Showing 21001 words to 24000 words out of 81703 words

Chapter 8 - NI NA RAINETA COMPLETE HAUSA NOVEL

FCWA   

20 Dec 2025

48

ya shigo, kamar ba zan duba ba kuma sai na ja wayar na ga sunan Inya raWau a jiki, na buWe na shiga karantawa a fili kamar haka _Amincin Allah Ya tabbata a gareki Yayata kuma Ammata, ha?i?a abubuwa marasa daWi sun faru tsakaninmu amma har raina wallahi na yafe miki, ban ri?e ki don dukan da kika sa aka min ba, ina farin cikin sanar da ke wannan asabar Win mai zuwa za a Waura aurena da Alhaji, don ma?iya sun mana ca suna neman raba mu, muka yanke matso da bikin, Allah Ya haWa kanmu ya bamu ikon yi wa Alhaji biyayya, in sha Allahu ba za a samu matsala daga Sangarena ba, a gaida Inno_ na haWiyi wani abu mai Waci, na yi murmushi mai ?una. Duk yadda na so na daure na cigaba da walwala ta zuciyata ta min nauyi, wai yau Inya ce ta kira ni ta gaya min maganganun cin mutuncin nan ai ya zama dole ma na ?ara ?aimi wajen karSar takaddata, kamar daga sama na ji muryoyin mata, na Waga kai na kallesu dangin Muntari ne suna Wauke da akwatuna mai guda uku, nan aka shiga gaisawar mutunci, kowa ya buWi baki ya ce "Hadiza an miki ba daidai ba, amma ki yi ha?uri tun da babu haramci komai mai wuce wa ne, in sha Allahu za ki ga hasken abin", Ni dai ban da bakin magana ban da gyaWa kai don na dai gama zama da Muntari kome ne za su ce ba zama zai yi ba, bayan gaishe-gaishe Inna Yalwa wadda take kamar ?anwar uwa wajensa ta ce "Hadiza ta so mu je ciki mu yi magana", na mi?e na bi bayanta, muka kuma gaisawa ta kama hannuna ta ri?e ta zaunar da ni kan gado ta ce "Hadiza zan soma da baki ha?uri,ki yi ha?uri,ki yi ha?uri tabbas an miki ba daidai ba, babu wanda za a yi wa haka zuciyarsa ba ta sosu ba,ban da namiji namiji ne ban ga abin da kika rasa da zai so Inya ba, amma da yake matar mutum kabarinsa Allah Ya tsara zai aureta, don Allah don darajar Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama ki koma Wakinki gaban yaranki, yaranki mata ne, ki sani in har don auren Muntari da Inya za ki rabu da su kuma ba ki musu adalci ba, ki dubi ?arancin shekarunsu, idan kin tafi wa za ta ri?e su ta tallafe su tamkar uwarsu, wa za ta kula da tarbiyyarsu, da ciwo na sani, amma daurewa za ki, albarkacin ?a?anki, ba don Muntari ba sai dan ki tallafi rayuwarsu, ki koma ki tarbiyyantar da yaranki, wannan zamani ka yi tarbiyyar ma ya aka ?are bare ka mi?a yara a hannun bare, da bai san ciwonsu ba" zuwa lokacin kuka ?wace min ya yi, cikin kuka nake cewa "Inna Yalwa wallahi na bar su Nadiya a hannun Allah, ba zan iya komawa gidan Muntari ba, haba! Yarinyar nan fa NI NA RAINE TA tun ranar da aka haifeta ta dawo hannuna, a ce yanzu na koma mu haWa miji guda da ita, ba zai yiwu ba, su je su ?arata kawai"

