Showing 42001 words to 45000 words out of 132766 words
Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```59```
_Narasa kalma da zan yi amfani da ita wurin gode miki Fatima Umar{Mrs Umar} akan irin d'ibin son da kike yi wa wannan littafi na Ni da yaya Habeeb ina miki fatar alkhairi a rayuwarki Allah yasaka miki da gidan aljanna Firdausi "I really appreciated Fatee naa_😍
A wulank'ance yake kallon kayan daga bisani ya ja tsoki kamar zai gutsire halshenshi, Cike da takaici ya fad'a bisa kujera yadafe goshi kallon d'aya Hannah ta yi mishi ta tabe baki ta janyo wata 'yar 'karama kitt ta shigar da "Code kitt d'in ya bud'e tafito da "Necklaces na Gold cikin Yanayi na rashin damuwa da halin da yake ciki ta mik'a masa kitt d'in had'e da cewa yaya Habeeb ga Gold's d'in da mom ta siyawa Amaryarka na tabbata kai ma za ka yaba da za6i Aunty Mami a maimakon ya kar6i kitt d'in sai kawai yasa hannu ya bugeta tafad'a kan ciyoyin Hannah idanu ta zuba masa ta girgiza Kai dama tasan za'a yi haka ta ya ya kamar yaya Habeeb Wanda idanushi suka gama bud'ewa mom ta za6a mishi mata don kawai Yaya Habeeb yana da biyayya Sam bayaso b'aci rai Mom duk abunda tace tanaso koda shi d'in bayaso a dalilin Mom zai ce yanaso abun ba don ranshi yanaso ba kenan ya amince da aure Haleesa saboda mom lallai kuwa da saura rina a kaba gani yadda Hannah ta tsare shi da ido yasa yajuya wurin Asabe da yarinye yadaka musu tsawa kai! Ku bar nan jiki na rawa suka fice saida ya share tsawon "5 minutes yana dafe da goshi daga bisani yafara magana kamar mai rad'a Hannah banaso yarinya nan shiyasa bana farin ciki da wannan aure Kinga kenan bai kamata Mom ta dinga 6anata kud'inta akan abunda bana farin ciki da shi azahari gaskiya Hannah banaso yarinya nan ina mata tsanar da fatar bakina bara ta iya misalta ta, wannan ya zama "sirri a tsakaninmu Co's banaso Mom tasani yana k'arasa magana ya koma yalafe a jikin kujera.
"Hannah ta mik'e ta zauna bisa hannu kujera da ya ke kai cikin sanyi murya tace, ni a ganina yaya Habeeb Haleesa batada matsala kyakyawa tarbiyya da take da ita yajanyo hankali Mom har ta yi maka sha'awarta, ka jira har ta shigo gidanka na tabbata za ka so ta har ta dasa aya a zanceta ya na mata kallon hadari kaji kin gama yafad'a a yatsine"?"Cike da gansuwa Hannah tad'aga masa kai saida ya ja tsoki sannan yace ba abunda yashafe ni da tarbiyyarta, domin tsanarta ta dusashe duk Wani abu da yake tare da ita duk lokacin da na tuna cewa saura "2 weeks yarinya nan ta kasance matata sai naji na K'ara tsanarta bana tunani zan ta6a sonta.
Shiru Hannah ta yi tana kallonshi daga bisani tace Yaya Habeeb "So baya kwakwasa k'ofa kafin yashiga zuciyar d'a Adam ba kai ka keda iko da zuciyarka ballatana ka yanke hukunci shawara da zan baka ka sausauta wannan tsanar da ka ke yi mata kada rashe ya juye da mujiya "Habeeb ya yi murmushi had'e da Shafa sumar kanshi yace na fahimce cewa Hannah bakida hankali
Turo baki ta yi had'e da cewa ni ce banida hankali"?
Kwarai kuwa da kinada Hankali bara kifara tunani zan iya kamuwa da Son wannan "Illiterate girl karki manta naga kyawawa mata kala daban-daban masu ilimi da kyakyawa sura da Kansu suke kawo talla Kansu agareni ko kallo ba su ishe ni, ni Habeeb Lamido ace zan so "Illiterate ya kyabe baki had'e da yatsine fuska "never.
