Showing 78001 words to 81000 words out of 81703 words

Chapter 27 - NI NA RAINETA COMPLETE HAUSA NOVEL

FCWA   

20 Dec 2025

52

da dama wanda ba namu ba,kana ba wa yaro tarbiyya ka tura shi islamiyya amma in ya yi wani abun sai a Wauka kai mahaifinsa bamaguje ne ma ba kirista ba, Allah Ya yi mana magani, ina saurarenki"

Na dubi Inya na ce " yi magana mana"

Kanta a ?asa hawaye suka Wigo ta ce "Umma dama da muna ?awance da Siyama ne abubuwa suka shiga tsakaninmu marasa kyau,to bayan na yi aure sai na ce ba zan ?ara ba, ta yi ta bibiyata akan mu cigaba na ?iya, to ashe tana da hotuna da video na da muka yi tare babu kaya,ta watsa hotunan,videon kuma ta ce sai na bata kuWi miliyan Waya, na siyar da sar?ata ta gwal na ba ta kuWin..." Ba ta ?arasa ba mahaifiyarta ta dafe ?irji ta ce "miliyan Wayan kika bata?" Tana share wata uwar zufa.

"Cigaba" mahaifin ya ce yana goge fuskarsa da hankici.


"To shi ne yanzu ta kuma cewa wai sai na bata dubu Wari biyar" ta ?are tana hawaye.

Tana ajiyewa na Wora da cewa "da mahaifin nata cewa ya yi mu wuce a kai case Win police station sai na ga rashin dacewar hakan, ta yiwu kuma iyayenta ba ku san abin da ke faruwa ba tunda yaran yanzu sai addu'a, na ce gara na fara sanar daku ku tsawatar mata" ina rufe baki mahaifin ya ce "ba mu sani ba, wallahi bamu san haka halinta yake ba"

"Ina kika kai miliyan Waya don ubanki" mahaifiyar ta ce tana kwaWa mata mugun duka. Ta kurma ihu ta yi baya Uban ya rufar mata da duka yana tambayarta kuWin.

"Ku yi ha?uri duka ba ya magani. Da kun zaunar da ita ne kun ji, kuma maganar wancan kuWin ya wuce,videon ne kawai ake so ta goge yanzu"

"Ina videon yake?" Uban ya ce ransa a mugun Sace.

"Yana wayata, don Allah Bana ku yi ha?uri" ta ce cikin kururuwa.

"Ba ni wayar don uwarki,buWe min" jikinsa na ta rawa,uwar kuwa hawaye kawai take. Ta buWe wayar ya mi?o min ya ce "ku goge" bana son na ga Inya a yanayin hakan yasa na mi?a mata na ce "goge"

Minti kusan biyar muna tsaye sannan ta ce "na goge" ta mi?o wayar. Baban ya ce "ri?e ki tafi da ita ?ila akwai wasu ki duba da kyau in kin goge sai ki yar,don Allah don Annabi Hajiya ku yi ha?uri"

"Babu komai wallahi, Allah Ya shirya mana su bakiWaya" na ce ina gyara hijabita.

"Mun gode sosai" mamanta ke ta nanatawa har muka fito. A mota na ?ara wa Inya nasiha tare da tunatar mata sanar da ni duk wani abu da ya dameta. Ko bayan mun koma su Bahijja sun dawo da tsaraba lodi-lodi.

Shekara kwana, har shekaru biyu sun shuWe cikin abubuwan da suka faru akwai masu daWi da marasa daWi, cikinsu akwai buWi sosai da Alhaji ya samu haka mijin Tasleem don a yanzu ma sun koma Dubai can ya koma kasuwancinsa, haihuwar Tasleem ta samu ?a mace, kammaluwar karatun Bahijja na Sakandiri,rasuwar Inno,abubuwa da dama dai. Tun daren jiya nake Waukin zuwan Sabir,matashin saurayi ne da na so haWa shi da Inya tun kafin ta auri Alhaji, sai kuma inda yake karatu can UK suka ri?e shi aiki bayan ya kammala,har yanzu ban fidda rai ba ina son Inya da shi don yaro ne mai nutsuwa da kamala duk da dai bazawara ce gani nake ba ta yi wata maraba da budurwar ba,Wan wata Hajiya Asiya ne da muka ?ulla zumunci mai ?arfi da ita a Saudiyya mun je Hajji,mace ce mai tsananin kirki da iya zamantakewa. Su Bahijja ne ke ta rawar ?afar shirya snacks, da yammaci ne zai zo, Bahijja sarkin kwalliya ta tasa Inya ta mata make up aka saka sabon kaya, na faWa musu ro?ona ga Allah ya sa ya ga Inya ne ya ce yana so, bayan isowarsa muka zauna a parlor muna gaisawa, na ?wala kiran Inya ta shigo sanye da mayafinta na ce "kawo masa ruwa mana"

