Showing 75001 words to 78000 words out of 132766 words

Chapter 26 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87957

min d'akina_
Da k'arfin yashiga janta zuwa part d'inshi yayinda Haleesa take kuka kamar ranta zai fita tsananin kukan da take yi ya hanata maidawa Habeeb Lamido martanin abunda ya yi mata.
"Cillata ya yi cikin bedroom yakoma gafen ya yi tsaye yana tsotsan baki kamar mai shan sweet Haleesa ta shar6e hawaye da hannunta tasoma gyara bedsheets yatsanta sai zogi yake mata a haka ta kintsa masa d'akin ta juya za ta fice ya tare mata hanya da hannunshi ya yi mata ishara da bathroom bata ce da shi komai ba tanufi bathroom tsaye ta yi tana kallon yaddda yak'awata bathroom d'in bashida banbancin da bathroom d'inshi na Yola ta tabe baki a zuciyata tace banza mai kwaikwayon Nasara hasarar duniya.
Ta wanke bathroom d'in tsaf tafito yana tsaye hannayenshi zube cikin aljihhun wando, ta ra6a ta gefenshi tafice.
''Habeeb yadawo parlounshi ya zauna yatalabe kumatunshi da hannun ya bud'e babin zance zuci _me yasa duk abunda na yi wa yarinya nan saidai ta yi kuka bata nuna 6acin ranta"?_
_hank'unrinta ne ya yi yawa ko kuma tsabar rashin son da ta ke mini ne yasanya take nuna halin ko in kula da cin zarafin da nake mata"?_
''Ya ja tsoki d'ayan bangare zuciyarshi yace rashin so ne Habeeb sanin kanka ne akwai Wanda har yanzu yake sarafa zuciyarta kai da banza da babu duk d'aya suke a wurinta.
ba zai yu ba....Habeeb yafad'a a baiyane ya mik'e tsaye yafara safa da marwa yak'ara Jan tsoki me ke faruwa da ni"?
Akan wane dalilin zan jefa kaina cikin damuwa ina ruwana da Wanda take so ae ni ba sonta nake yi ba Wanda take hauka akansa baya duniya me zai sa na nemi na damarda kaina"?
Amma kuma matata ce bai kamata tacigaba da son wani
"To in har bataso wani ba wa ka ke da shi da za ta so"?
Yafad'a kan kujera yadafe goshinshi yashiga nazari ko zai yi nassara lala6o amsoshin tambayoyinshi.
********************
```HALEESA```
Direct bedroom d'inta ta wuce ta yi kwance hawaye na fita a gefen idonta _me na yi wa yaya Habeeb ya tsane ni haka"?_
_me yasa a koda yaushe bashida buri da yawuce ya k'untatawa rayuwata"?_
_na yi danasanin amincewa da aurenshi a da nayi k'udirin zama da shi amma yanzu bana tunanin zan iya cigaba da zama da mashayi wanda babu tsoron Allah a zuciyarshi lallai ya zame mini dole na nemowa kaina mafita domin ba zan yarda ba rayuwata tak'are a haka_
Haleesa ta mik'e zaune ta sharce hawaye da bayan hannunta.
tun daga ranar Haleesa bata k'ara saka Habeeb Lamido a idonta ba.

```1 WEEK LATER```
_sunday morning_
Around 10:00 o'clock peter ya kamalla breakfast ya jerawa Haleesa nata a dining table yanufi part d'in Habeeb ya Jera masa nashi a table.
"A K'a'idar Habeeb baya breakfast sai _11:00am_
''Habeeb tsaye akan gym mat machine yana motsa jikinshi ya had'a d'an uban gumi tsawon lokacin yadauka akan machine d'in daga bisani yanufi d'akinshi ya yi wanka bayan yafito yashirya cikin black three quarter da armless shirt direct dining table yawuce ya yi taking breakfast yana gamawa yadawo parlour ya zauna ya afka tunanin abunda yasha masa kai tsawon _1 week_ da ya yi tafiya zuwa Lagos sai Daren jiya yadawo yarasa dalilin da yasa yakeson ganin Haleesa bashida aiki sai na tunaninta a hankali ya lumshe idanunshi a zuciyarshi yace ba shakka sha'awar yarinya nan takamani tun daga ranarda naganta half nacked na rasa sukuni shiyasa nakejin wani abu a game da ita ya ja iska yafesar kamar Wanda aka mintsina ya mik'e yanufi part d'in Haleesa yana Shiga parlournta ya ga wayam bata ciki tsabar miskilincin da girman kanshi suka hana shi zuwa bedroom d'inta shi a dole kada tagano yafara shiga wani yanayi akanta sai kawai yanemi kujera ya zauna.
