Showing 129001 words to 132000 words out of 132766 words
Haleesa tana cin d'an wake tana gyad'a kai alamar da ke nuna ba k'aramin dad'i ya yi mata ba.
Haleesa tacinye d'an wakenta Tass...ta sud'e plate ta yi gyatsa.
Basu baro gidan ba saida baffa yadawo farin ciki sosai baffa ya yi da ya ga Haleesa Sai around _9:00pm_ suka suka yi sallama da baffa da Ammi.
"Habeeb ya yi parking dai-dai _Ni da yaya Habeeb tailoring center_ a rikice Haleesa take kallonshi hannunta yarik'o Leesa mu je ki ga shagonki da kanshi ya bud'e mata k'ofar mota tafito suka shiga shagon yaran da ke shago suka shiga gaida Habeeb Hasheem yace _sannu da zuwa Boss"_
''Yauwa Hasheem ya aiki"?
"Alhamdulillah boss!
Yau dai ga big boss d'inku na kawo muku Habeeb yak'arasa magana had'e da kallon Haleesa.
''Murmushi Haleesa ta yi ta dubi hasheem tace chief tailor da fatan baka had'a go slow a shago"?
Harararta hasheem ya yi yace ke kuma yaushe ki ka yi baki"?
Karaf d'aya daga cikin yaran shagon Wanda tun zamani margayi Habeeb yake zaune a shagon mai suna shamsu yatarewa Haleesa ta hanyar cewa dama can! Tana da baki Kaine ba ka gani.
"Habeeb yace kyalleshi kawai shamsu, idan bai daina tsokanar matata ba sai na yi mishi tsiya ta hanyar d'auke shi shagonan na mayarda shi Lagos dama gashi yafara soyayya shiyasa yake lalacin a shago.
Gaba d'ayansu suka yi Dariya Habeeb yarik'o hannun Haleesa ya kalli Hasheem yace idan da akwai matsala ka kirani a waya da haka suka fita daga shagon.
"Kan hanyarsu na zuwa gidan madam Hindu Haleesa ta mayarda hankalinta wajen Habeeb cikin sanyi murya tace nayi mamaki yanda ka gyara ni da yaya Habeeb tailoring center musanman yanda nasan kana kishi da ainihin mai shagon tak'arasa magana had'e da sadda kai k'asa.
"Murmushi Habeeb ya yi hannunshi d'aya yasa yarik'o hannunta yayinda d'ayan hannun nashi yake rik'e da steering yace Leesa na farfad'o da wannan shagon ne a dalilinki ba zan manta ba wata rana na nasame salman a shago na gaya mishi na bashi aiki a company na har nake tambaya wai meyasa suka sakawa shagonsu suna _NI DA YAYA HABEEB TAILORING CENTER_
Saida ya yi murmushi kafin yabani amsa yace a lokacin da za su bud'e shagon suna mahawara akan wane suna za su sanyawa shagon, kwatsan sai margayi Habeeb ya tambayeki sunan da yadace su saka da bud'an bakinki sai ki ka ce _NI DA YAYA HABEEB_ a dalilinki sunan shagon yasamu asali, yace saidai ahalin yanzu suna fuskanta na rashin customers a dalilin telolinsu sun tsofa kullum cikin gyara suke wannan matsala ita takesa su d'auki dogon lokacin basu gama d'inki yayinda customers suka danganta hakan da rashin cika alqawalin shiyasa shagon ya duk'ushe Wanda suna daf da rufe shi, ni kuma tun daga lokacin da salman yabani wannan labarin na k'udurta sai na faranta miki rai ta hanyar fad'ad'a wannan tailoring center a halin yanzu na bud'e miki tailoring center har guda 3 d'aya a Abuja akwai wani a Lagos anan Yola kuma akwai guda d'aya indan ki ka had'a da na unguwarku guda 4 kenan burina Leesa _NI DA YAYA HABEEB TAILORING CENTER_ ya yi suna a fad'in Nigeria shiyasa na nemo kwararin mad'unka daga Senegal na zuba a tailoring center d'in duk karshen wata nake kar6a k'udin da suka tara nayi matuk'a mamaki a last month kudin da suka bani a matsayin na aikin da suka yi na wannan wata kud'i ne masu yawan gaske tun lokacin na tabbatar da d'inki babbar sana'ace ta hannu sai na yanke shawara na dinga shigo musu da tsadadun textiles suna d'inka ready made ana siyarwa kwara d'aya Ana kuma siyarwa akan sari cikin d'an k'ank'anin lokacin na tara miki k'udi masu kaurin gaske a account dama inajira irin wannan rana ne na sanarda ke.
