Showing 120001 words to 123000 words out of 132766 words

Chapter 41 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87938

murya yace 'yan mata na kawo ki gida amma kisani zan yi kewarki sosai na tabbata da kyar ne Daren yau na iya bacci.
Cikin tsokana Haleesa tace ni kuma ga ka ba abinda zai hanani bacci har da minshari.
"Murmushi Habeeb ya yi yada'go fuskarta cikin idanunta yake kallo da sauri ta runtse idanu nata ki bud'e idanunki ki kalle ni kice ba za ki yi kewana ba.
"Turo baki ta yi ni ka kyalleni na tafi tun kafin mom tadira gidanan asirinmu yatonu.
Iskan bakinshi ya hura mata akan fuskarta, babu shiri ta bud'e idanunta murmushi ya saki mata can! K'asan mak'oshi ya furta da gaske ba za ki yi kewana ba"?
Lamgwa6e kai ta yi kaima kasan da wasa nake.
"I know baby yadda ki ka saba kwanciya anan wurin yanuna k'irjinshi da yatsa yau za ki kwana a mattress dole ki yi kewana yak'arasa magana had'e da kashe idonshi d'aya.
"K'irjinshi tadaka da hannunta Uhm... Ni ban iya abunda ka iya ba.
"Dariya ya yi karki damu I'll teach you kema ki iya make kafad'a ta yi ni bud'e mun k'ofa na fita.
"Zuciyarshi na bugawa ya bud'e mata k'ofa har ta zura k'afarta guda k'asa ya riqon hannunta promise me da kin shiga gida za ki switch on phone naki"?
Kai ta gyad'a ya sumbace hannunta I love you Leesa"
Ta yi fari da idanu I love too badan yanaso ba yasaki hannunta har ta fita sai kuma tak'ara leqawa cikin mota peck tasaki mishi a lips kamar jira yake ya chafke lips d'inta da kyar yabarta ta tafi tajuya ya bita da kallo tana zuwa k'ofar da zai sada ta da cikin gida ta yi tsaye had'e da waigawa yana cikin mota yana kallonta peck ta yi a hannunta ta hura mishi da sauri ya lumshe idanu cikin yad'aga murya yace _I LOVE YOU LEESA_ dariya ta yi tajuya tak'arasa shiga cikin gida Habeeb yaja mota yafita zuciyarshi cike da so da k'aunar Leesa.
"A Main parlour Haleesa tarrarda Hannah zaune tana kallo, da gudu tafad'a jikinta cikin nishad'i suka rungume juna Haleesa tafara janye jikinta ta gyara zamanta had'e da yaye veil ta jefar tace kai Hannah ba abunda yakai soyayya dad'i musanman in ka had'u da Wanda iya ta.
Hannah ta zaro ido ta saki baki da hanci tana kallon Haleesa.
"Haleesa ta d'auki remote tarage volume d'in tv tace Hannah ashe yayanki bala'i ne a soyayya"?
Hannah ta kyalkyale da dariya tace bani nasha 'yar uwa.
"Kallon sama da k'asa Haleesa ta yi mata me zan baki kisha"?
Kanun labarai mana domin da alama yayana yatafi da zuciyarki.
"Sirrin mata da miji zan baki kisha eh! Lallai kuwa Hannah bakida hankali.
Dariya Hannah tak'ara kyalkyalewa da ita nima fa remain 2 month na bi ayarinku.
"To ae sai ki jira har ki bi ayarin namu sai na daura miki lecture amma fa gaskiya Hannah ba karya yayanki ya yi tak'arasa magana tana dariya.
''Duka Hannah takai mata karki cinye mun d'an uwa.
Haleesa ta mik'e bari na dauko phone d'ina na kira yayanki naji lafiyarsa.
Yanzu-yanzu nan ku ka rabu kira na me"?
Dariya Haleesa ta yi ko na fad'a miki ba za ki gane ba Hannah tana magana ne had'e da juyawa.
"Lallai yaya Habeeb ya yi nassara tafiya da zuciyarki.
"Ba zuciyata kadai yatafi da ita ba har gangar jikina tana tare da shi.
''Hannah ta yi shewa tana tafa hannaye Haleesa ta kad'a kai tak'arasa shiga bedroom.