```HALEESA```
Tun wayewar gari Haleesa takejin kanta wani irin kad'aicin yadame ta ita kadai zaune a gida kamar mayya Imaan ce dama ke d'ebe mata kewa gashi tun jiya Hannah ta tafi da ita za ta yi musu weekend har k'arfe _12:00pm_ ya buga Haleesa na kwance yau ta tashi da sha'awa ta yi wa kanta girki tagaji ta cin abincin Peter musanmman yau da peter yake zuwa Church sai k'arfe 1:00pm yake dawowa sannan ya yi musu lunch abun na masifar k'onawa Haleesa rai tarasa dalilin da yasa Habeeb yake da sha'awar rayuwar nasara hatta da abinci sai wani k'aton Arne yadafa ya bashi ita dai daga yau bara ta sake cin abincin Peter da wannan tunanin tanufi parlour tana shiga parlourn ta yi turus...sakamako hango Habeeb Lamido zaune a parlournta, kallon d'aya ta yi mishi tadauke kai tashige kitchen.
Habeeb na ganin Haleesa yasaki ajiyar zuciya ganinta da ya yi yak'ara motsu mishi da abunda yakeji a game da ita ya runtsin idanu yana Mai jin haushin kanshi yarasa yadda aka yi sha'awarta ta yi masa mummunan kamu.......

Jeeddah Aliyu🌹




[21/11 8:36 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```75```

~~Habeeb ya bud'e idanunshi yak'urawa k'ofar kitchen ido yana mamaki yadda Haleesa ta wuce shi batare da ta gaida shi ba ya ja tsoki nan take zuciyatshi tafara kintsa masa zance zuci kala dabam- dabam, watakila tafara gano kana sha'awarta shiyasa takeso ta rainaka.
Sumar kanshi yashiga hargitsawa kamar mai ciwo tabin hankali, a wani gefen bana ganin laifin kaina saboda ni lafiyaye namiji ne dole ina buk'atar mace kenan ko na yi sha'awar Haleesa ba illah bane saidai banajin zan iya had'a shinfid'a da ita koda ace sha'awarta zai illatani yakoma jikin kujera ya lafe yana mai cigaba da tunano tsari da kyawon surar Haleesa.
**********************
```KITCHEN```
Haleesa na shiga kitchen ta bud'e diff freezer tafito da katuwar kaza ta ajiye ta a gefe k'ank'arar jikinta yasake tadauko fresh tomato da tattasai da tarugu adadin da za ta yi amfani da shi ta wanke ta zuba cikin blender had'e da yin switch on d'in blender tsabar wauta irin na Haleesa ta d'age murfin tagani ko tomatoes ya yi blending ga blender yana aikin tana lek'awa tomato ya yi tsale yadira a idonta, tasaka hannun tadafe idanunta tafara zunduma ihu _Wayyo Allah idona, wayyo idona_
Gaba d'aya ta rud'e tafita haiyacinta sai faman lallube take kamar makauniya kamar daga sama Habeeb ya ji sautin ihun Haleesa ya ja d'an 'karamin Tsoki ita wannan me ta ke yi wa ihu"?
Ihun ya ji yak'aru da sauri ya mik'e yanufi kitchen d'in _ke! Lafiya ki ke yi wa mutane ihu kefa abun ihu baya miki wuya_
Idona yaya Habeeb wayyo idona bana gani
Me yasa me idon naki"?
"Ya ji ne yashigar min ido
Tabe baki ya yi yana mata kallon sama da k'asa garin lullube Haleesa ta d'ank'o shi da k'arfi ta chukuikuye masa riga please yaya Habeeb help me
"Habeeb ya yi sororo yana kallonta ihunta yadawo da shi cikin natsawarshi yarik'o hannunta ya bud'e fanfo ya wake mata fuska chan 'kasan mak'oshi ya furta ki bud'e idanunki iska yashiga sannan za ki daina jin zafi.
