Showing 1 words to 3000 words out of 81703 words

Chapter 1 - NI NA RAINETA COMPLETE HAUSA NOVEL

FCWA   

20 Dec 2025

26

??ࡱ?>?? ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????0Table????????BData
???????????????????? P?? KSKS??o???????tt? ? ? ? i } ??%D? ?$?
?3
*t? ? ? ? ? ? ]
?} ]
} ]
} ? }  *NI NA RAINETA*

*?M...*


*FCWA*

*Bismillahi rahamanir raheem*


1??



"Wannan kwalliyar ai dole ki kasance ke kaWai a wajen Abba, wallahi Amma kin yi kyau" cewar Tasleem tana kashe min ido Waya cikin dariyar sha?iyanci, na rarumi pillown da ke kan kujera na jefa mata cikin dariya na ce "ja'ira mara kunyar yarinya" na shige hanyar da za ta sada ni da sashen Alhaji cikin takuna Wagwas Wagwas kamar budurwa, bakina Wauke da sallama na tura ?ofar Wakinsa, ban same shi a ciki ba sai dai na ji alamar shower da ke kunne wanda hakan ya tabbatar min yana banWaki ne. Duk da komai na Wakin yana nan tsaf da shi bai hana ni mi?ewa ba na ?ara ?al?ale wajen tare da jona burner na ?ara turaren wuta, gudun AC na ?ara sannan na nufi gado, hannuna na mi?a na Wauki wayarsa da ke kan gadon na latsa don duba lokaci, Alhaji da ya fito daga wanka ya yi hanzarin isowa gareni ya amshi wayarsa ya ce "wai ba ni da halin ajiye waya sai kin taSa Hadiza?"

Na taSe baki na ce "lokaci na duba" ban kawo komai a raina ba duk da password Win da ya ma?ala wa wayar tasa da bai taSa sawa ba tsayin lokacin da muka Wauka tare, sama da shekara ashirin a inuwar aure.

Abinci na gabatar masa marar nauyi ya tsakuri abin da zai tsakura ya mi?e yana faWin "wallahi cikina a cunkushe yake,Wan sa Inya ta dafa min shayi"

"Bari na dafa maka, Inya yanzu ai ina jin karatu take yi" na ce ina mi?ewa.

"A'a Hajiyata kira ta a waya ki ce ta dafa min shayi ta kawo min, ke zauna a nan na kalli wannan kwalliyar da aka yi min na more" ya ce yana Waga min gira. Na yi murmushi na ce "an gama ranka ya daWe" na Waga waya na saka Inya ta dafa shayin ta kawo min. Na juya ga Alhaji ina jin daWin yadda soyayyarmu har yau bayan mun hayayyafa take nan kamar ta saurayi da budurwa. Hira muka shiga yi ta abin da yake faruwa a ?asar har Inya ta shigo, sanye da sabuwar doguwar rigar da na siya musu Wazu ita da Tasleem, ta Soye dogon gashinta cikin hula sai doguwar jelar da ta kitse da ke ta reto a ?asan wuyanta, hannunta Wauke da tray wanda aka Wora flask Win shayi ?arami na zamani da ?an kofuna. Ta Wora tray Win kan centre table Win da ke Wakin tare da cewa "ga shi nan Amma"

"Na gode, Allah Ya yi miki albarka" na ce

"Ameen, sai da safenku" ta ce da murmushi ta yi waje.

Na dubi Alhaji da murmushi na ce "ga shayin da ka Wauka ibada a kwanakin nan"

Ya yi ?ar dariya ya ce "yanzu na gane masa ne". Hira ce ta kuma Sarkewa a tsakaninmu kafin daga bisani muka koma Waki don kwanciya. Bayan na idar da addu'a na shafe jikina na dubi Alhaji da ya tsiri latse-latse a waya cikin ?an kwanakin nan, na taSe baki na ce "wai fisabilillahi me kake yi da waya ne duk dare yanzu"

Ya Wago ya kalleni ya ce "Hadiza ai yanzu duk cinikayya ta koma ta yanar gizo, kuma kin ga ni ba wani samun lokaci nake da rana ba, yanzu nan muna magana ne da Basiru kan kayan da zai turo mini daga China"

