Showing 24001 words to 27000 words out of 81703 words

Chapter 9 - NI NA RAINETA COMPLETE HAUSA NOVEL

FCWA   

20 Dec 2025

32

Ubangiji ya raya miki zuri'arki ya albarkacesu, ya raba ki da ma?iya, ya sanya albarka a rayuwarki da ta iyalinki, tashi ki je ki fara shirin komawa Wakinki", na gyaWa kai tare da cewa "in sha Allahu Malam, za ka sameni bai bin umarninka da shawarwarinka, na gode sosai, Allah Ya ?ara lafiya da tsawoncin rai, na gode sosai" ko da na tashi babu kuzari a tare da Ni, haka na shiga Waki na jaSe, baccin da ban cigaba ke nan. Tun daga nan Inno ta shiga shirin tafiyata Inna na taya ta, wani abin nasu ma dariya ya Win ga bani don sosai suke aikin haWa min kayan ?arin ni'ima ba su san wanda nake amfani da su ba haWaWWu ne wasu ma daga Indonesiya, amma Alhaji ya tsallake ni ya daka Inya a gadon aurena, ina dai sha da ci don ko ba komai da nagartattun kayanmu ake samar da su, ko ba don ni'ima ba sa ?ara ma wani abun, na dai ?udurta a raina shimfiWa har gaban abada ba zan kuma haWata da Muntari ba, tsohon injina zan adana shi ba zai kuma tashi ba har ?arshen rayuwata.

Ana gobe zan koma mulkeni Inna ta yi da lalle wanda ya sha haWi, ta haWa kurkur Winta da ?wai da madara ta dilkeni, sosai farar fata ta ta Wauka sai she?i take yi, Ni dai dariya kawai nake wa tsofaffin yadda duk suka gigice suna ta gyarani, ba su son babu abin da bana yi ba, gyaran jiki ?arshen watan duniyan nan sai na je da gyaran ?afa, da rana Inna ta kira mai lalle da kitso, aka yarfa min ?ananun kitso har suka zubo a dokin wuyana, har wasu ?ananun duwatsu Inna ta siyo aka kitse min kan da shi sosai kuwa ya yi kyau wallahi har ba a magana, aka yarfa min lallen saletif ya yi raWau a hannayena da ?afafuna, ko da na kalli madubi sai na ganni kamar wata matashiya wadda ba ma za ka ce ta yi talatin ba, a daren ranar raba dare muka yi da Inno muna hira tana bani shawarwari, sai da Waya da rabi ta doka muka kwanta, washegari ko kafin na tashi Inna ta ji?a lalle ta zuba iyayen madarar turare, da na yi wanka ta sakani tsugunno kan wasu itatuwa da ta haWa da kanumfari. Sai da iccen ya ratsa jikina na tashi, bana so na ce musu su bar wahalar da kansu don ba zan kuma haWa shimfiWa da Muntari ba, amma na san suka ji ?arshenta Malam ya yi min kaca-kaca da wa'azi wanda ba na ma son ji bare ya sanyaya zuciyata na fasa. ?arfe sha biyu direban gida ya zo Waukata a sabuwar mota, Inna ta tisani na ?ara wanka na sake da na ji?a??en lallen nan da ya sha turaruka, ko da fito kai ka ce an yi Sari ne na kantin turare a jikina, na saka atamfa mai laushi, fara tas sabuwa mai adon ja da kore, Winkin riga da zani, na feshe jikina da turarena bakarat rouge,sai ga ?walla a idona kamar ?aramar yarinya, haka na shiga mota iyayena da ?an uwa, ma?ota na ?warai na ta kwararo min addu'a.

