Showing 81001 words to 84000 words out of 132766 words

Chapter 28 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE HAUSA NOVEL

HAUWA   

22 Oct 2024

87970

"Haleesa ta yi murmushi domin tasan abunda Mus'ab yafad'a ba gaskiya bane Habeeb Lamido ne zai ce a bata hankuri ae ba yau ya sa6a cin mata zarafi Wanda yafi wannan ya yi mata bai ce a bata hankuri ba sai wannan.
''Idanunta suka ciko da hawaye bata damu da ta goge su ba, tace ba zan 6oye maka ba Mus'ab a da ina da ra'ayi zama da yaya Habeeb koda ace zai dinga yanka naman jikina sai yagajin don kanshi ya saleme ni, amma a yanzu nayi nadamar aurenshi ba don komai sai don ya kasance mashayi ni kan bara iya rayuwa da mashayin giya tak'arasa magana cikin shasshek'a kuka.
''Mus'ab ya zaro idanu a rikice yace giya fa ki ka ce Haleesa"?
''Kwarai Mus'ab abokinka mashayi ne Sam babu tsoron Allah a tare da shi a cikin gidanan yake shan abarsa ya yi tatul.
"Da mugun mamaki Mus'ab yake kallon Haleesa daga bisani yace to ke Haleesa menene shedarki Lamido yana shan giya"?
Ni kuwa nakeda sheda mu je part d'inshi ka ganewa idanunka Haleesa tashige gaba Mus'ab yana biye da ita saboda iya zamanshi da Habeeb yasan ko cigarette ba yasha asalima ya tsanin duk wani abu da yake saka maye.
''Haleesa ta turo k'ofa suka shiga cikin parloun ta nunawa Mus'ab glassblower da ke d'auke da jerin white wine kala-kala Mus'ab ya yi ajiyar zuciya ya bud'e glassblower yaciro bottle gudu ya mik'awa Haleesa da sauri ta ja baya tana wani zare idon Mus'ab ya kyalkyale da dariya yace ki k'ar6a mana so nake ki karanta rubutu da ke jikin bottle d'in a sanyaye Haleesa ta k'ar6a ta karanta juice ne da aka sarafa da fruits sannan kuma an rubuta non alcoholic Haleesa tasauke ajiyar zuciya wani sanyi ya ziyarce zuciyata ta runtse idanu daga bisani ta ware su cikin jin kunya tace gaskiya na yarda da maganar yaya Habeeb da yake cewa ni villager ce amma kuma Mus'ab karka ga k'auyancin na saboda ban tashi a gidan da ake shan irin wad'annan abubuwan ba.
Mus'ab ya yi murmushi yace ki kyalle Lamido shima bak'auye ne sannan kuma ba ke kadai ki ke kallon wannan juice a matsayin giya mutane da dama Wanda ba su San juice bane a haka suke kallonsa.
''Haleesa ta yi dariya tajuya Mus'ab ya Mara mata baya suka koma parlournta, yacigaba da bata hank'uri saida ya tabbata da ta hank'ura sannan ya yi mata sallama.
_5:00pm_
Haleesa tana zaune a parlournta Imaan ta isheta da rigima a dole sai sunyi wasan 'yar 6oya Haleesa ta yatsine fuska ta ajiye phone d'inta bisa hannun kujera ta rik'on hannun Imaan suka nufi compound daga idan suke zuwa main gate akwai tazara sosai Haleesa taciro d'an kwalin kanta gashinta yasauka a gadon bayanta, tace da Imaan zo nan babyn aunty na daure miki idanunki
''Imaan tadaka tsalle cikin shagwa6a tace Allah aunty ke ce first ni kuma second Haleesa ta yi dariya tace kai....ka ji min yarinya da wayyo tana magana tana daure fuskarta idanunta na rufe tace 1.....2....3.... Start tasoma lallu6en Imaan tana jin dariyar Imaan amma takasa kamata, haka tacigaba da lullube.
''Bala yaddano hancin mota cikin compound Habeeb na owners corner a zaune tun kafin su k'arasa parkingc space ya hango Haleesa da Imaan suna wasa yaja tsoki a zuciyarshi yace k'aramar kawai Bala yana dariya ya bud'ewa Habeeb k'ofa yafito
"Boss yau amarya ta tuna da k'urciya wasan 'yar 6oya sukeyi yak'ara sa magana yana wani Sosa kai.
Harara Habeeb ya watsa masa yace kadauko briefcase ka shigar min da shi ciki Yajuya yanufi cikin gida.
"Babyn aunty where are you I'm tight zan bud'e idanuna in bara ki bari na kama ki ba Imaan ta kyalkyale da dariya tace _yeee.... Aunty if you're can catch me_
Da sauri Haleesa tanufi idan takejin sautin muryarta dai-dai Habeeb yakawo da sauri Imaan ta boye bayanshi garin lallube Haleesa ta yi tuntube za ta fad'i da sauri Habeeb yatare ta tafad'o kan k'irjinshi..........


