Showing 39001 words to 42000 words out of 132766 words
sai naga kamar ban sami kar6uwa a wurinku.
Ammi ta numfasa tace an gode Allah yasaka da alkhairi
"Ameen a lokacin d'aya Habeeb da Bala suka fad'a.
Haleesa ta mik'e tsaye tanufi window ta yaye "curtain ta lek'a saura kiris numfashinta yadauke sakamako hango Habeeb Lamido da tayi yana duk'e a k'ofar d'akin Ammi da sauri-sauri numfashinta yadinga fita, Habeeb da Bala suka yi ma Ammi sallama suka fice da baya-baya Haleesa tayi tafad'a bisa katifarta da6as wani irin gumi ya lullu6e ta jin tayi an yaye curtain d'in d'akinta tad'ago da sauri Ammi tagani tsaye tana mata kallon "mamaki tabe baki Ammi tayi tace kitashi ki shirya ga bak'i chan a k'ofar gida suna jiranki karki 6ata musu lokacin Haleesa kamar za ta fashe da kuka tace Ammi me zanyi musu"?
"Ammi ta galla mata harara had'e da cewa bansaniba tajuya tafice Haleesa tayi ajiyar zuciya tsawon "5 minutes tadauko a zaune tana tunani irin had'uwa da za ta yi da "Habeeb Lamido jin tayi Ammi na kwad'a mata kira ta mik'e a firgice ta nufi d'an k'aramin "table da take Jere da tarkace kayan "make up d'inta tashafa 'yar powder akan face d'inta ta chanza kayan jikinta zuwa atamfar Deviva wax "blue colour da touch d'in pink" tasanya hijab pink tad'an Shafa body splash" cikin sanyi jiki tafi ce daga d'akin.
Habeeb yaja tsoki had'e da kallon wrist watch kirar Rolex da ke daure a hannunshi ya yatsine fuska yace Bala me wannan kuchaka yarinya take nufi ne zan 6ata almost "20 minutes a banza inajiranta"?
Ka K'ara hank'uri "Boss kasan halin mata da kyalkyali watakila ta tsaya yi ma kwalliya ne.
Tsanani haushi da takaici Bala suka lullu6e Habeeb yakasa furta komai, sai faman huci yakeyi.
"A hankali Haleesa take tafiya kamar mai jin tsoron taka k'asa gabanta na ta fama dukan tara-tara taja tayi tsaye a zaure ta d'an lek'a ta hango Bala tsaye yayinda Habeeb yana cikin mota da sauri tadawo da kanta cikin Zaure tasoma tunani yadda za'ayi ta fita k'ofar gida ta tsaya da wani d'a namiji da suna zance ba yaya Habeeb d'inta ba, hawaye suka cika "mata idanu ga wani tsanani tsoro Habeeb Lamido da ke ratsa jini da gangar jikinta tasauke numfashi yafi a kirga daga bisani ta yi k'undubala had'e da k'unar bak'in wake tak'arasa fita, Bala yasaki ajiyar zuciya domin shima ya kagara Haleesa tafito ya huta da "complains d'in "Boss d'inshi barka da fitowa ranki yadad'e Bala yafad'a yana washe hak'ora Haleesa tayi murmushi yak'e had'e da cewa yauwa Bala ya gida"?
"Gida lafiya da fatar mu sameki lafiya"?
"Lafiya qalau Daga haka kowane su ya yi shiru Habeeb yak'ara harzuk'a a zuciyar shi yace me wannan 'yar iska yarinya ta taka ne da bara ta iya gaida ni tana nufi ni ne zan fara yi mata magana"?
Tsoki yaja yacigaba da zance zucinshi lallai kuwa za mu kwana anan "I think she don't know who I'm that why take d'aukar kanta wata Tsiya batasan cewa Habeeb Lamido baya taking nonsense from local girl's like her" musanman ita da na tsana yak'ara ja tsoki.
Tsawon "10 minutes suka share ba Wanda yace da d'a uwanshi k'ala Bala ne yakawo kashe shiru nasu ta hanyar cewa ranki yadad'e ki k'arasa "Boss yana ciki Ku gaisa Haleesa tad'ago ta du6e Bala tace ka fad'awa "Boss d'in naka ya fito mana ko yana nufi cikin motar zan shiga ta'karasa magana tana yatsine fuska.