Ko da muka isa na sanya ?afata guda waje ta taka ?asar gidan Muntari sai na ji wani irin ba?in ciki ya cika Ni, iskar gidan kuwa da na sha?a sai na ji numfashina na ?o?arin sar?ewa kamar wata me asthma ban sani ba ko hakan ya haWa saboda zazzafar tsanar Muntari da nake ji, na shiga ciki ri?e da jakata ina jin wani abu na yawo a ?irjina, gabaWaya yarana suka yo kaina suna faWin "oyoyoo Amma", na rungumesu ina jin ?aunarsu na kuma ratsa ni cike da farin ciki, Nadiya ta fashe da kuka tana cewa "Ni dai ba zan yadda ki kuma tafiya ki bar ni ba, ina Anty Inya, au Abba ya ce sai ranar asabar za ta dawo" na rungumeta na share mata hawaye ina cewa "to suda"

"Yaushe ne ranar asabar Win Amma, ina son na ga Anty Inya" Tasleem ta bige mata baki tare da galla mata harara ta ce "me na ce miki", Nadiya sarkin rigima ta zumSura baki ta shige jikina, nan parlor na shiga gaisawa da yarana, Tasleem ta kawo min dankalin turawa da ta soya da miyar ?oda, sai da na yi nak na shige Waki lokacin an yi kiran magariba, ban fito ba sai da aka yi isha'i bayan na yi wanka na saka sassau?ar doguwar riga. A parlor muka zauna bayan yara sun kammala home work Win su,muna kallon wani film nan home alone muna ta dariya, Nadiya dai na ma?ale da ni, da na motsa ta kuma ?wa?umeni, sai nake jin zuciyata sayau da na ganni cikin yarana, sai a lokacin na ji ina ma ban Wauki yarinyar da za ta zame min annoba ba ta rusa wannan gida mai cike da farin ciki, ina wannan tunanin Alhaji ya shigo, yana gani na ya shiga wage baki, kamar ya ture Nadiya ya zauna kusa da ni, ya mi?a wa su Tasleem leda suka baje gasasshiyar anta da ta ji haWi, ina matu?ar son anta na san shi ya sa ya siyo, ana kallo ina jin idon Alhaji a kaina, ni ko bayan gaisuwa ban kuma ce masa ci kanka ba, sai wajen tara da rabi na sa aka kashe kallon, da ?yar Tasleem ta ja Nadiya zuwa Wakinsu wai firr da ni za ta kwana, bayan na shiga Waki sai na dauro alwala na yi sallah raka'a biyu na ro?i Allah Ya haWa ni da alkhairan da ke gidan duk abin da zai zame mini sheri ya nisanta ni da shi, ina naWe dadduma Alhaji ya shigo bakinsa Wauke da sallama.

"Wa'alaikha salam" na amsa ciki-ciki ba tare da na dube shi ba.

"Hadiza sannu da dawowa" ?amshin turarensa ya gauraye Wakin,sai na dube sa don na ga da wacce ya zo, wanka ya sha ta dakakkiyar shadda fara ?al ya murza hula da agogo, irin wankan da nake bala'in so a baya, amma yanzu ko kusa da burgeni bai yi ba. Ya ajiye leda cikin fara'a ya ce "ga abin da kika fi so"

"Na gode kana iya tafiya" ban ko dube sa ba.

"Haba! Yau ai sabon ango nake Hadiza, more daren zamu yi, wallahi tun shekaran jiya nake mafarkinki"

Na saki siririyar dariya mai sauti na kallesa da dariyata na ce "ko dai ka za ta Inya ce Alhaji, Hadiza ce fa wannan tsohon injin"...


*Wanda ya karanta min book kyauta da ha?kina akan sa, zai biya ni gobe ?iyama*



*My book is 500 only via 1401611541,Fatima Lawal Sa'id,Access bank, DM 08167888934*

RAHUSA DATA AVAILABLE (MTN)

1GB-280
2GB-560
3GB-840
4GB-1120
5GB-1400
10GB-2800
(1401611541, Fatima Lawal Sa'id, Access bank. Call 08167888934) All network available.
1?? 7??