Jeeddah Aliyu🌹




[24/11 7:33 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```77```

_this page dedicated to you *Ayshat D'ansabo lemu* thanks for the love & support it's means a lot_

~~k'amshin perfume da ta yi amfani da shi ya ratsa k'ofufi hancin Habeeb baisan lokacin da ya lumshe idanunshi yak'ara matso da ita zuwa k'irjinshi ya matse ta gam Tsigar jikinta ta tashi Yarr! Hancinshi yadaura a gefen wuyanta yana shak'ar k'amshinta tuni Habeeb ya manta suna tsaye ne a compound yafita haiyacinsa, numfashinsa yana fita da sauri-sauri ya kasa daurewa ya ziro hannunshi cikin rigarta da sauri Haleesa ta taka masa birki ta hanyar furta _please yaya Habeeb stopped Imaan is looking at us_
A rikice yadawo hayyacinsa ya tureta daga jikinsa dama hausawa sunce tabarma kunya da hauka ake nad'eta sai kawai ya gallawa Haleesa harara _wannan wane irin sakarcin ne huh"?_
_shine illah auren k'anana yara dube ki wai wasa 'yar 6oya ki ke yi danasani na barki ki fad'i ki karya k'afa ko hannunki naga d'an iska da zai yi jinyarki dallah! Bani wurin in wuce kin yi wani tsare ni da idanu_
A zafafe yak'arasa shiga gida Haleesa ta bi shi da kallon tasauke ajiyar zuciya, tajuya ta hango Imaan zaune cikin flowers tana wasa sai faman tsinko Flowers take tana tarawa a gefenta, Haleesa tak'ara sauke ajiyar zuciya a cikin zuciyarta tace, _thank God_ ashe ba Wanda ya ganmu tanufi wurin Imaan tarik'on hannunta suka shiga cikin gida.
_9:00pm_
Haleesa na kwance a bedroom d'inta ta yi rub da ciki ta d'aga k'afafunta sama ta yi zurfi a tunanin rungumar da Habeeb Lamido ya yi mata d'azu da yamma abun yakasa fita daga zuciyarta duk lokacin da ta tuna da kyakyawar rungumar da tasamu a wurinshi sai ta yi murmushi ta kasa tantance wannan murmushin da take yi na menene ta yi wani juyi tadawo rigingine idanunta a lumshe tasoma fasalta kyakyawar Surar jikinsa ba abunda yafi burgeta a jikin Habeeb Lamido irin lallausar sumar kanshi koda yaushe idaunshi a lumshe suke kamar mai jin bacci da kyar Habeeb ya yi magana batare da ya ja iska ba kamar Wanda yacin yaji, yana yawan tsotsan bakinshi za ka yi tsanmani sweet yake sha in kuma yana magana d'aya-d'aya yake furta harafi sai kace mai bita, Haleesa ta yi murmushi a zuciyata tace _Handsome_ kenan ga kyau saidai mugun hali da miskilancin tsiya, ta mik'e zaune ta k'urawa wall clock idanu _10:09pm_ ta d'an ja tsaki ko kad'an batajin bacci dama Imaan ce abokiyar firarta tun 8:00 o'clock ta yi bacci.

```HABEEB LAMID'O```

Habeeb na zaune a parlournshi yana tura bayanai a system yunwa yakeji kamar 'yan hanjinshi za su tsinke ya rasa dalilin da yasa tun jiya da yacin abincin Haleesa d'andanon abincin yakasa fita daga bakinshi duk abunda yacin sai yaji ba tested yature laptop a gefe yanufi part d'in Haleesa cikin sand'a kamar barawo yak'arasa wurin dining table ya bud'e warmers k'amshin Egusi soup ya buge hancinshi ya cigaba da bud'e warmers yana ganin abunda ke ciki a zuciyarshi yace ba shakka wannan abincin yarinya nan ce ta girka shi yadauki Ledar tuwo semo guda d'aya yasaka cikin plate ya zuba soup a d'an k'aramin plate d'ayan plate kuma zuba farfesun kifi da sauri yakoma parlournshi yana ci yana wani kad'a kai _ashe haka yarinya nan ta kware da girki"?_
_Gaskiya tafi Peter iya sarafa abincin nayi kuskure wulaqanta ta saboda banta6a cin abinci da ya yi min dad'i irin nata ba kuma har abada bara ta6a nuna mata ina jin dad'in girkinta duk ranar da tagano ina cin abincinta ajina da girmana za su zube a idonta ni kuma bara sake da abunda zai rage mini class_
