Showing 78001 words to 81000 words out of 132766 words

Chapter 27 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87965

Haleesa za ta k'ara koda kallonshi ne ballanta magana ta fatar baki Tashiga tsakaninsu da kyar ya iya bud'e bakinshi ya amsa da _lafiya lau_
''Daga haka bata k'ara cewa da shi komai ba ta yi shigewarta cikin gida
''Habeeb ya yi ajiyar zuciya cike da mamakin Haleesa yafara zance zucin _ita wannan tana nufi har ta manta da abunda na yi mata jiya"?_
Wani 6angare na zuciyarshi yace da shi
In kuwa haka ne gaskiya tana da hank'uri da batada kyakyawar zuciya da 'yarka bara ta k'ara bata kulawa ba yanzu nan akan idonka ta wuce da Imaan da alama tana matuk'ar son Imaan kamar 'yarta ta cikinta, gaskiya Habeeb ka chanza tsari kadaina musgunawa yarinya nan tun kanada sauran daraja a wurinta kafin tadaina ganin darajarka ta rainaka.
Ya ja iska ya fesar a sanyaye yanufi bakin gate yana kwallawa Bala kira.
_11:00am_
Habeeb na zaune a office ga tarin aiyunka sunyi mishi yawa yarasa abunda ke masa dad'i da yarufe idanunshi Haleesa yake gani a nashi tunanin sai yadanganta hakan da abunda yafaru tsakaninsu jiya yana cikin wannan halin Mus'ab ya tura k'ofa yashigo har ya zauna Habeeb yana masa kallon k'asan idon.
"Mus'ab ya murtuk'e fuska had'e da mik'awa Habeeb hannu suyi musabaha bayan sun gama gaisawa Mus'ab ya gyara zamanshi yace ba sai gaya maka dalilin zuwa na office d'inka kwakwalwarka kadai ta isa ta zayyano maka dalilin zuwa na.
Yad'an numfasa yacigaba da cewa abunda ka aikata jiya Sam baiyi min dad'i ba jiya na kwana da takaicinka haba! Lamido da iliminka da komai za ka mayarda matarka abun wulaqantawa Na fi kowa sanin yadda ka tsaneta amma bai kamata ka yi amfani da tsanar da ka ke yi mata ta zame maka hujja da za ka dinga wulaqantata ka ji tsoron ''Allah ka tuna duk abunda ka ke aikatawa Allah yana ganinka in har ka 6oyewa mom irin mugun zaman da ka ke yi da Haleesa ka tuna ba ka isa ka 6oyewa ubangijinka ba.
''Har Mus'ab yadasa aya Habeeb yana kallonshi had'e da tsotsa baki wannan tsotsar bakin ya zame masa d'abi'a ya mik'e a hankali yataka zuwa wurin water disperser yadauki glass cup ya matsa ruwa mai sanyi ya kwararawa mak'oshinsa ya lumshe idanu yana fesar da iska daga bisani ya koma mazauninshi.
''ya tabe baki ya dube Mus'ab a d'age yana wani cizo lips look Mus'ab karka shiga abunda ba ruwanka a ciki kafin kowa sanin halina, na tsani katsalanda a rayuwana bana shiga rayuwan kowa bai nima kanemi ka shiga rayuwana bansan menene b'acin rai ba sai da na had'u da yarinya nan ban ta6a d'aga hannun na mari mace sai akanta, banta6a kwanciya na k'asa b'acin sai akanta a da ni mutum ne mai sanyi amma Shigowar yarinya nan a rayuwata ya sauyani na dawo mutum mai tsananin zafin gaske na rok'e ka Mus'ab karka sake yi min maganarta saboda tun farko saida na gargad'enta akan ta bi dokoki na domin ta zauna lafiya da yake ita mai kunnen k'ashi ce sai ta yi fatali da doka ta ni kuwa me zai sa na d'aga mata k'afa"?
''Mus'ab ya girgiza kai yace Lamido fahimce wani abu mana Haleesa fa k'aramar yarinya ce a hankali yakamata ka bi da ita har, ta fahimce tsarin rayuwarka ko wannan miskilancin naka kadai ya isa ya cutar da ita kuma ni ba zan fasa fad'a maka gaskiya ba saidai ka yi ta kallona a matsayin mai katsalanda a rayuwarka.