"Kul! Hadiza kika yi haka ai ke ce a ?asa,me aka yi ke nan in baki nuna wa Inya ita ta zo duniyar ta tarar da ke ba,ki koma kan yaranki ki ri?e gidanki ?am, ki ga ?arshen rashin kunya da butulci irin nata" sai take cire Muntari ta manta shi ma butulcin ya yi min, ban iya cewa komai ba, ta dafa kafaWata cikin ?asa da murya ta ce "kin san Allah mijinki ba ?aramin sonki yake ba, da ya zo min nan har da kukansa in taimakesa ki dawo,na ji labarin mahaifin yarinyar biye-biyen malamai yake yi wallahi, tunda ma kika ga yana so ki koma ba ?aramin sonki yake ba duk da asirin da ke Wawainiya da shi,ki koma kan yaranki ki dage da addu'a, ga kaya can na toshiyar baki akwati uku da kit in ji mijinki, Allah Ya baki juriya da ha?uri, ki koma Wakinki wallahi tun kan yarinyar ta tare, ta tarar da ke daram a cikin gidanki"

"Inna Yalwa ku maida masa..." Ta toshen baki ta ce "kar na ji komai daga bakinki Hadiza, kar ki bani kunya, ki dai yi ha?urin nan, wallahi in har don a Sata miki aka yi hakan, Allah zai nuna miki ?arshen ma?etaci" ta sa kai ta fice, na zabga uban tagumi hawaye na cigaba da gangaro min, ina jin hayaniyarsu suna wa su Inno sallama, Waya bayan Waya suka ri?a Waga labulen suna min sallama, ban ha?urin na koma Wakina. Bayan fitarsu Inno ta shigo ta zauna ta dubeni ta ce "Hadiza kin ga komai na duniya Wan ha?uri ne, kin san Allah Ubangiji na sonki da rahama, ki ga yadda dangin mijinki ke ?aunarki da mutuntaki,mijinki babu laifi yana sonki tunda har kayan faWar kishiya ya yi miki ba ki ji labarin an Waura auren a gari ba, ki taimaki kanki ki koma Wakinki, kin ga Ni fa ba ?uruciya nake ?arawa ba, ina daf da rami tun da har na wuce sittuna, Malam kuma da nauyi a kansa, ke marainiya ce gatanki Allah, gatanki Wakin mijinki, wallahi babu macen da ba ta fuskantar ?alubale a rayuwar aurenta, kowa lallaSawa take tana zaune da daWi da ba daWi, da zan buWe miki cikina ki ga irin zaman auren da na yi da mahaifinki lokacina wallahi sai kin ga lamarinki gidan aljanna ne, to duk mace dole ta haWu da ?alubale a gidan aurenta, ke ba yarinya ba ce da in kin kashe aurenki za ki samu wani gidan da ba mace ki zauna ke kaWai, wallahi inda zaki Win sai ki ga gara gidanki sau dubu akan nan Win, wani lokacin har gara mugun da ka sani akan wanda ba ka sani ba, Inya ba ta isa ta miki isa a gidanki ba, wani gidan kuwa sai yadda kika tarar ana yi za ki yi, mijinki bai rage ki da komai ba, a faWin ?araye ana sakaki cikin matan da suka yi dacen aure, don me saboda wata banza Inya za ki bar gidan mijinki, ki bar yaranki, tarbiyya da ta zama yadda ta zama, ka kula ya aka ?are bare ka yi wasarairai,wallahi tun baki tuna bara ba, ki koma Wakinki" ta mi?e ta fice, ban iya motsawa ba daga inda nake sama da minti goma, gabaWaya jikina ya yi sanyi ?alau, duk maganganunsu sun shige ni amma gani nake ko na koma wula?anci kawai zan fuskanta don ga shi ?iri-?iri tun ranar da muka rabu da Alhaji bai kuma nemana ba, kiran duniya na masa kan takaddata ma bai ko Waga wayar ba, ina sa?a da warwara har aka yi kiran magariba, ko da na idar ban Waga sallayar ba sai da aka yi isha'i. Ina idar da sallah kiran Tasleem ya shigo wayata, na Wauka cikin tashin hankali take cewa "Amma hau WhatsApp ki ga wani abu." Sai da n shafe jikina da addu'a tukunna na yi shirin kwanciya, na hau gado na kunna data, wani irin dokawa ?irjina ya shiga yi, na kira sunan Allah na tashi zaune,bakina bai yanke daga salatin da yake ba, sai gani ina kokawa da numfashi na,Inya tik haihuwar uwarta tsaye ga Siyama a bayanta ta ma?al?aleta itama ba kaya, Wayan kuwa da wani namiji yana ri?e da nononta, jikina na rawa na danna kiran Tasleem.