_3 hour's later_

Madam Hindu tana zaune a parlour tana sauke gajiya Haleesa da Hannah suna zaune a gefenta ta dube Haleesa tace ina fatar da ba nan son bai zo gidanan ba"?
"Haleesa da Hannah suka dubi juna sai wani wuk'i-wuk'i suke da idanu sai kace munafukai madam ta katse musu hamzari ta hanyar cewa da alama ya zo koh"?
"A rikice Haleesa tashiga girgiza kai Hannah ta yi karaf tace mom ya za'ayi ya zo bayan kinsan Haleesa bata bashi fuska.
"Haleesa tasauke ajiyar zuciya madam tace da kyau haka nakeso karki sake ki bashi fuska, har sai yak'are watani shi so nake yad'and'ani illar da miskilancin yake haifarwa Haleesa dai sai faman gyad'a kai take yi kamar k'adangarwa.

_9:00PM_

Haleesa na tsaye tana saka sleeping dress d'inta Hannah kuma na kwance akan gado, Haleesa ta gama abinda take yi taciro wayarta daga charging ta hau gado ta kwanta ta yi dialing number Habeeb ringing 1-2 ya yi received cikin muryarshi mai matuk'ar dad'in gaske ya furta _Hello_
"Saida Haleesa ta lumshe idanu sakamako yadda muryarshi ta haddasa mata kasala cikin shagwa6a tace _Hi my handsome Don ka manta da ni koh"?_
"Habeeb da ke kwance akan 3 seater ya gyara kwanciya yak'ara dafe phone _in har zan iya mantawa da kaina to tabbas zan manta da ke cikin 'yan awani nan da rabuwar mu Leesa baki ga yadda nadawo ba_
Ni ma baby nayi missing naka sai yanzu na k'ara tabbatarwa sonka ya bi jinin jikina.
Habeeb ya ja iska had'e da fesarwa Leesa in har da gaske ki ke yi kin yi missing d'ina me zai hana ki bani dama gobe da sassafe na sanarda sweetheart kin janye sharad'inki za ki dawo gareni.
"Haleesa ta yi ajiyar zuciya had'e da cewa......

_I'm sorry fans jiya banida lafiya datz why ban yi post ba ina bara addu'arku😪_

Jeeddah Aliyu🌹
[10:47PM, 21/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [21/12 2:37 pm] J: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```97```