Babu shiri Bala ya hadiye wasu miyau saura kiris su sark'e shi, ya yi k'asa da murya ta yadda Habeeb ba zai ji abunda yake fad'a cikin Sigar lallashi yace "please Haleesa ki yi hank'uri ki daure ki k'arasa in kika ce za ki fara da haka basan ya zamanku zai kasance anan gaba ko ba komai ke ce k'arama Dan Allah za ki je ba don ni ba ko kuma "Boss.
Haleesa ta yi shiru kamar mai nazari daga bisani ta nufi 6angare da Habeeb yake zaune tadafa k'ofar mota cikin sanyi murya tace ina wuni yaya Habeeb"?
"Ignoring nata ya yi for some minutes" yayinda Haleesa tafara gajiya da tsayuwa kawai ta yi "decided tayi tafiyarta bara ta iya jure irin wannan wulak'anci "Habeeb ya ja tsoki sanadi da yasa Haleesa ta dube shi 'kas'kantace kallo ya watsa mata mai cike da tsana da sauri tadauke fuskarta da bari kallonshi, chan k'asan ma'koshi ya kira ta da sunan da tafi tsana ke! Akan wane dalili za ki bata mini lokacin"?
Cikin tsanani mamaki Haleesa ta dube shi daina kallona da wannan "ugly face naki yafad'a yana yatsine fuska kamar ya ga kashi ran Haleesa in ya yi dubu ya6aci a rayuwarta Sam ta tsani wulak'anci sai ga shi yau har k'ofar gidansu ake ci mata fuska kuma takasa d'aukar mataki gani yadda tasada kai k'asa batada niyar bashi amsa tambayarshi, sai kawai yacigaba da gasa mata maganganu masu matuk'ar zafi da sosa rai, na zo gidanku ne a dalilin mahaifiya ta ba wai don kinada wani matsayi a wurina na kuma amince zan aurenki ne domin na koya miki tarbiya saboda na fahimce cewa ke d'in bakida wadataciya tarbiya Wanda hakan ne yabaki damar shanya ni a k'ofar gidanku to kisani mace bata min wulak'anci, na kyaleta batare da na d'auki mummuna hukunci akanta yad'an numfasa me kika d'auki kanki"?
"I say who do you think you're"?
A tsorace Haleesa ta ja baya tana zarar ido domin ita kanta lamari Habeeb Lamido yafara bata tsoro ko a garin mahaukata bata ta6a gani neman aure irin nashi ba, wani shege murmushi yasaki Wanda Haleesa ta yi ma lak'abi da murumshin mugunta ya d'aga mata gira yad'an cije lips d'inshi na k'asa kamar mai rad'a ya furta "you're nothing but useless sai kinyi danasani shigowa rayuwa na banza 'yar k'auye "remember I told you for the first time my saw on you naji na tsaneki tsana mai tsanani gaske "I hate you I absolutely hate you I'll do anything just to make your life miserable yak'ara sa magana yana murmushi.
Haleesa tasauke ajiyar zuciya idanuta taf da kwalla muryar ta na rawa tace Allah yafika yaya Habeeb duk wani sharri da kake nufi akaina Allah zai kareni saboda banta6a nufar wani mahaluki da sharri, yadda baka sona nima haka abu yake a wurina, duk irin zaman da ka tanada min nayi a gidanka bazan ji ciwo ba saboda kai d'in ba komai bane a wurina tana k'arasa magana tashige cikin gida tabar Habeeb da rad'ad'i kalamai ta cikin k'unar zuciya yace wai Bala uban me ka ke jira ne"?
Da sauri Bala yashiga mota yaja suka fice daga unguwar, Bala ya yi k'asa da murya yace "Why you do this to her boss"?
Habeeb yasaki ajiyar zuciya a kasalance ya furta "b'cos I hate her bana sonta in fact yarinya nan bata dace da ni ba.
"I Known boss amma kuma in har madam ta ji irin wulak'anci da ka tsulawa yarinya nan me kake tunani zai faruwa"?
Harara Habeeb ya galla masa yace sai in Kaine munafuki da zai je ya sanar mata da abunda yafaru.
Bala ya yi murmushi had'e da cewa Allah ya huci zuciyar "Boss.
