Showing 111001 words to 114000 words out of 132766 words
gashi ba gwanin surutu ba amma yak'ure malejinshi yadawo tamkar parrot duk don Haleesa ta fahimce irin mugun sonta da ke d'awainiyya da shi takasa fahimta sai wani banza zance da tashigo mishi da shi wai yana ,pretending.
"Habeeb ya mik'e a sanyaye ya zauna kusa da ita ta matsa da sauri yak'ara matsawa ita ma tak'ara matsawa haushi ya turnuk'e Habeeb ya d'ank'i hannunta yashiga murza yatsunta da k'arfi ihu taje kurmawa da sauri ya had'e bakinshi da nata tsawon lokacin suka, dauka a haka daga bisani yasaketa ya had'e goshinshi da nata yad'anna mata cizo a hanci ta runtse idanunta hawaye, yasoma gangaro mata ban yarda ba yaya Habeeb baka sona yaudara ta ka ke yi za ka cuce ni ne watakila har yanzu da raguwar sona wata a zuciyarka
Can! K'asan mak'oshi yafurta meyasa bakida tausayi leesa"?
''Ko makaho ya dubi zai gano I'm in love with you leesa.
"Yatsine fuska tayi tace watakil ni makauniya, ce shiyasa nakasa amincewa da kai.
"Habeeb ya girgiza kai yace mu ajiye wannan zance a gefen banaso ki amince ki ta kallona a matsayin Wanda baya sonki, don ma kinsamu ina rarrashinki kidaina gani mom tana cewa sai na sake ki fad'a ne kawai take yi don taji dad'in bakinta tasaki nishad'i amma wallahi koda za ta aza mun bakin bindinga aka zan furta mata inasonki ba wai kalma saki ba yanzu ki yi favour d'aya za ki yi min kitash mu tafi hospital a duba min idanu nan naki banaso wani abu yasame ki.
"Murmushi takacin Haleesa tayi tace ae ba wannan ne karo na farko da kasaba mari na idanuna su yi kwancin jini yatsunka su sami muhalli a kumatuna karka damu kanka wannan ba bako bane a wurina
"Murmushi Habeeb yayi had'e da d'anke yatsunta, uhm...leesa yanzu abunda yafaru almost 3 years ashe baki manta ba"?
Harara ta zuba masa ta kauda fuska.
Duk yadda Habeeb yaso Haleesa ta saurare shi tak'i daga karshe ma ta yi mik'e tanufi k'ofar fita da sauri yadawo da ita da kyar ta amince ta zauna.
"Cikin tsawa tafara magana nace bana sonka yaya Habeeb ka kyalleni kai ka manta irin wulaqancin da ka dinga zuba min eyeee"?
Ko angaya maka banida zuciya a kirjina to ina gargad'inka kafita harkata I don't love you anymore banaso ganinka please stay away from me tak'arasa magana cikin sautin kuka.
"Habeeb ya ja iska cike da takaici yake kallonta ahalin yanzu kalamai bakinshi suna daf takarewa.
"Tsawon lokacin suka dauka ba Wanda yak'ara magana Habeeb ya kai dubanshi akan wrist watch d'in hannunshi zaro ido yayi cikin kaduwa yake kallon Haleesa daga bisani yace ki dubi tsawon lokacin da na dauka a d'akinan ina miki magiya wannan kadai bai isa ya gansar da ke inasonki ba.
"leesa ba abunda nake ba wa mahimmancin irin lokacin domin da yawuce ba zai dawo ba amma gashi throughout ba inda naje ina zube a gabanki ina miki magiya ki ji tausayina leesa kiyafemin.
"Haleesa ta yi shiru kamar tana nazari daga karshe brain d'inta ya nazarto mata mugunta da za ta yi wa Habeeb yadda za ta yi hurting nashi very badly tad'ago idanunta fuskarta d'auke da wicked smile, tafara magana tana yatsina kamar yadda Habeeb yake mata a da zan amince na kar6i tayin soyayarka amma a bisa sharad'i d'aya ta d'an suke numfashi tana jiran ta ji ta bakinshi.