~~Ban amince ba sai ka yi hak'uri har watani 3 su cika ni kuma nayi maka alqawali koda mom batace nadawo ba zan baka izzini ka zo ka yi mata magana, amma gaskiya yanzu Uhm...Uhm...in fact 2 weeks kawai ka yi.
"Ajiyar Zuciya Habeeb ya yi shikenan Leesa tun da haka ki ka za6a mana amma inason kisani hakan ba k'aramin cutar da ni yake yi ba.
"Ae ba kai kadai yake cutar wa ba nima inajin jiki daurewa kawai nake yi
Hum....fad'a kawai ki ke yi Leesa da rashina yana cutar da ke da ba Ki bijiro da wannan buk'ata ba don haka mu ajiye wannan zance a gefe d'aya domin cigaba da yi sa zai iya 6ata mun rai.
"Murmushi Haleesa ta yi da yafi domin nima ba amincewa zan yi da buk'atarka ba.
Wannan kuma ke ta Shafa ni nasan yadda ki ke sona "you can't live without me za ki gaji da shirme ki ne kidawo gareni.
''Oho!..tun da kasan da haka miye na wani dauko zance"?
Lumshe idanu ya yi kamar ba za yi magana ba daga bisani ya shafi sumar kanshi, saboda inasonki Leesa, nisanta daga gareki zai iya haddasa mun gagarumar matsala.
''Nima inasonka yaya Habeeb so da baki ba zai iya misalta shi ba amma kasani ba zan dawo gare ka ba har sai nan da wata uku.
"A tak'aice duk yanda Habeeb yaso ya shawo kan Haleesa cikin sauk'i abin ya fask'ara ta tsaya kai da fata ita lalle-lalle sai yacika watani 3 ko za ta dawo gidanshi daga karshe ma sai suka rabu baran-baran kawanensu ya aje waya a fusace.
"Hannah da ke kwance a gefen Haleesa ta kwashe da dariya lovebirds ya haka ashe za Ku iya fad'a da junanku"?
Mtsww.....Haleesa ta ja tsaki Hannah yayanki Zuma ne sai da wuta har abada ba zai daina wannan d'abi'a nashi na sauri d'aukar abu da zafi ba.
"Tabe baki Hannah ta yi tace ae ba zai daina ba saboda a jininsa yake.
Ae kuwa yana tare da aiki Haleesa tafad'a had'e da make kafad'a.

```HABEEB```

Yana gama waya da Haleesa ya ji a ranshi zai nisanta kanshi daga gareta har wa'adin da ta deba masa yacika a washe gari ya tattara kayanshi ya yi kaura zuwa Lagos har yadira a Lagos bai nemi Haleesa ba yayinda ita ma bata nemi shi ba su dole fushi suke yi da juna.

_5 day's later_

Habeeb yagaji da shan k'amshin sa yakira Haleesa a lokacin tana zaune a parlour ita da Hannah madam kuma tafita she's always busy saboda lokacin bikin Hannah da yakarato.
''Saida wayar ta yi kusan tsinkewa sannan Haleesa ta d'aga adak'ile tace _Hello_
"Leesa kina mun wulaqancin ko don kinga ina sonki ne"?
_sarkin korafi ae ka jira mu gaisa kafin kafara kwararo min k'orafin naka"?_
Haka ma za ki fad'a"?
_Nop...kawai naga dacewar hakan ne amma in bakaso gaisuwa nawa sai na rik'e abina_
"To ki rik'e abarki banaso kin damu da ni ne da har za ki gaida ni"?
_Hum....ni kuwa na damu da kai_
''Kin damu da ni miyasa ba ki nemi ni ba"?
_saboda kana fushi da ni kuma iya sanani bansan nayi maka laifi ba_
"Murmushi ya yi yanzu dai na d'auki laifina tun da gashi na kira ki sai kuma ya canza zance, ta hanyar cewa Leesa nayi missing naki fa Allah da kyar nake iya bacci.
Dariya Haleesa ta yi my handsome Don kenan ko za ka zo ne mom tafita daga ni sai Hannah ne kadai a gida"?
"Iska ya ja kamar ba zai yi magana ba daga bisani yace ke ni fa ina Lagos tun washe gari da ki ka 6ata mun rai na baro abuja.
''Shikenan ka yi wa kanka
"Habeeb ya yi dariya bani kadai na yi wa kaina ba ke ma kinyi wa kanki, saboda kin yi missing gani kyakyawar fuskata.
_Uhm....kamar yanda kaima ka yi missing gani kyakyawar fuskata ba_
"Zancenki ba karya Leesa ke kyakyawa ce ga kyau fuska ga kuma kyau hali shiyasa duk lokacin da na tuna da ke sai na godewa ubangiji da albarkace ni da samun ki.
