Showing 63001 words to 66000 words out of 132766 words

Chapter 22 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87907

ki na ba ki _5 good minutes_ ki gyara parlour nan ki same ni a upstairs parlour yana k'arasa magana ya haura stairs yabar Haleesa sake da baki tadafe goshi kamar za ta fashe da kuka ta mik'e jiki a sa6ule, tanufi socket in kayan kallo ta yi switch off Imaan tace aunty me yasa kika kashe min kallo"?
ni ki kunna min na kalli "Dora
Haleesa batasan lokacin da ta galla mata harara, Imaan tafashe da kuka ta mik'e tanufi upstairs Haleesa ta girgiza kai tasoma aikin da ke gabanta, cikin d'an k'ankani lokacin ta gyara barna da Imaan ta yi parlour ya yi fess da shi saidai tana tsoron yadda za ta tunk'ari Habeeb domin batasan irin hunkuci da zai yi mata tsawon lokacin tadauka tana shawarwari ta je ko kada ta je, daga bisani ta yanke shawara ta je a natse ta shiga parlour ta yi sallama yana zaune a 2 sitter Imaan na kwance a jkinshi tana cin chocolate
Adak'ile ya amsa mata sallama
"Yaya Habeeb gani tafad'a cikin sark'ewa halshe
Banza ya yi Mata kamar bai ji abunda tafad'a
Saida ta share kusan _10 minutes_ a tsaye yayin da shi kuma hankalinshi na kan movie d'in da yake kallo
Yaya Habeeb gani tak'ara fad'a
A d'age yad'ago ya had'e girar sama da ta k'asa ya dube ta ya wani yatsine fuska ya ja tsoki ke! Banaso iskanci banza da wofi angaya miki ni makaho ne da za ki dame da ga ki karki sake ki kaini bango na yi miki wulaqanci ki cigaba da tsayuwa har sai zuwa lokacin da naga dama kulla ki
Tsawon _1 hour_ Haleesa tadauka a tsaye zuwa lokacin k'afafu ta sun d'auke wuta jin take kamar k'afafunta za su cire ga wani irin zogi da tafin k'afarta ke yi
Habeeb yad'ago ya dube ta a wulaqanci yace za ki iya tafiya
A sanyaye tajuya da kyar take iya ja k'afafuta da ke barazana fita daga gangar jikinta tafice daga parlour tana zuwa kan stairs takasa sarafa k'afafuta ta yi zaune tafara gurgura duwawu ta a haka takai karshen stairs da rerafe tak'arasa bedroom d'inta tana Shiga ta zube k'asa tafashe da matsananci kuka mai had'e da sambatu marasa ma'ana _wayyo Allah yaya Habeeb me yasa katafi ka barni gashinan wannan mugun maras tausayi da imani zai kashe ni_
Tun kafin tafiya ta yi nisa yafara gallazawa rayuwata na tabbata nan da d'an k'ank'ani lokacin zai gama da ni haka tacigaba da kuka da sambatu..

_2 hour's later_

Haleesa na kwance akan pray mat d'in da tagama sallah azhar, hannunta rik'e da casbaha idanuta sunyi luhu-luhu alama taci kuka Imaan ta turo k'ofa tashigo aunty ki zo Daddy na kira ki Imaan tafad'a had'e da juyawa
Haleesa ta kwa6e fuska tuni hawaye suka fara tsiyaya daga idanuta a baiyane tace to ni me zan masa Fissibillah wannan mutumi so yake ya kashe ni yana ci zarafi na ni fa ba baiwa bace ballatana yace siyo ni ya yi ko angaya mishi aure k'iyayya hauka ne
Gani wannan tsoki burutsu bara fishe ta ba ta mik'e da kyar tafice tun daga nesa ta hango shi zaune bisa dining table ya wanke ta da mushiriki murmushi zo nan amarya Habeeb Lamido ki ci abinci yak'arasa magana yana mai k'ara fad'ad'a murmushinsa
Wani irin k'ugi ciki Haleesa Ya yi tsanani tashin hankali ya baiyana k'arara akan fuskarta hawaye suka soma anbaliye akan fuskarta, domin zuciyata ta hasko mata wannan ta yi da Habeeb Lamido ya yi mata akwai wata manufa a k'asa
Ya mik'e chak yana murmushi yanufi wurinta ba zato balle tsanmani ta ji..........


