Showing 45001 words to 48000 words out of 132766 words

Chapter 16 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87944

had'e da Murmushi.
Tun lokacin da yafara magana kai Haleesa yana sunk'unye a k'asa hawaye na bi kumatu ta, Habeeb ya mik'e tsaye hannunshi guda yana ciki aljihu yanufi inda Haleesa take Zaune daf da ita ya tsaye yad'an rankwafa yace ke!
A firgice ta d'ago tasauke ganinta akan fuskarshi k'asa jure kallon tsanar da yakeyi mata ta yi ta sada kanta k'asa.
Murmushi jin dad'i Habeeb yasaki sakamako hawaye da yagani akan fuskar Haleesa yace you hears all what's am saying right"?
K'asa magana ta yi kawai tad'aga masa kai cikin isa da tak'ama yacigaba da cewa "Don't you think is too early ace kin fara zubar da hawaye ki"?
"Is better ki share hawaye ki saboda bai kamata kifara zubar da su tun yanzu domin ina da buk'ata su a gida na Haleesa tacigaba da share hawaye ta masu masifar Zafi da k'ona Zuciya.
"Habeeb ya ja tsoki had'e da cewa kina da aiki yarinya ya yi dialling number Bala yak'ara a kunnenshi "Hello! Bala wai me kike yi ne da har Yanzu ba ka k'araso ba"?
"Boss ina k'ofar gida nufina na dan ba Ku wuri za ka fi jin dad'i sakewa Ku sha fira
Kai! Banaso shirme banza da Wofi na baka _3 minutes_ ka shigo ko nayi maka abunda ba kayi tunani ba yana k'are magana ya yi hanging up"
Haleesa ta sa gefen hijab d'inta ta goge hawaye ta "Bala yashigo had'e da sallama yadire wani k'aton kwali had'e da farar Leda Habeeb ya dube Bala yace na ba ka "5 minutes kayi Mata bayani abunda ke ciki ni ina k'ofar gida kuma karka sake ka wuce time d'in na ba ka yaficewar shi batare da ya dube inda Haleesa take Zaune.
Bala yace ranki yadad'e dama "invitation card's ne mu kawo miki ga kuma waya nan akwai sim card a ciki had'e da numbers in "boss duk abunda Ku ke buk'ata Ke da k'awaye ki a lokacin biki sai ki kira "boss gobe insha Allah Zan zo na fita da Ke 'kawayeki Ku kai wa 'yan uwa da abokai arziki katin gaiyyata
[11/10 7:01 pm] Jeeddah Aliyu🌹: Har Bala yadasa aya a zance shi Haleesa bata ce komai ba gani ta yi shiru yasa yace ranki yadad'e kin yi shiru ba ki ce komai ba"?
Saida tasauke Numfashi daga bisani tace Zai fi kyau kayi min Serving in number domin bana tunani zan iya "calling in wani''
"Bala d'an murmusa yafito da Biro daga gaban aljihu shi ya rubuta number shi akan kwalin da yashigo da shi ya yi mata sallama yafice.
Saida Haleesa ta share tsawon "10 minutes kafin tashiga cikin gida kaitsaye tashiga d'akin Ammi ta ajiye kwalin hannunta bata ce da Ammi komai ba ta nufi d'akinta.

```WASHE GARI ```

Tun misali k'arfe 10:30am Bala ya zo yadauki Haleesa da k'awaye ta suka tafi raba "invitation saida suka share kwana ki 3 suna raba invitation tun safe in suka fita sai da yamma lis suke dawowa.

```ON TUESDAY ```

Ita ce ranar da aka fara gudanar da shagalin biki kamu za'a yi a gidan Aunty Juwairiyya tun daga Lagos Madam Hindu ta yo "Booking d'in Aunty funke da yaranta suka k'awata gidan Aunty Juwairiyya da "Decoration yayinda Aunty funke za ta yi wa Amarya Haleesa Makeover tun lokacin da Haleesa tashiga "bathroom da suna wanka ta rufe k'ofa tun Aunty funke tana saka ranta fitowar ta har tagaji da jira tafito daga bedroom ta nufi parlour wurin Aunty Juwairiyya ta Fad'a mata abunda ke faruwa a harzuk'e Aunty Juwairiyya tanufi bedroom d'in tadinga knocking in k'ofar had'e da kiran sunan Haleesa shiru kamar ba mai rai a ciki Haleesa da ke Zaune dirshan a tiles d'in bathroom tasaka kanta tsakiyar cinyoyinta sai faman shashekar kuka take bata tunani akwai Wanda ya isa yasaka ta ta bud'e k'ofar nan har sai sun gama shirme su, jin yadda Aunty Juwairiyya take duka k'ofa yasa Haleesa tace Aunty ki daina wahalarda kanki bara ta6a bud'e k'ofar nan har sai kun gama shagalin bikinku.
Cikin 6aci rai Aunty Juwairiyya tace a gidan uban wa Haleesa kika ta6a gani anyi kamu ba Amarya"?
"Daga yau za'a fara a kaina Haleesa tafad'a had'e da murgud'a baki...


