Showing 9001 words to 12000 words out of 132766 words
Dakata malama an gaya miki shi bawa ki ne da in fara d'iki ba zai tsaya ya huta ba"?
Budurwa ta zaro ido had'e da cewa ke kuma baiwar Allah daga ina"?
Ba'a saniba Haleesa tafad'a tana murgud'a baki yaya Habeeb yana dariya yace kin ga kareema ki K'ara hank'uri bani nace ki jirani ba"? Insha Allahu ba za ki fita shagonan ba sai da kayanki.
Wane irin na'kara hank'uri Habeeb"? Kalli gari ka ga yadda hadari ya yi bak'i ga kuma unguwa mu da nisa
Haleesa ta tabe baki tace kinsan unguwa Ku da nisa wayace kika kawo d'iki anan"?
Yaya Habeeb na gani Haleesa na k'ok'ari tsokano masa fitina ya mik'e tsaye yarik'o hannuta ya yi k'asa da murya yace zo mu je na rakaki babylove kada Ammi ta ga kin dad'e
Haleesa ta yi murmushi tace yi zamanka yaya Habeeb ka 'karasawa wannan mayya d'ikinta, Habeeb yace _okay baby ki kula da hanya kuma karki jima saboda kinga an fara yayyafi da alama ruwa zai sauko_
Haleesa wance tuni ta juya tasoma tafiya tace to yaya Habeeb.
Tun kafin tak'arasa gidan Delu aka fara ruwa da gudu tashiga gidan Delu bayan ta kar6i aiki da akayi mata, har ta juya Delu ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar Haleesa ki dawo ki jira har ruwa nan su tsagaita sai kitafi ba don ran Haleesa yaso ba ta zauna har akayi kiran sallah magariba ruwan basu d'auke ba tad'ura alwala tayi sallah tana sallamewa bata tsaya yin doguwa addu'a ba ta mik'a had'e da yi ma Delu sallama tafita da sauri.........
[25/08 7:44 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```15```
Tsanani sauri da takeyi yasa ko gabanta bata gani gashi an d'auke wuta gari yak'ara yin duhu ga ruwan sama da ake tsullawa kamar, da bakin kwarya da gudu taje tsallaka titi wani mahaukaci birki da taji a bayanta yasa ta rikice tarasa in da zata dosa, kawai taja tayi tsaye duk iya k'ok'ari direba{driver} motar da kwarewarsa da tuk'i{driving} sai yada ya kai ga jikinta ta zube k'asa Allah yasa bata ji ciwo ba, ta mik'e tsaye da kyar da gudu direba{driver} motar yafito sannu Hajiya baki ji ciwo bane"?
Har Haleesa ta bud'e baki tabashi amsa taji sauti murya da ko a mafalki za sheda ta hasken fitilar motar ta hasko mata kyakyawa fuskarsa mai kama da ta larabawa.
Ke! Wace irin dabbace"?
Kin wani danno kan titi kamar mahaukaciya kin yi Sa'a kinada raguwa kwana a duniya da kin mutu a banza.
Haleesa ta hadiye yawu da kyar jikinta yad'auki rawa yayinda tsanani tsoro ya lullube ta, kallon d'aya tayi masa ta kauda fuska duk da tsawon shekara d'aya har da watani rabon da tasake gani wannan fuska mai matuk'ar razanata da sauri Haleesa ta tattara siket d'inta ta kwasa da gudu bala'i gudu takeyi kamar ranta zai fita saida takai zaure gidansu sannan ta tsaya ta dai-dai numfashinta, duk haka jikinta bai daina rawa, ba ta shak'i iska ta furzar daga bisani tak'arasa shiga gida kaitsaye d'akinta tashiga Sam batayi la'akari da jik'ak'u tufafinta, tafad'a bisa katifa tasaki razananiya ajiyar zuciya tadafe saitin da zuciyarta take taji yadda zuciyarta take bugawa da sauri-sauri ta lumshe idanu ta, nan take tasoma gani sa, sanye yake da _suit_ kamar yadda tafara gani sa saidai na yau _black colour_ ne idanushi manne da black _shade_ fuskarsa a murtuk'e ras ras! Sautin da ke fita daga k'irjin Haleesa kenan da sauri ta mik'e zaune ta lankwashe k'afafu ta a tsakiyar katifa tafara zance zuci waye wannan mutumi mai siffar larabawa daga ina yafito"?