''Habeeb ya ja tsoki cike da takaicin Mus'ab ya koma jikin kujera ya lafe yayinda kujerar tadinga jujuya shi.
Mus'ab ya mik'e ranshi a b'ace yace tunda kai girman kanka bara bari ka bata hankuri ni zan je gidan naka na bata hankuri yana k'arasa magana bai jira jin ta bakin Habeeb ba ya yi ficewarsa.
''Habeeb ya bi shi da harara a baiyane yafara magana ba hankuri za ka bata ba in ka je ka goyata ka yawace garinan da ita ba abunda yadameni, ko angaya maka ni bawan mace ne irinka yak'ara Jan tsoki....

```HALEESA```
_Haleesa_ tana cikin kitchen sai ta ji ana sallama, da sauri ta fito ga mamakinta sai taci K'aro da Mus'ab zaune akan 1 sitter da murmushi tak'arasa shiga parlourn _sannu da zuwa Mus'ab_
''Yauwa Haleesa ya gida duk da naji gidan tsit yak'arasa magana yana 'yar dariya.
Haleesa ta yi murmushi ta koma kitchen tadauko masa kwalin fruitta mai sanyi had'e da glass cup ta tsiyaya ta mik'a masa tanemi kujerar da ke facing d'inshi ta zauna ta sada kai k'asa saboda tana mai jin kunyar abunda yafaru jiya.
''Mus'ab ya d'an yi slipping juice d'in ya ajiye cup bisa stool ya yi gyaran murya, yace Haleesa dama zuwa na yi na baki hankuri akan abunda yafaru shi kanshi lamid'o ya yi Nadama abunda ya yi miki kawai yana jin kunyar yadda zai yi facing d'inki yabaki hankuri amma yace nace da ke ki yi hankuri Sharrin shed'an ne.
"Haleesa ta yi murmushi domin tasan abunda Mus'ab yafad'a ba gaskiya bane Habeeb Lamido ne zai ce a bata hankuri ae ba yau ya sa6a cin mata zarafi Wanda yafi wannan ya yi mata bai ce a bata hankuri ba sai wannan.
''Idanunta suka ciko da hawaye bata damu da ta goge su ba, tace ba zan 6oye maka ba Mus'ab a da ina da ra'ayi zama da yaya Habeeb koda ace zai dinga yanka naman jikina sai yagajin don kanshi ya saleme ni, amma a yanzu nayi nadamar aurenshi ba don komai sai don ya kasance mashayi ni kan bara iya rayuwa da mashayin giya tak'arasa magana cikin shasshek'a kuka.
''Mus'ab ya zaro idanu a rikice yace giya fa ki ka ce Haleesa"?
''Kwarai Mus'ab abokinka mashayi ne Sam babu tsoron Allah a tare da shi a cikin gidanan yake shan abarsa ya yi tatul.
"Da mugun mamaki Mus'ab yake kallon Haleesa daga bisani yace to ke Haleesa menene shedarki Lamido yana shan giya"?
Ni kuwa nakeda sheda mu je part d'inshi ka ganewa idanunka Haleesa tashige gaba Mus'ab yana biye da ita saboda iya zamanshi da Habeeb yasan ko cigarette ba yasha asalima ya tsanin duk wani abu da yake saka maye.
''Haleesa ta turo k'ofa suka shiga cikin parloun ta nunawa Mus'ab glassblower da ke d'auke da jerin white wine kala-kala Mus'ab ya yi ajiyar zuciya ya bud'e glassblower yaciro bottle gudu ya mik'awa Haleesa da sauri ta ja baya tana wani zare idon Mus'ab ya kyalkyale da dariya yace ki k'ar6a mana so nake ki karanta rubutu da ke jikin bottle d'in a sanyaye Haleesa ta k'ar6a ta karanta juice ne da aka sarafa da fruits sannan kuma an rubuta non alcoholic Haleesa tasauke ajiyar zuciya wani sanyi ya ziyarce zuciyata ta runtse idanu daga bisani ta ware su cikin jin kunya tace gaskiya na yarda da maganar yaya Habeeb da yake cewa ni villager ce amma kuma Mus'ab karka ga k'auyancin na saboda ban tashi a gidan da ake shan irin wad'annan abubuwan ba.