"Har Habeeb yadasa aya Haleesa na kallonshi hannunshi da ke sark'e da nata ta sumbata, na gode my handsome Don tabbas ka sanyani cikin farin ciki ba zan 6oye maka my handsome Don a lokacin da yaya Habeeb yarasu sai nake ganin kamar daga kanshi ba zan k'ara samun wani d'an namiji da zai so ni kamar yanda yake sona ashe wauta nake yi ashe za ka shigo rayuwata ka so ni fiye da son da yaya Habeeb ya yi mun, hak'ik'a zuwanka rayuwata alkhairi ne inasonka mijina Kaine abin alfahari na tak'arasa magana tana hawaye.
"Dai-dai lokacin da suka iso gidan madam Hindu Habeeb ya yi parking yakashe mota yad'ago fuskar Haleesa halshenshi yasa ya lashe hawayen fuskarta, Banaso na k'ara ganin hawaye akan fuskarki koda kuwa na farin ciki ne.
"Murmushi ta yi had'e da cewa your wishes is my command.
"Habeeb ya bud'e k'ofa yafito ya bud'e mata ita ma tafito suka nufi cikin gidan a parlour suka iske madam Hindu da aunty Mami da mugun mamaki madam take kallonsu daga bisani ta kawo karshen mamakin nata ta hanyar cewa Ku kuma daga ina"?
"Habeeb yashiga Sosa k'eya dama sweetheart Leesa ce nadawo miki da ita yayinda Haleesa ta sadda kai k'asa tana wasa da gefen hijab d'inta.
"Dariya madam Hindu da aunty Mami suka yi madam tace ae ni tuni na sallame Ku daga gidanan, cikin tsananin farin ciki Habeeb ya mik'e yanufi kujerar da madam take zaune ya rungume ta thank you my sweetheart you really make me happy you're the best Mom in the eye's of the would I love you so much mom muaah....ya sumbace kumatunta.
"Dariya madam ta yi ta shafi sumar kanshi I love you too son tashi ka d'auki matarka kutafi.
"Habeeb ya mik'e yana murmushi ya dubi aunty Mami yace lah......ashe aunty Mami tana parlour nan.
''Harararshi aunty Mami ta yi sai yanzu idanunka suka bud'e koh"?
Yana dariya ya matsa daf da aunty Mami yarad'a mata idan Leesa tana gaba na idanuna rufewa suke yi aunty Mami ina fa son yarinya nan sosai sonta yabi jinin jikina yak'arasa magana yana dariya.
"Zaro ido aunty Mami ta yi tana tafa hannaye da sauri Habeeb ya katseta ta hanyar _cewa aunty Mami karki fad'awa sweetheart it's secret between me & you_ aunty Mami da madam suka kyalkyale da dariya yayinda Habeeb yarik'o hannun Haleesa suka fita daga parlour.
"Koda suka iso gida _10:15_ agaugauce Habeeb ya had'a musu ruwan wanka suna fitowa daga wanka da kanshi ya shafawa Haleesa mai yasaka mata sleeping dress suna manne da juna bacci ya yi awon gaba da su.
*washe gari*
Sai around _11:30am_ Haleesa tafalka koda tashi har Habeeb ya yi wanka yashirya, yana zaune kusa da ita murmushi yasake mata ita ma ta mayar mishi da martanin murmushin nashi tasauko daga bed tanufi bathroom ta yi wanka tafito daure da towel Habeeb yatayata ta shirya cikin atamfar super Sheraton ta yi matuk'ar kyau ruwan Lipton kadai tasha Rarrashinta Habeeb yashiga yi haba! Leesa ruwan Lipton ba zai rik'e ki ba ki daure ki cin abinci mai d'an nauyi ko don saboda babynmu.
"Yatsine fuska ta yi kamar za ta yi kuka banaso yaya Habeeb in naci amai zan yi ni dai katashi ka kaini gidan Hannah maybe a can na iya cin abincin tak'arasa magana ciki shagwa6a.