Shin mutum ne ko aljani miyasa tsawon shekara d'aya da watani da na ta6a haduwa da shi yanayi zafin ransa yana nan bai sauya ba"?
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu🌹
[26/08 9:23 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [26/08 9:40 am] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```16```
Haleesa ta dafe kanta tsanani tsoron mutumi yak'ara lullube ta, cikin zuciyarta tace _ya Allah ina tawassali da kyawawa Sunaye ka masu girma da daukaka Allah karka 'kara had'ani da wannan mutumi domin na tsorata da shi tamkar yadda nake tsoron maciji haka nake tsoronsa Allah ka shiga tsakanina da shi_ Haleesa tak'arasa addu'arta hawaye na zuba akan mata fuskarta.
Jin Ammi na kwalla mata kira yasa ta mik'e a hanzarce ta sauya kayan jikinta, zuwa _gown_ ta atamfa nan take ta tuna da kudi da ta kar6o ma Ammi gidan Delu a lokacin da mota ta bugeta ta jefarda kudin, tsanani tsorata da tayi da gani mai siffa larabawa yahanata d'aukar kudin na shiga uku, yau sai Ammi ta yanka ni Haleesa tafad'a tana zarar ido.
Haleesa! Wai me kike yi ne a cikin d'aki"?
Na'am Ammi ganinan zuwa, tafice hannuta d'auke da jik'ak'u kayanta saida ta sanya su sannan tanufi d'akin Ammi, tana shiga d'akin ta ja tayi tsaye Ammi tace ina aike da nayi miki"?
Cikin sark'ewa halshe Haleesa tace Uhm...ta bada dubu biyar a kawo miki da sauri Ammi ta tari numshinta ta hanyar cewa _madallah wannan karo Delu tayi abin kanta ta cika alqawali_
Haleesa tak'ara tsorata saboda ta fahimce Ammi buk'ace take da kudin ke! Haleesa bani kudin ki je ki kwashe tuwo Ammi ta katsi mata zance zuci _Haleesa ta dawo kala tausayi cikin rawar murya tace dama Ammi bayan na kar6o kudin ina cikin tafiya sai kare gidan oga tunde ya biyo ni garin gudu na jefarda kudin kuma na nema ban gansu ba Dan Allah Ammi kiyi hank'uri kaddara ce_
Tun lokacin da tafara magana Ammi take kallonta gani ta dasa aya yasa Ammi tace Naira na gugar Naira har zunzurutu Naira dubu biyar kika jefar Haleesa wannan wane irin sakarci ne"?
Ammi kaddara ce Haleesa tafad'a kamar za tayi kuka, a harzuk'e Ammi ta rarumi tsintsiya ta yi kanta da gudu Haleesa tafice daga d'akin, tanufi zaure Ammi ta jefarda tsintsiya tana huci tace ```kin yiwa kanki ``` dama ke zan siyawa _dinner set_ ae shikenan tun da kin jefarda kudin.
Haleesa na fita taci Karo da yaya Habeeb tayi tsaye tana hak'i Habeeb yak'araso daf da ita ya haskata da fitila wayarsa, da sauri ta kare fuskarta da tafin hannuta.
_babylove me kike yi anan"?_
_kudin Ammi na jefar shine za ta dakeni ni kuma na gudu_
Hamm... Babylove gaskiya yau kin debo da zafi amma bara na je na ba Ammi hank'uri Habeeb yanufi cikin gida yabarta tsaye.
A madafi{kitchen} yatarda Ammi tana kwashe tuwo ya tsugunna yayi k'asa da murya _yace Ammi nasan mu yi miki laifi musanmman a wannan lokacin da kudi suke da wuyar nema a wurin talaka amma kiyi hank'uri ki danganta hakan da kaddara_
Ammi ta yi dariya daga bisani tace in ban yi hank'uri ba me zan yi"?
A kullum Haleesa k'ara mayarda kanta k'aramar yarinya takeyi kuma wai a hakan za'a yi mata aure lallai za ka kwashi kayan takaici Habeebu.
Habeeb ya kyalkyale da dariya yace da zarar mu yi aure za ta daina Ammi.
Yatsine fuska Ammi tayi tace to tashi katafi duk abunda takeyi da sa hannuka, yaya Habeeb ya mik'e tsaye yana dariya yanufi zaure wurin Haleesa......
