Showing 15001 words to 18000 words out of 81703 words

Chapter 6 - NI NA RAINETA COMPLETE HAUSA NOVEL

FCWA   

20 Dec 2025

46

da kake yawo da ita ka siya mata alawa da pampers ita ce ka daka ka ha?eta a Wakin da ta koyi zama, duk wannan ba haramci ba ne Muntari, wallahi tsanarka nake ji,dama ka nisanceni da ka rufa wa kanka asiri"

"Ni ban san me zan ce miki ba, kin riga kin gina zuciyarki akan zargi,aure na da ke daram Hadiza, auren Inya kuma babu fashi ba gudu ba ja da baya, tun da ba saSon Allah na yi ba" ya ce yana nufar ?ofa.

"Ka ci kutumar ubanka da zargin Muntari!" Na kwarara ihu sai dai tuni ya fice.

Inno ta sako kai Tasleem na bayanta, Inno ta kwasheni da mari ta ce "lallai Hadiza kin haukace, mijin naki kika kutuntumawa ashar haka, sam yanzu ban ga laifin Muntari ba wannan wani irin rashin arziki da rashin wayo ne, akan ki aka fara kishiya ne?"

Ban ji zafin marin da ta min ba don suyar da zuciyata ke min tafi shi zafi, na dubi Inno na ce "Inno na gama zaman aure da Muntari, wallahi ko shi ne autan maza na ha?ura da shi, babu yadda zan zauna da Inya matsayin kishiya, na bar mata shi, abin da suka yi min su je da Allah, yaudara da ha'inta ta da suka yi na bar su da rabbil samawati, amana da yardar da na dam?a musu suka mini butulci Allah Ya min ba?ar isa a kansu, ban taSa ri?e wanninsu da zuciya biyu ba, na yi ?o?arin da zan yi akan su, na kusa kashe kaina akan kyautata wa Muntari, na ?aunaci Inya na ri?e ta da ?arfi,lafiya, da dukiyata, na yi wahala da ita wahalar da ban yi da Tasleem ba amma sakayyar da za su min ke nan, su je don kansu, Allah Ya isar min, gobe zamu tafi ?araye, ki yi wa Malam magana ya amsar min takaddata" Tasleem ta fashe da wani irin kuka...


*SHARE*


*NI NA RAINE TA*

*?Mss Flower
*FCWA*

*My book is 500 only via 1401611541,Fatima Lawal Sa'id,Access bank, DM 08167888934*

RAHUSA DATA AVAILABLE (MTN)

1GB-280
2GB-560
3GB-840
4GB-1120
5GB-1400
10GB-2800
(1401611541, Fatima Lawal Sa'id, Access bank. Call 08167888934) All network available.

1?? 2??