Jeeddah Aliyu🌹



[11/11 5:24 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```67```

~~Ya dank'i hannunta kaitsaye yanufi dining table ya ja kujera ya zaunar da ita, yayin da Haleesa ta ke rarraba idanu takasa boye mamakinta
ya bud'e food flask yadauki plate ya zuba white Rice saida ya yi kusan cika plate ya zuba tomato stew akai ya kuma lullu6e stew d'in da had'in con slow ras-ras gaban Haleesa yafadi sakamako kwalba "Bama cream da taga yadauko ya dube ta ya sake haske ta da tsadade murmushi spoon 4 ya zuba na Bama cream ya ja kujera da ke facing d'inta ya zauna yana mai cigaba da murmushi mugunta k'amshin Bama cream kadai da Haleesa tashak'a yafara hautsine mata 'yan hanji tashin zuciya ya turnuke ta, hawaye suka cika mata idanu saboda ta hal6o mugunta da Habeeb yakeso yi mata
Tana kallo yana juya abinci da spoon ta yadda Bama cream zai gauraye abinci yace _yauwa Amarya Habeeb Lamido yau da kaina zan yi feeding naki kinsan me"?_
Bai jira jin ta bakinta yacigaba da cewa banaso sweetheart ta zargeni da rashin baki kulawa, shiyasa na yi decided yau da kaina zan cika miki tumbinki
Hawaye suka wanke mata fuska cikin tashin hankali tace _yaya Habeeb banaci Bama cream amai yake sani ka tausaya min karka tilassata ni cin shi_
Tak'arasa magana tana mai goge hawaye da bayan hannunta
Ya zare mata ido ya wani murtuk'e fuska Allah ba ki isa ba kice bara ki ci abunda nakeso tun da kika shigo rayuwata bakida za6i dole sai abunda na za6a miki yaciko spoon da abinci yanufi bakinta _oya bud'e baki_
Yaya Habeeb banaso zai sakani amai tafad'a cikin marairaice murya
Ranshi a b'ace ya galla mata harara ya mik'e ya dank'o bayan wuyanta za ki bud'e bakinki ko sai na tsinka miki mari
Haleesa tak'ara rud'ewa _wayyo Allah wuyana you're hurt Me yaya Habeeb please have mercy on me_
Ba zan taba tausaya miki saboda ke kika fara Shiga gona ta, alfamar d'aya zan miki ki ci abinci nan
To ka sakeni zan ci
Yasake ta ya koma ya zauna spoon d'aya yabata tafara kakari Amai ke! Karki sake ki yi min amai anan wuri yak'arasa magana cikin shouting"
Tsanani tsoro ya lullu6e ta batasan lokacin da ta hadiye abincin tsabar mugunta irin na Habeeb sai yaciko spoon yadank'ara mata a baki, a wahalce ta ke hadiyewa
Yaya Habeeb zan sha ruwa tafad'a cikin rawar murya
Mugun kallo ya watsa wuta za ki sha ba ruwa ba dallah! Malama bud'e baki saida ta cinye fiye da rabin abinci sannan ya kyale ta tashi ki b'ace min da ganin in yaso ki je ki amayar da 'yan hanjinki ba abunda yadame ni Burina yacika na daura miki abunda bakyaso wannan kad'an daga cikin hukunci da zan dinga yi miki a duk lokacin da kika karya mini doka tashi mana yadaka mata tsawa ta mik'e a firgice ta kwasa da gudu tanufi bedroom d'inta agigice ta afka bathroom tafara kwara amai, saida ta amayar da abinci da taci duka ta cire kayan jikinta tasakarwa kanta shower tsawon lokacin ta d'auka ruwa na sauka akanta ta kashe shower ta daura towel tafito ta zube akan bed tafashe da kuka mai cike da k'unci _me na yi wa wannan d'an taliki ya za6i ya dinga kuntatawa rayuwata"?_
_ashe dama haka rashin so yake"?_
Wani irin ciwo kai yarufe ta da kyar take iya bud'e idanuta
Ta mik'e zaune ta share hawaye fuskarta ba komai Habeeb Lamido zan cigaba da yi maka biyayya akwai lokacin da zan ci riba biyayya da na yi maka tun da narasa yaya Habeeb nasan na yi bankwana da farin ciki
Ta 6angare Habeeb yana ganin Haleesa tafice daga gudu ya ja tsaki yafara zance zuci, narasa dalilin da yasa a duk lokacin da na kalli yarinya nan nakan ji tsanarta na k'ara tasiri a zuciyata ya lumshe idanu mik'ewa ya yi yadauki Imaan suka fice daga gidan.