Ya cinye tuwon tass! Har da su sud'e plate daga bisani yanufi bedroom ya zarce bathroom ya yi brush agajiye yafad'a kan bed cikin d'an k'ank'anin lokacin bacci yadauke shi a cikin baccin nashi yafara mafalkin leesa Zaune take a garden tana wasa da ja da farin fure tashagala da abunda take yi a hankali yake sand'a har yak'araso daf da ita ya zauna tana juyowa suka had'a ido tasake masa k'ayatace murmushi shima ya mayar mata da martanin murmushin nata kasa d'auke idanunshi ya yi akanta cikin sigar shagwa6a ta turo d'an k'aramin bakinta mai jefa Habeeb cikin tsantsar sha'awarta _yaya Habeeb wannan kallon fa"?_
Cikin shauk'in so yarik'o hannunta ya jefa yatsanta a bakinshi yana tsotsa kamar yasami lollipop, da sauri leesa ta fisge hannunta ta wani yatsine fuska, Habeeb yadawo kalar tausayi chan k'asan mak'oshi ya furta _please leesa ki barni mana_
Shiru ta yi tana kallonshi da k'arfi yafisgota tafad'o kan k'irjinshi ya matse ta gam ya lalla6o bakinta tsawon lokacin suka dauka a haka daga bisani ta ture shi ta mik'e da gudu tanufi cikin yayinda shima ya mik'e ya Mara mata baya a parlour ya yi nasara kama ta ya d'auke ta chak! Yanufi bedroom da ita yadireta akan bed Daga nan komai yacigaba da wakana.
A firgici Habeeb ya falka daga mafalkin da ya zame masa, jiki gumi ya tsatsafo masa yadafe kanshi da hannayen, ya runtse idanunshi gam! Photon abunda yafaru tsakaninsa da Haleesa yadawo masa da sauri ya ware idanunshi ya ja tsaki cike da jin haushin kanshi ya mik'e yanufi bathroom.
Habeeb wanka ya ke yi yana zance zuci _me yasa duk lokacin da na kwanta bacci sai na yi mafalkin ina saduwa da yarinya nan"?_
_ina da wannan mafalkin nawa zai kasance gaskiya tabbas da ba k'aramin tafiyar da ruhina za ta yi ba_
Jiki ba lakka ya gama wanka yafito har aka yi kiran asuba yana fama da tunanin leesa da yarufe idanu kyakyawar fuskarta yake gani.
********************
_7:00am_
Haleesa na tsaye cikin kitchen tana had'awa Imaan abincin da za ta tafi da shi school tuni ta takatar da peter da Girka abinci da ita da kanta take shiga kitchen ta girka duk abunda ranta yakeso agurguje ta kamalla had'awa Imaan lunch box d'inta tanufi d'akin Imaan tayi mata wanka had'e da shirya ta cikin uniform ta zarce da ita dining area ta ja kujera ta zaunar da ita ta had'a mata tea had'e da chip's Imaan tana gama breakfast Haleesa tarik'on hannunta suka nufi compound suna, fita ta hango Habeeb da Bala a tsaye Habeeb na jefawa karnuka{ police dog's} nama suna Cin kasa k'arasawa parking space ta yi saboda tana jin kunyar had'a ido da Habeeb.
Imaan tadaka tsalle _yeee yau Daddy ya fiddo da Rahul da Rita bara naje mu yi wasa_
Da sauri Haleesa ta taka mata birki ta hanyar furta ke Imaan banaso shirme ke da za ki tafi school me ye gaminki da karnunka karki sake naga kin tsaya a wurinsu ko kinmanta yau za Ku fara test ne"?
Imaan ta girgiza kai Haleesa tace to kama hanya kitafi ga sa'eed driver yana jiranki ta mik'a mata lunch box d'inta Imaan tajuya tanufi wurin Daddynta _Good morning Daddy_
Morning my angel
Cikin shagwa6a Imaan tace Daddy shine saida kaga zan tafi school ka fiddo Rahul da Rita koh"?
Habeeb ya yi murmushi ya shafi kumatunta kin ga my angel banaso rigima kitafi school in kindawo auntynki ta fiddo miki su ku yi wasa.