Mus'ab ya yi murmushi yace ki kyalle Lamido shima bak'auye ne sannan kuma ba ke kadai ki ke kallon wannan juice a matsayin giya mutane da dama Wanda ba su San juice bane a haka suke kallonsa.
''Haleesa ta yi dariya tajuya Mus'ab ya Mara mata baya suka koma parlournta, yacigaba da bata hank'uri saida ya tabbata da ta hank'ura sannan ya yi mata sallama.
_5:00pm_
Haleesa tana zaune a parlournta Imaan ta isheta da rigima a dole sai sunyi wasan 'yar 6oya Haleesa ta yatsine fuska ta ajiye phone d'inta bisa hannun kujera ta rik'on hannun Imaan suka nufi compound daga idan suke zuwa main gate akwai tazara sosai Haleesa taciro d'an kwalin kanta gashinta yasauka a gadon bayanta, tace da Imaan zo nan babyn aunty na daure miki idanunki
''Imaan tadaka tsalle cikin shagwa6a tace Allah aunty ke ce first ni kuma second Haleesa ta yi dariya tace kai....ka ji min yarinya da wayyo tana magana tana daure fuskarta idanunta na rufe tace 1.....2....3.... Start tasoma lallu6en Imaan tana jin dariyar Imaan amma takasa kamata, haka tacigaba da lullube.
''Bala yaddano hancin mota cikin compound Habeeb na owners corner a zaune tun kafin su k'arasa parking space ya hango Haleesa da Imaan suna wasa yaja tsoki a zuciyarshi yace k'aramar kawai Bala yana dariya ya bud'ewa Habeeb k'ofa yafito
"Boss yau amarya ta tuna da k'urciya wasan 'yar 6oya sukeyi yak'ara sa magana yana wani Sosa kai.
Harara Habeeb ya watsa masa yace kadauko briefcase ka shigar min da shi ciki Yajuya yanufi cikin gida.
"Babyn aunty where are you I'm tight zan bud'e idanuna in bara ki bari na kama ki ba Imaan ta kyalkyale da dariya tace _yeee.... Aunty if you're can catch me_
Da sauri Haleesa tanufi idan takejin sautin muryarta dai-dai Habeeb yakawo da sauri Imaan ta boye bayanshi garin lallube Haleesa ta yi tuntube za ta fad'i da sauri Habeeb yatare ta tafad'o kan k'irjinshi..........

Jeeddah Aliyu🌹

[22/11 4:05 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```77```

~~A hankali ta bi jikinta da kallo gaba d'aya zo6o yabata mata kaya a harzuk'e tad'ago idanunta Wanda suka canza colour zuwa red, kallo d'aya za ka yi mata ka hango b'acin ranta yadda ta tsare Habeeb Lamido da ido za ka yi tsanmani za ta zanga masa mari ne.
"Kallo mai cike da zazzafar tsana Habeeb yake watsawa Haleesa cikin tafarfasa zuciya yadaka mata tsawa cikin angry voice ya furta _How dare you ni za ki wulaqanta in front of my friends"?_
''Kafin Haleesa ta ba shi amsa Mus'ab ya taso yashiga tsakaninsu ranshi a b'ace yace _what's wrong with you Lamido akan wane dalilin za ka yi mata wannan d'ayen wulaqancin matarka ce fa"?_
''Kallon banza Habeeb ya watsa masa so what's don tana matata shi zai bata dama tacin min zarafi a gabanku"?
Haleesa ta yi karaf tace ancin zarafin naka yaya Habeeb ka yi duk abunda za ka iya ae ba tsoronka nakeji ba, tana k'arasa magana ta yi shigewarta bedroom tabar Habeeb Lamido sake da baki sai faman huci yake yi bai ta6a tunanin Haleesa za ta iya maida martanin abunda yake mata.
"Mus'ab ya ja tsoki ya dube khaleel yace tashi mu tafi khaleel a zahirin gaskiya nayi danasanin zuwanmu gidanan da bamu zo ba Lamido da bara ka, same damar wulaqanta 'yar mutane ina mamaki wannan miskilancin da girman kan naka Lamido ka gyara halayyarka ko za ka jin dad'i rayuwa.