"A Rikice Habeeb yad'ago muryarsa na rawa yace menene sharad'in naki"? muddin za ki amince da ni zan iya.
"Wani shu'umin murmushi Haleesa ta yi tace............
Jeeddah Aliyu🌹
[10:42PM, 15/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [15/12 5:23 pm] aliyujeeddah: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
_this page dedicated to only you my sweet Mrs Umar Billions words can't ever exprees how much I love you but I wants you to known that Fatee you're very special person to me remember that & always saying KE D'AYA CE FATEE_
```93```
~~Ta d'ago da sauri ta dube shi, ta yi fari da ido cike da mugunta tafara magana anyya kuwa yaya Habeeb za ka iya?
"Murmushi ya yi had'e da lumshe ido wannan ba matsalarki bace, ke dai kawai ki fad'i sharad'in naki matar na tuba ae bata rasa mijin aure.
''Ta tabe baki uhm......sharad'in na ba wani mai zafi bane inaso in tabbatar da soyayya da ka ke kirarin kana yi min ta gaskiya ce ko kuma pretending ka ke yi domin kasami damar cigaba da kawarda sha'awarka akaina.
Da sauri ya kalle ta ya kawar da kai wannan ya ba wa Haleesa damar cigaba da cewa indan har da gaske yaya Habeeb kana sona ba sha'awata ka ke yi ba daga yau karka k'ara zuwa inda nake kuma karka kirani a waya, na har tsawon watanin 3 idan da gaske kana sona za ka iya jure wad'annan watani batare da ka waiwaye ni ba indan kuma sha'awa ce na tabbata kwana d'aya tak ba za ka iya ba batare da ka zo inda nake ba yanzu dabara taragewa mai shiga rijiya za ka iya"?
"Sai lokacin Habeeb yad'ago ya yi mata, kallo lalle yarinya nan kin zare da mugun mamaki yafurta _3 month_ fa ki ka ce leesa"? Ina laifi ki ce 3 day's su d'in ma zan yi sune adaddafe haba gaskiya I can't do this!
Haleesa ta ya mutsa fuska idanuta suka ciko da kwalla cikin muryar kukan kissa had'e da shagwa6a tafara magana, ni dama nasan baka sona yaudara na ka ke yi idan da gaske soyayya gaskiya ka ke mun miye _3 month"?_
''Please leesa ki fahimce ni irin son da nake miki ba zai barni na d'aukin tsawon wannan lokacin batare da nayi tozali da kyakyawar fuskarki ba indan nace zan tilassawa kaina hakan zai iya cutar da ni ina miki so na hak'ik'a dai-dai da second 1 banaso na nisata da ke yak'arasa magana cikin sanyin murya.
"Juya masa baya tayi shikenan yaya Habeeb za ka iya tafiya amma kafin katafi kasani a kowane lokacin za ka iya nema na karasa domin ba zan iya cigaba da zama da mutume da ba zai iya jajircewa akan farin cikina ba Wanda hakan yanuna mini har yanzu zuciyarka tana wasiwasi da soyayyata.
''Zuwa wannan lokacin Haleesa tafara k'ular da shi ya mik'e a fusace I can't leesa ni da nake fatar yau d'inan mom tabarki ki koma gidana mu fara shinfid'a kyakyawar rayuwa shine za ki tsiro da wannan shirme"?
''Kafin Haleesa tabashi amsa madam Hindu ta turo k'ofa tashigo tana rafka salati cikin kad'uwa Habeeb da Haleesa suke kallonta.
"Ohh...ohh....son dama har yanzu kana cikin gidanan"? Shine ka kad'a mun yarinya a parlour kai kuma ka zo nan ka kasa ka tsare uban me yashigo da kai nan shin ba nace banaso na k'ara ganin k'afarka a gidanan ba"?
"Cikin sark'ewar halshe Habeeb yace ni fa ba wani abu ne yashigo da.........
''Kai dallah! Saurara wannan tsayin da na tarar da kai kana yi karatu ne ka ke koya mata ko me"?
Huh......sweetheart hak'uri ne nake bata.