Hannah ta zaro ido har da su tafa hannu kai yaya Habeeb wannan sharri har ina "last year Haleesa ta gama secondary school ta kuma haddace Al-qur'ani shine za ka kira ta da "Illiterate
Habeeb ya tabe baki yakasa Furta komai daga bisani ya mik'e tsaye hannaye shi zube cikin aljihu wando shi yace Hannah mu je ki rakani unguwa saboda na gaji da sauraro wannan surutu naki.
"Cikin Zumud'i Hannah ta mik'e ina za mu je yaya Habeeb"?
Ba ruwanki da inda za. Mu je murad'i kawai ki d'auko mayafinki ki sameni a parking space ina jiranki batare da yajira jin abunda za tace yafice.
```HALEESA```
Haleesa kwance a d'akinta photo Marigayi yaya Habeeb manne a k'irjinta sirirai hawaye na fita ta gefe da gefen idonta ta yi nisa sosai a tunani rayuwarsu ta shagaltu iya shagaltuwa Sam bata ji motsin shigowar Aunty Juwairiyya wance ke tsaye rik'e da "curtain d'in k'ofa tana mata kallon tausayi sake la6ulle ta yi tak'arso ta zauna a gefen katifa a hankali ta d'ora hannaye ta a k'afafun Haleesa a firgici tad'ago ganin wance bata yi zato gani ba yasa ta mik'e zaune da sauri ta share hawaye da tafin hannu muryarta na rawa tace sannu da zuwa Aunty Juwairiyya saukar yaushe"?
Hannuta Aunty Juwairiyya ta rik'o a sanyaye tace yanzu nan daga "Airport kaitsaye nan driver ya ajiye ni ban ga kinfito kin yi min oyoyo na tambaye Ammi kina ina sai tace da ni kina d'aki a kwanaki nan tarasa gane kanki"
Haleesa ta sada kai k'asa tana kallon hannuta da ke sark'e da na Aunty Juwairiyya hawaye da take k'ok'ari boyewa suka zu6o akan hannun Aunty Juwairiyya a d'imauce Aunty Juwairiyya tad'ago fuskarta Haleesa! Shiru Haleesa ta yi bata amsa ba Haleesa! Aunty Juwairiyya tak'ara kiran sunan nata
"A wannan karo ta amsa da cewa Na'am"
Wannan wace irin rayuwa ce kika za6awa kanki shin me yasa har izuwa yanzu kika k'asa raba zuciyarki da soyayya yaya Habeeb"?
Bata jira amsar da Haleesa za ta bata tacigaba da cewa Haleesa Wanda ya mutu ba ya dawowa ballatana ki saka aranki cewa wata rana Yaya Habeeb zai dawo gareki hankuri za ki yi ki cigaba da yi masa addu'a ki tuna Haleesa aure za ki yi gidan wani za ki tafi, kinga kenan ko ta karfi tsiya ne dole ki manta da yaya Habeeb ki yi yak'i da zuciyarki tafitar da soyayya Yaya Habeeb Karki manta inna mairo ita ce ta yi kayan cikin Habeeb wata Tara da kwana tara tasha zafi da rad'ad'i nak'uda shi ta haife shi ta bashi kyakyawa kulawa har ya kai muzali girma ya zama abun sha'awa har kika ganshi kika bashi babban matsayi da shi a zuciyarki duk duniya babu Wanda yafi Uwa son d'ata amma ta hakura da rashinsa domin tasan cewa Ubangiji da yabata shi a lokacin da yaga dama shi yakar6i abinsa ke Haleesa me yasa bara ki hank'ura ba"?
Ki yi gaggawa yak'i da zuciyarki tun kafin ta raunata miki imani ki in har ban yi kuskure a lissafi na yau wata 7 har da Sati biyu da rasuwa yaya Habeeb amma ke a kullum mutuwar shi sabuwa take zame miki wannan wane irin rayuwa ne"?
Ki sani aure ba abun wasa bane muddin kika ce irin wannan rayuwa za ki gudanar a gidan mijinki bara ki ta6a Jin dad'i.
Haleesa tafashe da kuka tafad'a jikin Aunty Juwairiyya ta k'ank'ame ta cikin shassheka kuka tace ban yi kaina bane Aunty Juwairiyya zuciyata tace takasa hank'ura da soyayya yaya Habeeb, amma insha Allah zan yi k'ok'ari na danne duk wani abu da nakeji akan yaya Habeeb Aunty Juwairiyya ta d'agota had'e da cewa oya share hawaye ki banaso na k'ara gani idanu ki da hawaye kinji koh"?
