Showing 123001 words to 126000 words out of 132766 words

Chapter 42 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87972

da Hannah tak'araso gate d'in gidan ta yi horn saida suka d'auki tsawon _3 minutes_ kafin gate ya bud'e su shiga yayinda Haleesa ke cigaba da waya da Habeeb.
"Parking Hannah ta yi Haleesa ta bud'e k'ofa tacire wayar daga kunnenta ta yi k'asa da murya yadda Habeeb bai zai ji abunda takeso fad'a ba what's time za ki dawo dauka na"?
Batare da Hannah ta yi magana ba tad'aga mata yatsunta uku.
_3 o'clock"?_ Haleesa tafad'a.
Hannah ta gyad'a mata kai Haleesa tajuya tanufi cikin gida yayinda Hannah ta ja mota.
"Direct part d'in Habeeb ta wuce tana mai cigaba da waya da shi a hankali ta turo k'ofa cikin Sa'a k'ofar ya bud'e ta hango Habeeb kishigid'e da waya a kunnenshi ta katse kiran miyarda phone d'inta cikin purse cikin sand'a tashiga parlourn ta bayan kujeri ta bi ta la6a6o ta rufewa Habeeb fuska.
"A tsorace Habeeb yashiga kacaniya cire hannayenta daga fuskarshi finciko ta ya yi da k'arfi tafad'o bisa kujera razananen ihu tasaki had'e da kai mishi duka da purse d'in hannunta haba! Yaya Habeeb karya ni za ka yi ne"? Irin wannan fincikowa da ka yi min Allah saura kiris na yi targad'e.
"Fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi yajuyo yana facing nata hannayenta yarik'o yacire purse daga hannunta ya jefa bisa kujera da ke kusa da shi ya ja iska yana mata kallon k'asan ido mekika zo yi wurina bayan ni kin haramta min zuwa wurinki"?
"Au! Haka ma za ka fad'a ae ni a tunani ba wannan tambaya yakamata ka yi mun ba tak'arasa magana had'e da fizge hannayenta tasoma k'ok'arin tashi da k'arfi ya mayarda ita zaune ya aza kanshi bisa cinyoyinta yace na yi matuk'ar mamakin ganinki Leesa domin wannan kiran da nayi miki na bankwana ne har na k'udiri anniyar gobe da zaran andaura auren Hannah zan koma Lagos daga can na haura Canada ba za ki k'ara ganina ba har sai kin nemi ni da kanki.
"Haleesa ta tabe baki da kuwa kayiwa kanka domin ba neman naka zan yi ba.
"Nasan za ki iya Leesa saboda ba damuwa ki ka yi da ni ba shiyasa a koda yaushe nake godewa Allah da yakare ni daga matan banza yak'arasa magana kamar zai yi kuka.
''Tausayinshi yakama Haleesa ita kanta tasan Habeeb yana cikin maza masu k'arancin sha'awa mata basa gabanshi shi dai barshi da neman k'udi a hankali take Shafa sumar kanshi muryarta asanyaye tace ka yi hak'uri my handsome Don nasan kana jin zafina amma yakamata ka yi min adalci ka tuna irin d'an banzan wulaqancin da dinga yi min har fa ce......da sauri yatoshe mata baki karki dawo da hannun agogo baya Leesa abunda yawuce bai kamata ki tadinga dawowa da shi ba kisani a yanzu inasonki tamkar numfashina KE D'AYA CE a zuciyata daga kanki na rufe ba wata.
"Murmushi ta yi cike da jin dad'in kalamanshi mai hira mai dad'i suka shiga yi daga bisani salon hirar ya canza cak d'auke ta yanufi bedroom d'inshi da ita tabbas Haleesa ta yarda ita d'aya ce a zuciyar Habeeb Lamido domin yanda yadinga zuba mata, zazzafan kalamai abun ba kama hannun yaro bayan komai ya wakana Haleesa na tsaye a gaban mirror tana busar da gashinta da hand dryer Habeeb yafito daga bathroom yak'araso daf ita ya kar6i hand dryer d'in yacigaba da busar mata da gashin Leesa kin ga yanda ki ka dawo 'yar lukuta musanman nan wurin yak'ara cikowa yana magana had'e da Shafa k'irjinta da hannunshi d'aya yana wani lumshe ido.
"Ta cikin mirror ta zabga mishi harara ae kai abun a cikin jininka yake duk mace da ta aurenka sai ta zama katuwa sai dai bana fatar na kai girman wannan matar tak'arasa magana tana yatsina.
"Dariya Habeeb ya yi had'e da kashe hand dryer ya ajiye ta a gefen mirror yajuyo da Haleesa suna facing junansu ashe bani kadai nake kishi da matace ba ke ma kina yi.
"Ture shi ta yi tanufi wajen wardrobe ta bud'e taciro black colour Long sleeve d'inshi ta kwashe inner wears d'inta tanufi bathroom tasanya kayan tafito Habeeb yana tsaye daga shi sai white vest da boxer ya yi crossing hands nashi a k'irji kallon mai cike da so da k'auna yake mata ni kuwa Leesa in tambaye ki mana"?
"Gira ta d'aga mishi had'e Yeap!
Yasauke hannanye shi yarik'o hannunta suka nufi k'ofar fita daf kunnenta yarad'a mata yaushe za ki fara saka kaya a gabana"?
"Ignoring nashi ta yi kamar bata ji abunda yafad'a ba suka yadda zango a parlour Habeeb ya kwanta akan 3 seater yajanyo ta jikinshi a wannan karo idan na tambaye ki kada ki yi ignoring nawa.
Turo baki tayi indan kuma tambayar naka ba mai buk'atar amsa bane to kasani ba lalle bane kasame amsa ba.
Ya ja iska had'e da dage gira ko yana buk'ata ko ba ya buk'ata dole ki nemo amsa Yaushe za ki dawo gareni"?
"Huh....dama wannan ne tambayar naka"?
Amsa yakamata ki ba ni firstly kafin ki yi naki tambaya.
"Haleesa ta yi murmushi tace idan an k'are bikin Hannah ka je ka ga mom na amince zan dawo gareka........