"Ae yanzu bakada sauran kalma da za ka yi amfani da ita wajen bata hak'uri tajuya wajen Haleesa tace hukuncin da ki ka zantar ya yi mun dai-dai ni anawa ra'ayi so nayi yabani takarda ki kowanenku Allah ya had'ashi da rabonshi.
"Habeeb ya hadiye wasu yawu masu mugun d'aci yana kallon madam Hindu a tsorace yana mamakin yadda take k'ok'arin shiga tsakaninshi da farin cikinshi, Iya saninshi Sam baya laifi a wurinta, amma sai gashi yau ta zo mishi da abunda bai saba da shi ba.
''Daga yau karna k'ara ganin k'afarka a gidanan har sai watanin 3 sun cika maganar madam ce ta katsiwa Habeeb tunani yayinda Madam tacigaba da cewa idan kuwa ka kuskura tsautsayi yasa ka tak'o k'afarka gidanan to kasani a bakin aurenka ko ba haka ba Haleesa"?
''Da sauri Haleesa ta gyad'a kanta.
Habeeb ya yi sororo yana kallonsu Madam ta galla masa harara tace kama hanya katafi cikin zafin zuciya yanufi k'ofa ya bud'e da k'arfi yafice a downstairs parlour ya tararda Hannah tana kallo rankwashi mai zafin gaske ya zuba mata aka _wayyo Allah mom yaya Habeeb zai kashe ni_
Ke! Munafuka yafad'a a tsawace shiru ko na wanka miki mari duk gargad'in da nayi miki bai shige ki ba da yake ke munafuka ce saida ki ka fad'awa sweetheart ina d'akinki tare da leesa koh"?
"Allah yaya Habeeb bani na fad'a mata ita ce da kanta tagane.
Harara ya watsa mata yanuna ta da yatsa yayi kyaci yafita yana huci cikin zafin rai da baqar zuciya yanufi parking lot ya bud'e k'ofar mota yashiga Bala yagani ya kwa6e seat yasaki Ac yana sharar bacci hadda su dogon minshari.
Wawan duka Habeeb yakai masa a kafad'a kai! Dallah tashi a rikice Bala ya tashi ya gyara zaman seat yayi hamma had'e da mik'a cikin murya mai d'auke da alama bacci yace "Boss wai kana nufi duk tsawon wannan lokacin munan gidan"? gaba d'aya na manta da inda nake.
Hararashi Habeeb yayi yace ae dole ka manta da inda ka ke saboda hankalinka a kwance yake jiya-jiya ka yi wa motar nan ''full tank dubi yadda fuel ya yi k'asa ka k'ure Ac kana sharar bacci abinka ni kuma ina cikin gida ana mun barazana da rayuwa.
"Tuni Bala ya watsarke ya zaro ido boss wane mai k'arare kwana ne yake maka barazana da rayuwa"?
"Tsaki Habeeb yaja yace kai banaso shirme banza ja mota mu tafi Bala ya yi wa mota key yanufi gate maigadi ya wangame musu gate suka fice.
"Madam ta dubi Haleesa tace ina mai k'ara baki hak'uri akan abunda son ya yi miki Haleesa shiyasa nakeso, ki yi amfani da damar da Allah ya ara miki kema ki rama abunda "son yadad'e yana miki.
"Murmushin jin kunya Haleesa ta yi tace tun jiya ki ke ta bani hak'uri mom har kinsa nafara jin kunyarki.
Madam tayi murmushi had'e da rik'o hannun Haleesa tace tsakanina da ke ba, jin kunya Haleesa ni fa tamkar mahaifiya ce a gare ki shiyasa nake gargad'inki kada ki yi sauri ba wa ''son fuska har sai yagano shayi ruwa ne.
''Haleesa tayi murmushi had'e da sadda kai k'asa.
Madam tajuya da murmushi tafita Haleesa ta yi ajiyar zuciya ta koma ta kwanta, ta lumshe idanu wani irin dad'i yana ratsata.