"To Allah Ya taimaka" na ce ina gyara kwanciya, ya jima yana latse-latsensa kafin na ji kwanciyarsa a bayana yana rungumata, na yi murmushi kan yadda Alhaji sam ba ya gajiya da abu Waya kullum jin sa yake kamar sabon ango, sai da na sa ma masa nutsuwa sannan muka mi?e don tsarkake jikinmu, wayarsa da ke gefen pillownsa ta kawo haske idona ya kai kan screen Win,ban iya karantawa ba sai kalmar ?arshe da na gani wani abu sannan aka ?ara da baby, Alhaji ya yi saurin Waukar wayar ya kashe bakiWaya, jikina ya yi wani irin sanyi ?alau na kasa motsa wa, ya ja siririn tsaki ya ce "yaron nan Basiru sam ba shi da hankali, bai son mutum na bu?atar hutu ba, yanzu fa muka gama magana da shi amma kin ga ya sake turon wani sa?o akan kaya." Ya wuce hanyar toilet, na bi bayansa ina ?aryata idanuwana da suka gane mini Baby, na tilasta wa zuciyata cewar Basiru idanuna suka gani, da wannan na samu na ya?i zargin da ya so ya Warsu a zuciyata.

Assalatu na farko na tashi, sai dai ko da na tashi babu Alhaji babu dalilinsa, ba Wabi'arsa ba ce tashi da wurwuri, wani lokacin ma sai na yi da gaske yake tashi, nauyin bacci garesa. ?arar famfo da na ji na ta zuba babu ?a??autawa sama da minti goma ya sa na nufi banWakin da nake kyautata zaton Alhaji ne ke amfani da shi, ina ?o?arin buWewa sai na ji kamar wanda yake magana da wani a ciki, na tura ?ofar na gansa tsaye da waya a kunne alamun waya yake, cikin daburcewa ya fara inda-inda tare da sauke wayar yana washe baki da cewa "ashe kin tashi, nima yanzu na tashi ba a yi ko minti biyar ba, Sagiru ya tasheni"

"Shi ne kake waya a banWaki" na ce ina kallon yanayin da ya shiga na rikicewa.

"E, ai..." Ya fara sosa ?eya daidai lokacin aka fara kiran sallah hakan ya sa ya ratsa ta gefena ya wuce da sauri, na bi bayansa da kallo ina mamakin wannan sabon sauyin da ya shigesa. Alwala na Waura zuciyata cike da tunannuka na nufi dadduma, na yi sallah, da na idar sai na tsinci kaina da kwararo addu'o'i ga mijina kan Allah Ya tsare min shi daga sharrin wannan zamani, ya kauda duk wani abu da zai shigo rayuwarmu wanda ba alheri ba, bayan na shafa na jawo Qur'ani na soma karantawa, da wannan na samu nutsuwar zuciya. Bayan na idar na rufe tare da mi?ewa na nufi sashen yara don na faWi abin da za a Wora don na san sun tashi. Tasleem sam da asuba ba ta da mamora, duk yadda ka so ta yi maka aiki ba za ta yi ba, sai ta koma wannan baccin nata na ?a'ida yayin da Inya kuma ba ta komawa bacci kamar Ni, sai an gama gyara gidan tass yara sun tafi makaranta ta karya sannan za ta koma, da sallama na tura ?ofar Wakinsu Bahijja da Nadiya, sanye suke cikin kayan makaranta, Bahijja na duba littafi yayin da Nadia ke kwance kan gado tana bacci, "Amma ina kwana" cewar Bahijja.

Na yi murmushi na ce "lafiya lau, har kun yi wanka"

"E, yanzu na gama shirya Nadiya ta koma bacci" ta ce.

"Madalla, Allah Ya yi miki albarka, bari na saka Inya ta muku break fast" na ce ina ficewa.

Tura ?ofar Wakin na yi da sallama, kamar yadda nake zato Tasleem na kwance ta koma bacci, yayin da Inya ke linke hijabi alamun wadda ta yi salla ce, da murmushi ta ce "Amma ina kwana?"