"Da sauri Habeeb yatashi yadauko mata mayafinta suka fice a parlour suka iske Hannah kishingid'e tasha make-up tafito amarya sak cike da farin ciki ta rungume Haleesa cikin zolaya ta dubi yaya Habeeb tace Daddyn twins ina kwana"?
''Dariya Habeeb ya yi ke kuma twins ki ke mana fata"?
"Gyad'a kai Hannah ta yi yayinda Haleesa ta tabe baki had'e da cewa kwaji da shi Habeeb yace wai ina Mus'ab ne ko har yafita ne"?
"Murmushi Hannah ta yi tace yana kitchen watakila karar TV yahanashi jin muryarku.
''Zaro ido Habeeb ya yi me yake yi a kitchen"?
Breakfast yake had'a mana Hannah tafad'a had'e da kallon Habeeb.
Kyalkyalewa da dariya Habeeb da Haleesa suka yi mik'ewa Habeeb ya yi yanufi kitchen d'in yana mai cigaba da dariya tun kafin yak'arasa shiga kitchen ya hango Mus'ab yana tsame chips daga mai cike da tsokana Habeeb yace ango kasha k'amshi gaba d'aya ka d'umama gidanan da k'amshi.
"Mus'ab yajuyo ya dube Habeeb ya d'aure fuska uban me ka zo yi da sanyin safiya a gidana Lamido"?
"Habeeb yak'ara kwashewa da dariya me da wuk'a angon kitchen abincin amarya na zo ci abun mamaki sai na tararrada ango a kitchen amarya na hakince a parlour
[28/12 1:46 pm] aliyujeeddah: Wannan kuma wane irin Sabon system ne"?
"Mus'ab ya gallawa Habeeb harara cike da takaicin yace bansaniba yanzu kafad'a min muqasudin zuwanka gidana karka manta al'adace friends suna yi wa ango rakiya darensa na farko a gidansa sama da k'asa mun nemi ka muka rasa khaleel yakira ka a waya da ka d'aga kira me kace da shi"?
"A yatsine Habeeb yace cewa nayi da shi ni yayan amarya ne ba abunda zan je yi a gidanta.
''Hum.....To yanzu gayamun me yakawo ka"?
"Abincin ango na zo ci ko ba za'a bani bane"? Habeeb yak'arasa magana yana dariya murmushi Mus'ab ya yi yace ka dai anyi d'an iska wallahi karka manta Lamido ni fa in-law d'inka ne bai dace kana mun iya shege ba.
Habeeb yak'ara kyalkyalewa da dariya Haleesa ta dubi Hannah baki bud'e tace kai kamar fa sautin dariya yaya Habeeb nakeji"?
"Tabe baki Hannah ta yi ba kama bace shine watakila yana yi wa my love dariya don yaganshi a kitchen.
"Haleesa ta yi dariya tace in haka ne bari nima na leqa naga dariyar yaya Habeeb kinsan Allah idan yaya Habeeb yana dariya jin nake kamar na hadiye shi saboda yanda take mugun k'ara masa kyau. tak'arasa magana had'e da mik'ewa tanufi kitchen girgiza kai Hannah ta yi tace Allah ya yi miki sauki Haleesa ta mik'e da kyar tabi bayan Haleesa.
Kai,kai Kai, Haleesa tafad'a had'e da zaro ido me nake shirin gani Mus'ab yaushe ka zama chef"?
"Kafin Mus'ab yabata amsa Hannah tariga shi ta hanyar cewa ka ga my love kyallesu kawai ae gwara kai da wani tak'arasa magana had'e da boyewa bayan Mus'ab.
"Katuwa harara Habeeb yadanna mata da wa ki ke"?
Mus'ab yace da kai take ko akwai abunda za ka yi"?
"Wallahi yanzu ina lakad'a mata duka ba ruwana da zamanta amarya, kuma ba abunda za ka iya.
"Mus'ab ya ja tsaki yace za ka iya saboda ba hankali ne yawadace ka ba don haka ja matarka Ku koma parlour duk abunda Ku ke so zan had'a mu Ku ni dai fatana mu rabu lafiya da kai batare d kata6a min lafiyar mata ba.