_3 days later_
Habeeb na kwance a parloun'shi kwanaki 3 kacal har yafara fita hayyacinshi bashi da aikin yi sai tunani gaba d'aya duniya tayi mishi qunci yanaso zuwa gidan madam yana tsoro kada allura ta tono galma.
Mus'ab da Bala suka shigon parlourn sai faman kyalkyalar dariya Mus'ab ya zauna kujera da ke facing d'in Habeeb yayinda Habeeb ya watsa masa mugun kallo ya mik'e zaune wai kai Mus'ab wane irin marar imani ne kai"? Na kira ka ne don kanema min mafita inason matata ba zan iya jure tsawon watani 3 batare da na ganta ba yak'arasa magana cikin murya tausayi.
Mus'ab ya dube Bala suka wani zaro ido kowanensu ya yi murmushin shak'iyanci A fusace Habeeb yafara magana wannan wane irin iskanci ne ya ina muku magana kuna mini murmushin munafuncin gaba d'aya Ku na fahimcin farin ciki Ku ke yi da wannan hali da na shiga yayinda Habeeb rufe ido yadinga zazzaga masifa saida yagaji don kanshi ya yi.
Mus'ab ya hadiye dariyarshi yana mamakin zafin kan Habeeb shi dai komai da zafi yake d'aukarsa yanzu Wanda yake cikin wannan hali ina yaga bakin fad'a da wani.
''Tsanm.....Mus'ab ya mik'e yanufi kusa da Habeeb ya zauna yadafa kafad'arshi calm down abokina irin wannan tada jijiyoyin wuya har ina"? Yakamata kasawa zuciyarka salama ka sausautawa kanka wannan saurin fushi domin ba inda zai kai ka.
"Habeeb ya d'age gira ta kasan ido yake kallon Mus'ab daga bisani ya ja iska yace kaga malam za ka nemo min mafita ko kuwa"?
Girgiza kai Mus'ab ya yi yace akwai mafita guda d'aya chal, yanzu abunda nakeso da kai katashi kayi wanka peter ya had'a maka abinci ka ci domin Bala ya gayamin kwanaki 3 rabonka da ka ci abinci mai nauyi daga coffee sai Lipton ka ke ta faman, d'urawa cikinka.
Yatsine fuska Habeeb ya yi yace uhm....kai kana gani ina da kwanciya hankali da zan iya cin abinci"? malam kawai kafad'a min mafita d'in.
Mus'ab ya tabe baki yace ba zan fad'a ba har ka yi abunda na umarce ka da shi.
Habeeb ya yi ajiyar zuciya batare da ya tankawa Mus'ab ba ya tashi tsaye har yajuya Mus'ab yace jimana Lamido"! Habeeb ya tsaya cak yajuya yana tsotsa baki kamar yana shan sweet ya akayi ne.
"Cikin tsokana Mus'ab yace Allah yasa bakajin kashi domin nasan halinka indan har ka hau toilet seat za ka iya d'aukar dogon lokacin baka fito ba ni kuma sauri nakeyi Hannah darling na jirana zan fita da ita unguwa.
"Dogon tsaki Habeeb ya ja kamar zai gutsire halshenshi ya yi kwanfa had'e da juyawa yanufi bedroom d'inshi Mus'ab da Bala suka kwashe da dariya Bala ya tsagaita da dariyar da yake yi yace gaskiya wannan leesa ta rikita boss da yawa har wani sanbatu yake yi kamar mai ta6i hankali yana k'arasa magana shi da Mus'ab suka k'ara kwashewa da dariya.
''Mus'ab yace kaga malam Bala abunda yafi bani dariya a duk lokacin da na tuna da wani furucin da Lamido yake min _Mus'ab kadaina 6ata lokacin a soyayya kanemi k'udi domin sune magani kowace irin matsala bai wai kadinga kashe lokacinka a shirme banza da wofi soyayya ko 6ata lokacin_
Mus'ab na dasa aya suka k'ara barkewa da dariya sai kace wani abun farin ciki ne yasame su.
"Habeeb na fitowa daga wanka ko kaya bai saka ba yanufi parlour sanye da bathrobe Bala da Mus'ab suna daura idanunsu akanshi suka k'ara bud'e Sabon babi na dariya.
