Showing 30001 words to 33000 words out of 132766 words

Chapter 11 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87941

da ingantaciya tarbiya da takeda ita yasa na yi wa d'ana Habeeb sha'arwata ko ba komai tarasa Habeeb ga kuma wani Habeeb yadawo watakila ko don sunan Habeeb kadai zai iya saka tarage tunani marigayi Habeeb bansaniba ko iyayyenku za su amince su ba wa Habeeb aureta har madam Hindu ta dasa aya Juwairiyya tana mata kallon mamaki daga bisani tace mommy karki ce na katsi miki hanzari sai naga kamar Haleesa bata dace da Habeeb ba saboda mu talakawa ne duk zuri'armu ba mai kud'i Juwairiyya tak'arasa magana had'e da sada kai k'asa, madam Hindu tayi murmushi tace Juwairiyya Yakamata ki bada kyakyawa sheda akaina da zuri'arta bana d'aya daga cikin masu kud'in da ke kyamar talaka a wurina mai kud'i da talaka duk d'aya ne shawara na zo neman a wurinki ya kamata ki k'arfafa min guiwa domin na cima aikin alkhairi da nayi niyya karki manta shekaru biyar a baya da suka wuce Habeeb yarasa matarshi a waje haihuwa, dalilin haka yakasa k'ara aure Juwairiyya ina buk'atar Habeeb ya yi aure saidai duk lokacin da na tuntube shi da zance aure sai yace na nemo mishi matar aure, ni kuma narasa yarinya da zan nemo masa wance za ta soshi tsakani da Allah ba don kud'inshi ko kyakyawa sura da Allah yabashi sai gashi kwatsan Allah yakawo min Haleesa har gida, kuma ta cika duk wasu sharudd'a da nakeso matar Habeeb ta kasance da su Juwairiyya tasauke ajiyar zuciya tace shikenan mommy sai kifara sanarda Habeeb in ya amince da Haleesa a za6inki daga bisani sai a sanarda iyayyenmu domin su ne kadai a halin da Haleesa take ciki za su iya tankwarata ta amince da zance aure.
Habeeb bashida matsala Juwairiyya duk abunda nakeso shima yanasonshi bamu ta6a samu sa6ani ra'ayi, Haleesa ta d'aga hankalinta tana buk'atar ganin Ammi karki hanata tafiya ni kuma zanyi amfani da wannan damar naje Yobe na nemawa Habeeb aureta.
Ba matsala mommy duk yadda kika ce haka za'ayi'
"Madam tayi murmushin farin ciki tace kira min Haleesa mu yi sallama, Juwairiyya ta mik'e tsaye tana washe hak'ora kamar mai talla toothpaste Haleesa na kwance Abba na bisa cikinta yana wasa doki, Juwairiyya tana dariya tace wannan k'aton yaro za ki aza bisa ciki yana doki sai yafasa miki ciki, Haleesa ta mik'e zaune tace Abba naa ba k'ato bane, Juwairiyya ta tabe baki had'e da cewa ki taso Ku yi sallama da "mommy za ta wuce Haleesa ta mik'e tsaye suka fice tare Madam nagani Haleesa ta'kara fad'ad'a murmushinta tace Haleesa ni zan wuce ki gaida Ammi kafin nazo mu gaisa.
"To mommy zai taji na gode sosai da d'ibin alkhairi ki agareni madam ta zuge zip handbag d'inta tafito da bundle na dubu d'ari ta mik'awa Haleesa gashi Haleesa ki yi wa su Ammi tsaraba Haleesa ta girgiza kai had'e da cewa hidima da kike yi da ni mommy tayi yawa ba zan kar6i kud'inki ba.
Madam ta mik'e tsaye ta mik'awa Juwairiyya kud'in Juwairiyya takasa k'ar6a kad'a kai "madam tayi batare da tace komai ba ta ajiye kud'in bisa hannu kujera, tajuya tafice cikin sanyi jiki Haleesa da Juwairiyya suka Mara mata baya da sauri Aderwale yafito ya bud'ewa madam mota, tashiga Haleesa ta dafa k'ofa tace mommy narasa da wance kalma zaiyi amfani da ita wurin gode miki, banida abunda zan saka miki da shi mommy saidai, zan cigaba da yi miki addu'ar fatan alkhairi ke da zuri'arki.