"Imaan ta zaro ido kamar taga abun tsoro _Daddy aunty Haleesa tsoronsu fa take yi ranar ma mu je garden da ta gansu da gudu takoma cikin gida tadinga fad'a tana cewa shi wannan yaya Habeeb komai so yake yi yanzu yarasa abunda zai yi kiwo sai bak'ak'en karnunka sai nace da ita aunty ba fa sunansu karnunka ba sunansu R........_Imaan ta hadiye raguwar kalamanta sakamako katsinta da Habeeb ya yi my angel wannan labarin naki basan tsawon lokacin da zai d'auka kafin naji karshensa ki bari sai kindawo daga school ki k'arasa mun kinji"?
Imaan tad'aga kai sa'eed driver yarik'o hannunta suka nufi parking space
''Bala ya kyalkyale da dariya Habeeb ya galla masa harara Bala ya hadiye dariyarshi yace "Boss Imaan tana mugun burgeni saboda surutun nan nata.
Habeeb ya tabe baki yace ae dole ta burge ka saboda halinku d'aya
Bala washe hak'ora yace ni fa boss mamaki nake yi kai ga magana wuya take maka kuma ka tsanin yawan surutu sai gashi Allah yabaka 'ya mai bala'e surutu kamar Aku{parrot}
Habeeb ya ja tsaki yace _"Allah ya shiryeka Bala_
Bala yace ameen boss yau za'ayi ruwan sama har da k'ank'ara saboda ka yi min fata nagari da alama amarya tafara canza ka yak'arasa magana yana dariya
''Tsawon lokacin Habeeb yad'auka yana kallon Bala daga bisani ya girgiza kai, yace tun da kagama surutun naka daga ciki har da yi mun sharri sai ka tattara rahul da Rita ka mayarda su d'akinsu karka d'aure su kabarsu a sake kuma ka tabbata ka rufe musu k'ofa.
"Bala yace angama boss ae tun da na fahimcin amarya tana tsoronsu bara yi sake da za su fito su tsorata maka ita.
Habeeb ya yi murmushin takaicin yajuya yasan muddin yacigaba da tsayuwa Bala zai iya haddasa masa bugawar zuciya direct parlourn Haleesa yadosa bata ciki tana bedroom ya yi tsaye a tsakiyar falon yana k'are masa kallo _very neat_ sai k'amashin turaren wuta ke tashi karaf idanunshi suka hasko masa dining table da sauri yanufi wurin ya yi serving d'in chip's had'e da sauce na cabbage da carrot ya ji anta da k'oda dai-dai lokacin da Haleesa taddano kai parlourn ta hango abunda Habeeb
Yake yi da sauri ta la6e tana lek'onshi tana kallonshi har yashige part d'inshi Haleesa ta yi murmushi ta kad'a eye's ball d'inta lallai Habeeb lamid'o d'an rainin hankali ne ko ya manta da kirarin da ya yi kada na kuskure na dafa ko da noodles da sunanshi sai gashi na kama shi yana satar mun abinci daga yau bara ka k'ara ganin abincin ballantana har ka sata
"ta yi murmushin mugunta tun daga ranar Haleesa da tayi girki take zube abinta cikin warmers takai bedroom da, Habeeb yasud'ad'o yacin mai dad'i yatarar da dining table wayam!
Duk lokacin da Habeeb Lamido ya zauna bashida aiki sai tunanin Haleesa kuma baya iya cin abincin kowa sai nata yadda peter ya jera masa abincin haka zai dawo yadauke saboda ko kallon bai ishe ba cikin d'an k'ank'ani lokacin Habeeb yafara fita hayyacinsa, ganin yadda sha'awar Haleesa na neman kassara shi ya tattara kayansa ya haura Germany a tunaninshi in ya nisanta da ita zai manta da duk wani abu da yashafe ta baisan cewa hakan ba abunda zai k'ara masa sai d'inbin damuwa, da tunani kuma yak'i ya amince da soyayya Haleesa ce ta kama shi ba sha'awa ba.
*****************
```GERMANY```
Habeeb yana zaune a wani had'ad'en wurin hutawa kallon d'aya za ka yi masa kagano yana cikin damuwa yadda zuciyarsa ke azalzalarsa akan ya kira Haleesa ko muryarta za ta rage masa damuwar da yake ciki zuciyarsa na bugawa Ya yi dialling number ta.
Haleesa na zaune Imaan tayi pillow da cinyoyinta kiran Habeeb yashigo wayarta ta zaro idanu gabanta na fad'uwa ta yi picking................