'' cikin angry voice yace yadaka musu tsawa wannan wane irin wulaqancin ne"?
Ya za'ayi Ku mayarda ni kamar wani mahaukaci tun d'azu Ku ke ta faman yi min dariya, gaba d'ayanku Ku tashi Ku fita min daga parlour I don't whats you help yak'arasa magana cikin shouting fuskar nan tayi jajir kamar Jan k'osai{lol}.
Bala ya mik'e sannu alaikum yafita Mus'ab ya kasa control dariyarshi a zuciye Habeeb yajuya kamar zai tashi sama ya haura staircase yana shiga bedroom yafad'a bisa gado ya runtse idanunshi hawaye na zuba yafara magana shi kadai kamar mai Sabon hauka _how couldn't you this to me"? Kinga ni ko leesa Mus'ab da Bala suna min dariya suna mini kallon mahaukaci tabbas ni mahaukaci ne a sonki I'm crazy about you don't make my life miserable I beg you leesa please come back to me_
"Tsawon lokacin yadauka cikin mayuwacin hali daga bisani ya mik'e ya sanya kayanshi ba zance Shafa mai.
Duk wata hanya da Habeeb yasan zai bi don yasami gani Haleesa ko yaji muryarta abin ya faskara a takaice yarasa mafita zafin kanshi yak'ara k'aruwa tun yana kiran madam a waya yana magiya har yagaji yadaina in yakira Hannah tak'i picking, cikin d'an k'ank'anin lokacin Habeeb yadawo abin tausayi.
_2 weeks later_
Habeeb yana kwance a bedroom d'inshi sai fama rawan sanyi yakeyi hak'ora shi na had'ewa Bala yashigo ya durk'usa gabanshi yasa pity face Dan Allah boss kayi hak'uri ka barni na kira Dr saleem ya duba ka.
"A harzuk'e Habeeb ya gallawa Bala harara banaso kuma ina gargad'inka kada ka k'ara zuwa inda nake ku barni na mutu.
"Bala yadafe kai yak'ara yi k'asa da murya yace boss ko na kira madam a waya na fad'a mata halin da ka ke ciki"?
''Kada ka sake ka fad'a mata nafiso sai na mutu akai Mata gawa na Bala ya mik'e a sanyaye yafita tausayin Habeeb ya lullu6enshi nan take wani tunani yafado mishi yanufi parking lot yaja mota da k'arfi yafita.
"Direct gidan madam Hindu yanufa a parlour yatarar da Haleesa da Hannah suna kallo Indian movie ya yi sallama yanemi kujera ya zauna idanunshi sun kad'a sunyi jajir ya dube Hannah yace Hannah madam tana nan kuwa"?
Batanan ta tafi Lagos d'azu da safe lafiya Bala naganka a rikice"?
Cikin raunin murya yace a gaskiya hukuncin da aka yankewa boss ya yi tsauri da yawa yau tsawon sati 2 kenan baya cin abinci yadaina walwala bacci ya kauracewa idonshi shin waye baya kuskure a rayuwa"?
Haleesa ta zaro ido numfashinta na fita da sauri-sauri.
Bala yacigaba da cewa a halin yanzu boss bashida lafiya sosai ya hanani na kira Dr ya duba shi indan wani abun yafaru da shi Haleesa kece sila.
"Haleesa ta mik'e tsaye ta rikice iya rikicewa tafashe da kuka Hannah ta mik'e tadafa kafad'arta ba kuka za ki yi ba mayafi za ki dauko mu je mu gw hali da yake ciki da gudu Haleesa tajuya tanufi bedroom Hannah ta Mara mata baya ba su wani jima ba suka fito.
Akan hanya Bala yake basu labarin irin mayuwacin hali da Habeeb yashiga suna isa gidan tun kafin yagama parking Haleesa ta balle k'ofa tafita...
Jeeddah Aliyu
[8:10AM, 17/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [12/16, 9:45 PM] +234 803 391 3132: [16/12 6:20 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
_Double sorry fans