"Lafiya lau, kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau" ta ce.

"Madalla, ki yi hanzarin Wora doya da ?wai don Allah kar ki bari yaran nan su makara" na ce ina ?o?arin fita.

"In sha Allah" ta ce.

Ko da na tura ?ofar Wakin Alhaji gabana ne ya yanke ya faWi dalilin ganinsa da na yi, ya yi ruf da ciki yana waya har wani shilla ?afa yake alamun cike yake da shau?in wayar.

"Da Basirun kake waya da safiyar nan?" Na ce muryata na kakkarwa.

Ya yi wata iriyar hantsilawa ya dira kan ?afafunsa bayan ya kashe wayar yana sosa ?eya ya ce...


*YA KUKA GA KAFCEN?*


#SHARE


*NI NA RAINETA*

*?M...*


*FCWA*

*Bismillahi rahamanir raheem*


2??


"Wani irin sa ido kika koya ne Hadiza, ba hali in yi waya ko in latsa waya sai ki sakoni a gaba,ba zan yi amfani da waya kike nufi ba kome, to da Hajiya nake magana, ba na son sa ido" ya fitittike yana faWa sannan ya mi?e ya fice.

Alhaji bai shigo ba sai da sha Waya ta gota, a gaggauce ya shirya ya ci abinci ya fice ba tare da ya ko kalli inuwata ba, wannan abu ba ?aramin ciwo ya yi min ba, don hakan ba ta taSa faruwa tsakaninmu ba tsawon shekarun da muka kwashe, muna samun saSani amma duk faWan da zamu yi wuyarta na Sata rai, duk fushin da yake zai sauko ya shiga rarrashina ko da ni ce da laifi, bala'in sona yake, gaban kowa kuwa har da ?a?anmu ba ya Soye son da yake mini, bayan fitarsa sai na kwanta a gado cike da jimami,komai sai na ji ya fice min a rai, baccin ma na gagara komawa sai na yi ta juye-juye tunanin sauyin Alhaji na ta kai kawo a raina. Wajen sha biyu da rabi Inya ta shigo Wakin bakinta Wauke da sallama.

Da murmushi ta ce "Amma yau na ji ki shiru, halan ba kya jin daWi ne?"

"Kaina ke Wan sara wa, an kammala abinci ne?" Na tambaya.

"E, dambun couscous na yi da miyar hanta."

"Yawwa, kira Isiya ya kai wa Alhaji abincinsa don ba wani abincin kirki ya ci ba"

"La! Amma bari kawai na biya na kai masa, zan je saloon duk hanya Waya ce." ta ce.

"To shi ke nan, sai kin dawo Allah Ya yi miki albarka, Ina Tasleem ne?"

"Ameen. Tasleem tana kallo"

"Aikin ke nan!" Na ce ina mi?ewa yayin da Inya ta fice.

Alhaji yau kwata-kwata bai kirani ba, kira biyar na masa bai Waga ba. Sai gabanin magariba ya shigo gidan, duk da na ji dirar motarsa ban bi ta kansa ba don na tanada masa komai da zai bu?ata na ajiye a sashensa. Bayan sallar isha'i kwalliya na Wauka ?ar gaske kamar wata sabuwar amarya na karya Wauri, ko kusa ban yarda na maida kaina tsohuwa ba, duk abin da zamani ya zo da shi amsa nake, ban bari an bar Ni a baya ba, fannin kwalliya da girki na zamani ?aryar budurwa ta koya min sai dai ta koya a wajena. Na saka takalmi mai Wan tsini na bi ko ina na jikina da turaren da suke haukata Alhaji, ko laifi na yi masa in har na yi kwalliya ta musamman shi ke nan, ya gigice a kaina ke nan, na nufi locker ta da nake ajiye kayan mata na asalin sakkwatawa masu inganci na buWe, haWa wannan, dama wancan na shanye tass na kwankwaWi ruwan kwararo ni'ima, sannan na kuskure bakina na fesa mouth fresh na jefa mint a baki na fita ina takuna Was Was Was, a parlor na tadda yara suna kallo, nan kowa ya hau zuzuta kyawun da na yi, kullum cikin ado nake ba wai ban saba ba ne, amma adon yau Win na musamman ne, na yi murmushi na ce "Bahijja da Nadiya ku gaggauta tashi zuwa bacci"