"Amma kin gani?" Ta ce.

"Gidan ubanwa kika samu wannan hoton?" ?irjina bai bar dokawa ba don tsoro.

"Wallahi Siyama ce ta turo min, wai tunda Inya ita take wula?anta wa sai ta tona mata asiri, ashe ?ar iska ce, yanzun nan Abba nake ?o?arin tura wa kika katseni" ta ce...

*SHARE*


*My book is 500 only via 1401611541,Fatima Lawal Sa'id,Access bank, DM 08167888934*

RAHUSA DATA AVAILABLE (MTN)

1GB-280
2GB-560
3GB-840
4GB-1120
5GB-1400
10GB-2800
(1401611541, Fatima Lawal Sa'id, Access bank. Call 08167888934) All network available.
1?? 6??

"Tasleem!" Na kira ta da kakkausar murya.

"Na'am Amma ai kashinta ya bushe, zan ga ?arshen aure, ba ki ga iskancin da ta Wora a status Winta ba an mata lefe, wallahi Amma ki duba ma ki ga uban lefen da Abba ya yi wannan kazar yarinyar"

"Kar ki sake ki kuma tura wa kowa hoton nan, ki goge shi daga wayarki" na ce.

"Amma me ya sa?, Bayan tana ta buri ta raba mana kan gida tun kan ta shigo, Allah Ni sai na..."

"Ba ki ji me na ce ba! Kar ki sake ki tura wannan hoton ga kowa, kina hauka ne, mene ribarki in kin tozarta wani ne?"

"Amma duk butulcin da ta yi miki?"

"Tasleem Ni ta yi wa ko ke ta yi wa?, Allah da ba ya barci bare gyangyaWi yana sane da ita, shin ba za mu zuba ido mu ga yadda Allah zai yi da ita ba, sai mun yi abin da zai Sata rayuwar wani,kul! Na haneki da ?o?arin tona asirin wani, Allah ba ya son haka, in ta tuba fa?"

"Shi ke nan Amma, ba zan tura ba, Allah Ya yi mana sakayya, Amma don Allah ki dawo haka nan, Nadiya kullum hana min sukuni take, yau ma da ?yar ta je makaranta wai sai na kai ta ?araye", sai na rasa abin da zan ce, bana so na dawo Win har yanzu amma tabbas zuciyata ta yi wajen yarana. Ban bata amsa ba na yi mata sai da safe na kashe wayar. Sai na nemi baccin da nake son yi na rasa, hoton Inya na ta gilmo min da gardin ?ato rungume da nononta, na kunna wayata wai ko na ga editing ne na yi zooming fuskar, sai dai iya ganina wallahi Inya ce ba wani editing, gabaWaya yarinyar ta ?arar min da ruwan kai, wallahi ko Qur'ani ina dafa wa a baya in ka sa wa Inya yatsa a baka ba ta ciza ba, al'amarin da ya Waure min kai bai wuce yadda duk ta lulluSeni ba, duk tarbiyyar da nake ganin nawa Inya har ina fifita halayenta akan na Tasleem lokaci Waya ta yi wata irin rikiWar da ta tsorata Ni har ta susuta ni ba kaWan ba. Na kunna data don baccin ya gagari idona, ga shi ba na jin kuzari, jikina ya yi la?was, sa?onni na gani har guda 20 daga Inya, sai na ji zuciyata ta buga da mugun ?arfi, na san ko mene ba alkhairi ba ne, tada min hankali kawai zai yi, sai na share na kashe wayar, kamar wadda ake mintsinar zuciyarta sai na ji na kasa sukuni sa?onnin na ta faWo min a rai, na tashi zaune na jingina na jawo wayata na kunna, wasu video wasu hotuna, na buWe su tass, akwatuna na ne masu shida seti biyu da irin nawa mai kala uku da Muntari ya bani bambancinsu kala, akwatuna seti uku ke nan ya yi mata na lefe, na saki murmushi mai ciwo ina ta kallon videon da manyan atamfofi ne ko ta ina da manyan lesuka, ka rantse Muntari na da mu?ami a siyasa irin lefen da ya yi, idan aka ce ban ji zafi ba ma an Sata baki ne, wallahi ?una da ciwo zuciyata ta shiga yi, na tuna lokacin da ya kawo nawa lefen akwati biyu kacal kuma duk super print sai mai barewa, amma ga shi zai ?ara aure ya cika seti uku dam da kaya masu tsada da kyau, ya aiko min akwati uku duk da ban buWe ba, na buWe wani video wanda sar?ar gwal ce mai suna sar?a, seti ne har da mundulan awarwaraye, a ?alla kuWinsu yana miliyan Waya da rabi, na haWiyi wani abu mai Waci, take na ji zuciyata ta kuma ?e?ashewa a kar na koma gidan Muntari don ni na san zaman wula?anci da boranci zan yi, wannan shi ake kira da tsuntsun da ya ja ruwa kwata-kwata nutsuwa ta gagareni,na fa san dama ba alheri zan gani ba amma na buWe na ja wa kaina, sa?o na ?arshe Inya ta ce "a saka mana albarka.", Ko da na gama sai na mi?e na jawo akwatinan na buWe, ko kafin na gama cizan leSe kawai nake, ina murmushin ba?in ciki, babbar atamfa ita ce Chiganvy, sai shadda kampala guda uku, ban samu albarkacin lesi ba, sai jaka da takalmi ?afa uku, sai mayuka da tarkacen kayan kwalliya, sai na ji kamar na zazzaga wa kayan fetur na cinna ashana, na kuma buWe lefen Inya na gani, Ni na ja wa kaina bacci ya kasa ko saceni,yadda na ga rana haka na ga dare, sai da na yi asuba sannan na samu bacci Sarawo da sace Ni, ina cikin bacci na ji Inno na kirana, na yi hamdala na yi mi?a haWe da addu'a na tashi.