_9:30pm_
Haleesa na zaune a main parlour ta yi zurfi cikin tunani, Habeeb yashigo duba d'aya ya yi mata yadauke fuska _sannu da zuwa yaya Habeeb_
"Habeeb ya mata wani mugun kallo mai k'unshe da tsana ya ja tsoki ya haura sama Haleesa ta tabe baki ta nan zaune har yadawo yadda ya bar ta haka yadawo ya tarar da ita
Ranshi a 6ace yadaka mata tsawa ke!
Tad'ago a tsorace
Wai ke wace irin bagidajiya ce"?
Haleesa ta hadiye b'acin ranta ta kud'iri aniyar Zata yi hak'uri ta shanye wulaqancinsa
"Ke ba magana nake da ke ba kin wani tsare ni da idanunki masu kama da na mujiya narasa wace irin k'addara ce ta hau kaina na aure ki ba ki da amfani a rayuwata, na tsane ki bana k'auna na bud'e ido na ganki daga yau karki kuskure na sake ganinki a main parlour kidinga zama a parlour ki tashi ki bani wuri
"Haleesa ta mik'e tsam tanufi part d'inta ta haye bed ta k'undudune cikin blanket tana kukan zuci bacci ya k'aurace wa idonta da rufe ido fuska Habeeb Lamido take gani b'akin ciki da b'aci rai suka lullu6e ta komai ya dagule mata kanta ya dau zafi tana mamaki irin wannan zazzafa k'iyayya da Habeeb yake nuna mata sai kusan asuba baccin ya yi awo gaba da ita.
********************
_1 week later_
Tun daga lokacin Haleesa ta datse duk wata hanya da za ta had'a ta da Habeeb sai ta tabbata yafita sannan ta ke Shiga part d'inshi ta gyara masa suna ciki wannan yanayi yasami urgent call daga Canada a wani company da yakeda hannun Jari"
Haleesa na zaune a falonta tana tsifewa Imaan kai Habeeb, yashigo fuskarshi a had'e da sauri ta d'auki mayafinta za ta lullu6e jikinta saboda rigar da ke jikinta transparent ce rabin k'irjinta a bud'e bata manta da wulaqanci da ya yi mata ranar da yaganta da transparent night gown shiyasa ta yi wa kanta k'iyamunlaili tun kafin ya ci zarafinta
Ta yi mugun ba Habeeb Lamido haushi da k'arfi yaficike mayafin ya jefar
Haleesa ta yi galala da baki tana kallonshi
Ya dube imaan yace
Imaan tashi ki je room d'ina akwai chocolate akan bedside ki d'auka
jikin imaan na rawa ta mik'e tafice da gudu yak'arasa kusa da ita yadaura k'afarshi akan kujera da take zaune yad'ago fuskarta daf da ta shi numfashinsa yana sauka akan fuskarta k'amshinsa ya baibaye ta ya tsareta da manyan idanunshi "eye's ball d'inshi masu kama da na magge suka k'ara jefa Haleesa cikin rud'ani ya matsi mata baki ya ja iska duk ranar da ki ka sake ganina ki ka rufe, wannan busashe k'irji naki sai na yi miki wulaqanci ko mata kirki ba su ishe ni kallo ballatana ke mai kirge dangi yak'arasa magana had'e da Jan tsaki ya dungure mata kai cikin isa da tak'ama yanemi 2 sitter ya k'ame ya yi crossing legs d'inshi saida yagama shan k'amshi yafara magana a yatsine _zan yi tafiya gobe in da akwai abunda ki ke buk'ata you should tell me_
Haleesa ta yi ignoring nashi saboda batasan abunda za ta ce da shi
_ina magana da ke kin yi shiru yana d'aya daga cikin abunda yake k'ara mini tsanarki_
Tad'ago da kyar kamar za ta fashe da kuka muryarta na rawa tace bana buk'atar komai
Ya tabe baki gobe mom da Hannah za su wuce Abuja na yi magana da mom za ki bi su da fatar ba ki manta da dokoki da na shinfid'a miki"?
"ki tashi yanzu ki had'o kayan Imaan da ke bedroom d'ina har ta mik'e tsaye yadakatar da ita oh! I forgot to tell you chef peter da direba da zai dinga kai Imaan school tomorrow morning za su wuce so that ki had'a takarce ki su wuce miki da shi saboda a flight za Ku tafi