Haleesa na shiga gida ta zarce d'akinta tafad'a bisa katifarta tasaki kuka mai tsuma zuciya, nan take tafara tunani irin rayuwar da tayi da marigayi Yaya Habeeb tsawon rayuwa ta bata ta6a sani bak'in ciki d'a namiji sai akan Habeeb Lamido, lallai ina da aiki domin da ido na hango tsan-tsan tsana ta a kwayar idonshi to me nayi masa ne da yatsane ni haka"?
Rashin sani amsar wannan tambaya yasa ta mik'e tafice domin ta yi alwala sallah magariba.
```3 Day's later ```
"Iyayye Habeeb maza suka zo nema masa aure Haleesa Batare da kace nace iyayye Haleesa suka amince aka tsayarda lokacin nan da wata d'aya ranar Haleesa ta yi kuka kamar ranta zai fita gani ba Wanda ya kulata yasa ta dangana ta share hawaye ta.
```Gidan Alhaji Yusuf Lamido ```
Da gudu Maryam tafad'o parlour Hajiya khareema d'a kwalin da mayafinta a hannuta, tafad'a jikin Hajiya khareema tafashe da matsananci kuka a tsorace Hajiya khareema tad'ago Maryam cikin rawar murya tace lafiya Maryam kukan me kike yi"?
Maryam tak'ara rushewa da kuka hawaye kaca-kaca akan fuskarta shikenan Hajiya a karo na biyu narasa yaya Habeeb wallahi Hajiya mutuwa zan yi in har ban aure yaya Habeeb saboda, shine bugun zuciyata ba zan iya rayuwa ba shi yanzu nasami labari a babban gida wurin Dada wai Habeeb zai yi aure.
Hajiya khareema tasauke ajiyar zuciya tace kutuma ubanan yanzu dama d'an banza yaro nan yana da niyar K'ara aure a rayuwarshi, ba hanyar da ba mu bi ba ni da mahaifinki ya amince ya aure ki amma yak'i to wallahi bai isa ba ko yana so ko ba yaso sai ya aure ki wai 'yar gidan uban waye zai aura waye ubanta duk fad'in "Nigeria"?
"Maryam ta shar6e hawaye tace Hajiya 'yar talakawa ce ba su mallaki komai ba sai tari tsiya da fatara.
Hajiya khareema taja tsoki cike da takaici tace yanzu akan 'yar matsiyata Habeeb ya yi fatali da soyayyar da kike yi masa tabbas zan bi kowace hanya don gani Habeeb ya zama mallaki ki.
Maryam tasaki murmushi jin dad'i..
Jeeddah Aliyu🌹
[10/24, 11:43 AM] +234 813 417 9191: [03/10 5:25 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```Dedicated```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```58```
Ta wani kad'a kai kamar kadangarwa tace da kuwa har abada Hajiya ba zan ta6a mantawa da ke, a rayuwa ko a wance lokacin ni nafi cancanta yaya "Habeeb ya aura amma ya buge da aure aunty salma shi a dole baisan daraja da k'imar soyayya Dan Allah Hajiya ki yi duk yadda za ki yi na maye gur6in aunty salma a gidan yaya Habeeb "kin fi kowa sanin irin tsananin 'kuncin da nake ciki tun daga ranar da yaya Habeeb ya aure aunty salma har "Allah ya kar6i ranta ina fama da ciwon sonshi akan yaya Habeeb zan iya salwatar da rayuwa ta, da sauri Hajiya khareema ta katsi mata hamzari ta hanyar cewa ki kwantar da hankalinki muddin ina numfashi sai Habeeb ya aure ki don ba zan zuba ido ina kallon ki ki k'are rayuwarki ba aure tunda kin riga kin sakawa ranki in ba Habeeb ba za ki rayuwa ba.
"Maryam tasaki ihu farin ciki had'e da k'ank'ame Hajiya khareema.