Jeeddah Aliyu🌹
[10/24, 11:44 AM] ‪+234 813 417 9191‬: [15/10 4:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```62```

Note:- _na yi kuskure a wurin fadar sunan garin a farko labari mai karatu zai ji nace yola a wani wurin kuma zai ji nace Yobe to yola ne ba Yobe da fatar za'a gafarce ni_

_10:30am_

"Habeeb na tsaye gaban "dressing mirror yana sharce suma shi da "Comb Mus'ab ya murda handle ya shigo ta mirror ya had'a ido da Habeeb ya kyalkyale da dariya da sauri Habeeb ya had'e rai ya d'auke kai yace banaso iskanci Mus'ab hali yanzu ka fara kaini bango tun dare jiya ka ke ta fama yi min dariya shin akwai uban da baya mafalki ne da za ka sakani a gaba kana dariya, Mus'ab yak'ara kyalkyalewa da dariya har yana dukan gefen bed abunda yak'ara harzuk'a Habeeb ya jefa masa comb in hannunshi ka ga Mus'ab na rok'e ka da ka had'a "luggage in ka ka bar min gidana Mus'ab ya tsagaita da dariyar da yake yi au abin har da su kora to ba ida zan tafi ina nan tare da kai har sai Amarya ta zo''
Amma kuma kaima kana da gida sai ka je gidanka ka tare ka jira zuwan Amarya ni kan bara iya cigaba da zama da mahaukaci"
Kyalkyalewa da dariya Mus'ab sake yi yace to ae ni narasa gane tsakanin ni da kai waye mahaukaci ko ka manta kuka ka ke yi wa mace a mafalki wannan ke nuna cewa kai d'in zarare ne Mus'ab bai jira me Habeeb zai ce ba ya juya yafi ce daga d'akin yana dariya shak'iyanci Habeeb ya bi shi da kallo daga bisani ya ja tsoki kai amma yarinya nan ta gama da ni me ke shiri faruwa da ni da na ke mafalki na sadu da ita"?
Lallai sai na musgunawa yarinya nan sai ta yi danasani zuwa mini a mafalki cike da takaici ya murd'a handle yafi ce Mus'ab ya tarar akan dining table yana breakfast batare da ya dube ida yake zaune ba ya ja kujera ya zauna, chef Peter ya yi masa "saving har suka gama breakfast ba Wanda ya tankawa d'an uwanshi Habeeb ya dube ida yake zaune yadauke kai in ka ga dama katashi mu tafi Mus'ab ya yi murmushi had'e da cewa gaskiya tsarin gidanan ya burgeni matuk'a ba k'aramin more rayuwa za Ku yi kai da Amarya Haleesa wai... Ina nufi dream girl domin Haleesa bata kai matsayin da za'a more rayuwa da ita ko ba haka bane aboki na"?
Ran Habeeb yak'ara 6aci jin yake kamar ya zabgawa Mus'ab mari ya ja tsoki ya fice daga parlour Mus'ab ya Mara masa baya yana dariya har suka iso gidan Madam Hindu Mus'ab yana tsokanar Habeeb tun yana jin zafinshi har yagaji ya zuba masa na mujiya.