"To Amma" ta ce cikin sanyinta. Ta kawo ta ajiye masa. Muna zaune yana ta bani labarin can ?asar turai sai ga Nadiya ta fito da gudu hannunta ri?e da waya, Bahijja ta biyo bayanta tana cewa "wallahi Nadiya na kama ki sai kin ji jiki,ki zo ki bani wayata" ta ?are cikin shagwaSarta da haka yanayinta yake. Nadiya ta ajiye mata hannun kujera ta yi mata gwalo, ta yi ?wafa tare da cewa "zan kama ki ne" za ta yi ciki ke nan na ce "ba ki iya gaisuwa ba"

Ta saki murmushi tana sosa kai,wani lokacin sai in ta ganin ?uruciya sharr a Bahijjan duk da tana da girman jiki ta cika budurwa sosai, kana iya cewa ta yi ashirin duk da shekarun nata sha takwas ne. "Au ina yini,sannu da zuwa"

"Yawwa!" Ya iya furtawa yana ta kallonta.

"Je ki Wauko masa kayan taSa wa na ga Asma'u ta shige" na ce.

"To" kawai ta ce, ta je ta ciko tire ta dangwarar gabansa ta yi gaba, na girgiza kai ina yaba wautar Bahijja. Yadda na kula Sabir sai kallon ?ofa yake har ya tashi da niyyar tafiya.

Bayan isha'i Hajiya Asiya ta kira ni,shaida mini ta yi cewar Sabir ya ga mata a gidana, sai da zuciyata ta doka don daWi,burina bai wuce na aurar da Inya ba yanzu, girma take ta yi gabana, ga Tasleem har yarinyarta ta shekara,sam ba na jin daWi, amma kwatakes na yi da na ji description Win da Sabir Win ya yi, ba Inya ba ce, Bahijja ce. Na bar ta a zamu yi magana da Alhaji sai na kirata daga baya. Alhaji da shigowarsa ke nan ya dafa ni yana "my Deeja"

Na sakar mai hararar wasa na ce "meye wani Deeja don Allah da tsufana,har fa jika gare Ni"

Ya lakace min hanci ya ce "ita soyayya ai ba ta tsufa", na yi murmushi na ce "?warai masoyi"

"Ya na ganki haka kamar da magana", na langaSar da kaina na ce "ka ga wanda nake ta wa Inya kamu wai shi kuma Bahijja yake so, ga shi har na fallasa musu cikina"

Ya Wan taSe baki baya ?aunar duk wata magana da zan yi na sa masa Inya,kafin ya Waga gira ya ce "to ko kina wa ?ata ba?in ciki ne, don na kula shi yaron ai kina ji da shi"

Na yi murmushi na ce "Allah Ya sa hakane alkhairi" mun yi magana da Alhaji inda ya ce na tuntuSi Bahijja, ganin yarinyar nake kamar ma hankali ba ta yi ba shegen wasa gareta, amma na sani yana Waya daga cikin kuskuren da Iyaye ke yi shi ne ?in aurar da yara bayan sun kai munzali.

Ban ja al'amarin ba a washegari na sanar da Inya kan wai Bahijja yake so, ba ta nuna wani rashin jindaWi ba nan ta sanar min dama akwai wani da yake ta son ya turo, Bahijja kuwa ba kunya ta ce ta amince.