''Khaleel ya kar6e zance ta hanyar cewa wannan abun da kayi Lamido kasanin ba burgewa bane, wulaqanta mace ba abu bane mai kyau muna jiye maka ranar Nadama.
''Yana k'arasa magana yarik'o hannun Mus'ab mu tafi kawai Mus'ab kana kallon irin kallon banzar da yake mana.
''Habeeb ya ja tsaki yace sai me don kuntafi dama can! Ban gaiyyace Ku ba ra'ayin kanku ne yakawo gidanan don kuntafi bara jin zafi ba asalima zuwanku wulaqancin ya janyo min tunda nake da yarinya nan banta6a magana ta mayar mun da amsa ba sai zuwanku banzaye kawai.
''Mus'ab ya galla masa harara yace ae Kaine banza Wanda baisan darajar matarshi ba wallahi Lamido in na cigaba da tsayuwa a gabanka haushinka da nakeji zai iya haddasa min hawan jini.
''Habeeb ya ja tsoki had'e da ficewa daga parlourn yabar Mus'ab da khaleel tsaye suna mamaki wannan halayen nashi daga bisani suka kama gabansu.
***********************
Kuka Haleesa taci kamar ranta zai fita tabbas Habeeb Lamido yade6o da zafi daga yau bara k'ara d'aga masa k'afa saidai ya yanka ni a gidanan.

```WASHE GARI ```
_Monday morning_
Kamar yadda Haleesa tasaba tashi da wuri ta shiryawa Imaan zuwa school tana rik'e da hannunta suka nufi compound har wurin mota ta yi mata rakiya, da kanta ta bud'e k'ofa tashiga ta yi pecking goshinta ta mik'awa sa'eed driver lunch box d'inta yayinda driver ya ja Motan zuwa gate Imaan tana d'aga mata hannun Haleesa ta mayar mata da cewa bye, babyn aunty ki yi karatu sosai Saida suka fice gate sannan Haleesa juya tana juyawa ta hango Habeeb tsaye da sauri yad'auke kai, kamar ba shi bane yake tsaye yana kallonsu, ta raba ta gefenshi dai-dai za ta shiga cikin gida tace _ina kwana yaya Habeeb"?_
"Saida zuciyarshi ta buga da k'arfi saboda baita6a tsanmani Haleesa za ta k'ara koda kallonshi ne ballanta magana ta fatar baki Tashiga tsakaninsu da kyar ya iya bud'e bakinshi ya amsa da _lafiya lau_
''Daga haka bata k'ara cewa da shi komai ba ta yi shigewarta cikin gida
''Habeeb ya yi ajiyar zuciya cike da mamakin Haleesa yafara zance zucin _ita wannan tana nufi har ta manta da abunda na yi mata jiya"?_
Wani 6angare na zuciyarshi yace da shi
In kuwa haka ne gaskiya tana da hank'uri da batada kyakyawar zuciya da 'yarka bara ta k'ara bata kulawa ba yanzu nan akan idonka ta wuce da Imaan da alama tana matuk'ar son Imaan kamar 'yarta ta cikinta, gaskiya Habeeb ka chanza tsari kadaina musgunawa yarinya nan tun kanada sauran daraja a wurinta kafin tadaina ganin darajarka ta rainaka.
Ya ja iska ya fesar a sanyaye yanufi bakin gate yana kwallawa Bala kira.
_11:00am_
Habeeb na zaune a office ga tarin aiyunka sunyi mishi yawa yarasa abunda ke masa dad'i da yarufe idanunshi Haleesa yake gani a nashi tunanin sai yadanganta hakan da abunda yafaru tsakaninsu jiya yana cikin wannan halin Mus'ab ya tura k'ofa yashigo har ya zauna Habeeb yana masa kallon k'asan idon.
"Mus'ab ya murtuk'e fuska had'e da mik'awa Habeeb hannu suyi musabaha bayan sun gama gaisawa Mus'ab ya gyara zamanshi yace ba sai gaya maka dalilin zuwa na office d'inka kwakwalwarka kadai ta isa ta zayyano maka dalilin zuwa na.