Haleesa tashiga girgiza kai bara iya ba Yaya Habeeb ka busa min
Me zan busa"?
Habeeb yafad'a da alama mamaki akan fuskarshi''
Idona za ka busa min shiru Habeeb ya yi kamar mai nazari daga bisani yarik'o kanta yad'aga idonta ya busa saura wannan Haleesa tafad'a had'e da nuna d'ayan idonta.
Tsoki ya yi had'e da cewa ke karki mayarda ni yaronki yanzu nan ki ka wuce ni a parlour don tsabar iskanci ko ki gaida ni yak'ara sa magana had'e da busa mata idon sannun a hankali Haleesa ta ware idanunta duba d'aya ta yi masa ta kauda fuska tajuya wurin blender ta yi switch off had'e da zareta daga socket.
''A yatsine Habeeb yace a garin yaya ki ka zubawa idonki yajin"?
Kamar bara ta amsa ba daga bisani tace murfin blender na d'age nagani ko tomatoes ya markad'u shine yashiga min idon ''Habeeb ya ja tsoki yace bak'auya kawai da nasan wannan ne dalilin da yasa yaji yashiga idanunki da saidai ki makace bara busa miki ba.
Cigaba da aikinta ta yi kamar bataji abunda yafad'a ba.
''Wai me za ki yi da wannan tomatoes da ki ke markad'a"?
Da mugun mamaki Haleesa tajuya ta dube shi, kana nufi bakasan abunda ake yi da tomatoes ba"?
"Yad'age girar sama yana kallonta a yatsine in nasani zan tambaye ki ne"?
Tabe baki Haleesa ta yi a dak'ile ta furta girki zan yi
''Harara ya galla mata girki za ki yi ko jagwalgwale"?
Oho... nima bansaniba Haleesa tafad'a a yatsine
"Habeeb ya zaro ido ke ni za ki ce ma bakisaniba"?
Na fahimcin yau wani rashin kunya ki ke ji ina magana kina amsa man a tsasaye sai kace kina magana da sa'anki
D'an bazawarin murmushi Haleesa ta yi tace karka ga laifina yaya Habeeb tun lokacin da na fahimce waye kai na kuma fahimce alkila da ka dosa nima sai nafara koyon rashin kunya tak'arasa magana had'e da murgud'a masa baki.
''Habeeb ya yi shiru yana kallon Haleesa ranshi ya yi mugun b'acin a zuciyarshi yace dama abunda nake gudun kenan kada yarinya nan tagano yadda nakeji akanta ya cije lips d'inshi na k'asa ya kad'a kai yafice daga kitchen.
yayinda Haleesa bata Masan yanayi ba aikin gabanta kawai take cikin _30 minutes_ k'amshin girkinta yafara gauraye gida Habeeb da take zaune a parlour ya shak'i k'amshin girkin Haleesa ya lumshe idanu ya shafi sumar kanshi a zuciyarshi yace ko me wannan yarinya tasaka a girkinta yake k'amshin haka"?
Sanin ba Wanda zai bashi amsa yasa ya tabe baki yacigaba da kallon da yake yi.
"Had'ad'iya jellof rice da farfesun kaza Haleesa ta had'a ganin tana da sauran lokacin sai kawai ta had'a zobo drink yasha pineapple ta yanka cucumber k'anana a ciki tasaka ice block yadda zai yi saurin yin sanyi saida ta Jere abincinta akan dining table sannan tanufi bathroom domin ta yi wanka lokacin da ta zo shigewa bedroom ta tararda Habeeb yafita.
_20 minutes later_
Habeeb na zaune a parlournshi kaitsaye Mus'ab da khaleel suka fad'o falon kowane su yanemi wuri ya zauna kallon mamaki Habeeb ya bi su da shi a yatsine yace Ku kuma daga ina"?
Khaleel ya amsa da cewa daga wurin gararin gari mu ka fito kuma wallahi mun d'ebo 'yar banzar throughout ba abunda nasaka a cikina kuma da alama mun taki babbar Sa'a tun daga compound mu ke shak'ar k'amshin girkin amarya yak'arasa had'e t kwashewa da dariya Mus'ab na taya shi
''Kallon banza Habeeb ya watsa musu ya ja tsoki yace ''look karku nemi Ku raina min hankali angaya muku gidana restaurant ne''?