Alhaji ya yi bincike akan dukkansu ba su da wata makusa, Inya mijin yana koyarwa ne a wata Secondary da ke nan kusa da mu ya kuma san Inya Win bazawara ce, yayin da Bahijja ma lulu?awa za ta yi can wata ?asa UK kamar Tasleem, Inya ce dai a kusa da ni. Bayan bincike iyayen kowanne suka turo aka saka rana watanni huWu masu zuwa, number Maman Mujahid da nake ta ajiye da ita na Wauko (08066726866) muka yi magana na siya kayan sanyinta masu inganci, don na san sanyi muguwar illa yake wa ?a mace, duk wani gyara da za a yi in da sanyi asara ce. Muna gama wayar Alhaji ya shigo na gutsiri ayabar da ke gefena, ya zauna tare da jingina kansa a kafaWata yana ta kallona, na yi murmushi na ce "ranka ya daWe!"

Ya langaSar da kai ya ce "Hadi ni ba ki bani ba" kullum cikin canza min suna yake, na yi murmushi na mi?a masa ya gutsura.

Ya ce "Hadi nima ina so" na kalle shi ya yi narai-narai da furfurarsa da ta firfito sosai na ?yal?yale da dariya na ce "me kake so" shagwaSa ce dai Alhaji ba zai daina ba, sai in bai samu wuri ba,tamkar ?aramin yaro yake koma mini in ya so.

"Baby nake so Hadi,Baby nake so ki haifa mana" ya ce yana matsa hannuna. Na yi dariya na ce "kai ko yanzu ma ka fara ganin babies amma ba daga wajena ba, daga wajen yaranka"...

*Ayyah jiya ban ji daWi ba ne wallahi ban yi tunanin zan kai yau ba, ban taSa fashin post ba sai rannan sau Waya kuma na sanar muku na kuma biyaku abin ku on weekends, ban ji daWin yadda wasu suka yi min maganganu marasa daWi ba a pc sam, Ni ba yarinya ba ce a ?alla idan ko ra'ayin za a faWa a tausasa harshe don Allah,mu mutunta juna as i believe oll of us are matured, wanda suka kira suka ya jiki da duba lafiyata na gode ?warai da gaske,masu message ma na gode Allah Ya bar wannan ?aunar har gidan aljanna, masu ?orafinma na san ?aunar al?alamina ta sa haka kuma na fahimta, ina muku ?auna ta gaskiya, Allah Ya bar wannan taren>?? har a aljanna, jazakumullah bikhair*

*Practical class for baking ga mutanen Sokoto is still going on, with just 10k zaki zama CEO Win kanki*


*My book is 500 only via 1401611541,Fatima Lawal Sa'id,Access bank, DM 08167888934*

RAHUSA DATA AVAILABLE (MTN)

1GB-280
2GB-560
3GB-840
4GB-1120
5GB-1400
10GB-2800
(1401611541, Fatima Lawal Sa'id, Access bank. Call 08167888934) All network available.

3?? 5?? =??

Bayan bikin su Bahijja da Inya, sai gidan ya zamana ya yi min shiru, Nadiya na ta fama da karatu,soyayya muke gudanarwa mai tsafta Ni da Alhaji, rayuwar ba ta taSa gara maka a kodayaushe farin ciki tana cakuWe ne da ?alubale a kowane taku, amma ha?uri, juriya da soyayya sun taka muhimmiyar rawa a zamantakewata da Alhaji, duk wani abu ya gani ko ya samu Hadiza, haka nima a kodayaushe yake a ma?ale a zuciyata da cikin addu'ata, Alhaji ya shiga islamiyya tunda shekaru sun ja ya Wora yara bisa kasuwancinsa, hakan kuwa ya ?ara mana kusanci a kodayaushe muna manne da juna cikin aminci, da neman rahamar Allah.


*15 years later*

Tana kwance saman ledar Wakinta ta yarda filo yaronta na gefenta suna bacci ta ji an banko ?ofar, "Ya Rasulillahi" ta ce tana dafe ?irjinta da ya yi wani irin bugawa, haka take fama da bugun zuciya da sauri-sauri musamman in abu ya razanata,wani lokacin haki ya taso mata, hawan jini take fama da shi ba Wan kaWan ba.