Yad'an numfasa yacigaba da cewa abunda ka aikata jiya Sam baiyi min dad'i ba jiya na kwana da takaicinka haba! Lamido da iliminka da komai za ka mayarda matarka abun wulaqantawa Na fi kowa sanin yadda ka tsaneta amma bai kamata ka yi amfani da tsanar da ka ke yi mata ta zame maka hujja da za ka dinga wulaqantata ka ji tsoron ''Allah ka tuna duk abunda ka ke aikatawa Allah yana ganinka in har ka 6oyewa mom irin mugun zaman da ka ke yi da Haleesa ka tuna ba ka isa ka 6oyewa ubangijinka ba.
''Har Mus'ab yadasa aya Habeeb yana kallonshi had'e da tsotsa baki wannan tsotsar bakin ya zame masa d'abi'a ya mik'e a hankali yataka zuwa wurin water disperser yadauki glass cup ya matsa ruwa mai sanyi ya kwararawa mak'oshinsa ya lumshe idanu yana fesar da iska daga bisani ya koma mazauninshi.
''ya tabe baki ya dube Mus'ab a d'age yana wani cizo lips look Mus'ab karka shiga abunda ba ruwanka a ciki kafin kowa sanin halina, na tsani katsalanda a rayuwana bana shiga rayuwan kowa bai nima kanemi ka shiga rayuwana bansan menene b'acin rai ba sai da na had'u da yarinya nan ban ta6a d'aga hannun na mari mace sai akanta, banta6a kwanciya na k'asa b'acin sai akanta a da ni mutum ne mai sanyi amma Shigowar yarinya nan a rayuwata ya sauyani na dawo mutum mai tsananin zafin gaske na rok'e ka Mus'ab karka sake yi min maganarta saboda tun farko saida na gargad'enta akan ta bi dokoki na domin ta zauna lafiya da yake ita mai kunnen k'ashi ce sai ta yi fatali da doka ta ni kuwa me zai sa na d'aga mata k'afa"?
''Mus'ab ya girgiza kai yace Lamido fahimce wani abu mana Haleesa fa k'aramar yarinya ce a hankali yakamata ka bi da ita har, ta fahimce tsarin rayuwarka ko wannan miskilancin naka kadai ya isa ya cutar da ita kuma ni ba zan fasa fad'a maka gaskiya ba saidai ka yi ta kallona a matsayin mai katsalanda a rayuwarka.
''Habeeb ya ja tsoki cike da takaicin Mus'ab ya koma jikin kujera ya lafe yayinda kujerar tadinga jujuya shi.
Mus'ab ya mik'e ranshi a b'ace yace tunda kai girman kanka bara bari ka bata hankuri ni zan je gidan naka na bata hankuri yana k'arasa magana bai jira jin ta bakin Habeeb ba ya yi ficewarsa.
''Habeeb ya bi shi da harara a baiyane yafara magana ba hankuri za ka bata ba in ka je ka goyata ka yawace garinan da ita ba abunda yadameni, ko angaya maka ni bawan mace ne irinka yak'ara Jan tsoki....

```HALEESA```
_Haleesa_ tana cikin kitchen sai ta ji ana sallama, da sauri ta fito ga mamakinta sai taci K'aro da Mus'ab zaune akan 1 sitter da murmushi tak'arasa shiga parlourn _sannu da zuwa Mus'ab_
''Yauwa Haleesa ya gida duk da naji gidan tsit yak'arasa magana yana 'yar dariya.
Haleesa ta yi murmushi ta koma kitchen tadauko masa kwalin fruitta mai sanyi had'e da glass cup ta tsiyaya ta mik'a masa tanemi kujerar da ke facing d'inshi ta zauna ta sada kai k'asa saboda tana mai jin kunyar abunda yafaru jiya.
''Mus'ab ya d'an yi slipping juice d'in ya ajiye cup bisa stool ya yi gyaran murya, yace Haleesa dama zuwa na yi na baki hankuri akan abunda yafaru shi kanshi lamid'o ya yi Nadama abunda ya yi miki kawai yana jin kunyar yadda zai yi facing d'inki yabaki hankuri amma yace nace da ke ki yi hankuri Sharrin shed'an ne.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login