```HABEEB```
Habeeb na kwance bisa "three star a katafare parlour madam Hindu hannunshi rik'e da "remote control madam Hindu tashigo parlour fuskarta d'auke da murmushi ta zauna akan kujera da ke "facing d'inshi "son dama inason ganinka dagane da zance gidan da Haleesa za ta zauna madam ta dakata da zanceta domin taji ta bakin Habeeb"
D'agowa ya yi ya tsurawa madam ido sai kace yau yafara ganinta daga bisani ya mayarda ganinshi wurin TV" madam ta yi murmushi saboda tasan halin d'a nata miskili ne na bugawa a jarida ba magana zai yi ba tacigaba da kallonshi can tace son wannan shine "right time da yakamata ka tare a sabon gidanka sabuwar Amarya a sabon gida tak'arasa magana tana murmushi yayinda Habeeb ya yi shiru zuciyarshi na tuk'uk'i don tsabar takaici jin yakeyi kamar ya hadiye zuciya, ko zai huta da zance da aure nan ya tsani zance Haleesa amma ita mom ba za ta gane ba ya yatashi zaune yana yatsina fuska yace "Mom gaskiya ni ban shirya zama a wannan gidan ba in fact ko "furniture's ba bu ciki kuma banida lokacin da zan yi odering nasu a yanzu Wani kallon madam ta watsa masa ta tabe baki banaso shirme banza Habeeb furniture's har wani Abu ne da za ka ce bakada "time na odering na su ka bud'e kunnenka da kyau ka saurare ni banaso dangin mahaifinka su San cewa, ni ce na nema maka aure Haleesa don haka ina gargad'inka da kada kasake kafito da alama da za ta nunawa duniya cewa Haleesa ba za6inka ba ce, ina fatar ka fahimce inda zance na yadosa"?
"Habeeb ya lumshe ido zuciyarshi cike da tsanar Haleesa ya gyad'a kai"
Cikin rashin kula da yanayi da yashiga madam tacigaba da cewa a matsayina na mahaifiyarka na umurce ka da gaugauta zuba duk wani abu da gidanka yake da bukata domin anan Haleesa za ta zauna kafin ka wuce da ita gidanka na Abuja.
'Dumm' Habeeb ya yi yana kallon madam da kyar ya iya sarafa halshe shi ya furta me kuma za ta je yi abuja"?
Harara madam ta galla masa had'e da cewa bansaniba sai kuma magana lefe kasan yanzu ne nake da tabbaci za ka yi aure saboda wance aure naka kai, kadai kayi kid'aka ka kuma taka rawarka a wurina yanzu ne za ka yi aure.
"Mamaki kalamai madam suka hana Habeeb magana sai fama musu-musu yake da baki k'iyayya Haleesa na 'Kara link'aya a zucyarshi gani mom ta mayarda hankalinta wurin TV hakan yabashi tabbaci cewa tagama maganarta ya numfasa ya lankwashe murya "sweetheart duk yadda kika tsara banida matsala "I'm ready to obey your decision ya d'a numfasa yacigaba da cewa "next week zan tafi Japan na yi "Ordering duk wani abu da gidan yake da buk'ata yak'arasa magana kamar zai fashe da kuka.
"Madam ta yi murmushin jin dad'i kalaman Habeeb tace Allah ya yi maka albarka dama nasan bara ka ta6a bani kunya.
"Humm! Habeeb yafad'a had'e da murmushi yak'e a zuciyarshi ya k'udiri aniya sai ya k'auntatawa Haleesa sai ta gwanmace tak'are rayuwarta a "kirikiri prison" da ta rayuwa a gidanshi ya ajiye "remote d'in hannunshi ya mik'e yanufi k'ofar fita daga parlourn.
```HALEESA```
A dai-dai wannan lokacin Haleesa da zainab suka fito daga islamiyya suna tafiya suna fira, har sun yi kusa shiga unguwarsu wata mota "dark blue kirar Prado tasha gabansu had'e da taka wawa "brake ba k'aramin tsorata Haleesa da zainab su ka yi a lokacin d'aya k'ofofi motar suka bud'e Maryam da k'awarta zeely suka fito kowanesu yasha "black shade Haleesa da zainab suka dube juna fusk'ok'insu shinfid'e da mamaki zeely ce ta kawo karshen mamaki nasu ta hanyar furta wacece Haleesa a cikin Ku"?
Haleesa ta ji "rass-rass"! Gabanta ya yanke yafad'i ta zare ido tarasa kalma da za ta furta
Zainab ta yi karaf tace lafiya Ku ke neman Haleesa"?
Sai kace had'in baki a lokacin d'aya suka zare "black shade d'in da ke lullu6e da kwayar idanusu Maryam ta aika musu wulak'antace kallo tace Ku! 'Ya'ya matsiyata za Ku amsa tambayar da aka yi mu Ku ne ko za Ku tsaye nuna halinku na 'ya'ya maula.