Jeeddah Aliyu🌹



[25/11 4:57 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```78```

~~cikin muryarta mai sanyi da zak'i ta furta _hello_ Wani irin sanyi ya ziyarce zuciyar Habeeb har ya yi nasara saukar masa da natsuwa, ya sauke ajiyar had'e da lumsashe idanu tsabar miskilancin irin na Habeeb Lamido a maimakon ya furta abunda ke neman raba shi da jin dad'insa sai kawai ya yi shiru yayinda katin wayarshi{recharge card} ke tafiya a banza jin shiru nashi ya yi yawa yasa Haleesa tak'ara cewa _hello_ ya ja iska ya fesar adak'ile yace ki ba wa Imaan waya zan yi magana da ita, jiki a sa6ule Haleesa taciro wayar daga kunnenta ta d'anko hannun Imaan ta daurawa mata ranta a b'ace tace ki yi magana da Daddynki, ta rafka tagumi tunanin hali irin na Habeeb shin ko ya manta da matsayinta na matarshi da bara iya tambaya ko da lafiyar jikinta ne ta ja d'an siririn tsaki ta mayarda hankalinta wurin Imaan tana sauraro yadda ta ke zuba masa surutu, mai d'auke da tambayoyin _Daddy ina ka tafi ne na daina ganinka in na tambayin aunty Haleesa ina ka ke sai tace batasaniba''?_
''A hankali Habeeb ya bud'e idanunshi ya cize lips d'inshi na k'asa kenan yarinya nan bata ma damu da ni ba ni kadai nake fama da sha'awa da tunaninta.....cike da jin haushin Haleesa yaja tsaki yace my angel na yi tafiya shiyasa ki ka daina ganina.
'' Daddy Ya sunan garin da ka je"?
Ya yi murmushi a kasalance ya furta Germany
"Daddy yaushe za ka dawo"?
Dafe goshi ya yi saboda yafara gajiya da tambayoyin Imaan da kyar ya furta very soon my angel
Daddy me za ka siyo mun"?
_Anything you wants my Angel_
Imaan ta yi shiru tana tunanin abunda za ta fad'a kamar daga sama tace Daddy ka siyo min monkey da snake da lizard da......cikin zafin rai Haleesa ta kwace wayarta ta yi hanging up ta gallawa Imaan harara ke wace irin yarinya ce Imaan"?
Duk lokacin da Daddynki ya yi tafiya bara ki lissafa masa abun Kirki da zai siyo miki sai na banza da wofi ko angaya miki nan gidan zoo ne da zai kwaso wad'anan tarkace ya kawo miki.
Imaan ta kwa6e fuska kamar zai ta yi kuka cikin shagwa6a tace aunty ban gama magana da Daddyna ba kin kar6e waya
''Haleesa ta tabe baki ta shafi sumar kan Imaan tace ae kin gama magana Imaan fatana d'aya kada Allah yasa wannan Daddy naki 0ne & d half ya biye wa shirmenki ya kwaso miki wad'annan masifun da ki ka lissafa saboda, shima irinki ne bai ji sauki ba ta k'arasa magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login