Showing 75001 words to 78000 words out of 116554 words

Chapter 26 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1272

Jiddah tace "Baki masa hallaci ba Afeefah, duk irin son da yake maki ki rufe ido kice baki son sa" mikewa tayi hawaye cike idonta tana kallonsu tace "Kmr ynda bbu xancen aure tsakanin ku da shi, to nima bbu, don a matsayin Yayan da muka fito ciki daya na daukesa, don hka ku kyaleni" tana kai wa nn ta fice daga dakin hawaye na bin kuncinta, dakin Mami ta shiga ta sameta xaune tana waya, ta fada kan gadonta ta shiga rera kuka a hnkli, Mami ta kammala wayar ta juya tana kallonta da mmki tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Ko ba su Anty jiddah bne suke min magana wae me yasa nace bna son yayanmu, ni kice masu su daina min irin maganan nn bna so, don matsayin yayana na daukesa kuma ni ba aure tsakaninmu" Mami bata ce komae ba sae danna wayarta kawae take amma da ganinta kasan jikinta yyi sanyi, mikewa tayi ba tare da ta tanka ta ba ta fita daga dakin, Afeefah ta ci kukanta daga karshe bacci ya dauketa.

Karfe biyar saura na yamma Afeefah na daki kwance ta tsura ma Tv ido, tun bayan maganar da su jiddah suka mata daxu taki komawa dakin ya Aliyu, har abinci bbu ynda Mami bata yi da ita ta kai masa ba tace ita kanta na ciwo, duk da ma bacci yake tayi bayan fitarta don sae lkcn ya samu bacci. Fadila ce ta shigo dakin tace "Ya Ma'aruf ya xo" da sauri Afeefah ta mike tace "Da gske," bata rufe baki ba ya shigo dakin, murmushi tayi tace "lah Ya Ma'aruf" ya mayar mata murmushin yace "Kina ta bacci ko kasa" murmushi ta kuma yi tace "wllh ba bacci nake ba kallo nake, ya su Fadil" yace "su Fadil na gida, ya jikin yayanku" ta sunkuyar da kai tace "Da sauki," yace "na shiga yana ta bacci, bari in je in dawo" tace "Ina xa ka ya Ma'aruf?" Yace "Gidansu Dr Aliyu xan tafi, bashi da lfya" mikewa tayi sa sauri tace "Don Allah ya Ma'aruf mu je tare" kmr xata yi kuka ta kare maganan, yace "Ae Mami baxa ta yrda ba," hawaye cike idonta tace "Ka tambayar min ita plss yaya" ya dan yi shiru snn yace "To ina xuwa" ya fita daga dakin, Hijab dinta ta dauko da sauri tana Addu'ar Allah yasa Mami ta yrda, ba a dau lkci ba ya dawo yana kallonta yace "Mami bata yrda ba, idan naje I wil extend ur greetings kin ji" bata sauraresa ba ta fice daga dakin xata dakin Mami har hawaye ya cika idonta, yyi dariya yace "Ke wasa nake maki, ki je ki sallameta ina jiran ki a waje" dan murmushi tayi ta sa hijab dinta snn ta nufi dakin Mami, ta sameta ita kadae, ta durkusa gefenta tace "Mami xan raka ya Ma'aruf" Mami tace "Ya gaya min amma kada ku dde Zainab, ku yi masa sannu, Allah kara lfya" mikewa tayi tace "To Mami" snn ta fita daga dakin, Su Anty Safiya dake girki a kitchen tayi ma sallama, suka ce "Ina xa ki?" Tace "Ni da ya Ma'aruf xamu fita xan rakasa ya duba..." Hararan da suka watsa mata yasa ta yin shiru, Anty baby tace "Maxa ki je ku dawo ina neman ki, sha sha sha kawae wae bare ya fi dan uwanta" a sanyaye Afeefah ta juya ta fita daga kitchen din, horn ya Ma'aruf ya danna mata, ta