Madam tayi murmushi da ke nuna taji dad'i kalamai Haleesa daga bisani tace ba komai Haleesa ni na d'auke ki tamkar Hannah, Haleesa da Juwairiyya suna tsaye har motar madam tafice daga gate d'in gidan sannan suka juya zuwa cikin gida, Haleesa tafad'a bisa kujera ta ja wata doguwar ajiyar zuciya Juwairiyya ta zauna kusa da ita cikin sanyi murya tace Haleesa meyasa kike so komawa Yobe alhali da bakinki kika ce sai kinyi _3 week's_ za ki koma gashi _1 week_ kawai kika yi kince za ki koma ko anyi miki wani laifi ne"?
"Ba abunda akayi min kawai dai nagaji da garinan
Shikenan bara na shirya na rakaki kasuwa gobe sai ki bi morning flight"
Murmushi Haleesa ta yi, cikin zuciyarta tace hakan shi zai saka Habeeb Lamido yagano kwakwalwa da zuciyarshi sun cuce shi da suka haska masa cewa na zo Lagos ne saboda shi, ta yatsine fuska a baiyane tace _disgusting_ Juwairiyya ta zaro idanu tace lafiya kike Kuwa Haleesa"?
"Yes am absolutely fine
Murmushi Juwairiyya tayi ta mik'e tsaye had'e da cewa ki je ki d'auko mayafinki mu tafi batare da ta jira amsar da Haleesa za ta bata tashige bedroom d'inta.
Yinin ranar sun k'arace shi ne a yawon siye banza siye wofi ba su ne suka dawo gida ba sai ana kiran sallah magariba, don haka a gajiye suka shiga cikin gida kaitsaye kowane su yanufi bedroom d'inshi Haleesa ta jefarda mayafinta bisa bed tanufi bathroom tayi alwala bayan ta gama sallah ta zabga tagumi tasoma tunani Habeeb Lamido zuciyarta cike da mamaki shi wai ina bibbiya shi to me zan tsinta a wurinshi mtss mahaukaci kawai marar tunani, da kyar ta samu ta rinjaye zuciyarta tabarta ta gabatarda sallah isha dawowar masa'ud yasa tafito parlour ba rarrashin da banyi mata akan tayi zamanta koda _1 week_ ne ta'kara musu amma Haleesa ta k'ek'ashe k'asa tace ita dai tafiya za tayi dole masa'ud ya kyaleta......
[15/09 8:00 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```50```

```WASHE GARI ```


Da wuri Haleesa ta tashi ta yi wanka tana jiran fitowar Masa'ud yakaita airport, saida yagama ja mata rai sannan yace tafito su tafi koda tafito _10:30am_ ta buga gashi flight d'in da zata bi zai tashi k'arfe _11:30am_ sai faman complaints take mishi ya6ata mata lokacin Juwairiyya sai faman dariya take yi gani yadda Halee take zumud'i tafiya saida suka ga tashin jirgin su Haleesa sannan Masa'ud da Juwairiyya suka nufi gida.

```YOBE```

Jirgi na sauka bayan Haleesa tafito batare da 6ata lokacin ba, taja trolley d'inta taxi tashiga tana gani driven taxi d'in yashiga unguwarsu tasaki sanyaya ajiyar zuciya tasaki iska ta furzar tace _Home, sweet Home_ har k'ofar gidansu taxi d'in tayi parking cikin zumud'i ta balle k'ofa tafito, dai-dai lokacin da Hasheem 'kanin marigayi yaya Habeeb yafito daga cikin gida Haleesa ta tsura masa ido da sauri-sauri numfashinta yake fita saboda sai yau ta'kara tabbatar da tsanani kama da Hasheem yakeyi da Yaya Habeeb banbanci su kawai yaya Habeeb yafi shi, tsayi gani yadda take kallonshi yasa yasake mata murmushi yak'araso daf da ita cikin tsokana yace babylove ya akayi ne naga kin wani tsare ni da ido sai kace yau kika fara ganina ke da kika je Lagos a maimako ki waye sai kika k'ara kwaso k'auyanci.
"Ko kwakwara motsi Haleesa ta kasa yi da k'arfi Hasheem ya kira sunanta Haleesa!
Haleesa ta dube shi tayi ajiyar zuciya, kafin ta yi magana mai taxi yace malama sallame ni na tafi Hasheem yace nawa ne kud'inka"?