Ya dafe kai tare da cewa "Hadiza wai me ya sa kika son tuna abin da ya wuce don Allah, zancen nan fa bisa kuskure na yi shi kuma ya wuce,amma sai kike tuno baya da ba ta da amfani"

"Wace baya?, Kai da za ka yi sabon injin ai tsohon ya haramta a gareka, jira sabon ya iso nan da kwana uku" ban kuma kallonsa ba na nemi waje na kwanta ina jin tsayuwarsa sama da minti goma kafin ya fice bayan ya ja tsaki ya bugo min ?ofa, na taSe baki tare da cewa "ohoo dai", bacci mai daWi ya fara kwasata. Kamar a mafarki na ji ana laluba ta na tashi bakina Wauke da addu'a na ture hannun da yake shafata. Na kunna fitilar wayata na ga Alhaji ya yi min ?uri jikinsa har rawa yake idanu sun sauya kala, muguwar jarabar ta ci yo sa take tunanin watsewa suka gama???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yi a waya da Inya hankalinsa ya tashi, ya zo ya rage zafi da ni tun da ba ta kusa, da sauri na ture sa na haWe girar sama da ta ?asa na ce "wai meye haka ne Muntari?"

"Don Allah Hadiza wallahi a matse nake" ya ce cikin wata iriyar murya gwanin ban tausayi, da ada ne lokacin da zan saka shi a ?irjina na sarrafa shi da baiwata ban ma sani ba, ko kusa Allah Ya sani bana barin sa cikin damuwa bare Sacin rai,ta kan sex yadda ka san shugabar da ke koya kama sutra haka nake, don ma bai jure dogon romance, amma yanzu sai na ji wani haushinsa ne ma ya turnu?e ni na ce "kar ka kuma zuwa wajena ka kawo min irin wannan bu?ata, ba don na dawo gidanka ba ne za ka Wau ciwon da kuka cusa min a zuciyata ya warke, ko kuma dattin da nake ganin ku da shi ya wanke, wallahi na tsaneka Muntari, ka nisance ni"

"Hadiza kina cikin hankalinki kuwa, ke fa matata ce, ni za ki ke jifa da irin wannan kalaman?" Ya ce cikin fusata.

"Muntari ka san Ni matarka ce ka tsallakeni a lokacin da nake taltalinka ka watse da yarinyar da na ri?a, ka dakata a gidan aurena, ka murje ta bisa gadon aurena don ba ka da kunya, ko ka yi tunanin don na dawo gidanka na manta ne Muntari?"

"Ya isa! Na fita ha??inki, Allah Ya sani na yi bakin ?o?arina sai yanzu nake ganin mugayen halayenki Hadiza, yarinyar nan sau da ?afa biyayya take miki, ta kira ki ta miki sa?o don ta baki matsayinki, na lallaSaki na rarrasheki na yi ta bibiyarki duk a banza, muna son junanmu don ke sai mu ha?ura da abin da yake halastacce har a addini, na gaji,in sha Allahu Ni Muntari na shafa miki lafiya Hadiza, ki yi wadda kika so" ya fice ya bar ni. Hawayen ba?in ciki suka gangaro min sai a yanzu na tabbatar da lallai namiji Wan bushiya ne, wai suna son junansu, wai ni Inya ta ba wa girma, yarinyar da ta din ga surfa min rashin arzi?i kamar wadda ba su taSa zaman mutunci ba, na yi ?wafa, baccin da ban iya yi ba ke nan sai talatainin dare ya kwasheni. Washegari ta kama alhamis da safe wajen ?arfe goma sai ga Tasleem nan ta shigo Wakina, ta ajiye min kuWi dubu ashirin da ?ar takadda tana cewa "ga shi Abba ya ce na baki kafin ya fita"

Na buWe takardar na karanta kamar haka _Assalamu Alaikum, Hadiza ga kuWi nan a yi abincin rana mai kyau don ?an jere za su zo misalin sha biyu, zan aiko da kaji in na fita da lemo_

"Kutumar uba! Amma ke za ki wa su Inya Win abincin ?an jere", murmushin na yi kawai mai mugun ciwo, Allah kaWai ya san irin tafasar da zuciyata ke yi, bana son duk abin da zai jawo ?ananan maganganu ko raini daga yarinyar da danginta, uwa uba bana son duk wani abu da zai tsawaita maganata da Muntari don haka na dubi Tasleem na ce "je ki gidan Maman Amira ki ce Talatu ta zo don Allah" Maman Amira ma?ociyata ce kuma muna mugun mutunci da ita, haka Talatu mai aikinta, mace mai barkwanci da dattako.