A fusace Haleesa tace ni ce Haleesa kuma ina shawartaki da ki saita kalamai ki domin duk wani rashin kunya da kike tak'ama da shi ni nan zan yi magani ki Haleesa tak'arasa magana had'e da yi musu kallon sama da k'asa.
Maryam da zeely suka kwashe da dariya har suna tafawa Zeely tace da kyau 'yar talakawa nasan cewa ba ki San ko mu su waye bane shiyasa har kike da baki fad'a mana magana ta juya wurin Maryam tace k'awata kora mata bayani kina dasa aya na d'ora daga inda kika tsaya domin na fahimce cewa wad'annan dak'ik'ai sai mun wanke musu allonsu ciki da waje.
Maryam ta yi murmushin tace Haleesa ba wani abu bane ya kawo mu a wurinki illah mu yi miki gargad'i akan Habeeb Lamido"
Da sauri Haleesa tad'ago ta dube ta sakamako sunan da ta ji ta Kira yayinda Maryam tacigaba da cewa sani kanki ne bakin rijiya ba wurin wasa makaho bane in ban da ke da rigima ina ke ina yaya Habeeb ae yafi k'arfin ajinki, to wallahi ina gargad'inki da kaukausar murya ki koma waje bokanki ya warware k'uli da ya yi miki har yaya Habeeb ya furta kalma mafi tsada da daraja akanki domin ba yadda za'a yi yaya Habeeb yana cikin haiyyaci sa yafurta kalma so akan 'yar matsiyata irinki"
Cikin tsawa da bacin rai Zainab tace ko a cikin dabbobi narasa jinsi da zan daganta Ku da shi jahilci da rashin tarbiyya ne da ya yi muku katutu yasa Ku ka tsayar da mu akan hanya, Ku na fad'a mana magaganu marasa tushe balle kan gado, shawara da zan ba Ku Ku je Ku nemi tumakai irinku Ku kwada masu halinku na dabbobi mu nan ba mu da lokacin saurare wannan shirme naku.
Maryam ta fusata ta cakmi hijab d'in zainab tace ke! 'Yar matsiyata har ni za ki fad'awa maganar banza lallai yau sai na ci ubanki a wurinan.
"Sakar mata hijab kafin ni na fara cin ubanki Haleesa tafad'a tana huci Maryam ta zaro ido kafin ta furta abunda ta yi niyar fad'a Haleesa ta yi kukan kura cikin fushi ta fusge hannuta daga wuyan Zainab ta ware hannayeta tashiga tsakaninsu, tace Zainab rik'e min jakka ta domin wannan fad'a nawa ne ke bara ki iya ba Maryam tasaki murmushi dama haka takeso ta jingi Haleesa ta kuma daki banza, domin tasha alwashi lallai yau sai ta kassara Haleesa"
"Maryam tad'aga hannu da sunan ta wanke Haleesa da bahago mari Haleesa ta rik'e hannuta yayinda ita ta kai mata mari har saida maryam taga wasu farare taurari suna shawagi akan fuskarta Maryam ta durk'ushe k'asa dafe da kumatu cikin hargowa Zeely ta yi kan Haleesa wani k'aton dutsi Haleesa ta k'ink'ima tace na ratsi kina k'arasowa zan rusa miki kai babu Shiri Zeely ta taka birki Haleesa tana huci tace na fahimce cewa ba Ku da tarbiyya ba Ku san daraja iyayyenku hakan ne ya jawo muku fad'a a titi akan d'a namiji to kun yi kuskure domin Habeeb Lamido nawa ne ni kadai in har kin cika mace ki je wurin boka da naje, ya dasawa Habeeb sona kema ya nema miki gur6i a zuciyarsa Haleesa na k'arasa magana ta rik'o hannun zainab tace zo mu tafi Zainab wad'annan k'anana kwari ne rashin kunya nasu na k'arya ne.
Wannan kalamai na Haleesa sun yi matuk'ar k'onawa maryam rai nan take ta ji wani mashahuriya tsanar Haleesa ta darsu a zuciyata ta ji a ranta sai ta dauki mummuna mataki akan Haleesa.
Haleesa ta shar6e hawaye tace kin gani ko zainab tun tafiya bata yi nisa ba, har na fara cin karo da k'alubali auren Habeeb Lamido.....
Jeeddah Aliyu🌹
[10/24, 11:43 AM] +234 813 417 9191: [10/10 3:28 pm] Jeeddah