_8:00pm_

```HALEESA```

Duk lokacin da Haleesa ta tuna cewa saura kiris ta zama mallaki Habeeb Lamido sai ta zubar da hawaye ta yi nisa a tunani Aunty Juwairiyya tashigo Haleesa ki tashi ki je wanka Aunty funke na jiranki za ta yi miki makeover na tafiya _Dinner_ Haleesa ta kwa6e fuska wai ni Aunty dole ne sai na je dinner"?
"Dole ne Haleesa sai kin je don haka ki tashi ki je ki yi abunda na umurce ki Karki 6atawa mutane lokacin''
Haleesa ta shar6e hawaye na fahimce cewa Aunty Juwairiyya ko tausayi na bakyaji ta kare magana had'e da mik'ewa Aunty Juwairiyya ta tabe baki sai anan a gaba za ki gano alkhairi da ke cikin wannan aure"
Tun da zuciyata bataso
Ya za'a yi na fahimce akwai alkhairi a wannan aure kawai zan yi biyayya da dukkan Umarni da ki ka bani domin banida mafita bata jira jin abunda Aunty Juwairiyya za ta fad'a ba tashige "bathroom.
"Aunty Funke tsantsarawa Haleesa kwalliya wance tafi ta jiya kyau da tsaruwa Amarya Haleesa ta yi matuk'ar kyau cikin wedding gown "golden colour" da head blue colour kafarta sanye da blue hill's hannaye da k'afafuta sun sha Zane k'umshi ja da baki Haleesa ta nemi gefen bed ta zauna ta zabga tagumi gani take wannan abun kamar almara hawaye suka wanke mata fuska da sauri Aunty Funke ta rik'o hannunta haba! Haleesa me yasa bakya gajiya da kuka"?
Haleesa ta sada kai k'asa had'e da ja majina da k'arfi tana k'ok'ari danne hawayeta Aunty Juwairiyya tashigo d'akin ta yi turus ya akayi ne sarkin kuka"?
Ki sausautawa kanki Haleesa wannan kuka bara ya K'ara ki da komai ba kullum kuka abu yak'i ci yak'i cinyewa sai hawaye ki sun kare a wofi tashi mu tafi karki 6atawa mutane lokacin''
Da kyar Haleesa ta mik'e hawaye na ta ambaliya akan fuskarta Aunty Funke ta rik'e ta Haleesa ki daina kuka karki 6ata kwalliyarki kinji"?
Saida tak'ara Jan majina sannan tad'aga kai Aunty funke tayago tissue ta yi wiped in hawaye fuskarta ta k'ara Shafa mata powder sai ga fuskar Haleesa na kyalli kamar ba ita ne tagama kuka Aunty Juwairiyya ta wuce gaba Haleesa da Aunty Funke suna biye da ita har zuwa "Compound Aunty Funke ta bud'e mota kirar "Lexus 2016 model'' ta zaunar da Haleesa cikin dusashiya murya Haleesa tace Aunty bara iya tafiya ni kadai ki kira Zainab da khadeejat mu tafi tare'
"Aunty Juwairiyya ta kya6e baki tace tuni Zainab da khadeejat suka tsofa a "Hotel in da za'a yi dinner in kin je kya had'u da su Aunty Funke ta rufe mata k'ofa driver ya ja mota yayinda Aunty Juwairiyya da Aunty Funke suka shiga ta su mota had'e da marawa motar da Haleesa take baya.