''Mus'ab ya kar6e zance ta hanyar cewa gidanka ba restaurant bane amma akwai sabuwar amarya dal a cikinsa, don haka bara mu fita gidanan sai mu d'ebi girki.
''Harara Habeeb ya galla masa yace idan wannan ne yakawo Ku to ba Ku zo da Sa'a ba saboda bata dafa da Ku ba sai Ku tashi Ku k'ara gaba ko yak'arasa magana yana kallon fusk'ok'in su khaleel yace ba ka isa ba Lamido ko kanaso ko bakaso sai mun cin abincin nan.
''Habeeb yadafe kai yasoma tunanin irin wulaqanci da ya yi wa Haleesa da kuma dokar da yakafa mata ko noodles bai amince ta dafa da sunanshi ba tsananin biyawa da ranshi ya yi da abinci da ta dafa ya kuma San miskilanci da girman kanshi bara su barshi yaci abincinta yasa ya gudu daga parlounta, sai kuma ga wad'annan rikitatun friends in nashi ba shi da za6i da ya wuce ya kwashe su zuwa part d'in Haleesa.
"Wai tunani me ka ke yi khaleel ya katsi masa hamzari
Tsoki ya ja yafi a kirga daga bisani ya mik'e tsaye ya dube su a d'age yace to ae sai Ku tashi mu tafi part d'inta mayu kawai sai kace wani shege yahanaku aure.
Mus'ab da khaleel suka dube juna had'e da zaro ido Mus'ab yace kaima yaushe ne ka yi auren da za ka yi mana gori dad'i abin nima na yi kusan angwancewa da k'anwarka suka kyalkyale da dariya har da tafawa sa6anin Habeeb da ya yi kici-kici da fuska can! Ya ja tsoki yashige gaba suna biye da shi suna shiga parloun Haleesa direct dining area suka wuce cike da takaice Habeeb yake kallonsu kowane su ya loda plate da jellof rice k'amshin abincin yadaki hancin Habeeb babu shiri ya zare plate ya yi serving, ba ka ji komai sai karar spoon's.
"Haleesa taci kwalliya cikin riga da siket na atamfar super Holland ta yi matuk'ar kyau jikinta na fitarda fitinane k'amshin designer perfumes a hankali ta taka zuwa parlour idanunta suka sauka akan dining table Habeeb da zugar abokai shi suna wawosar abincinta, ranta ya yi mugun b'acin musanmman da ta tuna da dokar da yakafa masa tabbas wannan shine right time da zan yi amfani da shawara Hannah na nunawa Habeeb Lamido I'm not scare of him
_Amarya barka da fitowa kafin kifito har mun cinye miki girki_
Muryar khaleel ce ta katsiwa Haleesa tunani cikin tafiyarta mai kama da na mai tsoron taka k'asa tak'arasa wurinsu fuskarta d'auke da tsadad'e murmushi tace _sannunku da zuwa_
"Mus'ab yace Yauwa amarya gaskiya abincin nan naki ya yi matuk'ar dad'i na dad'e ban ci abincin da ya yi dad'insa.
"Da sauri Habeeb Lamido ya yi dropping d'in spoon ya sada kai k'asa yana juya glass cup mai d'auke da zobo tsananin kunya mai cike da danasanin biyewa friends d'inshi da ya yi yaci abincin Haleesa suka lullu6e shi.
''Haleesa ta gyara tsayuwarta ta dube Habeeb da yasada kai k'asa ta tabe baki tajuya wurinsu Mus'ab ta yi fari da ido karaf akan idon Habeeb wani irin mashi ya ji yadaki zuciyarshi.
Haleesa tace na gode da yabawarku duk lokacin da Ku ke da buk'atar abincin irin wannan da ma Wanda yafi wannan k'ofa abude take saboda kunfi wasu masu cika baki da fankama tsiya sai d'an banzan girman kai rawanin tsiya ko yanzu kasuwa ta tashi d'an koli yaci riba ko komai Haleesa tafara fatali da dokar mutum yak'arasa magana had'e da yi wa Habeeb kallon sama da k'asa ta kama tsotsan bakinta kamar yadda yake yi da sauri Habeeb Lamido ya runtse idonshi ya mik'e azafafe hannunshi rik'e da cup yana huci kamar zaki adawa yad'aga cup d'in ya wankawa Haleesa zobo tun daga fuskarta zo6o ke d'iga........