"Tabbb! Amma to me za a yi in an kirata?" Na san Tasleem ba ?aramin zafi ta Wauka ba, hakan ya sa na daure nake ?o?arin tausar zuciyata don na san Sacin raina kuma harzu?ata zai yi, ba kuma na san ta yi abin da za a tafar min da yarinya a baki. Don haka na yi murmushin ?arfin hali na ce "to meye a ciki Tasleem?, In ka ba da abinci ma lada za ka samu ai"

"Tabb! Gaskiya Amma kar ki yi, lallai ma"

Na yi ?ar dariya na ce "ai ba ni zan yi ba, ke da Talatu za ku yi,maza je ki kira min ita"

"Ai kuwa wallahi gishiri zan zambaWa musu in kin matsa da ni za a yi aikin nan" ta tashi tana ?wafa. Fitar Tasleem wasu hawaye masu ?una tun daga zuciya suka sauka kundukukina. Babu jimawa na ji sallamar Talatu, na fita parlor muka gaisa cikin mutunci kana na ce "Talatu kina wani abun ne?"

"A'a na ?are aikina" ta ce.

"Yawwa abinci nake so ku yi da Tasleem don Allah, dafa dukar shinkafa mai kyau, ba?i ne zamu yi ?an jere kin san baban Tasleem zai ?ara aure ranar asabar Win nan, to ba na jin daWin jikin nawa aikin kuma ya wa Tasleem yawa"

"Allah Sarki! Ubangiji Allah Ya haWa kawunanku, ba komai je ki zamanki, zan musu abinci mai kyau in sha Allahu, Allah Ya ?ara sau?i"

"Ameen!" Na ce a gajarce tare da kiran Tasleem na ba ta dubu ashirin Win nan ce "a yo cefane, a sawo jan nama da duk abin bu?ata"

Sai da ta fita ne ma nake tunanin to ina Alhaji zai saka Inya, gida guda zai haWa mu ke nan duk gidajensa, ko kuwa abincin za a kai can inda za a yi jeren, ina wannan tunani na ji wayata na ringing, na duba na ga Alhaji na ?i Wauka, sai da ya yi kira uku na cira.

"Wai ina kika ajiye waya ina ta kira" ya ce a zafafe. Ban amsa masa ba na yi shiru

"Kina ji na?" Ya ce.

"Ina ji"

"Yawwa don Allah ki duba drawer ta ta hannun dama, za ki ga mukullan part Win nan na gefen nawa, in sun zo a ba su" ya ce.

"Gida Waya za ka haWa mu?" Na tambaya cike da mamakin part Win da nake ta ?umin komawa yana hana wa wai kar na yi nesa da yara ya Waukar wa Inya,part Win da dole sai an bi ta nawa sashen za a isa garesa,wato ta ga dukkan sirrina, duk filin gidan nan, har da wani part sak irin nawa daga can waje bai Waukar mata ba sai a cikin nawa.

"Kin ga zamu yi magana in na dawo" ya katse kiran. Tun da na zabga tagumi na lula duniyar tunani ban Wago ba sai da na ji ana buga kafaWata.

"Amma kuka kike yi?" Tasleem ta fara matsar ?walla. Na yi hanzarin gogewa don wallahi ni kaina ban san kukan nake ba, na yi murmushi na ce "ke ba kuka ba ne, wani ?waro ne ya faWan ido amma na ma cire ai"

"Hmm! Amma ni fa ba Nadiya ba ce ba, an siyo komai dubu bakwai aka kashe"

"Me ya sa ba a saka wadataccen nama ba?"

"Na dubu huWu fa, ga kaji Abba ya aiko, halan kuraye ne su"

"Allah shiryeki"

"Amma na san sun kusa zuwa ga kaya can na Wauko miki, don Allah ki yi kwalliyar da dole su raina kazar da za su kawo "

"Wace kaza kuma Tasleem?" Na ce don ban fahimta ba.