D'ari uku ne yallabai Hasheem yafito da _N 500_ ya mik'a masa shi kuma ya bashi chaji yadauki trolley d'inta ya wuce gaba tana biye da shi sai tambayoyi yake zuba mata yayinda Haleesa takasa bashi amsar ko d'aya daga ciki da sallama yashiga cikin gidan had'e cewa Ammi fito ga bak'in Lagos da rana tsaka da sauri Ammi tafito daga d'aki tana gyara d'auri d'an kwalinta tana had'a ido da Haleesa mamaki ya baiyana akan fuskarta da gudu Haleesa ta'karasa wurinta ta rungume ta tasa kuka Ammi ta bubbuga bayanta, haba! Haleesa meye kuma abun kuka"?
Cikin muryar kuka mai cike da shagwaba tace Ammi nayi kewarki'
Hasheem da ke gefe ya kyalkyale da dariya yace lallai yarinya nan dad'i ya yi miki yawa ki ce kukan dad'i kikeyi to ni zan tafi anjima zan dawo na kar6i tsaraba na yak'arasa magana had'e da yaficewa.

```3 hour's later```

Haleesa na zaune a d'akin Ammi sai labari madam Hindu take ba wa Ammi, kwarai Ammi ta yaba da kirkin "madam Hindu
Tace duk lokacin da tashigo Yobe zata zo Ku gaisa.
Murmushi Ammi tayi tace Allah yakawo ta lafiya
"Ameen Ammi bara na je na gaida inna mairo ta zari hijab d'inta had'e da ficewa, tana Shiga gidan zainab ta shek'o suka rungume juna sai da aka fara kiran sallah magariba Haleesa ta koma gida bayan ta gama sallah tafito tsakiyar gida tasha iska yaya salman ya yi sallama yashigo, Haleesa ta amsa mishi, ya zauna kusa da ita tana bashi labari Lagos Salman ya kyalkyale da dariya yace Haleesa manya ke da kika yi _1 week_ kacal a Lagos har wani labari za ki bayar
Haleesa ta turo baki tace Allah yaya salman nayi yawo saidai ba sosai ba kuma baka ga gidan da na zauna Allah gidan yahad'u kamar a abroad ae kuwa Salman da kamal suka dinga yi mata dariya Haleesa ta gallawa kamal harara tace gwara ni na je lagos nayi kauyanci kai kuma kamal baka ta6a zuwa ba tak'arasa magana had'e da yi masa gwalo har baffa yashigo gida suna zaune tsakiyar gida suna fira shima ya zauna akayi firar da shi kowane su zuciyarshi cike da tsan-tsan farin ciki sakamako gani yadda Haleesa take annashuwa da nishad'i sai misali k'arfe _11:44pm_ kowane su yanufi d'akinshi Haleesa tasuya kaya zuwa wata 'yar k'aramar vest ta daura zani bisa ta kwanta tana daura kanta bisa pillow ta lumshe idanu nan take face d'in Habeeb Lamido yafara yi mata shawagi a eye's nata da sauri ta bud'e idanuta _"why Habeeb why don't leaves my heart to be in peace"?_
Ba gidanku kadai ba har garin Lagos na baro maka _but you still following me_
Hawaye suka ziraro mata a gefen idanu suka sauka bisa wuyanta, kuka Haleesa tayi sosai daga bisani bacci ya yi awo gaba da ita anan ma bata tsira ba saboda mafalki shi tadinga yi Habeeb ya zamewa rayuwarta karan tsaye.

```BAYAN SATI D'AYA ```

Haleesa da zainab sun dawo daga islamiyya yamma suna tafiya suna fira, tun daga nesa Haleesa ta hango mota kirar _KIA cerato_ a Parke a k'ofar gidansu wani matsananci fad'uwar gaba taji saboda ta ta6a gani Habeeb Lamido cikin irin wannan motar, zainab tace Haleesa bak'i masu kud'i mu ka yi ne na hango had'ad'iyar mota a k'ofar gidanmu"?
Haleesa tad'ago ta dube ta tasauke ajiyar zuciya tace oho! Tafad'a kaitsaye suna k'arasawa k'ofar gida idanu Haleesa suka sauka bisa number motar _Habeeb Lamido 5_ abunda idanuta suka hasko mata kenan tsanani tsoro had'e da tashin hankali suka chukuikuye mata zuciya Wanda hakan ya haddasa mata zaro idanu tanemi yawu bakinta tarasa, a zuciyarta tace na shiga uku me wannan shu'umi ya zo yi a gidanmu..."?