Jeeddah Aliyu🌹



[22/11 4:05 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```76```

~~A hankali ta bi jikinta da kallo gaba d'aya zo6o yabata mata kaya a harzuk'e tad'ago idanunta Wanda suka canza colour zuwa red, kallo d'aya za ka yi mata ka hango b'acin ranta yadda ta tsare Habeeb Lamido da ido za ka yi tsanmani za ta zanga masa mari ne.
"Kallo mai cike da zazzafar tsana Habeeb yake watsawa Haleesa cikin tafarfasa zuciya yadaka mata tsawa cikin angry voice ya furta _How dare you ni za ki wulaqanta in front of my friends"?_
''Kafin Haleesa ta ba shi amsa Mus'ab ya taso yashiga tsakaninsu ranshi a b'ace yace _what's wrong with you Lamido akan wane dalilin za ka yi mata wannan d'ayen wulaqancin matarka ce fa"?_
''Kallon banza Habeeb ya watsa masa so what's don tana matata shi zai bata dama tacin min zarafi a gabanku"?
Haleesa ta yi karaf tace ancin zarafin naka yaya Habeeb ka yi duk abunda za ka iya ae ba tsoronka nakeji ba, tana k'arasa magana ta yi shigewarta bedroom tabar Habeeb Lamido sake da baki sai faman huci yake yi bai ta6a tunanin Haleesa za ta iya maida martanin abunda yake mata.
"Mus'ab ya ja tsoki ya dube khaleel yace tashi mu tafi khaleel a zahirin gaskiya nayi danasanin zuwanmu gidanan da bamu zo ba Lamido da bara ka, same damar wulaqanta 'yar mutane ina mamaki wannan miskilancin da girman kan naka Lamido ka gyara halayyarka ko za ka jin dad'i rayuwa.
''Khaleel ya kar6e zance ta hanyar cewa wannan abun da kayi Lamido kasanin ba burgewa bane, wulaqanta mace ba abu bane mai kyau muna jiye maka ranar Nadama.
''Yana k'arasa magana yarik'o hannun Mus'ab mu tafi kawai Mus'ab kana kallon irin kallon banzar da yake mana.
''Habeeb ya ja tsaki yace sai me don kuntafi dama can! Ban gaiyyace Ku ba ra'ayin kanku ne yakawo gidanan don kuntafi bara jin zafi ba asalima zuwanku wulaqancin ya janyo min tunda nake da yarinya nan banta6a magana ta mayar mun da amsa ba sai zuwanku banzaye kawai.
''Mus'ab ya galla masa harara yace ae Kaine banza Wanda baisan darajar matarshi ba wallahi Lamido in na cigaba da tsayuwa a gabanka haushinka da nakeji zai iya haddasa min hawan jini.
''Habeeb ya ja tsoki had'e da ficewa daga parlourn yabar Mus'ab da khaleel tsaye suna mamaki wannan halayen nashi daga bisani suka kama gabansu.
***********************
Kuka Haleesa taci kamar ranta zai fita tabbas Habeeb Lamido yade6o da zafi daga yau bara k'ara d'aga masa k'afa saidai ya yanka ni a gidanan.

```WASHE GARI ```
_Monday morning_
Kamar yadda Haleesa tasaba tashi da wuri ta shiryawa Imaan zuwa school tana rik'e da hannunta suka nufi compound har wurin mota ta yi mata rakiya, da kanta ta bud'e k'ofa tashiga ta yi pecking goshinta ta mik'awa sa'eed driver lunch box d'inta yayinda driver ya ja Motan zuwa gate Imaan tana d'aga mata hannun Haleesa ta mayar mata da cewa bye, babyn aunty ki yi karatu sosai Saida suka fice gate sannan Haleesa juya tana juyawa ta hango Habeeb tsaye da sauri yad'auke kai, kamar ba shi bane yake tsaye yana kallonsu, ta raba ta gefenshi dai-dai za ta shiga cikin gida tace _ina kwana yaya Habeeb"?_
"Saida zuciyarshi ta buga da k'arfi saboda baita6a tsanmani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login