"Haleesa tarik'o hannun Habeeb zo mu koma parlour my handsome Don ko yak'i ko yaso ya zame masa dole yadafa yabamu, mu ci.
Habeeb ya yi dariya yace haka ne fa my Leesa kinsan Mus'ab kwarare ne a faggen girki cikin dariya suka fice daga kitchen d'in.
Akan 3 seater suka zauna k'afafunta ta daura a cinyoyinshi yana ja yatsunta a hankali Mus'ab yashigo d'auke da k'aton tray a tsakiyar rugs carpet ya ajiye tray kallo d'aya ya yi musu yadauke kai yajuya kitchen ya kwaso plate yayinda Hannah take rik'e da flask mai d'auke da ruwan zafi, Mus'ab ya dube su yace in kun ga dama Ku sauko k'asa Ku yi wa kanku serving Habeeb yarik'o hannun Haleesa sauko k'asa my Leesa na yi miki serving mak'e kafad'a ta yi banacin.
"Habeeb ya yi k'asa da murya haba! Leesa ke fa ki ka ce in mu zo gidanan za ki ci abincin shine dalilin da yasa k'afata ta tak'o gidanan Dan Allah ki daure ki ci ina jin tsoro kada yunwa ta ta6a mana babynmu.
"A shagwa6e tace indan naci amai za yi ni yanzu d'an wake ko shinkafa da mai da yaji nakeso cin.
''Mus'ab ya kalli Hannah suka kyalkyale da dariya Habeeb ya galla musu harara yace lalura ce bata wuce ta hau kan matarka ba.
"Mus'ab yace katashi kashiga kitchen domin zama bai sameka ba.
"Tabe baki Habeeb ya yi to ae ni ba d'an daudu bane irinka yak'arasa magana had'e da dauko phone d'inshi ya kira Ammi ya fad'a mata ta ta yi wa Leesa d'an wake da shinkafa da mai da yaji Bala zai zo ya kar6a yakawo mata gidan Hannah.
"Yana gama waya ya yi wa Mus'ab gwalo had'e da cewa shiga kitchen sai Ku Mus'ab marasa dabara Sabon babi na fira suka bud'e sai sautin dariyarsu ka ke ji a haka Bala yashigo yasame su ya ajiye foodflask d'in hannunshi yanemi kujera ya kame Haleesa nagani d'an wake kamar za ta yi hauka nan take ta zuba a plate tashiga ci shinkafa kuma ta ajiye sai da rana ta cin.
"Anan Habeeb yabar Haleesa suka fita shi da Mus'ab da Bala sai misali k'arfe _8:30pm_ Habeeb ya dawo d'aukar Haleesa.
"A washe gari Habeeb da Haleesa suka koma Abuja suka bud'e Sabon shafi na soyayya kamar za su cinye junansu, in fita Habeeb ya yi suna manne da waya idan kuma ya yi tafiya adaddafe yake gama abunda ya je yi yadawo, musanman yanzu da cikin Haleesa yashiga wata na 6 ya yi girma sosai.
Haleesa na kwance akan 3 seater Imaan na matsa mata k'afafunta Habeeb yashigo yana waya hannunshi yasa yadauke kanta ya zauna ya aza kanta bisa cinyoyinshi yana gama waya ya kira sunanta Leesa!
"Na'am
"Tafiya Lagos yakamani amma ina gani ba zan wuce _1 week_ ba.
"Bata fuska Haleesa ta yi kamar za ta yi kuka ni gaskiya my handsome Don banaso wannan tafiya da ka ke yi sanin kanka ne duk lokacin da ka yi tafiya ba wani baccin kirki nake yi ba.
"Ni ma Leesa ba so tafiya nan nake yi ba banida yanda zan yi ne ba zan wuce _1 week_ ba zan dawo kinji"?
"Shikenan Allah yadawo da kai lafiya.
"Ameen Leesa naa.
_3 months later_
Haleesa tana kitchen tsaye hannunta rik'e da wuk'a tana gyara kankana Habeeb yashigo ya rungumeta ta baya ya zura kanshi ta kafad'arta yabata peck a kumatu mai ciki sarkin kwad'ayi me ake had'a mana ne"?
"Fruits salad ne tun safe na tashi da kwad'ayinsa.