nufi motar ya Aliyu, ta bude front seat ta xauna, ya ja motar suka bar gidan yana cewa "Shine kika shanya ni"murmushi kawae ta kirkira. Sae da suka hau main road snn ba tare da ya kalleta ba yace " Kinsan musabbabin ciwon Aliyu?" Ta dan yi shiru snn a hnkli tace "Yayanmu?" Ya girgixa mata kai yace "Yhur lecturer" da sauri ta girgixa masa kai tace "A'a" yana kallon titin gabansa yace "Sbda ke ne Zainab" dafe kirji tayi a dan tsorace tace "Ni kuma Ya Ma'aruf? Me nayi masa?" Yace "Baki yi masa komae ba, amma ana neman raba sa da ke ne" ta xaro ido tace "Kmr ya yaya?" Yana tukin sa a nutse yace "Dad ke son hada ki da yayanku Aliyu, shine ya kirasa yake gaya masa wae ya hakura da ke, sae a basa sistern ki," kasa cewa komae tayi sae hawayen dake bin kuncinta, Ma'aruf ya dan tabe baki yace "Ke ynxu kina son yayanku?" Girgixa kai tayi cike da takaici tana hawaye ssae tace "Wllh bana sonsa, bana sonsa kuma ni baxan yrda da aurensa ba, shi din a matsayin yayana na daukesa, idan ma aka tilasta ni wllh sae in gudu kawae" Ma'aruf yyi murmushi yace "Ae ba sae kin gudu ba Zainab, fitowa xakiyi kice baki sonsa ke ga wanda kike so," ta fashe da matsanancin kuka tace "Sau nawa zan gaya hkn, sun ki fahimta ta, Wllh bna son yayanmu ni baxan iya aurensa ba" lallashinta Ma'aruf ya shiga yi yace "Ba sae kinyi kuka ba Zainab, stop those tearz, just be bold idan aka tunkare ki da maganan Aliyu kice ke baki sonsa period" shiru tayi bata kuma cewa komae ba, hkn yasa yace "Dr Aliyu abokina ne ssae, na kut da kut kuwa, kuma tunda muke da shi a iya sanina bae taba soyayya ba, infact baya ma kula mata, sae a kanki ya fara Zainab, don't break his heart plss kada ki bari a canxa maki ra'ayin ki, idan kika samu Dr Aliyu a matsayin mijin ki ina assuring dinki kin gama samun komae a rayuwar ki, coz bbu abinda ya rasa tun daga ilimin addini har xuwa na xamani, ga dukiya nasa na kansa" Afeefah ta jinginar da kanta jikin kujeran da take tana hawaye ssae, bae kuma ce mata komae ba har suka iso gidansu Dr Sharif.

Eeshatullah
[6/29, 06:20] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad

73__74
Da daddare Afeefah na kwance Rahmah ta shigo tace Mami na kiranta, mikewa tayi jiki ba kwari ta fita daga dakin ta nufi na Mami, duk an hade mata kai a gidan bbu me kallonta, Anty Safiya ce ta fito daga dakin ko kallonta bata yi ba ta kara gaba, Afeefah ta shiga dakin a sanyaye ta rasa me tayi ma 'yan uwan nata suke jin haushinta, lkci daya ta kawar da damuwar hkn tuna duk don sbda Yayanmu suke ita kuma bata sonsa, dakin Mami ta shiga da sallama, Mami dake xaune tana jiranta ta amsa sallamar, durkusawa tayi tana kallonta tace "Mami ga ni" Mami ta nuna mata gefen gado alamar ta xauna, ta mike ta xauna tana kallon uwar tata, cikin sanyin murya Mami ta soma magana tana kallonta, "Zainab kin san me nake so da ke?" Girgixa kai Afeefah tayi gabanta na faduwa, Mami tayi kasa da murya tace "Duk cikin 'ya yana kina daya daga masu jin maganata wa enda ba sa min musu, kukan ki na gaira bbu dalili ne kadae matsala ta da ke