Ajiyar zuciya Haleesa ta yi yayinda Habeeb yacigaba da kwararo mata zazzafan kalaman soyayya daga bisani yake sanarda ita gobe Imaan za ta dawo Haleesa tadinga ihun murna saboda ta yi kewar Imaan ba kad'an ba gani yanda take ihu yasa yace ke in gama ihunki anjima zan kira ki kafin Haleesa tak'ara magana har ya yi hanging up.

_washe gari_

Maryam tadira garin Abuja tare da Imaan kyakyawar tarba Haleesa da Hannah suka yi mata kasa sake jiki ta yi sai wani d'ari-d'ari, take saboda kunyar Haleesa take ji musanman in ta tuno da yankar k'auna da ta yi wa akan Habeeb sai gashi kuma za ta aure d'an uwan Haleesa da kyar Haleesa ta shawo kanta tasaki jikinta suka sha hira Hannah na tsokanar maryam ta hanyar cewa kishiyar Haleesa ada matar yayan Haleesa a yanzu kwanan Maryam 2 a abuja ta juya Yola.
Tsakanin Habeeb da Haleesa saidai su yi waya yini Haleesa take bata fito parlour ba tana d'akin k'unshe tana zuba wayar soyayya da Habeeb a kwana a tashi asarar mai rai gashi har Habeeb ya yi cinye watani 2 daga cikin watani 3 har tsawon wannan lokacin Habeeb bai tako k'afarsa Abuja ba a bisa alqawalin da yadaukawa kanshi ba zai k'ara zuwa inda Haleesa take ba har sai wa'adin watani 3 sun cika.
Lokacin bikin Hannah yak'araso wannan yasa madam ta tattaro su Haleesa suka nufi garin Yola saboda anan za'a gudanarda shagalin biki.

Ranar yau ta kasance ranar da za'a yi kamun Hannah su Haleesa manyan k'awaye amarya ansha makeover,ta yi matuk'ar kyau tayi fari tass kamar kata6a skin d'inta Jini ya zubo ga wata 'yar uba 'kiba da tayi ita kanta tana mamakin wannan 'kiba da tayi sai ana washe gari daurin aure Habeeb yadira a Yola lokacin da ya Kira Haleesa ya sanarda ita ya iso ta yi mishi girki mai dad'i zai zo anjima ya ci a rikice tace Dan Allah _my handsome Don_ ka yi hak'uri karka zo saboda banaso mom tagano akwai wata alaqa tsakanina da kai za ta d'auke ni maras kunya.
ran Habeeb ya yi matuk'ar 6aci gani yake yi duk wannan abun da Haleesa take yi tana yi ne don ta k'untatawa rayuwarshi ya tana matsayin matarshi sannan za ta haramta mishi zuwa inda take a bisa wani banza dalilin nata a harzuk'e yace wai Leesa mekika d'auki kanki ne huh"? Ko don kinga ina hauka sonki ne shiyasa ki ke mun yanda ki ka ga dama"? Idan ki ka dama in watani 3 suka cika karki dawo gidana ki cigaba da zamanki wajen sweetheart ki gani zan mutu ne ko zan yi rai batare da ya jira abunda za ta fad'a ba ya kashe waya.
"Haleesa ta yi sororo da waya a hannu tarasa mafita takasa
zaune takasa tsaye bakin rai mijinta takeso gani kamar yanda shima yake da Muradin so ganinta watani biyu kenan rabonsu da ganin Juna.
"Ta rafka tagumi jikinta ya yi mugun sanyi kuka takeso yi amma tana tsoro kad'a wani ya ganta tana kuka ya tambaye dalilin kukan nata saboda gidan cike yake da 'yan biki tana cikin Wannan halin Hannah tashigo tadafa kafad'arta what's wrong Mrs Lamido naga kamar kina ciki damuwa"?
''Ajiyar zuciya Haleesa ta yi NI DA YAYA HABEEB ne yanzu nan muka gama waya kinsan halinshi na sauri d'aukar zafi akan abu qalilan ya isheshi fushi tacigaba da ba wa Hannah labari abunda yafaru a tsakaninsu.
''Tsaki Hannah ta ja yakamata zuwa wannan lokacin Haleesa ki daure ki ba wa mijinki dama ya zo ya ga mom ki koma gidanki kisani duk wannan horo da mom take yi wa yaya Habeeb tana yi ne saboda ke da kin furta kin janye sharad'in naki shikenan nan take za ta amince ki koma amma wannan zaman da ki ke yi anan amfani me yake qara ki da shi"? ba za ki gane kinyi wauta ba sai natafi na barki mom ba zaman gida take yi ba za'a barki gida daga ke sai Housemaid ki bi umarnin mijinki ko don saboda aljannarki kitashi yanzu nan ki shirya kitafi wajen mijinki in kin je can! Kya masa girki duk da nasan ba girki yakeso ba kawai dai yafake da sabara ne ya harbi barewa tak'arasa magana tana dariya.