"Hooo! Amma wallahi kin wanku kamar a injin" cewar Tasleem, na girgiza kai ina dariya na dubi Inya na ce "ki saka su Bahijja su kwanta yanzu, Ni na shige, sai da safenku"

"To Amma, wallahi kin yi kyau sosai" ta ce tana murmushi. Murmushin nima na yi na wuce su. Ina jin daWin yadda gidan nawa yake cikin farin ciki da ?aunar juna a kodayaushe.

Da sallama na tura ?ofar Wakinsa, sassanyan ?amshin da ya gauraye da sanyin Ac suka hura ni, na Wan lumshe ido ina jin wani abu da ya taso ya tokaren zuciya yayin da na yi tozali da Alhaji yana latsa waya yana ta sakin murmushi, na daure zuciyata na shimfiWa murmushi a leSena, so nake yau na yi nasarar shafe koma mene yake yi a wayar nan, na farfaWo da soyayyata da na ga tana neman disashewa, na ?arasa wajensa cikin takun ?aniya na zauna gefensa, ya yi hanzarin latsa wayarsa ya kashe ya Wago yana kallona, na saki murmushin zuciyata fal takaici na yi narai-narai da idanuwana tare da kama kunnena ina aika masa kallon da na san yana gigitasa, ya kauda kansa gefe, na taushi zuciyata da ke azalzalar na tashi na ba shi wuri bai da gaskiya sam, na kwanta a kafaWarsa na ce "karon farko tsayin zamana da kai ba ka taSa ?in Waga wayata da watsar da lamurrana ba sai a yanzu, me na aikata da zafi haka Alhajina?"

Ya ja doguwar ajiyar zuciya tare da kamo hannuna ya ri?e yana cewa "ke ce ai Hajiyata na kasa gane miki, da na Wauki waya sai bin diddi?i kamar wata ?ar sanda"

"Ni ai ba zan taSa zama ?ar sanda ga mijina ba sai dai lauya" na ?are ina kanne masa ido Waya.

Ya saki murmushi ya ce "amma fa dole na ba da tukwicin wannan kwalliya, don an burge ni"

Na yi wal da ido na ce "tukunna ma dai burgekan"

"Allah ko, ki ce yau akwai harka"

"?warai! sai na ga tun?wal uwar daka" na mi?e ina dariya. Ya sa hannu ya janyoni na faWa jikinsa ya ce "ai ba zan iya jira ba Hajiyata, yanzun nan za a fara dakan"

Mun murji juna sosai cike da soyayya, sumbatu sosai na saka Alhaji kafin muka rankaya toilet don wanka. Daren hanasa latsar wayar na yi, a ?irjina ya kwanta har bacci ya sure shi, na bisa da kallo ina jin ?aunarsa da mugun kishinsa na rufeni, sai na tsinci zuciyata da addu'a Allah Ya sa ba tarkon mace ya faWa ba, na ?an?ame kayana ina jin wani bacci mai cike da nutsuwa na figata, na yi nisa na ji zum zum akan katifa, na buWe idona cikin bacci na dubi gefen Alhaji da wayarsa ke haske, na janyo cike da mamakin wane zai kirasa a irin wannan lokacin. _Sweet baby_ idona ya sauka a kai wani abu ya caki zuciyata, kiran ya yanke wani ya shigo. Sosai zuciyata ke tunzura ni na Wauka na zagi uwar wadda ke kira, jiki babu ?wari na Waga tare da sallama,ba a amsa ba aka yi shiru, na ciji leSena na ce "yanzu baiwar Allah bai yi dare a wajenki ba ki kira mutumin da kika san yana da aure, in ke ce aka yi wa haka ya za ki ji?" Tausar zuciyata kawai na yi ban cusa mata zagin kutumar kutumar ba. Katse kiran aka yi daidai lokacin da na ji kuka na ?o?arin kufce min, na sauke wayar ina bin fuskar Alhaji da kallo da ya tashi yanzun nan, wani mugun haushinsa ya samu gurbi a zuciyata,na cilla masa wayarsa...