[26/08 6:00 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```17```
Ya lek'a fuskarta had'e haska mata fitila wayarsa murmushi tasake masa, ya lumshe idanu yace babylove bakyaji magana koh"?
Haleesa ta turo baki tace me nayi"?
Ya girgiza kai had'e da cewa ba ki ma San abunda kika yi ba"?
A shagwa6e tace da nasani ba zan tambaye ka ba yaya Habeeb
Shikenan mu ajiye wannan magana a gefe ki zo mu shiga gida ki bani labari mai dad'i yak'arasa magana had'e da juya Haleesa tabiyo shi a baya tace ina sonka yaya Habeeb
Yasaki dariya mai sauti yace kin renani babylove har kwakwayo magana ta kike yi
Haleesa tace _Ni da yaya Habeeb jini mu d'aya duk abunda ya yi nima zan iya kwaikwaya_
Habeeb yajuya ya fuskanceta yana mata kallo mai d'auke da kwayar _so d'aya_ kunya ta lullube Haleesa da gudu tara6a ta gefensa tashige d'akin Ammi Habeeb ya yi murmushi had'e da bin bayanta zaune yatarar da ita bisa gadon Ammi, ta mik'e k'afafu ya yi tsaye yana kallonta cikin zuciyarsa yace narasa wane irin so nake yiwa Haleesa na tabbata son Haleesa ba zai ta6a duk'ushewa a zuciyata, ina matuk'ar son Haleesa tamkar numfashina kafin Habeeb ya gama zance da zuciyarsa aka mayarda wuta _Nepa_ haske ya gauraye d'akin yak'ara haskaka masa kyakyawa fuskarta sai faman doka murmushi take Habeeb yaji yake kamar ya hadiye ta don so, Cikin 'yar muryarta mai matuk'ar dad'i da gard'i tace yaya Habeeb ka zauna mana ni fa a kwanaki nan narasa gane kanka sai kadinga kallona kamar baka ta6a ganina ba tak'arasa magana had'e da murgud'a baki.
Habeeb ya zauna kusa da k'afafuta cikin rauni murya Habeeb yafara magana nima bansan dalili da yasa nakeso kallonki babylove, iya abun d'aya nasani Sam bana tajuya da kallon kyakyawa fuskarki.
Haleesa ta sada kai k'asa tana murmushi tana d'agowa ta ga Habeeb ya runtsi idanu sa ya kuma dafe cikinsa da hannu a tsorace Haleesa ta rik'o hannushi kamar za ta fashe da kuka tace yaya Habeeb miyasa ba za ka je asibiti ba"?
Ciwon ciki nan yana damu ka sosai
Habeeb ya cije lebb'e shi yace......
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu🌹
[26/08 9:23 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [26/08 8:03 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```18```
Kema kinsan dalili da yasa banaso zuwa asibiti _babylove_ ki kyaleni kawai da zance asibiti nan.
Haleesa tak'ara marairai ce murya tace _please yaya Habeeb ka amince gobe na rakaka hospital ka ga likita wallahi hankalina yana matuk'ar tashi duk lokacin da naganka cikin wannan yanayi na ciwon_
Habeeb ya yi murmushi k'arfi hali had'e da cewa karki dame kanki akan wannan ciwo ba wani abu damuwa bane.
Haleesa ta girgiza kai hawaye suka cika mata idanu na fahimce cewa yaya Habeeb zuciyarka tafara yi wa soyayya ta tafiyar hawaiyani hakan yana nufi ka daina marmari kwanciya hankalina.
K'ank'ame hannuta Habeeb ya yi cikin yanayi na zafin ciwo had'e da zafin da Haleesa take yunk'uri haddasa masa yace Haleesa ina sonki fiye da tunani ki a kullum burina bai wuce naganki cikin farin ciki da kwanciya hankali don haka gobe insha Allah zan je asibiti don kawai, kisami natsuwa ki kuma k'ara amincewa da irin son da nake miki.
Haleesa tayi murmushi jin dad'i hawaye ta suka sauka bisa hannu Habeeb, a kid'ime Habeeb yad'ago fuskarta karki yi min haka Haleesa sani kanki ne ba abunda na tsana irin na ga hawaye akan wannan kyakyawa fuska taki yasaka yatsa shi yalak'ato hawaye ta.
Haleesa ta goge fuskarta tace Kaine farin ciki na shiyasa banida buri da ya wuce naga na zama mallaki ka.