Matar da ba za ta wuce shekaru ashirin da biyu ba ta watsa mata kallo tare da cewa "kai Yusuf zo ka siyo min maggi don uwarka"

"Idan ya ?i zuwa fa?" Inya ta ce ranta a bala'in Sace, duk wani Wan hutu ko bacci ta samu Samira ta yi ta takalen bala'i ke nan, saboda jarabarta sai da Imaan babbar ?arta da ta ci sunan Amma ta bar gidan ta koma can wajen Amma.

"Na ci uwar yaro na gurji bakinsa, ubansa ya dawo ya ?ara masa wallahi" Samira ta ce tana tauna cingam Win bakinta.

Ba ta haWa kwana biyu ba ta share hawayen tashin hankalin da Samira ke sakata ba, kuma ta yi magana Adamu mijinta ya rufeta da bala'i tana son wai lalata tarbiyyar yaransa, ta sani tunda ya fara neman auren Samira ta rabu da Wan kwanciyar hankalinta, fifiko yake nuna wa sosai akan Samira, har ranar kwananta watarana sai ya ce ta je shi ba shi da lafiya, cikin dare in za ta banWaki ta ji nishinsa a Wakin Samira, ban da ciyarwa da sutura duk sallah,Adamu ya sakar mata ragamar kula da yaran nasa guda uku, ba don ?ar NCE Win da ta yi ba take aikin koyarwa da rayuwar ta yi mugun hajijiya da ita duk da lokuta da dama Amma kan taimaka mata takan ga kuma sa?on Tasleem da Bahijja jefi-jefi. Hawayen ne suka silalo mata kamar kodayaushe ta dubi Yusuf ta ce "tashi ka je!"

Ya fita Win ya siyo amma da kuka ya dawo, Samira ta wanke farar fuskarsa da mari har da shatin hannunta rangaWau a kai, ba ta da ikon magana don ta san zaman boranci take yi, ta yi magana Adamu ya hayayya?o mata in ba ta yi sa'a ba ya taSa lafiyar jikinta. Ba zata ce kwata-kwata rayuwar ?unci take ba a'a,ta kan dara ta kan koka kamar yadda kowani Wan Adam yake yi. Ban da matsalar Samira da yadda Adamu ya yi juyin masa da soyayyar da yake mata tun shigowar Samira rayuwarsu,ban da wannan rayuwa take da tasa ta gane farin ciki ba kodayaushe yake zuwa da kuWi ko wata riritawa ba, yana zuwa ne idan aka samu wadatar zuciya da zama iya inda Allah ya zaunar da kai, sosai takan yi tunanin rayuwar da ta yi a baya,da mutanen da suka sota suke kan nuna mata son sama da kowa a rayuwarta,da yanda ta yi amfani da wannan so da ?aunar da suke mata ta cutar da su. Ta kan tuna mahaifinta tana kuma nema masa gafara duk da ta san tarin zunubansa, takan koka akan rashin tuban da ya yi har lokaci ya ?ure masa.

Yau ranar asabar ce, gidan Amma take yini, al?awari ne da Adamu ya Wauka tun kafin aurensu, ta na farin ciki da kuma har yau bai karya shi ba duk da zugar Samira ya ri?e al?awarin, zuciyarta cike da nishaWi ta share ledar Wakinta ta goge, ta Wauki Nihal da ke bacci ta wanke ta shirya, ta zuba wa Yusuf ruwa a bokiti nan tsakar gida ya yi wanka, itama wankan ta yi ta janyo atamfarta ta shirya, ba dai wata shiga ce ta a zo a gani ba amma ba a wula?ance take ba, tana cikin masu rufin asiri ko ya yake, Wakinta ta sa wa kwaWo don Samira jifa da neman bayanta take hai?an sai ta rabata da gidan aurenta,ba ta samu nasara ba ne kawai saboda ?arfin ibada da ta dage da shi,haka kullum cikin neman afuwar Allah take, abubuwan da ta yi ne ke ta dawo mata ta sani. Napep ta tarar musu, ba su zame ko ina ba sai gidan Amma.