_am sick really need ur prayer's😪_


Jeeddah Aliyu🌹

[9:10PM, 23/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [22/12 6:33 pm] aliyujeeddah: 💝```NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa shehu Aliyu🌹

*®NWA*

*°°°°In Dedication°°°*
*Shehu Aliyu Family's*

*98*

_°°°°Hurray up today it's your birthday Autar Hajiya in my heart I make wishes for you to have peace & successful life_ °°°Happy birthday once again my Auta°°°°

~~Habeeb yasaki ihun farin cikin had'e da k'ara k'amk'ameta kamar zai shigar da ita k'irjinshi Sai zuba mata ruwan peck yake yi akan fuskarta zuwa, wuyanta muah...muah..I love you Leesa.... I really so much love you Leesa....wannan rana ta kasance d'aya daga cikin rananku da ba zan ta6a mantawa da su a rayuwana, Haleesa ta yi murmushi had'e da cewa d'an sausauta wannan matsar da ka yi min kada garin murna ni kuma kafasa mun k'irji.
"Karan hancinta ya ja ya sausauta rungumar da ya yi mata yashiga shafa cikinta yana lumsashe idanu Leesa...yakira sunanta
"Uhm.....tafad'a
Yaushe za ki bani baby"?
''Tabe baki ta yi ka nemo Wanda za yi min ciki ne"?
Mitsineta ya yi tasaki ihu washh....tafad'a had'e da Shafa fatar cikinta kai fa yaya Habeeb mugu ne sai ka yi ta yi wa mutum mugunta.
''Dole yasa nake miki mugunta Leesa kunnen k'ashi ne da ke nace da ke banaso abunda yawuce kina dawo min da shi sai naga kamar ba kiyafemin ba.
"Amma kuma abunda ka fad'a ne nake maimaitawa tak'arasa magana tana murgud'a baki.
"Shine nace da ke banaso don haka kidaina in baso ki ke mu yi fad'a ba.
Shikenan nadaina tacusa hancinta cikin k'irjinshi tana shinshinar k'amshin perfume d'inshi.
"D'ago kanta ya yi yana kallon cikin idonta yana dariya meye haka Leesa"?
"Allah yaya Habeeb k'amshin perfume d'inka yana mun dad'i har banaso nadaina shak'arsa.
''Habeeb ya kyalkyale da dariya yana shafar sumar kanta Lessa rigima ta yaya Habeeb Haleesa ta yi dariya wane yaya Habeeb ka ke nufi"?
"Harara ya galla mata baya ni kina da wani yaya Habeeb ne"?
"Peck ta yi mishi a kumatu kai d'aya ne baya kai ba Wani.
Dad'i ya lullu6e Habeeb cikin tsokana yace ae na yi zaton za ki kira sunan wannan mutume
"Rausayar da kai ta yi Wannan mutume ya zama past a yanzu Kaine presently, saboda haka kadaina zancenshi saidai in addu'a za ka dinga yi masa wannan ba zan hanaka ba.
"D'an bazawarin murmushi Habeeb ya yi, turo baki Haleesa ta yi ko ba za ka iya masa addu'a ba"?
Ni na isa nace ba zan masa addu'a ba yafad'a yana k'ok'arin cireta daga jikinshi Haleesa ta mik'e da kanta daga jikinshi ya yi mik'a ya dubi Haleesa yace Leesa yunwa nakeji fa
"Ta mik'e tsaye da sauri tace ka bani _15 minutes_ na dafa maka abunda za ka ci"?
Shima ya mik'e tsaye mu je na rakaki ta wuce gaba ya Mara mata baya.