Habeeb yasaki murmushi had'e da cewa nan da k'ank'ani lokacin burin mu zai cika _babylove_
```TSAKIYAR DARE ```
Da misali k'arfe _2:30am_ tsanani ciwon ciki na fitar hankali ya tayarda Habeeb sai faman juyi yake, had'e da nishi mai k'arfi gaske Wanda ya yi sanadi da Hasheem ya falka a firgici yanufi wurin Habeeb yana girgiza shi had'e da kiran suna shi yaya Habeeb ciwo ciki ne ya motsa"?
Da kyar Habeeb yad'aga kai da gudu Hasheem yanufi cikin gida ya fad'awa baba Audu Habeeb bashida lafiya.
lokacin da baba Audu yashiga d'akin ya tararda Habeeb yafita haiyyaci sa, baba Audu yajuya wurin Hasheem yace yi maza ka je ka fad'awa mal Usman bayan fitar Hasheem da kamar _5 minutes_ sai ya ga shi yadawo tare da baffa da salman a rikice salman yad'ago Habeeb yace sannu Habeeb Allah yabaka lafiya ya rabaka da wannan ciwon yayinda Habeeb bai ma San yanayi ba baffa yace Hasheem je ka kade6o ruwa nayi masa tofi da sauri inna mairo da ke a bakin k'ofa tajuya ta de6o ruwa a Kofi ta mik'awa Hasheem ya ba baffa cikin ikon Allah baffa na ba Habeeb ruwan ciwon ciki yalafa Habeeb ya yi bacci.
Salman yace babba matsala da anan a tsakiyar dare nan ba inda zan samo aron mota ballatana akai shi asibiti saidai mu jira wayewa garin.
Duk wannan bidiri da akeyi Haleesa batasaniba tana chan tana sharar bacci.
Har asuba tayi Habeeb yana bacci baffa da baba suka nufi masallaci suka bar Salman da Hasheem tare da Habeeb, kamar daga sama Habeeb ya bud'e idanushi da sauri salman yarik'o hannushi yace sannu Habeeb ya ciki naka yadaina ciwo"?
[26/08 9:23 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```19```
Habeeb yatsine fuska yace yadaina yajuya wurin Hasheem yace Hasheem de6o min ruwa nayi alwala Hasheem yajuya da sauri, yade6o masa ruwa gaba d'aya suka nufi masallaci, bayan gama sallah suka fito daga masallacin sai kawai suka ga Habeeb ya yanke jiki yafad'i k'asa a some da sauri Alhaji Garba makwaci su yadauko mota aka saka Habeeb, suna isa asibiti aka nufi d'akin gagawa{ _emergency & Accident Ward_}da shi.
Da gudu kamal yashiga gida yana kwadawa Ammi kira a rikice Ammi tafito daga d'aki tace lafiya kamal"?
Cikin rawar murya yace muna fitowa daga masallacin yaya Habeeb ya suma su baffa sun tafi su kai shi asibiti.
Dai-dai lokacin da Haleesa ta sallame sallah tafito a gigice had'e da cewa wayyo Allah na, nashiga uku tafashe da mai tsanani gaske, Ammi tarik'o ta tana lallashinta da kyar Ammi tasamu tadaina kuka.
```k'arfe 10:20am```
Da misali k'arfe _10:20am_ Haleesa, Ammi da inna mairo tare da zainab suka shiga d'akin da aka kwantarda Habeeb cikin tashin hankali marar misaltuwa Haleesa tashiga d'akin ta hango Habeeb kwance hannu shi na hagu d'aure da _drip_ da sauri ta nufi wurinsa tarik'o hannusa na dama ta matsi cikin nata, tafashe da kuka hawaye had'e majina suka soma zuba akan fuskarta da sauri salman yataka mata birki ta hanyar cewa karki tsira mana kuka anan in kuma kuka za ki yi kifita waje dole Haleesa ta hadiye kukanta sai tadawo na zuci tanayi hawaye na zuba, ta ra6a gefen Habeeb ta zauna a hankali take murza hannushi da misali k'arfe _11:30am_ Habeeb yafarfad'o yana bud'e idanusa suka sauka bisa fuskar Haleesa wance cikin d'an k'ank'ani lokacin har tayi rama cikin tsanani jin dad'i Haleesa tace _sannu yaya Habeeb_
Murmushi yasake mata daga bisani yace yauwa babylove saura mutane da ke cikin d'akin suka fara yi masa sannu ya amsa fuskarsa d'auke da murmushi, daga bisani Ammi da inna mairo suka fice daga d'akin Yaya salman ya mik'e yace bara na d'an mik'a kafata yana fita Haleesa ta matsa kusa da Habeeb ta lek'a fuska sa ta tsura masa ido gani yadda yayi masifar yi mata kyau fuskarsa sai kyalli take, tasaki ajiyar zuciya tace ciwon nan naka yaya Habeeb yana masifar tsoratani.