HADIZA

Ina zaune ?asan bishiya ri?e da casbaha,lazimi nake domin shi da karatun Qur'ani sune suka zame min abokai a kodayaushe, ?ar matashiyar budurwar wadda take takwarata babbar ?a ga Inya ce ta fito hannunta ri?e da kofi, ta ajiye da dariyarta ta ce "ashe nan kika gudo Amma ina ta nemanki, ga ruwan tufarki", na yi murmushi na ce "takwara ni surutunki na gujewa ki bar ni na yi tasbihi ko dubu biyar ne kan ki fara hirar" ta ?yal?yale da dariya ta ce "kamar kin san labari zan baki wallahi, amma idar tukunna" ta ajiye min ruwan tufar ta juya, na yi murmushi ina jin ?aunarta, ina Wauka na ji sallamar su Inya, na faWaWa murmushina ina warewa Yusuf hannu da ya rugo wajena da gudu. "Kai ba ka da hankali ya zaka Wane kanta haka, so kake ka karya min uwa" Inya ta ce cikin faWa. Na saki ?ar dariya na ce "wa ya ce miki nima ruwa-ruwa ce irinku, ta ya zai karyani"

Ta yi murmushi ta zube har ?asa ta ce "Amma ina kwana, kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillahi su Nihali bacci ake yi?" Na tambaya.

"Ai kuwa, bari na fara gyaran gidan tukunna na zo, me kike marmarin ci yau Amma?" Ta tambaya da ?ar dariyarta.

Na yi murmushi na ce "Ni kam da zan samu fate da na ji daWi"

"To bari na Wora kuwa, da shuwaka ko?" Ta tambaya, na gyaWa mata kai. Na bi bayanta da kallo, tausayinta nake ji sosai, tun can da ban da al'amarin da ya gifta tsakaninmu wanda ba na jin zan manta,amma na yi ?o?arin binnesa a zuciyata,sanyi gareta,?addarar aurenta mai wahala ce,duk da ba kodayaushe dama rayuwa ke cike da jin daWin ba, ban yarda ma akwai shi wai dawamammen farin ciki ba,amma rayuwar aurenta mai wahala ce. Lokuta da dama takan share hawaye ta ce "Amma in na tuna na kan ji na tsani kaina,duk da ina ta girbar shukar da na yi,na kan kwana da ba?in ciki a duk na lula duniyar baya" yanzu da tsufa ya kama ni alkhairan da na yi ke ta dawo min,da na watsar da Inya kamar yadda kowa ya so na yi a baya da kaWaici ya dame ni a yanzun da na yi rashin wani jigo na rayuwata,Alhaji Muntari ina fatan Allah Ya haWa fuskokinmu a Darussalam, babu Kubra,babu Malam nawa, Tasleem da take kasuwanci can Dubai take da iyalinta, haka Bahijja itama tana ?oli sai dai mu yi waya na ga aikensu, Nadiya auta ta zama cikakkiyar likitar mata duk da ta samu jinkirin aure amma ba kasafai take zama ba saboda yanayin aikinta, Inya Win dai ita ke kusa da ni, ta zo ta taya ni hira ta Webe mini kewa, ta mini shara da gyaran gida, ta mini girki, ?arta ta mini wankin ?ananan kaya da aiken Wauko wannan Wauko wancan,mu yi hira mu yi wasa mu yi dariya, jikokina na ?a?an da na haifa sai dai na gansu a hoto ko in sun kawo mana ziyara lokaci-lokaci,ita rayuwar kamar shifcin gizo ce, ba komai ba ne a cikinta,idan ka tsaurara komai zai zo maka a tsaurare, idan ka sau?a?a komai zai zo maka a sau?a?e,haka kuma mu duka ?an cirani ne da muke haWuwa da mutane mabanbanta a hanyar mu,kowa da irin halayya da Wabi'unsa amma idan ka ha?ura ka jure sai ka zamo tauraro a tsakankanin waWanda zamantakewa ta haWaku. Rayuwar ba ta zo min da sau?i ba Ni da yarana,?addarata da ta yarana ba ta kai mu matsayin da muke cikin sau?i ba,ba ni da tabbacin yadda rayuwa za ta ?are wa yaran nawa bayan ?asa ta rufe idanuwana,amma ?aunarsu ga juna ta sa ina da ya?inin in dai suna kan zumuncin da na Wora su, ko ya rayuwa za ta gara da su,Waya zai tashi Waya ko da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login