Haleesa ta yi murmushi ta bi umurni Aunty Juwairiyya ta hanyar share hawayeta Aunty Juwairiyya na rik'e da hannuta suka fito d'akin Ammi suka shiga anan Haleesa takeji Juwairiyya da Ammi suna zance lefenta da dangin Habeeb Lamido za su kawo da Yamma Haleesa tadafe k'irji tasoma Zance zuci shikenan ba makawa na yi kusa zama mallaki Habeeb Lamido.
```5:30pm```
Tsadad'i Motoci ne ke ta fama parking a k'ofar gidan Malam Usman mai kifi kallon d'aya za ka yi wa motoci, kagano mamallaka motoci sun ci sun sha sun tada kai da Naira Kaitsaye mata suka dinga fitowa daga ciki motoci suna shiga gidan Malam Usman mai kifi daga bisani Wasu kartti majiya k'arfi suka fito da ratsatsu trolley's suna shiga cikin gidan dangin Haleesa sai faman karama b'akin nasu sukeyi ta hanyar nuna musu wurin zama, a hankad'e Hajiya khareema take kallon Mutane gidan da kyar ta dosana duwawu ta akan farar kujera roba ta zunguri Hajiya batula matar k'anin Mahaifin Habeeb ta Wani yatsine fuska had'e da cewa Hajiya batula ta ya ni figa Saida Hajiya Batula ta kya6e baki daga bisani tace Uwar miji ta Zama kaza anyya kuwa Madam Hindu tana ciki haiyyaci ta da ta amince Habeeb ya aure 'yar Matsiyata ni da naga Wannan uban lefe na yi tsanmani 'yar Governor ko 'yar Minister ce yake nema ashe 'yar gidan babu ce Wannan ae asara ce da rashin sanin zafin kud'i
"Bari kawai Hajiya Batula tun lokacin da muka tunk'aro unguwar nan bak'i ciki da takaici suke nuk'urkusa zuciyata Jin nakeyi kamar na hadiye zuciya na mutu don takaici ba rok'a da ban yi wa Madam Hindu ta tilaswa Habeeb ya aure Maryam ta Maye gurbi marigayiya Salma Amma 'yar mata nan ta yi biris da buk'ata ta ke in tak'aita miki labari sai cewa ta yi ita bara ta yi wa ta d'a aure dole kinga ba ta yi masa dole ba shi kuma ya kwaso mata 'yar Matsiyata duk abunda suke fad'a akan kunnen inna mairo gani abun naso ba mai k'arewa bane ta mik'e tsanm tabar musu wuri.
Bayan dangin Habeeb da na Haleesa sun gaisa a tsakaninsu daga bisani dangin Habeeb suka gabatarda da abunda ke tafe da su yayinda dangin Haleesa sukayi musu sha tara na arziki suka baro gidansu Haleesa cike da Murna irin karamawa da akayi Musu sa6ani Hajiya khareema da ta dawo da mummuna k'udiri ko ta Wane sai tashigar da 'yar ta gidan Habeeb.
```8:30pm```
Aunty Juwairiyya da Zainab zaune a d'akin Ammi sun tusa lefen Haleesa gaba suna kallon sai faman santi da yaba kayan suke yi sa6ani Haleesa da ke kwance rub da ciki akan gadon Ammi ita ba kuka take yi ba amma a yadda takeji Zuciyarta na tarfafasa gwara ta yi kuka ko za ta same sausauci k'unci da take ciki babban bak'i cikinta bai wuce yadda Mutane Unguwa har ma da na cikin gidansu suke zuzuta kayan lefe ta basu San cewa a wurinta atamfar super prints ta fiye mata tarin kayanan Zainab tace Haleesa bara ki sauko ki taya mu ganin wannan abun arziki ko kunya kike ji kada Ammi tace bakida kunya tak'arasa magana cikin tsokana
"Cikin zafin rai Haleesa ta diro k'asa ta tsalleke kayan tafice Zainab da Aunty Juwairiyya suka bi ta da kallon, girgiza kai Aunty Juwairiyya tayi tana mamaki tauri kai da kafiya irinta Haleesa.