"Allah Ya kai mana rai da lafiya"Iya abin da Inno ta ce ke nan ta fice. Tasleem ta ?araso inda nake cikin kuka ta ce "Amma yanzu sai ki bar gidanki saboda wata Inya, Amma don Inya mu kuma sai mu ?are rayuwar mu cikin ?unci." Ban tankata ba na zauna ina dafe da saitin zuciyata sannan na dube ta na ce "in har ba so kike na faWi na mutu ba Tasleem kar ki yi abin da zai tsananta halin da nake ciki, wallahi zuciyata na iya buga wa matsawar na zauna a wannan gidan, ki kula da ?annenki,na bar amanarsu a hannunki, Allah Ya tsare min ku ya kare min ku. Wuce ki je ina son na rintsa" na kwanta tare da juya baya,tana fita wani kuka ya ?wace min, ban taSa hasaso zan riski irin wannan lokaci ba a rayuwa, tun da nake sama shekara ashirin da aure ban taSa fita gidana ba wai da sunan iyalaina sun Satan rai na tafi wani wajen ba, amma a yanzu zuciyata ta yi na'am da barin gidan nan shi ne hutunta,tsorona Allah tsorona nesa da zan yi da yarana mata,yadda zina take bashi ina tsoron abin da mahaifinsu ya aikata ya bibiyesu, na share hawayen da suka Wigo min na ce "bakina ba zai yanke daga muku addu'a ba, Ubangiji Allah Ya kare min ku, ya tseratar min da mutuncinku har gidajen mazajenku". Yadda nake ji, gidan kamar akan ?aya nake cikin haya?in barkano duk ya gundure ni, bacci dama ko na kwanta ba Waukata zai yi ba, don haka na Waura alwala na fara sallah ina ro?on Allah Ya bani juriya da ?arfin zuciya, da wannan na ji rai da gangar jiki sun mini sakayau, na janyo manyan akwatina na na kwashe kayana da abubuwana masu amfani da duk tarkacena,na buWe drawer ta da nake ajiye tsadaddun kayan matana wanda ma fi yawansu na ?asar Indonesiya ne. Sai dai wayam sama ko ?asa babu ko guda, kuWi tsababa kusan dubu Wari biyu amma ko abin da ba a so ba a bar min ba, sai na yi tunanin ko Tasleem ta canza musu waje, na bar shi zuwan gobe da safe na tambayeta na cigaba da tarkata abubuwana. Assalatu na yi wanka na shirya cikin doguwar rigar abaya, ina idar da lazimi na faWa kitchen na fere doya na tafasa na soya, na dafa shayi mai citta, na shirya wa su Bahijja da Nadiya food flask, kafin na fito daga kitchen Win Tasleem ta taimaka musu sun shirya duk da Bahijja ce kan yi musu komi na shirin school, na same su a parlor ana wa Nadiya bita wai za su yi spelling bee yau a makaranta, ta ajiye takardarta ta nufo ni ta ce "Amma me ya sa kika tashi yau da wuri, Amma ko banki za ki je ne?" Na yi murmushi ina ji a raina ba ?aramar kewar yarana zan yi ba, na shafa kanta na ce "ba banki za ni ba amma zan je unguwa ne, ba na son rashin kunyar da kike wa Bahijja, haka komai Anty Tasleem ta ce ki yi kar ki ?i ji, ban da tsokana" ta yi ?uri tana kallona ta ce "Amma ko kema Karaye za ki tafi, Anty Tasleem ta ce Anty Inya ta je Karaye"

"E, ba na son surutu, mu je a ci abinci" na tattara yarana kan dining, cikin dubara nake wa kowa nasiha, Tasleem in muka haWa ido da ita sai ta Wauke ?wallar da ke ta gangaro mata, gabaWaya zuciyata ta kakkarye, ba na ?aunar duk abin da zai nesanta ni da yarana, amma na sani hakan shi zai samar da nutsuwa da kwanciyar hankalina, abincin sam ba ya min wani WanWano ruwan citta kawai nake sha, ?arar buWe ?ofa ta maida hankulanmu gabaWaya kansa, kamar koyaushe waya yake yi yana ta sakin murmushi, ban san dalili ba amma sai na ji duk wannan Sacin ran da nake ji a baya in na gansa a haka ban ji sa ba, kwata-kwata ban ji Wigon damuwa ba, na masa kallo guda na Wauke kaina na mayar kan kofin da ke gabana ina kurSa, ya ja kujera a kusa da ni bayan ya tada Nadiya ya zauna, yaran suka shiga gaidasa ban da Tasleem da ta mi?e ma ta bar wajen, abin da ta yi na kula ya Sata ransa don a fili ya yi ?wafa, ya shiga hira da yaransa suna ba shi labarin makaranta har suka kammala direba ya musu horn, na kama kan yarana na yi musu addu'a kamar haka "u'ithuuki bikalmatillahi tamaat min kulli shaitaani wa hamma wa min kulli aini lamma walahaula wala quwwata illah billah", ina jin idonsa a kaina har na rakasu bakin ?ofa na dawo, na wuce ba tare da na kallesa ba, Wakin da Inno ta sauka na nufa na tarar ta shirya, ta gama karin kumallo tana lazimi, na gaisheta ta amsa na ce "yanzu idan direban su Nadiya ya dawo, zai kai mu tasha"