Zare jikinshi ya yi daga nata ya yi tsalle ya haye kitchen cabinet d'an Sam mini kankana nan naganta jajir da alama za ta yi zak'i harararshi ta yi tadauki yanka guda d'aya tasaka mishi a baki yana tauna yana lumshe idanu.
"Haleesa tace da zak'i koh"?
Gyad'a kai ya yi eh! Saida kin fita zak'i ina gani zak'in hannunki ne ya shafe ta shiyasa ta yi zak'i.
"Girgiza kai ta yi had'e da murmushi tana gama had'awa tasaka ice block Habeeb yadauka mata, bowl d'in suka nufi parlour in tayi spoon 1 tasakawa Habeeb suna gama shan fruits salad marar Haleesa tafara murd'a tun tana cize lebb'e sai gashi tadawo wash..... Wash... Bayana marata a rikice Habeeb yad'ago ta Leesa ko haihuwa ne"?
"Da kyar Haleesa tace ita ce saboda randa na ke a duniya banta6a jin masifar ciwo irin wannan ba.
"Da k'arfi Habeeb yashiga kwadawa yarinye kira sai gata tashigo Imaan tana biye da ita ki je bedroom d'in Leesa akwai trolley brown colour ki bud'e ki dauko kayan baby za mu tafi hospital.
"Cikin d'an k'ank'anin lokacin sai ga yarinye tadawo d'auke da medium size na trolley Habeeb yadauki Haleesa yafice tun kafin yak'arasa compound yashiga kwallawa Bala kira yi maza Bala ka dauko mota da gudu Bala yanufi parking lot yajanyo mota Habeeb yasaka Haleesa ya dubi yarinye yace kin saka kayan a mota"? Eh nasaka a seat d'in gaba.
"Shikenan ki d'auki imaan ku koma cikin gida sai mun dawo
Bala yafizgi mota yanufi gate maigadi ya bud'e musu gate suka fita.
_Some hour's later_
Haleesa tasauka lafiya tasami bouncing baby boy mai kama da Habeeb, farin ciki wurin Habeeb ba kama hannun yaro bayan drip d'in da aka sa ma Haleesa yak'are akayi discharged nata suka yo gida, washe gari suka bi flight zuwa Yola ranar suna baby yaci sunan mahaifin Habeeb Abdulmajeed suna kiranshi da Haleel.
_6 years later_
Habeeb yana zaune a palour hannunshi rik'e da news paper wata 'yar kyaKyawa yarinya wance shekarunta ba za su haura 2 ba tadanno da gudu tafad'a jikin Habeeb cikin muryarta ta yarinta, tace Daddy boyeni na yi fanna.
Da sauri Habeeb ya 6oyeta bayanshi Imaan yarinya 'yar shekara 13 tafito daga d'akinta hannunta rik'e da exercise book kamar za ta yi kuka tak'arasa wurin Habeeb tanuna mishi book d'in da ke hannunta Daddy kalli abunda Hibba ta yi mun da littafi.
"Habeeb yad'ago ya kar6i littafi ya yatsine fuska nagani ta yaga sau nawa ina gargad'inki ki dinga ajiye books naki Inda bara ta iya daukowa ba da yake ke mai kunnen k'ashi ce sai ki ka yi biris da maganata wannan shine maganinki.
"cikin pity face tace Daddy karatu nake yi fa gobe za mu fara exam nashiga bathroom na barshi akan bed koda nadawo na iske ta yaga mun, kuma uncle yaga book d'ina ya yage dukana zai yi tak'arasa magana hawaye na zuba akan cute face nata.
"Carelessness naki ne yajanyo miki sai hak'uri gobe zan baki k'udi ki siye wani.
"Daddy Note d'in da ke ciki fa"?
"Dafe goshi ya yi daga bisani yadaka mata tsawa ina ruwana da note sai ki yi copying in kuma bara ki iya ba sai ki bari kuka Imaan tasa a hankali take taka staircase tana sanye da lace Wanda yak'ara fitowa da ainihin kyauta tun kafin tak'araso cikin parlour tafara fad'a wai yaya Habeeb me yasa ka ke yi haka ne huh"?
Kafin kowa sanin halin Hibba a gidanan Sam bata jin magana yarinya nan shegiyar 6arna ne da ita har