```1 WEEK LATER ```
Tuni gidaje biyu sun fara gudanar da tsare- tsare yadda bikin aure 'ya'ya su zai gudana tsawon wannan lokacin Habeeb da Haleesa ba su k'ara gani Junansu.
Haleesa na zaune bisa kujera 'yar tsuguno a tsikiyar gida tana yanka alayahu almajiri ya yi sallama Haleesa ta amsa masa yace wani mai mota yana sallama da Haleesa a k'ofar gida, ras gaban Haleesa yafad'i nan take annuri da ke kan fuskar ta ya gushe tace je kace batanan
Ammi ta lek'o daga cikin kitchen ta ce je ki kace gatanan zuwa tajuya wurin da Haleesa take zaune ta galla mata harara had'e da cewa me kike Jira ne da bara ki tashi ba da sauri Haleesa ta mik'e ta jefar da wuk'a hannunta Ta Shiga D'aki tasaka Hijab tafito fuskarta ahad'e tanufi k'ofar gida dafe k'irji Haleesa ta yi sakamako motar Habeeb Lamido da ta ganin nan take Numfashinta yafara kai da kawo ta runtsi idanuta...
Jeeddah Aliyu🌹
[10/24, 11:44 AM] +234 813 417 9191: [11/10 6:25 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```60```
Jiki a sa6ule tak'arasa fita Wannan karo ma Bala ne yafito daga cikin mota yak'araso wurinta "Barka da fitowa ranki yadad'e"
Yauwa Bala ya gida"?
Lafiya Qalau ya hidimomi biki"?
Shiru Haleesa ta yi had'e da sada kai k'asa gani yadda ta yi yasa Bala ya yi murmushi yace ba fa ni kadai bane tare nake da "Boss'
Wani fad'uwa gaba Haleesa tak'ara ji tsanani tsoro ya lullu6e ta tamkar mai ciwo hak'ora ta bud'e bakinta tace Bala kace da shi yak'araso ciki ranar ma da na tsaya da shi a k'ofar gida saida Baffa ya yi Fad'a "Bala yace okay ba matsala bara na yi masa magana Bala yanufi wurin mota ya bud'e k'ofar da Habeeb yake Zaune fuskarshi ahad'e ba bu annuri ko misk'arazairatil a tare da shi da alama zuwan sa na dole ne "Boss tace ka shigo daga ciki saboda Baffanta bayaso tsayuwa a k'ofar gida"
A harzuk'e Habeeb ya ke kallon Bala daga bisani yace banida buk'atar shiga gidansu don haka za ka iya bata dalilin zuwa na gidansu"
Ka yi hank'uri "Boss ka daure ka k'arasa daga ciki karka manta ko yanzu kafin mu zo gidanan irin Fad'a da Madam ta dinga yi ta nuna 6aci ranta k'arara a dalilin rashin waiwaye Haleesa da ka yi Yakamata ace ka danne duk wata k'iyayya da ka ke yi mata saboda saura d'a k'ank'ani lokacin ta zama mallaki ka in tashigo gidanka kana da iko yi mata duk abunda ka ga dama ba bai hanaka saboda ikonka ce.
Habeeb yadage gira sama yana duban Bala cike da gansuwa da kalaman Bala yasaki tsadade murmushinsa mai narkar da Zuciyar 'yan mata
Haleesa nagani Bala na musu-musu da baki da alama magiya ya ke yi wa Habeeb haushi ya turnuk'e ta ta juya cikin gida tana shigawo ta ci karo da Ammi sai kawai tace Ammi Key's d'in d'akin yaya Salman za ki bani batare da Ammi tace da ita komai ba tashiga d'aki tadauko mata Key's ta mik'a mata a sanyaye Haleesa tak'ara juyawa k'ofar gida tana fita taci karo da su a bakin k'ofar shigowa Zaure ba shiri ta taka birki had'e da sunkuyar da kai Kallo d'aya Habeeb Lamido ya yi mata ya d'auke kai tsawon "5-6 minutes suka dauka a tsaye daga bisani Haleesa tanufi d'akin yaya salman ta bud'e k'ofa tajuya batare da ta bari sun had'a ido tace "Bissimillah! Banza Habeeb ya yi kamar bai ji abunda tafad'a "Bala yace Boss ka k'arasa daga ciki bara na je na fito da kayan da ke cikin mota Wani tsuke baki Habeeb ya yi kamar mai tsotsa "Sweet ko mai shiri d'aukar selfie ya yi kici-kici da fuska, yajuya ya kalle d'akin yaya Salman Wanda tuni Haleesa ta tsofa a ciki tana jiranshi ya ta6e baki yanufi d'akin batare da yacire "cover shoe d'in k'afarsa kawai yadanna kai Haleesa na Zaune akan kujerar roba kanta na sunkuye tana wasa da yatsu hannunta ''Ba don sani daraja da sallama da ke ita a musulunci da ba yadda za'a yi ya yi mata sallama"
"Assalamu Alaikum" yafad'a chan k'asan mak'oshi''
"Batare da Haleesa tad'ago kanta ta amsa mai masa da cewa "Wa'alaikum sallam warahmatullahi wabarakatih...''