"To ai na shirya tuntuni" na yi mamakin yadda Inno sam ba ta ?alubalanci tafiyata ba, duba da a kusan komai sai mun samu saSanin fahimta duk da ita mahaifiyata ce, amma ba zan Soye rigimammiya ba ce, in ta ga ba?i sai ta rantse fari ne ba kuma za ta bar abun ba sai ta tabbatar kuma kun ce fari ne. Daga nan Wakin Tasleem na shiga na sameta kan gado ta zabga uban tagumi, da alamu ba ta ma ko ji sallamata ba bare ta amsa, na ?arasa gadon na dafa kafaWarta na ce "tunani ba ya haifar da komai sai ciwon kai da damuwa"

Sai ga hawaye zirrr sun sauka kan kundukukinta ta dube ni ta ce "Amma na kasa aminta wai rabu wa za ki damu kan Inya, ni dai in ba za ki zauna ba kawai gara na bi ki, don ba zan haWiyi ba?in cikin nan ba, ba mai rarrashina."

"Wa ya ce miki sai dole da ni za ki rayuwa, in ban tafi ba ma yanzu kin san ai akwai mutuwa, kuma za ki aure dole watarana za ki tafi Wakinki"

"Ni dai Allah Ya isa tsakanina da Inya" ta rushe da kuka. Na rarrasheta tare da ban baki daga ?arshe na tsoratar da ita bisa biyayya da iyaye da kaucewa duk abin da zai Sata ransu, na san halin Tasleem sarai tsaf za ta yi ta abubuwan da zai Sata ran mahaifinsu. Rabuwar da muka yi was so emotional Tasleem na ta kuka kamar ?aramar yarinya ina share hawaye, don kar ta kuma karaya ne nima na daure zuciyata ban rushe da kuka ba, Inno kanzil wannan ba ta ce da mu ba har muka shiga mota, na jingina da kafaWar Inno ina kuka mai tsuma zuciya, ta ture ni ta ce "Hadiza ke kika so ai, abin da ha?uri bai bayar ba, rashinsa zai bayar ne, wa ya gaya miki rayuwa dole sai ta gara miki yadda kike so, a banza zamu shiga aljanna ba mu ga jarabawa ba, sama da shekaru nawa kike ji ana cewa gidan aure Wan ha?uri ne, kina neman kashe kanki saboda kishin banza da hofi akan wanda bai damu da Sacin ranki ba, yanzu Inya ta kore ki ta zuba ruwa ?asa ta sha don murna, wallahi na raina wayonki ko don ?a?ana da ganin ?arshen cin amana zan zauna na zuba ido na ga tun?wal", ban iya ce mata komai ba, don duk bayanin da zan yi ba za ta fahimci raWaWin da nake ji ba, na rantse har ga Allah ko da mata uku Alhaji zai ?ara a rana guda ba zan taSa fitar da Sacin raina irin haka ba, ba zan kiWima na rasa sukuni irin haka ba, amma yarinyar da nake wa kallon ?ata ce fa, yarinyar da na dam?a wa yarda na buWe wa dukkan sirrina, yarinyar da na raina tun tana jinjira, idona ya gane mini suna watsewa a gidana a gadona yake ?o?arin ha?arta,sannan kuma a ce ya aureta, na ci kashi da fitsarinta sannan a ce da ni wai na zauna gida guda da ita ?ar?ashin miji Waya, matsayi guda, na shiga turakarsa, ta shiga turakarsa, na yi girki ta yi girki, na yi kwalliya ta yi mai kwalliya, ya kusanceni ya kusanceta ai abin da ciwo, cin amanar da zafi tun da zuciyata ba ta ?arfe ba ce ai tsaf za ta yi rugu-rugu ta tarwatse, ni na san ba don ina da dauriya da hangen nesa ba a ranar da na fara ganin Inya da Alhaji sai na musu muguwar illa, ba don ni ba ce duk ha?urin da Tasleem za ta bayar da na kama su a karo na biyu sai an ?onesu yarda na yi niyya, a hakan za a ce ba ni da ha?uri, abin da yake hunting Wina dare, safiya da wuni kamar zautacciya, ba zan nema wa kaina magani ba sai na haukace a shiga yawo da ni asibitoci ?arshe a gaji a bar ni ina bin bola, saboda mace ba mutum ba ce ita komai sai dai ta yi ha?uri ba ta da gata, daga zarar da aka kai ki gidan miji an yayeki ke nan, ko yankar namanki ake ki dai yi ha?uri ki mutu an zo a miki wanka a kaiki kabari a yi jimami na kwanaki a watsar da lamarinki, mijin ya wanke sabuwa sai in an tuna a ce Allah sarki wance, ranar biki a yi shagali, cikin masu baki ha?uri har da su za a haWa masa gudummawa a je ganin amarya,taki ta ?are,su cigaba da gashi.