```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```


Jeeddah Aliyu🌹
[17/09 3:01 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```51```

Meke faruwa ne Haleesa na ga kina zarar ido''?
Muryar Zainab ce tadawo da ita daga natsuwarta taja gwaron numfashi daga bisani, tace ba komai zainab ta yi murmushi rashin yarda da amsar da Haleesa tabata Haleesa kenan nasan abunda kike yi wa zarar ido duk bai wuce sunan Habeeb da kika gani a jikin number motar nan ta'karasa magana had'e da nuna number motar da yatsanta tadafa kafad'ar Haleesa tacigaba da cewa yakamata ace zuwa yanzu kin manta da rayuwarki da Yaya Habeeb Co's He will never comeback to us yaya Habeeb ya mutu Haleesa ba zai ta6a dawowa so ki manta da shi ko Ke ma za ki ji dad'i rayuwarki, hawaye suka cikawa Haleesa idanu saboda a yanzu batada wata matsala da ta wuce Habeeb Lamido tarasa dalilin da yasa take yawan tunani shi, cikin sanyi murya tace zainab bara na shiga gida batare da ta jira amsa da zainab za ta bata tashige zaure gidansu, tana jefa k'afarta tsakiyar gida ta yi turus Ammi da madam Hindu sai wata kyakyawar budurwa mai kama da Habeeb Lamido ta hango zaune, suna fira nan take tagano cewa wannan budurwa ita ce Hannah, ajiyar zuciyar Haleesa ta yi cikin tsanani jin dad'i gani bak'i{visitor's} nasu tayi sallama a lokacin d'aya suka amsa mata madam Hindu tace idonki kenan Haleesa kin manta da mommy koh"?
Cikin yanayi naji kunya ta durk'usa tace ina wuni mommy"?
"Lafiya qalau Haleesa zo ki zauna anan ta nuna mata kusa da ita Haleesa ta zauna tajuya wurin Hannah da ke ta faman zabga murmushi, tace Mommy ko ban tambaya ba wannan ita ce Hannah madam ta yi murmushi tace kin chanka dai-dai Hannah da Haleesa sukayi dariya fira sukeyi Haleesa sai kyalkyale dariya takeyi madam tace ashe Haleesa kina dariya"?
Haleesa ta sada kai k'asa tana dariya k'asa-k'asa Ammi ta yi 'yar gajeriya dariya daga bisani tace tun daga lokacin da Haleesa tadawo daga Lagos take wannan fara'a narasa me Ku ka bata da yasauya ta a d'an k'ank'ani lokacin Ammi ta'karasa magana had'e da dariya madam da Hannah suka kwashe da dariya sallama baffa da baba Audu ce ta katsi musu dariyar da suke yi bayan sun gaisa a tsakaninsu madam tajuya wurin su Haleesa tace Haleesa da Hannah Ku ba mu guri za mu yi magana Haleesa ta mik'e had'e da rik'o hannu Hannah tace zo mu je gidan su zainab Ku gaisa.
"Madam ta gyara zama tafara magana malam Usman wata alfamar nazo nema a wurinka shine dalilin da yasa nace inaso magana da kai, bansaniba ko za ka amince da buk'atana"?
"Malam Usman yajuyo ya dube d'an uwanshi daga bisani yace fad'i Alfarma taki Hajiya kuma Allah yasa zan iya.
Malam usman dama alfarma da na zo nema alkhairi ne bansaniba, ko ta ya za Ku d'auki wannan al-amari azahiri gaskiya tun daga ranar da naga Haleesa na yaba da hankali da tarbiyyarta musanman da naji tarihi rayuwarta da marigayi Habeeb Wanda hakan ne yajanyo na yi wa d'ana Habeeb sha'arwata a tunani na Haleesa tarasa Habeeb ga kuma wani Habeeb yadawo ina matuk'ar tausayi rayuwa Haleesa 'yarku na buk'atar abokin rayuwa Wanda zai sota yabata kulawa wance za ta sa ta manta da rayuwa da tayi da marigayi Habeeb yanayi da Haleesa ta tsince kanta a ciki yadda ta mayarda kuka da tunani abokai rayuwarta, hakan zai iya shafar lafiyarta kun ga kenan za'ayi biyu babu an6ata d'aya biyu bata gyaru ba amma kuma a matsayinku na iyayyeta menene ra'ayinku"?