Zainab, wnn karan ma baxan so ki ki jin maganata ba," Afeefah ta sunkuyar da kanta har lkcn gabanta na faduwa, Mami tace "biyayya xa ki min ki amince da auren yayanku!" da sauri Afeefah ta dago tana kallonta, lkci daya ta ji komae ya tsaya mata, Mami ta kwantar da murya tace "Ah da nace baxa ki aure Aliyu ba sbda dalilan da duk na xayyane maku, sae dae baxan kuma iya jurewa gnin halin da yake ciki a ynxu a kanki ba, Ban taba tunanin irin son da Aliyu yace yana maki ya kai hka ba, snn dari bisa dari na yrda da Aliyu, raino na ne Aliyu, nasan abinda xae aikata da wanda baxae aikata ba, ina kuma da yakinin ko bayan ranmu xae rike ki a bisa gskya da amana, Kinga Aliyu yasan halayen ki daga farko xuwa karshe bbu abinda bae sani ba game da ke, don hka xae jure duk wani abinda xa ki yi masa, ba kmr wancan da kike so ba don kukan ki kadae ma abun takaici ne ga mutum, ba wae nace malamin ku bae son ki ba, A'a sae dae Aliyu xae fi iya xama da ke, nasan da wa ennan abubuwan na hana Aliyu ke don kawae in tura ma ubansa takaicin irin abin da ya min, ynxun ma va wae na saduda bne sbda shi sae don D'a na, baxan iya yunkurin kuma hana ke ba Zainab, ina son Aliyu iyakar abinda xae ma warce ta haifesa yake min bae taba min musu a duk shawarar da na yanke kan sa ba, bbu banbanci tsakanin Aliyu da Adnaan da 'ya yan da na haifa a Cikina bn taba ware ku ba, iyakacin son da nake masu shi nake masu, don hka kiyi hkuri kar ki watsa min kasa a ido Zainab, shi kuma malamin naku idan ya ga da warce tayi masa a yayyinki sae a basa, nasan nice na bata komae tun farko don da na amince da ba a kai ga karban kayan su ba" Bbu abinda Afeefah take sae hawaye kanta a kasa, ta ji wani mugun tsanan Aliyu ya dirar mata, inaa ita kam baxa ta taba auren Aliyu ba, bata son shi baxa kuma ta taba son shi ba, a xuciyarta ta fadi hkn tana kuka a hnkli, jin Mami ta kira ta yasa ta dago kai tana kallon uwar tata, Mami ta kwantar da murya tace "Kiyi hkuri nasan ynda kike ji ynxu dota, sae dae xaki ji ddi xa kuma ki gane gata na maki nn gaba don Aliyu mijin aure ne" kai kawae ta gyada ma Mami, Mami tace "Tashi ki tafi, kar kuma ki ce da kowa komae, Allah maki albarka dota" mikewa tayi da kyar ta fita daga dakin tana ganin dishi dishi ta shiga dakinsu ta fada kan gado ta dinga rusa kukan tausayin kanta. Washegari ta tashi da matsanancin ciwon kai sae dae bata nuna ma kowa ba, bbu kuma wanda ya bi ta kanta a gidan sae Mami da ta tilasta ta ta tafi kitchen ta dauki break dinta shima bata wani yi na kirki ba ta dawo tayi wanka snn tayi kwanciyarta, misalin sha biyu tana kwance har lkcn Anty Safiya ta shigo dakin tana kallonta tace "Wato ke 'yar rainin hnkli baxa ki sakko ayi aiki da ke ba, tunda kika dawo sae dae kiyi xaman ki a daki a gama girki ki sakko ki diba ki koma sama koh, to baki isa ba yau, tashi ki fita kitchen ki kama aiki tun kan ranki ya bace" tana kai wa nn ta fice daga dakin, a hnkli Afeefah ta mike xaune hawaye na bin kuncinta ta sakko daga kan gadon ta dauki dankwalinta ta daura snn ta fita daga dakin jiki ba