Cikin muryarta mai sanyi tace _toh_ tafice yayin da Habeeb ya bi ta da kallo Half gown ne sanyi a jikinta mai spaghetti hands idanushi suka sauka bisa hip's d'inta, da sauri yadauke kai ya ja iska had'e da lumshe idanu ohh! Gosh ashe baby nan mai zafi ce "she has Good body structures ya lashe lips d'inshi ina ma yanda jikinta yakeda zafi ace tana da gurbi a zuciyata, ina ma auren soyayya mu ka yi ya ja tsoki cike da jin haushin kanshi to wai me zai sa na dinga wasting time d'ina ina wannan tunani tun da ba sonta nakeyi ba asalima a tsarina banaso k'aramar yarinya yaushe wannan kwaila za ta iya da ni"?
Har Haleesa tadawo janye da trolley d'in Imaan yana zaune da waya a hannunshi yana buga game, ke! Ya kirata batare da ya dube ta very slowly yake magana kamar mai ciwo hak'ora ki shirya ke da Imaan za mu fita unguwa kuma karki bata min lokacin ta amsa masa a sanyaye tana shiga bedroom ta daka tsalle _yeee yau zan fita na shak'i iskan duniya tun da na zo gidanan ko k'ofar gida ban ta6a zuwa ba_
A gurguje ta shirya cikin Arabian gown orange colour da ado white stone's ta gyara fuskarta ta feshe jikinta da turare mai sanyi k'amshi ta yi rolling da d'an siriri white veil"
Imaan ta shigo da gudu _aunty Daddy yace ki yi sauri_
Jikinta na rawa ta sauyawa Imaan kaya suka fito main parlour yana tsaye a tsakiyar parlour yana ganinsu yafice Haleesa na rik'e da hannun Imaan ta Mara masa baya zuwa parking space
Bala na tsaye yana jiransu ya washe hak'ora yace
_Barka da fitowa amaryar Boss yau za'a fita evening show'?_
Murmushin yak'e Haleesa ta yi Habeeb ya ja tsaki ya bud'e seat d'in gaba ya zauna Bala ya bud'ewa Haleesa da Imaan seat d'in baya tun lokacin da suka d'auki hanya Bala ke ta fama zuba yayin da Habeeb ya yi banza da shi wani kyakyawan gate suka nufa Imaan tasa ihu _Daddy yau bara fita gidanan sai mom ta biyani gyad'a na da ta zubar_
Habeeb ya yi murmushi mai sauti yadauke ta yanufi cikin gida Haleesa na biye da shi har cikin parlour Hannah ta taso da gudu ta rungume Haleesa _amarya yaya Habeeb oyoyo_
Habeeb ya haura sama yabar su a parlour
"Humm....Hannah 'yan mata mommy ae ni na yi zato kin koma school
_ina nan ba idan na je bari kawai na matsu na gama karatu nan aure nakeso_
Haleesa ta zaro ido da tsanani mamaki take kallon Hannah
"Me ye haka amarya yaya Habeeb"?
Kafin Haleesa ta bata amsa tafisgo hannunta zo mu je ki gaisa da in-law d'inki kada tafara nuna miki halin uwar miji suka kyalkyale da dariya Haleesa tace kai amma wallahi Hannah bakida kirki, sai na gayawa mom abunda kika ce
"Madam na hakice akan 3 sitter Habeeb na kwance ya yi matashi da cinyoyinta su Haleesa suka shigo har k'asa Haleesa ta duk'a ta gaidata cikin fara'a ta amsa ta ture kai Habeeb d'agani magge sarkin son jiki Habeeb ya kwa6e fuska
"Madam ta janyo Haleesa ta zauna a gefen ta Nasiha ta shiga yi musu Kan Haleesa na sunkuye daga bisani madam tace Son tashi Kai Haleesa ta yi bankwana da su Ammi shiru ya yi kamar ba zai tashi ba ya mik'e madam da Hannah su ka yi musu rakiya har wurin mota Bala ya ja mota suka nufi unguwar su Haleesa Bala ya yi parking a k'ofar gidan su Habeeb ya dube ta a yatsine saura kuma in kin Shiga gidanku ki manta da mu a k'ofar gida
Batare da Haleesa tace da shi komai ba ta bud'e k'ofa tafita tana fitowa idanunta suka hasko mata Yaya Habeeb sanye cikin kayan ball ya tunk'aru ta fuskarshi d'auke da murmushi nan take kwakwalwa Haleesa ta d'auki zafi _dama ana mutuwa a dawo tambayar da tafara aikawa kanta_
"A lokacin d'aya tsanani tsoro da rud'ani suka lullu6e ta numfashinta yafara k'okari barin jikinta yana daf da yak'aroso wurinta ta kwaso da gudu tashiga zaure gidansu duk abunda ke faruwa Habeeb Lamido na tsaye a jikinsa mota yana kallonsu..........