Murmushi yayi daga bisani yace banaso ki saka damuwa a ranki
Babylove saboda naji sauki.
Tayi murmushin nan nata mai 'karawa fuskarta kyau tace saura kuma kace
Ba za ka sha magani ba nayi fushi da kai tak'arasa magana cikin siga shagwa6a.
Habeeb yayi 'yar bazawara dariya yace ina sonki Haleesa ita ma tayi dariya tace nima ina sonka yaya Habeeb
Haleesa da Habeeb sai faman zuba soyayya suke sai kace ba'a asibiti sukeb ba _drip_ na k'arewa Haleesa ta kira _nurse_ tacire masa.
Haleesa na rike da hannu Habeeb tana wasa da yatsu sa taji ya matsi hannuta da k'arfi a firgici tad'ago taga ya runtsi idanu had'e da cije lebb'e tace yaya Habeeb ciki ne kuma"?
K'asa magana yayi faman juyi yakeyi duk da haka hannaye su na sark'e da juna, Hasheem da ke zaune a gefen bisa kujera roba yana _chat_ a waya shi ya mik'e nufi wurinsu gani yadda Habeeb ke birgima yasa yafita da gudu yakira _Nurse_ da sauri tashigo da kyar ta6an6are hannushi daga rik'o da ya yiwa Haleesa, tafara dubashi gani abun yafi k'arfinta yasa takira _doctor_
Haleesa na dur'kushe a k'asa tana kuka mai matuk'ar ban tausayi _doctor_ yadaka mata tsawa ta hanyar cewa ke! Tashi kifita k'asa tashi tayi saida Hasheem yakamata suna kaiwa bakin k'ofa tajuya, ta kalli Habeeb sai kawai ta ji yana kalma shahada.....
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Jeeddah Aliyu🌹
[27/08 6:20 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [27/08 9:39 am] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```20```
Wasu yawu masu d'aci da masifar zafi suka cika bakin Haleesa saida taja dogon numfashi tayi nasara had'iye su kaitsaye suka, ratsa mak'oshinta suka dira cikin hanjinta nan take cikinta yafara k'ugi tamkar wance tayi _breakfast_ da fate wake Sam Haleesa bata lura da cewa sun fito d'akin ba saida ta ji sautin murya Ammi da kyar tad'ago kanta ta k'arewa Ammi da inna mairo da kuma zainab kallo ta ga kowane hawaye na zuba daga idanu sa, tsoro da zallumi had'e da tashin hankali Wanda tsawon rayuwa Haleesa bata ta6a gani irin sa ya ziyarce zuciya da gangar jikinta jin take wani irin mashahuri sanyi yasoma ratsa k'assa jikinta sai kawai jikinta yafara rawa kamar mazari da sauri inna mairo ta rik'e ta salman yak'araso daf da su muryasa na rawa yace Ammi meya faru naga kuna kuka"?
Kafin Ammi ta bashi amsa d'an tsamurare likita da ke cikin d'akin Habeeb yafito yana sharar gumi da _handkerchief_ da alama tak'are masa, cikin yanayi na tashin hankali Haleesa da yaya salman suka nufi sa a lokacin d'aya suka watsa masa rikitaciya tambaya _doctor ya jikinsa"?_
_doctor yaya Habeeb ya ji sauki koh"?_
Doctor ya girgiza 'kok'o kansa sai kace kadangare daga bisani yace _I'm sorry to say Habeeb is gone_
Sai Ku yi hank'uri mutuwa rigar kowa ce.
_innalillahi wa'inna illahi raji'um_ kalma da su salma ke ta mai-maitawa sabani Haleesa da ke tsaye kamar an shuka ta, ba k'arami jajircewa tayi wurin gani ta dai-daita numfashinta da ke barazana rabuwa da gangar jikinta, da kyar ta iya lala6o kalmar k'arya ce wallahi k'arya kake yi likita ya za'ayi yaya Habeeb ya mutu"? _you are bloody liar doctor_
Doctor ya yi