya Habeeb sai lokacin tadawo haiyaci ta tafad'a jikinsa tafashe da mashahuri kuka, yayinda yaya Habeeb ya rungume ta tsanm a k'irjisa, yana bubuga bayanta, yaya salman yajuya wurin zainab yace Zainab ina kika ga mutume yabi"?
Zainab ta nuna titi da hannuta, yaya salman ya bi hannuta da kallo, daga bisani yaja tsoki yace watakila rashin kunya tayi masa, shiyasa wanke 'yar banza da mari.
Cikin k'una zuciya yaya Habeeb yad'ago yana huci, yace don tayi masa rashin kunya shine zai bashi damar yaraunana ta haka"?
Na ratsi duk lokacin da naci karo da wannan mutum sai na nuna masa kuskuresa na mari babylove yak'arasa magana yana huci kamar bak'i kumurci yaya salman yayi murmushi had'e da cewa malam hank'uri za kayi domin da dukan alamu wannan mutum ya tsofa a kasar _Egypt ko labanon_ saidai in kuma chan za ka bishi ka nuna masa kuskure sa ba zan hanaka ba ko ba komai _diamond girl_ yata6a yaya salman yak'arasa magana yana dariya.
Yaya Habeeb yak'ara harzuk'a jin yakeyi kamar ya shak'o wuyan salman ya yi ta dukansa, domin a yanzu shi yake basa haushi fiye da mai siffa larabawa saboda mai siffa larabawa yariga ya k'ona masa zuciya yatafi shi kuma salman yanzu yake yayafa masa tafasashe ruwan zafi a zuciya saboda kalamai salman tamkar ruwan zafi yakeji su, ya tashe ta tsaye har zuwa lokacin kuka takeyi na fitar hankali......
```DEDICATAD TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu🌹
[25/08 8:32 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [25/08 2:55 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```12```
Yaya Habeeb yarik'o hannuta suka nufi gida, sautin kuka ta ne yafito da Ammi daga d'aki tana fad'ar to fitinaniya yau kuma da wace kika zo"?
Ammi na k'arasa fitowa daga d'aki tayi turus, faskarta d'auke da zalla mamaki tace iko Allah ashe tare kuke da ita kuka me take yiwa mutane"?
Yaya salman ne sanarda Ammi abunda yafaru.
yaya Habeeb sai cika yake yana batsawa yanufi bakin famfo yacika _bucket_ da ruwa yakai mata band'aki{bathroom} yasake shiga d'akinta yadauko mata zani ya mik'a mata, ta kar6a saida yaraka ta bakin k'ofar _bathroom_ sannan yadawo yajingina jikinsa da bango jin yakeyi kamar ya rushe da kuka Ammi tace ka ga Habeebu karka nemi ka d'aurawa kanka damuwa domin ba ga ni wannan mutum za ka yi ba mafi alkhairi a tare da kai ka lallashi zuciyarka.
Yaya Habeeb yad'ago ya kalle Ammi da jajaye idanu shi yace babban takaici na bai wuce yadda Salman yake k'ara tunzira ni yak'arasa magana had'e da nuna yaya salman da yatsa.
Yaya salman ya kyalkyale da dariya daga bisani ya tsagaita da dariyar yace Allah ya huci zuciyarka _my in law_ ni kaina da zan ga wannan balarabe da na tayaka dukansa.
Ammi ta tabe baki
inna mairo ce tayi sallama tashigo a rud'e Ammi tasaki murmushi had'e da cewa zainabu takai miki rahoto koh"?
Inna mairo tace bari kawai fatee wallahi da zainabu tasanarda yadda abun yafaru baki ga yadda hankalina yatashi kai wannan mai siffa larabawa bashida imani Allah yasaka miki Haleesa.
Ammi da yaya salman sai faman dariya inna mairo sukeyi gani yanda ta tak'ark'are tana fad'a Haleesa tafito daga _bathroom_ jikinta lullube da d'an kwali _uniform d'inta_ har wani Jan k'afa takeyi ita dole sai tanuna ta maru, a hanzarce yaya Habeeb yanufi wurinta, yarik'ota sai faman sannu yake mata inna tasaki salati tana tafa hannaye sakamako gani idanu Haleesa sunyi kwanci jini tace Amma wannan mutum rashin imani sa a baiyane yake so yayi ya makkata ki, to ta Allah ba tashi ba azzulumi kawai.
Haleesa da ke tsaye tana sharar hawaye sai faman gizo fuskar mai siffa larabawa yake mata, yaya Habeeb yace ki je ki saka kayanki babylove mu je _hospital_ a duba ki Ammi ta zaro ido tace wane irin hosfutal{hospital} Habeebu"?
Kai fa baka rabuwa da d'aukar dame magaji da nishi in banda tsabar tsirfa da ba kai wahala miye na zuwa _hosfutal_ {hospital} gishiri da ruwan masu d'an d'umi-d'umi za'a nema a gasa mata idon shikenan za ta Wartsake.
Yaya salman yak'ara kyalkyale dariya yace Ammi ba hosfutal ake cewa ba _hospital za ki ce_ Ammi ta gallawa yaya salman harara tace Ko ma menene akecewa banga amfani zuwa sa ba.
Haleesa tafito cikin shirita, har yanzu da raguwa kwanci yatsu mai siffa larabawa akan fuskarta yaya Habeeb yace Ammi duba idonta ki gani yadda yayi Ammi ta kya6e baki daga bisani tace dafin hannu ne Habeebu ba wani Abu ba da an gasa mata zai daina.