Ta yi dariya ta ce "ke dai Amma ki shirya", na yi Wan murmushi na gyaWa kai. Tana fita na kuma share hawaye ina ta jimamin wai yau Inya ce za a kawo kayan aurenta gidana, ina wannan tunanin aka turo ?ofar Wakina da sallama, ta yi tsaye tana kallona nima ina kallonta tsawon minti Waya, sannan ta taSe baki ta ce "hmm uhmm! Hajiya Hadiza to zaman me kike yi haka kin rafka uban tagumi cikin hijabi kamar me takaba"

Na harareta na ce "ki ji ki da wani zance, kowa ya tsinci kansa cikin halin da nake ai dole ki gansa a haka"

"Lalalala! Wallahi ban da ni, shiru na yi miki na ga za ki faWa min da kanki ko kuwa, amma sai na ji tsit shi ya sa na ce bari na zo na ji laifin da na miki da kika watsar da ni haka, ashe rabon zan yi mugun gani"

Na yatsina fuska na ce "hmmm! Ni ina na ga nutsuwar sanar miki ne dama?"

"Wai ta ya aka yi kika bari wannan abu ma ya faru har za a yi aure?"

"Namiji Kubra!" Na ce cikin Wacin rai.

"?warai! ?anin ajali, ita Inya dole aka yi mata?"

"Dole fa?, Inya na ta shuka min rashin arzi?i kar ki so ki ji"

"Lallai! Allah Ka yi mana katangar ?arfe da mugun iri, ke wai Winkin da kika kawon ita Alhaji ya farketa cikin gidanki?"

"Idona ya gane mini Kubra, a gadon aurena mijina ya surfa ta"

"Tabb! Kika kawon ita na Winketa, Winkin ciki da waje, kika Soye min a gaisheki!" Hawaye suka zubo min na ce "Kubra na yi zaton na farkon tsautsayi ne, haka suka lulluSeni, na yi ta Wirka mata gasashen nama da dahuwar ta matse, na gyarata tsaf Kubra ta haWe ram, na kuma kamata ta yi sashen mijina suka cigaba da watsewa"

"Kin yi sakaci Hadiza, wallahi kin yi sakaci", ban iya cewa komai ba na dai gyaWa kai na ce "na yi nadamar ri?e ta wallahi, na yi nadama, ba ki ji yadda nake fama da haki ba, abu kaWan ya taso min kamar zai halaka ni"

"Sannu, zan rubuta miki magunguna zai yi sau?i in sha Allahu, yau za a zo jere ko?"

"Har ni aka ba wa kuWin tarbar ba?i na yi musu girki" na ce cikin ?unar rai.

"Namiji!" Ta jinjina abin, ta kuma duba na ta ce "an yi girkin, ko na je na Wora?"

"Na saka a yi" na ce.

"Ba laifi, na san yanzu sun kusa isowa tashi ki watsa ruwa ki yi shiri Hadiza har da damuwar nan ki wanketa wajen wanka, kar ki bari wasu hawayen su Wiga, su jira har a yi auren"

"Shirin me zan yi Kubra?, Auren mijina ne fa da butulun ?ata"

Ta yi murmushi ta ce "ban manta ba Hadiza, duk rawar ?afar wuyarta a Waura, ba su wata uku ki yi kallon sarautar Allah, kul! Kika bari kishi ya sa gidanki ya salwanta a hannunki"

Na cije leSe na ce "gida?, Ni fa zaman ?a?ana nake"

Ta yi dariya ta ce "ko Ni ce a matsayinki, nima shi zan yi, amma a ganka cikin zati da ?awa ma kwarjini yake ?ara maka, ba don namiji kawai ake ado ba, ke me faWa wa wani ce"

"Haka ne!" Kawai na iya cewa na shige banWaki. Yadda nake wanka ruwan na kwaranyewa haka na ji kashi talatin cikin damuwata ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login