_20 minutes later_

Haleesa ta kamalla jallof d'in macaroni da pepper soup kifi ta zuba a food flask Habeeb ya tayata d'aukar food flask d'in ita kuma ta dauko plates a tsakiya Rug carpet suka zauna ta yi masa serving.
Sai wani kad'a kai yake yi gaskiya Leesa kin iya girki ko d'and'ano abincinki dabam yake da na sauran mata.
"Haleesa ta kyalkyale da dariya ta dauki murfin food flask ta yi masa waigi bari na tarbeka kad'a santi ya d'ebe ka kafad'i ka dauko mun aiki.
Ajiye spoon d'in hannunshi ya yatsine fuska ni fa santi nake yi ba.
"K'ara kyalkyalewa da dariya ta yi kad'a kai yacigaba da cin abincinshi yad'ago ya dube Haleesa wance ke ta fama yi mishi dariya ya galla mata harara in ba ki daina yi min dariya ba sai na matse d'an k'aramin bakinan da yake mun dariya.
"Rufe bakinta ta yi da hannayenta tana mai cigaba da dariya k'asa-kasa suna gama cin abincin Haleesa ta mik'e kan 3 seater ta dubi Habeeb tace my Handsome Don zo ka yi min taushe gaba d'aya jikina tsami yake min.
"Murmushi ya yi ya kai girgiza batare da ya tanka ba ya mik'e yanufi kujera da take kwance yasoma matsa mata jikinta a hankali ta lumshe idanu cikin d'an k'ank'anin lokacin bacci ya kwashe ta.
''Gani ta yi bacci yasa Habeeb ya yi tagumi ya tsura mata ido hannunta yarik'o yana kallon zanen k'umshi lalle da ke hannunta tsawon lokacin yadauka a haka saida yaga lokacin sallah azhar ya yi sannan yashiga tashe ta ta hanyar hura mata iskan bakinshi a kunne.
"A hankali ta bud'e idanuta ta ware su akan fuskarshi yasake mata sanyaye murmushi gira yad'aga mata, ki tashi mu yi sallah sarkin bacci.
''Ta mik'e zaune tana yatsinar fuska Habeeb ya mik'e yanufi bedroom a kasalance ta bi bayanshi saida ta mayarda kayanta ta linke masa long sleeve d'inshi da tacire ta mayar cikin wardrobe.
"Habeeb yafito daga bathroom ya yarfa mata raguwar ruwan alwala da ke hannunshi cikin shagwa6a ta turo baki tajuya tashiga bathroom bayan sunyi sallah Habeeb ya bud'e wardrobe yaciro kayanshi yacire farar Jallabiya da ke jikinshi da sauri Haleesa ta tashi ta koma parlour, Habeeb ya bi ta da kallo.
"K'amshin turare shi da ta shaqa yasa ta yi tad'ago da sauri suka had'a ido murmushi suka sakewa junansu
K'asa d'auke idanunta ta yi daga kanshi saboda ba k'aramin kyau kayan da ke jikinshi suka yi masa ba yak'araso kusa da ita ya zauna bisa hannun kujera da take zaune akai rungumo kafad'unta ya yi yadai 'yan mata naa"? Yak'arasa magana had'e da kashe idonshi d'aya.
"Murmushi ta yi ta shafi laulausan sajenshi ka yi kyau _my handsome Don_saidai matsala na d'aya da kai baka saka kaftan tsawon zama na da kai banta6a ganinka da shigarmu na hausawa ba.
"Ya yi murmushi kinsan halina banaso zafi da takura shiyasa bana sakawa in fact ni ba bahaushe bane.
"tabe baki Haleesa ta yi gashi ni kuma ina sha'awar na ganka sanye da su don haka sai kafara sakawa ko don saboda ni.
"hancinta ya ja angama my Lady yafad'a yana dariya.