"Haleesa ta rausayar da kai gefe d'aya to in ba girki yakeso ba me yakeso sarkin fassara"?
''Dariya Hannah tayi Oho! Ni ma bansaniba amma na tabbata amsar wannan tambaya tana bakin _handsome Don_
Mtcww....Haleesa ta ja tsaki ke dai kin zama 'yar iska wallahi tun kafin mu kai ki gidan Mus'ab kin lalace.
"Hannah tak'ara kyalkyalewa da dariya
Hannunta Haleesa tarik'o Hannah please kidaina wannan dariya kinemo min mafita.
"Hannah ta kad'a eyes ball d'inta mafita guda d'aya ce kitashi mu je na yi dropping d'inki wajenshi in yaso Ku nemawa kanku mafita
[21/12 8:10 pm] J: Idanu Haleesa ta zaro cab! da sake wai ayi wa mai dame d'aya sata gaskiya Hannah ba zan iya ba so ki ke mom tagano, ta dinga yi min kallon marar kunya da kawaicin.
"Harara Hannah ta zabga mata wai ke da kin bud'e baki sai kice kunya, kunya shin wai yaya Habeeb ba mijinki bane ko kuma zuwa wajenshi da za ki yi ya sa6awa mahalicinki"?
"A sanyaye Haleesa ta girgiza kai Hannah tak'ara jefata cikin rud'ani ba tunani za ki yi ba kitashi mu tafi, Hannah ta katse Mata hamzari.
Haleesa ta mik'e tsaye to amma kuma Hannah ta ya ki ke gani zan fita gidanan har nadawo batare da tasani ba kina gani har tambayarta nayi zan tafi na gaida su Ammi tace na jira har agama Shagalin bikinki.
''Hannah tace karki damu ni nasan abunda zan yi har ki dawo batare da mom tasan kin fita ba.
"Haleesa ta kad'a kai tanufi trolley d'inta taciro Riga da skirt na Swiss lace red colour mai touch d'in white tacire kayan jikinta tasanya lace d'in rigar ta yi tight d'inta musanman k'irjinta tajuya wajen Hannah tace Hannah dubi yanda k'irjina, yaciko nifa wannan k'iba yafara damu na tak'arasa magana tana yatsina.
''Hannah ta kyalkyale da dariya tace yarinya kinsame lafiya.
Tsaki Haleesa ta ja wane irin lafiya"? Haka kawai mutum yadinga kumburi kamar flour tana magana ne had'e da fesa perfume ta zari white veil d'inta I'm ready mu tafi koh"?
Hannah tace Yeap! Ta wuce gaba Haleesa na biye da ita direct parking lot suka nufa Hannah ta kwadawa sa'eed driver kira da gudu sa'eed yak'araso key d'in wace mota ne hannunka"?
"Na Kia cerato ne"
"Okay bani key d'in
Ciro key d'in daga aljihunshi ya yi ya mik'a mata ta kar6a tanufi wajen motar Haleesa ta bud'e k'ofa tashiga Hannah ta yi wa motar key ta ja suka nufi gate maigadi ya bud'e musu gate suka fice.
"Hannah tajuyo ta dubi Haleesa tace gobe insha Allah nima zan bi sahunku ba za k'ara yi mun wani gani-gani ba tak'arasa magana tana murgud'a baki.
"Tabe baki Haleesa ta yi had'e da cewa Allah ya shirye ki Hannah banta6a gani amarya mai zumudin aure irinki ba kafin Hannah ta bata amsa phone d'in Haleesa ya yi ringing.
"A kasalance ta bud'e purse d'inta taciro wayar gani Wanda ke kira yasa tasaki sanyaye murmushi ta yi receiving call takara a kunnenta ta yi shiru tana murmushi.

_HABEEB_

Habeeb da ke kishingid'e a parlournshi, yana dafe da waya a kunnenshi jin Haleesa ta yi shiru ba ta yi magana ba yasa ya ajiye zafin kanshi a gefe, yace _Leesa na yi fushi a maimakon ki kira ni ki bani hak'uri sai ki ka nuna mini halin ko in kula koh"?_
"Huh.... Yaya Habeeb kenan to ni wane laifi na yi maka da zan baka hak'uri"?
Dai-dai lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login