"Ba wayarki ba ce wai ake ta kira" Inno ta zungureni, na duba na ga lambar Alhaji na ja siririn tsaki a fili, daidai lokacin mota ta parker a tasha, na nemi mota guda na biya shata har ?araye. Har muka Wau hanya bai fasa kira ba, ban fasa yankewa ba, da ya gaji ya turo min sa?o _Hadiza har ki fita gidan nan ba da izinina ba ki je ?araye, me ya sa ba ki da ha?uri ne, zan zo gobe, yau ina da meeting_ na ja siririn tsaki.

Tafiya tafiya har muka isa ?araye gari mai tarin ni'ima da karamci, har ?ofar gida ya kawo mu, na ziro ?afata wata ni'imtacciyar iska ta doke Ni, na lumshe ido ina jin wani sanyi da shau?i na ratsa kowacce huda ta jikina. Inna kawai muka tarar tana tata, ta ajiye mataci ta dafe ?irji ta ce "na shiga uku Ni Indo, me nake gani haka Hadiza da akwatuna, gaske ne ke nan wannan raWe-raWin da ake yi wai Muntarin Hadiza zai auri Inya" ta ce tana gyara zaninta da ke ?o?arin kwancewa.

"Ga zahiri kin gani, don sokonci na Hadiza wai kuma saki take nema"

"Allah Ya mata mugun tsari, har dai ta huce, abin ne da ciwo da Waga hankali, wannan yarinya Inya an yi tambaWaWa wallahi, shegiya kullum kina ganinta simi-simi kamar wadda ?wai ya fashewa a ciki, kwantar da hankalinki Hadiza sakayya yanzu tun a duniya ake fara gani kan a je gidan lahira, Inya sai ta dur?usa gabanki ta baki ha?uri da hawayen jini, Allah Ya yi miki ba?ar isa akan ta,talaka dai bai da halacci na rantse uban Inya don ?armashewa sai ki ce in kin sa mai hannu baki ba zai ciza ba, amma wai shi zai Waura auren Inya, ina ruwan matsiyaci don dangin mahaifiyarta kaf na ji an ce sun ce babu hannunsu tun da ya fi ?arfinsu ya je da Inya duniya ce ta ishi kowa riga da wando"

"Ina ruwan butulu" cewar Inno.

"Butulu ko, a Wau jinjira a tsumma babu ko riga a jikinta, a rainar maka ita, a bata abinci, sutura da ilimi don kai Sarkin butulun duniya ka aura wa mijin wadda ta ma wannan halaccin"

Na yi murmushi mai ciwo, ban ce da su komai ba na faWa Wakin Inno. Yammaci na yi ?an uwa da abokan arzi?i kamar jira suke suka shiga Sarkowa da aiko da kwanukan abinci, mutunci irin na mutan ?araye sai muka rasa ina muka sa, ina muka aje da abinci, ban ma san labari ya watsu ba ban kuma san ta ina ya watsu ba kowa ya shiga ya jajanta min ya yi Allah wadai da Inya. Ni dai ba na cewa komai sai murmushi.

Kiran Saratu wadda nake siyan hakki na mata masu kyawun gaske ya shigo wayata, na Wauka tare da sallama.