_3:00pm_

Hannah ta zo d'aukar Haleesa a parlour ta tarrarda su Haleesa na zaune Habeeb ya yi matashi da cinyoyinta yayinda ita kuma take wasa da sumar kanshi shigowar Hannah parlourn bai sa Habeeb yatashi daga jikin Haleesa ba sai ma gyara kwanciya shi da ya yi yashiga tsokanar Hannah da kyar Hannah tasamu yabarta ta wuce da Haleesa a cewar shi da kanshi za maida ta.

_9:00pm_

Haleesa na kwance akan bed Hannah na gefenta tana waya da Mus'ab phone d'in Haleesa ya yi ringing gani Habeeb ne ke kira yasa tadauka da sauri cikin shagwa6a tace mai sanyi na ya akayi ne"?
"Habeeb ya amsa mata da cewa ki zo ki parking lot inason ganinki.
Me zan maka tafad'a tana zarar ido"?
Za ki zo ko bara ki zo ba"?
''Kamar za ta yi kuka ta furta ganina zuwa amma kasani ba zan wuce Just 5 minutes ba zan nadawo.
Batare da yabata amsa ba ya katse kiran.
Veil d'inta ta dauka tafice tana gunguni parking lot tanufa tashiga dube-dube Habeeb ya bud'e k'ofar mota yaturo kanshi waje yace ke zo garinan.
Tajuya da sauri ta dube shi harararshi ta yi sannan tanufi wajenshi tadafa k'ofar mota, fuskarta a had'e tace amma yaya Habeeb kasan ba haka nayi da kai ba koh"?
"Yacire lollipop d'in da ke bakinshi shima ya murtuk'e fuska ya ki ka yi da ni"?
"Cewa nayi ka jira har agama bikin Hannah sannan ka zo ka yi magana da mom to me kuma ka zo yi yanzu"?
"Tsaki ya ja ke karki yi min wulaqancin don kinga na zo wajenki.
Ba wulaqancin na ke yi maka ba yaya Habeeb banaso mom ta ga mu tare nafiso sai kafara yi mata magana first idan ta tambaye ni nace na amince zan koma amma yanzu ga shi ka zo me ka ke tunani zai faru in tafito ta ga mu a tare"?
"Har ta dasa alama tambaya a zancenta Habeeb yana tsotsa lollipop had'e da kallonta a d'age in kin gama ki zagayo ki shiga mota mu yi magana.
Ranta a 6ace ta balle k'ofa tashiga light d'in da ke cikin motar ta kunna galla mata harara Habeeb ya yi ya kashe haske ya marairaice murya Leesa please ki saki fuskarki mu yi hira in ki ka daure fuskarki sai ki dawo kamar wannan housemaid d'inan na sweetheart da ke Lagos ya ma sunanta"?
"Murgud'a baki ta yi bansaniba ae sai ka tambayi kanka.
''To ae nima ba ke na tambaya ba Uhm...uhm...Janet! Yafad'a yana dariya zaro ido Haleesa ta yi tashiga dukanshi Allah yaya Habeeb ka kashe ni wannan mummunar ka had'a ni da ita
Ya kyalkyale da dariya yarik'e hannayenta ta fizge daga rik'o da ya yi mata ta koma jikin seat talafe tana kumbura fuska lollipop d'in bakinshi yaciro yasa mata a baki yacire veil d'inta yarataya a wuyanshi saida ta shanye lollipop d'in sannan tasaki fuskarta ta dube Habeeb tana murmushi Allah yaya Habeeb lollipop d'inan da dad'i.
"don yafito daga baki na ne shiyasa ki ka ji shi da dad'i yak'arasa magana had'e da kashe mata idonshi d'aya.
Hira mai dad'i suka shiga yi yayinda rabin jikin Haleesa yake manne da nashi sai around _11:30pm_ Habeeb yabarta ta koma cikin gida.