Habeeb ya kya6e baki a zuciyarshi yace ka ji su Al-Sheikh za ki yabawa aya zak'i ta in kika shigo hannuna 'ya nema mai kai Kamar dunk'ule "cabbage' ya ja ya yi tsaye Haleesa bata ce da shi ga wurin zama hakan ne yasa yacigaba da zance zuci tana nufi bara tace na zauna ba amma bara naga iya gudun ruwanta kafin na wanke mata allonta saboda naga kanta na hayak'i.
A fakace Haleesa tad'ago ta sace kallonshi yana nan tsaye k'ikan hannaye shi zube cikin aljihu wandoshi da sauri ta d'auke kai a zuciyata tace tofah wata sabuwa inji 'yan caca shi wannan mai tsawo kamar fol waya yana nufi bai ga wurin zama bane ko kuma duk cikin, salon tsabar kwarewa da wulak'anci ne amma bara nace ya zauna a karo na biyu da tasake d'agowa amma bata dube shi ba tace "please have a seat''
Zaro ido ya yi daga bisani ya gyatsine fuska kamar ya ga "cockroach a zuciyarshi yace "Humm! I can't believe this Illiterate girl she known how to speak English''
Ya dube kujera da ta nuna masa da yatsanta akwai tazara tsakaninta da wance ta ke Zaune yafito da "handkerchief fari kal daga gaban aljihu "black colour coat d'in da yake sanye da ita ya shinfid'a akan kujerar sannan ya zauna ya yi crossing legs nashi yafito da "phone in shi yafara buga "game in crush candy''
Haleesa ta cika ta yi dam! Me wannan mutumin yake nufi me ye laifinshi Haleesa ke yakamata ki fara gaida shi abunda d'ayan 6angare Zuciyata yace da ita kenan......."ina Wuni yaya Habeeb"? tafad'a cikin sark'ewa harafi"
"Ignoring nata ya yi saida d'auke almost 3-4 minutes sannan yace da ban Wuni ba kya gani saida ya furzar da zazzafa iska yacigaba da cewa ke! Wai me yasa a duk lokacin da na zo gidanku sai kin yi "Wasting time in na"?
Numfashi da Haleesa ta sauke yafi a kirga da kyar ta iya controlling in "temperature' ta Co's wannan karo guy nan yakawo ta k'ul tace am sorry Yaya Habeeb wallahi.....
"Shut up please don't give me that fucking excuse yak'arasa magana had'e da cigaba da buga game in shi girgiza kai Haleesa ta yi cike da takaici tafara zance zuci na Shiga uku ni Haleesa wannan wane irin aure ne zan yi"?
"Very slowly yafara magana Kin d'auki kanki Wata tsiya sai kace ana sonki sai wani jiji da kai kike ko kin manta kina gaban Habeeb Lamido ne Wanda ba ya gajiya da furta miki kalma ```Tsana``` amma da yake ke Heartless ce har Wani Jan aji kike yi na kuma San duk wannan abu da kike yi kina yi ne don ki burgeni ni mutum ne kaifi d'aya ban ta6a sauya ra'ayi na musanmman akan abunda nace banaso don karki yi tsanmani in na aure ki wata rana za ki same gur6i a zuciyata tun daga lokacin da kika shigo rayuwata na nemi farin cikina narasa bana sonki wallahi na tsane ki tsanar da bara ta6a gushewa daga Zuciyata yak'are magana