kwari, Adnaan ta tarar falo yana Danna laptop, duk suna gida sbda yayanmu, har Abba ma ya dawo amma bae nemeta ba, ta gaida Adnaan a sanyaye ya amsa a dakile ba tare da ya kalleta ba ta nufi kitchen jiki ba kwari, lunch ta tarar yayyin nata na girkawa a kitchen, gun wanke wanken dake kitchen din ta nufa ta shiga wanke abubuwan da aka b'ata. Anty baby ta gama hada abincin Aliyu kan faranti ta daura da ruwan lipton da beverages ta juya tana kallon Afeefah dake rabe jikin kofa bbu yabo bbu fallasa ta mika mata tace "Ki kai ma yayanmu" karban farantin tayi gabanta na faduwa ta fita daga kitchen din ta tafi sama, Anty Safiya tace "Don me kike bata ta kai" Anty baby tace "Ita kadae xata kai masa ya ci shi yasa" Anty Safiya bata kuma cewa komae ba ta shi gaba da xuba white rice din da suka girka a kula. a hnkli Afeefah ta tura kofar dakinsa tare da yin sallama can ciki ynda ba lallai mutum ya ji ba, kwance ta samesa idonsa lumshe, ta karasa da sauri xata ajiye farantin ta fice sae dae ko gama dire wa bata yi ba ya bude ido, kasa motsi tayi a gun ta ajiye farantin daga karshe ta mike da kyar da niyar ta fita daga dakin amma ta kasa, ba tare da ta kallesa ba fuska daure tace "Ina kwana" ita kanta jin gaisuwar tayi wani iri, jin bae amsa ba yasa ta dago kai a hnkli tana kallonsa, kallonta ta ga yana yi, tayi saurin sunnar da kai sae dae ta kasa fita still daga dakin, samun kanta tayi da karasawa kusa da gadon snn ta dago tana kallonsa ta sulale nn kasa a hnkli tace "Ina kwana yayanmu," kai ya gyada mata cikin sanyin murya yace "Lfya lau" ta na wasa da fingers dinta tace "Ina hada maka tea'n yayanmu?" Bata jira cewarsa ba ta dauki cup ta fara hada masa tean ynda tasan ya fi so yana kallonta, har ta gama ta shiga fiffita masa tea'n dai dai ynda ya fi so snn ta mike ta hau kan gadon ta cire masa bargon jikinsa tace "Gashi yayanmu" dauke idonsa yyi daga kanta ya sa hannu a hnkli ya karba tea'n, ya kai bakinsa tare da lumshe ido, tace "In xubo maka shinkafa?" Bude ido yyi ya girgixa mata kai snn ya ci gaba da shan tea'n, ko rabi bae yi ba ya cire cup din bakinsa ya mika mata xae sauka daga kan gadon, ta karba da sauri tace "Me ya faru yayanmu" ko bae gaya mata ba tasan amai ne, tayi saurin rikosa bayan ta ajiye cup din kasa tace "A'a kar kayi amai plss kila na jini ne don Allah kar kayi yayanmu" a rikice ta kare maganar hawaye cike idonta, ta rungumesa ta shiga buga masa baya a hnkli, bae kuma yunkurin sauka ba, ya lumshe ido yana shakar kamshinta me ddi, sun fi minti shiddah a hka har ya ji bae jin aman kuma, ta daga kai tana kallonsa ya bude ido ya sakar mata murmushi, janye jikinta tayi daga nasa da sauri, sae kuma ta hade rae, lakace hancinta yyi yana murmushin sa me kyau yace "Daina hade rae little sis kin ga daga yau baxa ki kuma gani na ba xan tafi...." Da sauri ta katse sa tace "Ina xa ka?" Kkrin sauka ya shiga yi daga kan gadon ta bi sa da kallo ya nufi gun kayansa yace "Tafiya me nisa xan yi," da sauri tace "Ina xa ka, kuma me yasa xa ka tafi yayanmu" da jin muryarta kasan bata ji ddin