*DON'T FORGET TO COMMENT AND SHARE*

*NI NA RAINETA*

*?Mss Flower

*FCWA*

3??


Na janyo doguwar hijabi da ke rataye a hanger na saka na nufi hanyar ?ofa ina jin wani mugun kishi na taso min, abun da mugun ciwo a ce Alhaji tun da bai yi aure ba sai a yanzu da girmana yarana duk sun zama ?ammata a ce wai yanzu mijina zai ?aro aure, na cije leSena da mugun ?arfi lokacin da na zauna a gadona,na Waga kai na kalli agogo da ta nuna ?arfe uku na dare har ya gota, "watssatsiya ta rasa yaushe za ta kira mutum mai aure sai ?arfe ukun dare" na ce hawaye na zubo min. Bacci a daren bai san idona ba, kuka na dirza na ba?in ciki sannan na ?arasa raya daren da sallah,bayan na yi sallar asuba kwanciya na yi kawai, na san Inya za ta shirya su Nadiya, ta yi break fast, ban fito ba sai wajen ?arfe goma da rabi,a parlor na tadda Inya tana kallo.

"Alhaji ya fita?" Na ce ina ?o?arin zama.

"Ya fita tun Wazu, Amma me ya sameki?" Ta ce a rikice.

"Idona ke ciwo, kawo min break nan" na ce ina duban tv, babu wani abin da nake ganewa har ta dawo Wauke da tray. Duk ?aunata da dankalin turawa soyayye ban iya cin ko ?wara goma ba na ture, na kurSi shayi na koma Wakina, wuni zungur ina kan gado babu abin da ke tada ni sai sallah. Kafin magariba wani mugun zazzaSi mai ragargazar jiki ya kama ni, wayata na Wauka na kira Alhaji kira biyu bai Waga ba. Sai a na ukun ya Wauka ba tare da ya ce komai ba.

"Zan je asibiti" na ce.

"Allah Ya kiyaye" ?it ya kashe wayar, na bi ta da kallo. Ban taSa sanin wannan ba?in cikin wasu matan ke ?unsa ba sai a yau, haka na cije zuciyata na shirya muka fita tare da Inya.

Wani irin Waci nake ji a ?asan raina, na tuna yadda Alhaji ke shiga tashin hankali in ya ji kaina na ciwo, sai na tsinci kaina da matsar ?walla.

"Sannu Amma, tun da an miki allura muna komawa gida ki ci abinci, ki sha magani sai ki kwanta" ta ce cike da kulawa.

Na share fuskata ina jin wani sanyi na ratsani, ha?i?a ?a?a ni'ima ne, kulawarsu da nuna damuwarsu ga lamurranka kan sau?a?a wani raWaWin, da na tuna ni'imarsu da Allah ya yi mini kuma na sani har abada ba za su sake wata uwar ba kamar Alhaji da zai iya sake mata sai na ji nutsuwa na saukar min. Wayar Inya da ke cikin jaka ta sake tsuwwa, na kalleta da mamakin wa ke ta kiranta haka ta ?i Wauka. Na ce "ki Wau wayar mana ana ta kiranki"

Ta sunkuyar da kai tana wasa da zobenta ta ce "Amma zan kira in mun koma" ta kashe wayar bakiWaya.

Na yi murmushi ina yaba hankali da nutsuwarta don na san ba zai wuce saurayinta ne ke kira ba, na ja tsaki da na tuna a yanzu da yaranmu suka tasa suka kai munzalin aure wai a yanzu ne Alhaji ke fara soyayya.

"Amma me ya faru?" Ta ce.

Na girgiza kai tare da cewa "ba komai". Har muka ?arasa gida ban kuma cewa kanzil ba na shige Waki. Tasleem ce ta shigo da abinci Wakina ta ajiye tana min sannu, dole na Wan ci don takurarta sannan ta fita, ban waiwayi Alhaji ba don na ?udurtawa raina sai dai ya nemeni ba dai ni na nemesa ba, don ban masa laifi ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login