```HALL```

Motar su Haleesa ta yi parking har driver ya bud'e mata k'ofa ta zuro k'afarta d'aya Hannah ta dakatar da ita karki fito Haleesa koma ciki sai yaya Habeeb yak'araso za ki fito"
Yatsine fuska Haleesa ta yi batare da tace komai ba ta mayarda da k'afarta tsawon _6-7 minutes_ ta dauka zaune a mota tana jiran k'arasowa Habeeb sai gashi ya iso tare da Mus'ab"
Hannah ta bud'ewa Haleesa k'ofa tafito Haleesa na kyalla ido ta sai akan Habeeb Lamido yana sanye da suit "sky blue ya yi matuk'ar kyau yafito balarabe sak gabanta ya yanke yafad'i jikinta yafara "sharking kamar wance "electric shock ya ja da sauri ta d'auke kai a Zuciyarta tace shi wannan wai bashida kayan ne hatta da ranar Aurenshi suit zai saka "huh! Ta tabe baki jin ta yi an rik'e hannunta tad'ago da sauri Hannah ta gani damk'e da hannunta ta nufi wurin Habeeb Lamido da ita shima ta rik'o hannunshi ta had'e da na Haleesa ba yadda ya iya dole ya rik'e hannunta a lokacin d'aya wani shock ya ja su Wanda ya yi sanadi dagowarsu suka had'a ido kallon k'asan ido yake mata yayinda Haleesa takasa jure kallon ta d'auke "eye's ball in ta k'awaye Haleesa da friends in Habeeb Lamido suka fara haska su da camera wayoyinsu hannaye su na sark'e suka fara tattak'i bisa lallausar blue carpet Habeeb ya lalla6o yatsu Haleesa ya matse su da k'arfi tsanani zafin ratsa ta wabi irin zufa ya karyo mata jin take kamar za ta saki fitsari ta bud'e baki da kyar cikin wahalaliya murya da ke nuna ba k'arami zafin take ji tace it's hurt yaya Habeeb Dan Allah kadaina ko kallonta bai yi ba sai ma 'kara matse ta da ya yi a haka har suka k'arasa akan high table da aka tanada domin su a tunani Haleesa in suka zauna Habeeb zai sake mata hannu sai taga sa6ani hakan cigaba ya yi da murza mata yatsu da k'arfi yake murza su
[15/10 7:14 pm] Jeeddah Aliyu🌹: Haleesa tad'ago idanu ta taf da hawaye ya kalle Habeeb fuskarshi a had'e ya dank'ara mata harara da sauri ta sunkuyar da kai, Mus'ab yak'araso yadafa kafadar Habeeb yakai bakinshi dai-dai kunnenshi ya yi mishi rad'a haba! Ango na Haleesa da leesa ka Saki ranka mana duk yawan jama'a da ke wurinan saboda Ku suka zo amma kai wani had'e fuska "Habeeb yatsine fuska ya k'akaro murmushi dole Mus'ab ya yi dariya maras sauti ya d'an daki kafadar Habeeb "Good job abokina ya juya wurin Haleesa yace Amaryamu ya haka naga kin wani had'e fuska Dan Allah ki saki ranki ki k'awata kyakyawa fuskar nan taki da sanyaye murmushi Haleesa tasaki murmushi yak'e mai kama da mai so yi kuka "Ma'aruf MC ya umurce ango da Amarya su fito su d'an taka rawa Jikin Haleesa yadauki rawa tsawon rayuwarta bata ta6a rawa ba Habeeb, ya mik'e yad'an rankwafa dai-dai kunnen Haleesa kamar zai rada mata abun arziki ke! Villager tashi mu je karki yarfa ni a gaban jama'a ace Habeeb Lamido ya auro 'yar Daji tad'ago dara-dara idanuta masu d'auke da kwalla tasauke su akan fuskarshi alama ya yi mata da girar idonshi tadaina kallonshi da sauri ta d'auke idanuta yana rik'e da hannuta suka nufi tsakiyar fili Haleesa kan tsaye ta yi k'ik'an yayinda Habeeb Lamido yake juyi da hannaye Haleesa tuni filin ya rikice sai ruwan naira ake musu Maryam ta ratso tsakiyar filin ta nufi wurin Habeeb ta 6alle pose in ta taciro bundle na N1000 tasoma yi masa lik'e ta fakaci idanu mutane ta bangaje Haleesa ta matsa daf da Habeeb kamar za ta shige k'irjinshi kallo d'aya Haleesa ta yi musu ta dauke kai nan take ta ji wani bak'o yanayi na shigarta Mus'ab ya ankara da waina da ake toyawa ya yi wa Habeeb rad'a wani shegen murmushi yasake yarik'o hannun Haleesa su ka koma wurin zamansu sai misali k'arfe _12:15am_ aka tashi daga dinner har izuwa lokacin Habeeb na rik'e da hannun Haleesa yana Gana mata azaba ta hanyar matsi mata yatsu har wurin mota Habeeb yaraka Haleesa ya matsa daf da k'ofar mota ya yi k'asa da murya kamar mai rad'a Ina fatar za ki k'ara jajircewa ki zama jaruma domin zama da Habeeb Lamido sai jarumar mace ya wani dage girar sama oh! Kina mini kallon marigayi saurayinki koh"?