Jeeddah Aliyu🌹




[13/11 7:17 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```68```

~~Ammi na zaune tsakiyar gida Haleesa tafad'o kamar daga sama, ta fad'a jikinta tak'ak'ame ta _lafiya ki ka shigo min a firgice daga ina kike"?_
A lokaci guda Ammi ta aikawa Haleesa tagwaye tambayoyi
_Ammi yaya Habeeb na gani a k'ofar gida yana sanye da kayan Ball dama Ammi ana mutuwa adawo ko yaya Habeeb fatalwa ya yi"?_
Mtwww.....Ammi ta ja dogon tsoki cike da jin haushin ta yakice Haleesa daga, jikinta Anyya Haleesa mutuwa Habeebu bata ta6a kwakwalwarki ba"?
Haleesa ta yi duru-duru da idanu hawaye da majina suna ambaliya akan fuskarta Allah Ammi yaya Habeeb na gani tak'arasa magana cikin shasshek'a
Gafara chan shashasha banza da wofi yadda kwakwalwarki ta toshe kina tsanmani kowa haka yake Habeebu yatafi Haleesa bara yata6a dawowa ki sawa zuciyarki salama ki rungume mijiinki kada ki 6ata rawanki da tsalle.
Haleesa ta share hawaye da gefen mayafinta
A k'ofar gida kuma Hasheem na gani Haleesa tashiga gida da gudu zuciyarshi ta tsinke musanmman da ya ga mijinta tsaye ya hard'e hannaye fuskarshi babu annuri, cikin rashin k'uzari yanufi wurin Habeeb a zuciyarshi yana addu'ar Allah yasa Haleesa ba matsala tasamu da mijinta, sallama ya yi wa Habeeb had'e da mik'a masa hannu
Bala ne ya amsawa Hasheem sallama, a maimako Habeeb ya bai wa Hasheem hannu sunyi musabaha sai kawai yad'aga masa hannu da sauri Bala yad'anki hannun Hasheem suka gaisa a mutunce sa6ani Habeeb da ke tsaye k'ik'an yana operating phone d'inshi kamar bai Sam da tsayuwa Hasheeem a wurin
"Jiki ba lakka Hasheem Yajuya yashiga gidansu Haleesa zuciyarshi na aiyana masa Haleesa matsala tasamu da mijinta, da sallama yashiga gidan a firgice Haleesa tad'ago tana kallonshi, tasauke k'arfafa ajiyar zuciya ba shakka yaya Hasheem ne nagani zuciyata tabani yaya Habeeb ne
Tuni Ammi tagano Hasheem ne Haleesa tagani ba Habeeb domin tsanani kama Hasheem da shi yake da Habeeb sai ka kwatar da hankalinka za gano banbancinsu
_Ammi lafiya wannan bak'auya amarya ta zo mana gida"?_
Idanun Haleesa na tsiyaya hawaye ta galla masa harara Ammi ta sanarda shi tabargaza da Haleesa tashigo da ita dariya sosai Hasheem ya yi gaskiya Haleesa Yakamata zuwa wannan lokacin ki fitarda yaya Habeeb daga ranki a dalilin ka sa cire shi daga zuciyarki yasa yafara yi min gizo
''Haleesa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login