Yaya Habeeb ya girgiza kai yace ni dai Ammi nafiso mu je asibiti{hospital} Ammi tace Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo yaya Habeeb yaja hannu Haleesa suka fice yayinda yaya salman ya Mara musu baya.
yaya Habeeb yashiga cikin gidansu yajawo Babur d'insa Haleesa ta d'ale yaja Babur d'in suka tafi yaya salman yabisu da kallo yana, dariya.
Duk yadda yaya Habeeb yaso su ga likita abun yaci turu saboda lokacin tashin likita aiki yayi dole yanufi wani 'karamin _clinic_ mai 'yar banza tsada bayan an duba ta aka rubuta mata magani, kusan duba takwas da d'ari biyar akayi chaji yaya Habeeb in da Allah ya taimaki Habeeb yana da 'yan kudinsa haka yafito da su ya biya had'e da kar6a magani suka fito daga _clinic_ d'in tausayi shi yayi bala'i kama Haleesa nan take ta ji wani sabon sonshi yana ratsa jinita.
ya tsaya wurin wani mai siyarda lemu da ayaba yasiya mata sannan suka nufi gida.....
[25/08 4:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```13```
Suna isa gida yabata magani tasha ya kuma d'iga mata wanda ake sakawa a ido, yayinda Haleesa sai shagwa6a take zuba masa, ya6are ayaba yasa mata a baki Haleesa ta sada kai k'asa tana ci ayaba a hankali, tana d'agowa ta ga yaya Habeeb ya tsura mata ido yana kallonta tamkar zai cinye ta, tasaki murmushi tace yaya Habeeb wannan kallon fa"?
Yasauke numfashi cikin yanayi na damuwa yafara magana, babylove wannan mutum yacuce ni kalli yadda ya6ata miki fuska yak'arasa magana tamkar zai yi kuka.
Haleesa tace kasaki ranka yaya Habeeb idanu ba ciwo suke min ba.
Ta ya zan saki raina babylove alhali idanu ki suna cikin wannan yanayi"? nayi alqawali duk ranar da idanuna suka ci karo da wannan bak'in azzalimi sai na d'auki munmuna mataki akansa.
Cikin rauni murya tace Dan Allah yaya Habeeb kayi hank'uri ka manta da wannan abu.
Shikenan babylove na hak'ura yafad'a had'e da Jan karan hancita yace ni zan koma shago, cikin sigar shagwa6a turo baki tace a'a yaya Habeeb ni banaso katafi yaya Habeeb yayi murmushi had'e da cewa kin ganki yarinya nan kinaso ki had'a mini _go slow_ a shago Haleesa tayi dariya tace to shikenan tashi katafi amma anjima za ka dawo koh"?
Tun da farin cikina naso ganina me zai hanani dawowa
Tsanani jin dad'i had'e da nishad'i suka lullube zuciyar Haleesa Habeeb ya mik'e yafita ta bi bayansa da kallo.
A kwana a tashi gashi har Haleesa ta kamalla karatu ta, yayinda iyayyensu sai faman shirya-shirye bikin aure su sukeyi, nan da wata d'aya za'ayi bikin burin Haleesa da Habeeb ya kusa cika.
Yammaci ne mai cike da sanyaye iska mai ni'ima bishiyoyi sai faman kad'awa suke suna busa iska mai dad'i gaske yayinda hadari ya had'a kayansa gabass Wanda hakan yake nuna cewa ko kowane lokacin ruwa za su iya saukowa, a cikin wannan yanayi ne Haleesa tafito daga gida Ammi ta aike ta gidan Delu dillaliya tana sanye da _combination_ na _paperless da atamfa red&yellow colour_ da hajib d'inta _red colour_ jikinta na fitarda 'kamshi turare _pink love_ ta yi matuk'ar kyau musanmman yadda ta k'awata fuskarta da murmushi ga kuma yanayi na iska da ke kad'awa sai kawai ta tsinci kanta cikin nishad'i, tana tafiya a hankali wannan d'aya daga cikin 'dabi'a Haleesa da kyar ka ganta tana tafiyar sauri shiyasa sa'idawa ke cewa ta cika yanga kaitsaye ta nufi bakin titi ta tsallaka, shagon su yaya Habeeb ta nufa saida ta lek'a ta ga yaya salman baya cikin shagon sannan tashiga wata budurwa ta hango zaune bisa farar kujerar roba, ta kasa ta tsare sai wani girgiza k'afa take yayinda Habeeb ke zaune bisa tela yana d'ikin Haleesa tasaki murmushi domin tagano mutumi nata ya yi tsiya da sallama tashiga shagon da sauri yaya Habeeb yad'ago ya wanke ta da murmushi, yace _o'oo my baby you look so beautiful muah_
Haleesa ta washe hak'ora kamar gonar auduga, tace _thanks my love_
Daga ina kike"?
Ammi ce ta aike ni gidan Delu shine nace ba zan wuce ba sai na na zo naga tauraro na.
Habeeb yak'ara fad'ad'a murmushinsa yace kai gaskiya kin kyauta babylove da ace kin wuce banga wannan kwalliya ba da kin gama da ni......
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU```
Jeeddah Aliyu🌹
[25/08 8:35 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [25/08 6:46 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```14```
Haleesa ta kyalkyale da dariya tace _umh yaya Habeeb kai dai baka rabo da abin dariya_
Budurwa da ke zaune tana jiran tsanmani ta yatsine fuska da alama tafara k'osawa da surutun Habeeb da Haleesa tace haba Habeeb wannan wane irin wulak'anci ne tun d'azu nake zaune a shagonan sai yawo da hankali kake min gaskiya ni nagaji.
Cikin yanayi na mamaki Haleesa ta juya wurin budurwa, tace dallah!