To ki yi gaggawa ki fitarda da hakan daga ranki na barki lafiya Amarya taa yak'arasa magana had'e da sakin tsadad'e murmushinsa yabar Haleesa sake da baki tana mamaki shu'umanci sa.

```ON FRIDAY ```
_2:30:pm_

Tun daga farko layin su Haleesa har zuwa karshe sa d'an mutum ne ba matsaka tsinke tarin jama'a 'yan dauri aure ne Habeeb Lamido na hango cikin farar shadda d'inki babbar Riga kanshi d'auke da farar hula kum6e Mus'ab da khaleel sun saka shi tsakiya sai fama washe hak'ora dole yake k'arfe _2:40pm_ dai-dai dunbanni jama'a suka sheda daurin auren Habeeb Lamido da Haleesa Usman akan sadaki naira dubu d'ari ana Shafa fatiha gaban Habeeb yafad'i a zuciyarshi yace shikenan yarinya nan da tsana ta zama mallaki na ya yi murmushi had'e da Shafa gajerar gemun shi.

_5:00pm_

Aka gudanar da walima inda aka gaiyyato malama Hafsat Umar ta yi Nasiha akan zamantakewar Aure tafad'i irin azabobi da Allah tanardawa duk mace da bata biyayya ga sunnah ma'aiki s.a.w bayan gama wa'azi yaran Aunty funke su dinga raba katuwar jakka mai d'auke da pic d'in Amarya da ango in ka bud'e jakka za ka tararda 'yan uban kaya daga ciki har da atamfa mai kyau gaske tun lokacin da aka tashi daga walima Haleesa keta faman rusa kuka ta tsorata murtuk'a da Nasiha da malama Hafsat Umar ta yi nan take ta k'udiri anniya yi wa Habeeb Lamido biyayya koda ace zai dinga yanka naman jikinta bara ta ta6a tsalleke umurni sa.

_9:44pm_

Haleesa na durk'ushe a gaban iyayyeta suna kora mata Nasiha duk akan zaman aure yayinda Haleesa ke kuka kamar ranta zai fita Baffa yarik'o hannunta yanufi k'ofar gida yasanya ta cikin mota ya mik'a mata Al-qur'ani da pray mat had'e da casbaha yace Haleesa ki rik'e wannan domin shine magani kowace matsala ta d'an Adam Allah yabaku zaman lafiya yabaku zuri'a dayyaba Haleesa tak'ara fashewa da wani sabon kuka Baffa ya umurce driver yaja mota su tafi har aka fita daga unguwarsu tana kuka kamar ranta zai fita....

Jeeddah Aliyu🌹
[10/24, 11:44 AM] ‪+234 813 417 9191‬: [13/10 6:02 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```61```

Matuk'ar na kirga 3 ba ki fito ba wallahi zan kira Baffa a waya na Fad'a mishi abunda ki ke shirin aikatawa nasan duk iya shegenki kina tsoro Baffa"
Sosai Haleesa ta tsorota da jin furucin Aunty Juwairiyya ba shiri da mik'e ta bud'e k'ofa suna had'a ido da Aunty Juwairiyya wance ta cika ta yi fam cike da takaici ta gallawa Haleesa uwar harara d'auke kai Haleesa ta yi kamar ba ta ga Aunty Juwairiyya na harara ta, ta ra6a gefen ta za ta wuce cikin Zafin nama Aunty Juwairiyya ta fisgota ta igizata cikin "bathroom koma ciki don gidanku ki yi Wanka ko kina nufi bara ki yi Wanka ba"?
Idanuta taf da kwalla tace to ni Wanka me zan yi"?
"Bansaniba Aunty Juwairiyya tafad'a a zafafe tacigaba da magana ta hanyar nuna tsanani 6acin ranta wallahi Haleesa ki kiyaye ni sai na yi mummuna sa6a miki idan ki ka sake kwatata irin Wannan shashanci so ki ke mutane duniya su zage mu ace mu yi miki Aure dole.
"Haleesa ta shar6e hawaye had'e da k'argame k'ofa kuka takeyi sosai har ta gama Wanka tana kuka, idanuta sun yi luhu-luhu tana fitowa Aunty Funke tafara aikin nata na tsatsara mata Make-up ta kece raini ta yi matuk'ar kyau Aunty Funke ta fito da "Wedding gown ash& black colour ta mik'awa Haleesa tace ga wannan ki saka Yatsine fuska Haleesa ta yi ta Wani turo baki da ya masifar K'ara mata kyau tace me zan yi da Wannan abar"?
Galala Aunty Funke ta yi da baki tana duban Haleesa "OMG! Ni kan banta6a gani "Bride da irin wannan hali ke da yakamata ki yi farin ciki wannan fa ranar ki ce "Humm Haleesa tafad'a had'e da kyabe baki bata k'ara bin ta kan Aunty Funke ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login