"Ubangiji Allah Ya sanya alkhairi, na kuma gode da ciniki wallahi, ashe Inya lokacin aure ya yi, ina ta so in kira ki tun jiya da ta zo ta amshi kayan to bani da caji, har da kyautar dubu biyar Hajiya, Allah dai ya ?ara buWi,na kuma haWa mata kaya masu kyawun gaske, in sha Allahu ba dai ta yi boranci ba, Allah Ya sanya alkhairi, Ya ba su zaman lafiya" na haWiyi yawu mai Waci na ce "na gode sosai, a gaida yaran" na kashe wayar. Inya ba za ta daina bani mamaki ba, wato har maganin mata ta je ta siya a inda nake siya, lallai shu'umancin yarinyar mai girma ne, na lalubi wayata na kira Tasleem bayan mun gaisa na ce "kin canza min wajen kayan da nake sawa a ?aramar drawer ne?"

"A'a wallahi Amma, wani abu kike nema?" Ta tambaya.

"Ba komai, ki gaida su Nadiya" na kashe wayar.

Ina ajiye wa na ga sabon sa?o daga Alhaji, na ja tsaki har zan goge sai na ga gara na shiga na ji mai zai ce _KE CE RAYUWATA, NA JIMA INA RAINON SOYAYYARKI, KI BAR TADA HANKALINKI BABU ABIN DA ZAI SAKA A FASA AURENMU, INA SONKI NIMA SOSAI SWEET BABY_ wani abu ya daki zuciyata, kawai sai na danna masa kira in ji dalilin da zai sa ya turon sa?on wata shegiya sweet baby...

*SHARE*

*DON ALLAH KAR A KUMA TURON 300, MY BOOK IS 500, THE BONANZA IS OVER*



*NI NA RAINE TA*

*?Mss Flower
*FCWA*

*My book is 500 only via 1401611541,Fatima Lawal Sa'id,Access bank, DM 08167888934. Ga mutanen Niger 500f airtel za a tura wa wannan lambar +22795045822*

RAHUSA DATA AVAILABLE (MTN)

1GB-280
2GB-560
3GB-840
4GB-1120
5GB-1400
10GB-2800
(1401611541, Fatima Lawal Sa'id, Access bank. Call 08167888934) All network available.

1?? 3??

*ALHAJI*

Ban da Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un babu abin da yake nanatawa, hankalinsa in ya yi dubu ya tashi, yanzu da ya dace ya lallaSa Hadiza a yi abin nan cikin kwanciyar hankali, shi wane rashin nutsuwar ce ya kai sa tura mata sa?on da zai tura wa Inya, Allah Ya sani abubuwan da ke ta faruwa ba a son ransa ba ne, sam kasa controlling kansa yake in sun haWu da Inya a gu Waya, yarinyar wani fizgar hankalinsa take, ko kusa bai so Hajiya ta gansu a gida cikin wannan halin ba, kuskure ne, da iya office Win da mota suka tsaya babu abin da zai ja masa wannan mummunan tashin hankali, da ya san yadda zai tausheta a yi auren nan har a gama cikin salama, Allah Ya gani yana son Hadiza ta masa halacci ba Wan kaWan ba, lokacin da tana budurwa ya san shi bai kai ya kawo a manemanta ba, tausayi irin nata ta amince da shi, kuma ta yi ha?uri da shi tun bai da komai ai ba karen hauka ne ya cije sa da zai rabu da uwar ?a?ansa ba, yana sonta, amma kuma ba ya jin don Sacin ranta zai hana kansa Inya, yarinyar da ke gigita sa ta warware masa duk wani lissafin kansa, kiranta ya shigo wayar daidai lokacin ya ji wani shau?i ya lulluSe sa, kwata-kwata ba ya gajiya da jin muryarta da Wumin jikinta, ba ?aramin kewarta ya yi ba. Ya Wauka tare da cewa "Assalamu Alaikum"

Zazza?ar muryar nan mai gigita tunaninsa ta saki kuka cikin shagwaSa iya ?arfinta take cewa "gaskiya na fasa auren, Allah Ya sani ban yi da niyyar butulci ba, iya ?o?arina na yi don na cire sonka, amma ya na iya, so cuta ne da ba ya jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login