_Washe gari_
Misalin k'arfe 2:30pm aka daura auren Hannah da Mus'ab gaba d'aya Haleesa ta tashi cikin yanayi na rashin jin dad'i jiri da tashin zuciya ke damunta.
Around 4 o'clock Haleesa na kwance madam Hindu ta aiko kiranta ta mik'e a kasalance tanufi parlour tana shiga parlourn k'amshin abincin da k'awaye madam Hindu ke ci yabugi hancinta nan take zuciyarta ta tashi wani irin amai ya turnuk'e ta da gudu ta koma d'akin ta afka bathroom tashiga kwara amai kamar za ta amayar da 'yan hanjinta.......


_Ku yi hak'uri da short typing da nake mu Ku kusan ba isheshi lfy ne da ni ba_

Jeeddah Aliyu🌹
[8:35PM, 28/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [24/12 4:41 pm] aliyujeeddah: 💝```NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa shehu Aliyu🌹

*®NWA*

*°°°°In Dedication°°°*
*Shehu Aliyu Family's*

*99*

_Second to the last page_

~~Juyowa da Haleesa za ta yi taci karo da madam Hindu tsaye a bakin k'ofar bathroom tana mata kallo mai cike, da tuhuma Batare da tace da Haleesa komai ba tafita ajiyar zuciya Haleesa ta yi tafito daga bathroom jiri na d'ebarta tanufi bed ta kwanta bayan kamar _5 minutes_ da fita madam sai gata tasake dawowa, ta zauna kusa da k'afafun Haleesa, meke damunki ne Haleesa"?
"Da kyar Haleesa tad'ago muryarta ad'isashe tace tashi zuciya da jiri"?
Tun yaushe ki ka yafara jin tashi zuciya"?
"Yau da safe! Haleesa tafad'a kamar za ta yi kuka.
Murmushi madam ta yi Humm....bari na kira Dr Khaleesat Haydar ta duba ki domin za ta fini sani indan wannan ciwon naki yadosa.
"Haleesa ta marairaice murya mom ba sai kin kira Dr Khaleesat ba Allah naji sauki harara madam ta zuba mata sannan ta mayarda hankalinta ga wayar hannunta tashiga dialing digit d'in Dr Khaleesat Haydar ringing d'aya zuwa biyu Dr Khaleesat tad'aga cikin muryata mai zak'i da gard'in gaske tace _Assalamu Alaikum"!_
Madam Hindu ta amsa mata da cewa _wa'alaikum sallam Dr Khaleesat ya gida ya kuma hak'uri da Jama'a"?_
_Alhamdulillah Madam ya shagalin biki"? Allah naso nazo ko don kada Hannah ta yi mun gori amma aiyuka su yi mun yawa a hospital amma insha Allah zan ware lokacin na je naga gidan amarya Hannah_ Dr Khaleesat tak'arasa magana tana dariya madam ta tayata dariyar daga bisani madam tace Dr Khaleesat in da hali inason ganinki urgently akwai patient d'in da nakeso ki duba mun ita
Amma fa in ban takura ki ba Dr Khaleesat ta yi murmushi tace ba damuwa madam insha Allah yanzu nan za ki ganni dama ina bisa hanyar zuwa gida ne.
"Shikenan Dr inajira sai kin zo madam k'arasa magana had'e da katse kiran.

_10 minutes later_

Dr Khaleesat Haydar tadanno hancin motarta kirar Lexus 2016 model a farfajiyar gidan madam Hindu tanufi parking lot ta yi parking k'afafunta suka Fara fitowa daga bisani gangar Jikinta ta baiyana sanyeta ke da Arabian gown Blue colour ta yi rolling da pink colour veil kwayar idonta na lullu6e da farin gilashi ta bud'e seat d'in baya tadauko briefcase d'inta mai d'auke da kayan duba marar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login