"Wannan bacci ko na lafiya ne Hadiza?"

"Lafiya lau, ina kwana?"

"Alhamdulillahi! Malam ya jima yana ta jiranki kina ta bacci, ga shi zai fita shi ne na tasheki, tashi ki je yana tsakar gida" ta ce tana ficewa. Sai na ji ?irjina ya yi wata jriyar bugawa, sai nake jin kiran Malam ba zai zamo alkhairi a gare Ni ba, na saka hijabi na nufi tsakar gida, muka gaisa cikin mutunci ya ce "halan Hadiza jikin ba daWi ne wannan bacci"

"Alhamdulillahi! Ya iyalin"

"Suna gaida ku, dama kasuwa zan wuce sai na ce bari dai na biyo mu tattauna kada lokaci ya ?ure baki yi shirye-shirye ba"

"Shirin me fa Malam?" Na tambaya ina kallonsa, ya muskuta kan kujera ?ar tsugunno ya ce "watau Hadiza komai kika ga Allah Ya yi akwai hikimarsa ta aikata hakan, kin ga aure babban arzi?i ne ga ?a mace komai girmanta aure na suturta ta, zawarci ba ya da daWi Hadiza musamman ke da shekaru sun ja miki, da ni da ke da Inno ba shekaru muke ragewa ba a kullum kusantar kushewa muke, Hadiza idan yau na faWi na mutu, babu ran Inno duk duniya ba ki da wani gata da ya wuce Muntari, da daWi da ba daWi ke Win dolensa ce ko ba ya so, ke ce uwar yaransa, kin ga tsokar da ke nan!" Ya yi nuni da ?irjinsa ya ce "guba ce, zuciya ba, guba ce Hadiza na nanata miki na kuma faWa miki, wallahi ita ke kai mutum ya aikata da na sani, Allah Ya rufa miki asiri kina zaune gidanki cikin sutura, ina guje miki ta kai ki ga abin da za ki yi dana sani. Idan kin kashe aurenki kin shiga gidan wani kin san me za ki taras?, Saboda fushi kin jefa rayuwar ?a?anki mata a halaka, ki zo daga baya kina cizon yatsa, tun dare bai miki ba ki tattara ki koma Wakinki, jibin nan ki haWa kayanki Hadiza mota za ta zo ta maida ki gidan mijinki, da shi Muntarin gobe ya so, na ce ya bari zuwa jibi ki kimtsa, ki je ki tallafi rayuwar yaranki mata, ki gyara inda aka fi ki a gidan aurenki, ki tsare mutuncin ?a?anki da mijinki, kar na sake na ji an ce, bare kin yi, ki yi ha?uri kowacce rayuwar aure da na ta ?alubale da jarabawowi, ki daure ki cinye watarana sai dai ya zamo tarihi", "Malam..." Ya Waga min hannu tare da cewa "dakata Hadiza, ban bu?aci jin komai daga bakinki ba, ba shawara nake baki ba umarni ne, ki koma Wakinki don ba a yi miki komai ba, babu haramcin auren da mijinki zai yi a addini, don haka bana son dogon musu jibi za ki koma Wakinki, kin