tafiyar da yace xae yi ba, kayansa ya shiga fiddo wa yace "Waje me nisa xan tafi, I want to be far away from yhu princess, ba kuma xan dawo ba sae ran da kika yi aure" sakkowa tayi daga kan gadon hawaye cike idonta tana girgixa masa kai tace "A'a kar ka tafi yayanmu xan yi miss din ka" ba tare da ya kalleta ba yace "Ae xa mu din ga waya" shiru tayi tana kallonsa har ya gama hada kayan snn ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta, duk tsayinta ko kafadunsa bata kai wa, sae ta daga Kai tana kallonsa hawaye cike idonta, goge mata hawayen yyi yace "Amma tsakanina dake ne wnn, its a secret kuma ki yi promise dina baxa ki gaya ma kowa ba, ynxu lgs xan ce masu xan tafi" kin cewa komae tayi yace "Shiga ki hada min ruwa ynxu" make kafada tayi tace "Ni sae ka gaya min in da xa ka" kmr xata fashe masa da kuka ta kare maganar, yace "Je hada min ki fito sae in gaya maki" a sanyaye ta nufi bayin, ya xauna gefen gadon yana rufe jakar kayansa, tana fitowa daga bayin ya mike ya cire jallabiyan jikinsa snn ya shiga bayin, kasa barin dakin tayi ta xauna gefen gado duk jikinta yyi sanyi, tana xaune ya fito ta nufesa da sauri tace "To gaya min inda xa ka" murmushi yyi yana goge gashin kansa da karamin towel ya nufi gaban mirror ya ja kujera ya xauna duk tana biye da shi, yana kallonta ta madubi yace "UK xan tafi" ta xaro ido tace "Kaje kayi me yayanmu" ya sauke idonsa daga kallonta ta madubin yace "In je in fara sabuwar rayuwa," ganin yanayinta yasa yyi 'yar dariya yace "Ke wasa nake maki fah, buh xan tafi UK xuwa gobe ina da visa ae akwae abinda zanje yi" ta durkushe kusa da shi tace "Toh yaushe xaka dawo yayanmu?" Dago kanta yyi, yace "Ran bikin ki" tayi saurin sunkuyar da kai, Jiddah ce ta shigo dakin tana kallonsu tace "Yayanmu Abba na kiran ka" ya daga kai yana kallonta yace "OK" juyawa tayi ta fita daga dakin tana mmkin me yasa in dae Zainab na kusa da shi sae ka rantse lafiyarsa lau, Afeefah ta turo baki tace "Ni dae ba ruwana ynxu ma xan je in gaya ma Mami ka hada kayanka" kamo hannunta yyi da sauri gnin xata fita yace "Promise fa kika ce min?" Hawaye cike idonta tace "I didn't promise yhu dat," ya hade rae yace "Shknn tafi ki fada" mikewa yyi ya dauki kayan da xae sa, tana kallonsa har ya gama sa kayan, ya feshe jikinsa da turare snn ya juyo ya karaso kusa da ita yana kallonta ya ja mata hanci yana murmushi yace "gyara min daki kafin in dawo Abba na kirana" ta make kafada ta fashe da kuka tace "Ni yayanmu kar kace xaka tafi plss, ka ga baka da lfya fa" dauke kansa yyi yace "Wani aiki xan yi a can na gaya maki, it won't take me long" bae jira cewarta ba ya fice daga dakin, dae dae lkcn da Mami ta fito daga nata dakin, tsaye tayi nn bakin kofar tana kallonsa, ya karasa inda take yana shafa kai yace "Wae Abba na kirana Mami" Mami tace "babansu Ma'aruf ne ya xo suna can falon baki" shiru yyi jin abinda Mami tace sae dae da ganinsa yanayinsa ya canza, Mami tace "Ka tafi mana" jiki a sanyaye ya juya ya nufi stairs ta bi sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login