A lokacin d'aya baffa, baba da kuma Ammi suka sauke ajiyar zuciya domin abu ya zo musu a bazata basu ta6a tunani jin wannan, furucin daga bakin madam Hindu baba Audu ya numfasa, yace tabbas Hajiya kin zo mana da abu mafi girma, da farko inaso kisani mu talakawa ne ba mu da komai akullum fafutukar Neman nasawa a bikin salati mu ke ni aganina, sai naga kamar d'anki baidace da 'yarmu wutsiyar ragumi tayi nesa ga k'asa.
Ka ga malam Audu kada Ku fassara ni baibai, ni mutumce kamarku don kawai Allah ya yi min arziki sai Ku banbanta kanku da ni to kusani duk d'aya mu ke a wurin Allah sai Wanda yafi wani tsoronshi, ban zo nan don na cutarda 'yarku kafi nazo nan saida nasa akayi min bincike akanku nima na baku damar Ku yi bincike akaina da kuma d'ana Habeeb.
A wannan karo malam Usman ne yabata amsa ta hanyar cewa shikenan Hajiya, mu amince da buk'atarki domin bamusan abunda Allah yake nufi a cikin wannan al-amari Haleesa tarasa Habeebu a lokacin da tafitarda rai da tak'ara samu farin ciki sai kuma ga wani Habeebu yashigo rayuwarta Allahu Akbar Allah mai iko, mu amince Hajiya amma a bisa sharad'i d'aya sharad'i kuwa shine har sai Haleesa ta furta da bakinta ta amince da d'anki domin mu ba za mu yi mata dole ba.
Murmushi madam Hindu tayi da ke baiyanar da farin cikinta tace nima bana goyo bayan ayi mata dole, Ku barni da ita agabnku zan yi magana da ita insha Allahu za ta amince ae Haleesa yarinya ce mai biyayya......
[17/09 5:07 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```52```

Tun lokacin da su Haleesa suka shiga gidan su zainab fira ta barke a tsakaninsu, _ringing_ d'in wayar Hannah ce ta katsi musu firar tasu gani "mommy ce ta kira yasa Hannah bata yi picking ba ta mik'e tsaye had'e da cewa Haleesa tashi mu tafi mommy ce ta kirani watakila wuce wa za mu yi Haleesa ta mik'e zainab ta Mara musu baya da sallama suka shiga gidan madam tace zo zauna Haleesa za mu yi wata magana da fatar za ki bani had'in kai"?
Haleesa tad'aga kai madam ta rik'o hannuta cikin k'ask'antar da kai tafara magana Haleesa burin kowace uwa tagari d'anta ko 'yarta su sami abokin rayuwa nagari shiyasa na za6e ki a matsayin matar da nakeso Habeeb ya aura"
A firgice Haleesa tad'ago dara-dara idanuta tasauke su bisa fuskar madam kallo d'aya za ka yi mata gano tsintsa tashin hankali da take cikin, yayinda madam tacigaba da fad'ar amincewarki kadai nake nema Haleesa saboda iyayye ki sun amince, shin Haleesa kin amince da Habeeb ya maye gurbi marigayi Habeeb a wurinki"?
Wannan tambayar ta "madam Hindu ta yi matuk'ar gigita Haleesa had'e da haddasa mata shiga tashin hankali maras misaltuwa, ta zazzare ido tamkar ta ga wani abin tsoro yayinda zuciyarta ke bugawa kamar ana buga ganga nan take tafara shid'ewa numfashinta yafara k'ok'ari k'auracewa gangar jikinta tsanani tashin hankali da rashin mafita suka lullu6e ta sai faman zazzare ido take mayuwaci abu ne ta kalli tsabar idon madam Hindu tace batason d'anta babban tashin hankalinta bai wuce yadda za ta rayuwa da Habeeb Lamido mutumin da yakira ta da suna 'yar iska mai bibbiya d'an namiji kenan furucin sa zai tabbata na cewa ina sonshi.
Da k'arfi madam ta girgiza Haleesa tadawo haiyyacinta kin yi shiru ba ki ce komai ba Haleesa ko bakyaso Habeeb ne"?
Karki dame kanki Haleesa ba za mu yi miki dole ba har. madam ta dasa aya Haleesa tana kallonta ta sauke numfashi yafi a kirga daga bisani ta tattaro k'uzari had'e da jarumtaka ta cikin sar'kewa halshe tace, mommy ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login