ga duniyar nan ki kama sirrinki, babu abin da wata halitta ta isa ta yi miki in har ba Allah ne ya yi miki shi ba, don haka ki kama bakinki in har kin san ba za ki samu magani a gun mutum ba to kar ki yarda ki fallasa sirrinki gare shi, duk abin da ya dameki ki kai kukanki ga Allah, zai miki maganin ko mene, kar ki soma, Hadiza kar ki soma, kar ki kuskura ki soma ki biye wa ruWin duniya a ce za a kai ki gun wani ya miki maganin matsalar ki. Wallahi duk abin da Allah bai yi miki ba, babu mahalukin da ya isa ya yi miki shi,ki ji tsoron Allah, ina tunasar da ke ki ji tsoron Allah ki zauna da yarinyar nan da zuciya Waya tunda zama da muke fatan na dindindin ya haWaku, in har kika cutar da ita Allah na ganinki, ina sake miki tuni da ki ji tsoron Allah babu haramci a aurensu", kuka mai ?arfi ya ?wace mini, Allah Ya isa tsakanina da Inya ba zan taSa yafe mata ba wallahi, wai Ni ce yau aka zaunar ana mini nasiha irin ta yara, Allah sai ya saka min wallahi don ta jefa Ni cikin mawuyacin halin da ban taSa shigarsa ba tun zuwana duniya, na jima ina kuka Malam bai ce min komai ba na yi mai isata na yi shiru don kaina sai shassheka.

"Hadiza!" Ya kirani.

"Na'am" na amsa cikin sanyi.

"Hadiza shiga aljanna sai an daure, sai an ci jarabawa, ki Wauka auren Inya ?arki da mijinki na cikin jarabawoyinki na gidan duniya, ki yi ha?uri, duk abin da ya miki tsanani, ya baki tsoro ki kai kukanki ga Allah, wallahi ya isar miki, idan abu na baki tsoro ko fargaba Hadiza kafin ki ce komai yayin da kika haWu da shi ki ce HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL da SUBHANAL MALIKIL QUDUSSI,RABBIL MALA'IKATI WAR RUHI,JULLILATUL SAMAWATI WAL ARDHI BIL'IZZATI WAL JABARUTI. IDAN WANI AL'AMARI NE YAKE BAKI WUYA CE NE QADDARALLAHU WA MA SHA'A FA'ALA. IDAN MA?IYINKI YA NUFO KI KI CW IYYAKA NA'ABUDU WA IYYAKA NASTA'IN KO MENE NE YA NUFE KI DA SHI ZAI KOMA KAN SA. Kin ga Hadiza idan kika ri?i wannan, kika ri?i Allah, kika tsare azkar,kika ri?e addu'a da karatun Qur'ani wallahi kin gama, duniya babu mai ganin bayanki, da zatin Ubangiji sai dai ki ga ?arshen ma?iyinki, idan Sacin rai ya taso miki, Wauro alwala, ki kalli gabas ki ja salatin Annabi na Ibrahimiyya ki kwararo wa Ubangiji damuwarki wallahi sai kin ji zagwanyewar Sacin ran nan, Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login