Showing 78001 words to 81000 words out of 116554 words
da kallo. Bbu kowa falo hka ya sa ya nufi falon baki, ya samu Abba xaune da Dad din Ma'aruf da shi kansa Ma'aruf din, sae wani mutumi da bae sani ba, Karasowa cikin falon yyi ya nemi gefen Ma'aruf ya xauna snn ya gaida iyayen nasa, Dad ya amsa yana murmushi yace "Ka kyauta Ali, bbu ko sallama kayi tafiyar ka koh" dan murmushi kawae yyi a sanyaye, Dad ya kalli Ma'aruf yace "Har ynxu Dr Aliyu shiru?" Ma'aruf ya fiddo waya yace "Yace min yana hanya dad" dad yace "Allah ya iso da shi lfya" Aliyu na jin hka ya d'aga kai yana kallonsu cikin sarkewar murya yace "Dad ni fa na hakura" duk suka juya suna kallonsa, da mmki dad yace "Ka hakura da me?" Aliyu ya shafa kansa cikin sanyin murya yace "Zainab! Na hakura Dad a bata wanda take so Allah yasa hkn shine mafi alkhairi" da d'an murmushi ya kare maganar, duk jikinsu yyi sanyi aka rasa me cewa komae, ya mike ya fita daga falon, Abba yyi murmushi bae ce komae ba, text ne ya shigo wayar Ma'aruf ya bude ya ga Dr Sharif ne yyi masa text kmr hka "Frnd kar na bata maku lkci ayi ta jira na, ni kam na hakura da Zainab, Allah xae sa min hkurin rashinta, kaya kuma ba na bukatar komae na bar mata su kyauta Allah yasa hkn ne mafi alkhairi" Ma'aruf l ya kusa minti uku yana jujjuya wayar hannunsa daga bisanni ya mika ma dad.
Afeefah na xaune har lkcn dakin yayanmu ya shigp, ta mike da damuwa tace "Yayanmu ni dae don Allah kar ka tafi plss" ya xauna gefen gado yace "Sati biyu fa xan yi idan na tafi princess" xata yi magana Anty Safiya ta shigo dakin, hkn yasa ta mike sum sum ta fice. Washegari tashi suka yi gaba daya suka ga Aliyu baya gidan, bbu wanda ya kai Afeefah shiga tashin hnkli duk da tasan inda ya tafi, sae dae bata gaya ma kowa ba kmr ynda tayi masa hkuri, sae dae fa kowa na gidan ji yake kmr ya shaketa duk 'yan uwan nata haushinta suke, ita kanta Mami jikinta yyi sanyi ba kadan ba barin da mai gidan nata ya gaya mata ynda suka yi da Aliyu, gnin ynda ta tada hnkli yasa yace "Ae Aliyu ba yaro bne xae iya kula da kansa don hka kada ku sa ma kan ku damuwa, matar mutum kabarinsa dama" ssae ta ji nauyin mai gidan nata don ko kadan bae nuna yana jin haushinta ba duk da ita ce silar faruwan komae. Abba ne xaune falo da dad Washegari, Abba yace "Kasan wani abu Alhaji, ina son a bar maka kallon karamin mutum gun iyayen yaron nn, ka ga dae har yau ubansa bae ce maka uffan ba, ynxu abinda ya kamata kayi shine kawae ka cire kunya ka samu uban nasa kayi masa bayanin komae snn ka basa hkurin abinda ya faru, ka kuma kara masu da cewa an shawo kan komae su yanke duk ran da su ka ga ya dace a daura auren d'an su da Zainab" Dad yyi murmushi yace "Toh ae shima Aliyun baya Nigeria, ya fita tun ran da ya turo ma Ma'aruf wnn text din" Abba yace "Toh ae wnn ba matsala bace Alhaji, kawae a daura sae a gaya masa daga baya kaga bbu wanda xae kuma kallon karamin mutum tun da kar fa ka manta sun bada sadaki" Dad ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh shknn ngd kwarae da wnn shawarar, kuma na gamsu da ita, ynxu xan je in samu Mahaifin nasa" Har bedroom Abba ya samu Mami yyi mata bayanin ynda suka yi da Dad din Ma'aruf, Mami jikinta yyi sanyi ba kadan ba hawaye ya shiga sakko mata tace "Bnyi ma Aliyu adalci ba, da kun yi shawara da ni da baxa a je gun uban yaron can ba, don Aliyu ne yafi dacewa da Zainab ina kuma sane da hkn na danne sanin sbda kai" mikewa Abba yyi ya fice daga dakin don bae son abinda xae sa ya fara jin haushin matar tasa don ynxun ma danne xuciyarsa kawae yake, fushin da 'ya yanta ke mata ma kadae ya isa ynxu ba sae ya Dora da nasa ba.
[6/29, 06:23] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
By Ashmaad...
75.....
Dad bae wani sha wahalan shawo kan iyayen Dr Sharif ba da shi da wani abokinsa da suka je gun a tare, duk da wasu 'yan uwan mahaifinsa sun so nuna ae su tun da uban gayyan da kansa yace ya hakura to a bar xancen kawae Allah hada kowa da rabonsa, da ke Alhaji Shariff mutum ne me dattako da sanin ya kamata nn da nn yace magana bata kai ga hka ba, don tuni komae ya wuce gun su kawae dae kafin a yanke wani hukunci xae so sanin halin da dan uwan nata ke ciki ynxu, wato Aliyu, kuma yana fatan ba tursasa sa aka yi kan ya hakura da ita ba, Dad yyi murmushi yace "Ko daya Alhaji, da kansa ya furta ya hakura kuma wnn alama ce me nuna yarinyar ba matar sa bace," Alhaji Shariff yace "Toh shknn Allah datar da mu, sae dae fa Aliyun baya kasar" abokin Dad yace "Ae wnn ba matsala bace Alhaji don rashin jin ddin abin da ya faru ne ya sa shi fita, amma xa a iya daurawa ko bae nn, wnn ba damuwa bace in har kun amince" Alhaji Shariff yace "Shknn, se ku sa ranan da ku ka ga ya maku" Dad yace "Ko nn da sati ba matsala in kun amince" nn mahaifan Dr Sharif suka amince, dad yyi masu gdya ssae don ya ji ddin fahimtar sa da suka yi da wuri. Ranan Juma'ah aka daura auren Zainab Mahmoud da Dr Aliyu Shariff, daurin auren da ya samu halartar mutane da dama, sae dae bbu ango sae dae abokansa da suka cika wajen, tun da aka daura auren bbu abinda Afeefah take sae kuka ta kuma rasa dalilin kukan nata, Momy da wata kanwar Mami me sunanta kadae ne suke ta aikin rarrashin ta, don daga yayyinta har kanninta bbu wnda ya bi ta kanta, Anty Zainab tace "Ni kam Zainab baki da kawaye ne," don kawayen su jiddah kadae ne nn, Afeefah ta dago da kyar tace "Ni bni da su" Anty Zainab tace "Haba ya xa ki ce hka Zainab, yana da kyau ai ko da biyu ne ki ke kulawa ku saba ssae," wata sistern Abba tace "Uhm rabu da ita Anty Zainab wasu kawayen ma bala'i ne wllh don ko 'ya ta Farida na raba ta da kawaye, kawae dae ta rungumi dangin mijinta ta bi su sau da kafa su ne kawayenta ynxu, don a xamanin nn ynxu da wasu Kawayen gwara ba su" Anty Zainab tace "Hka ne kuma, Allah dae yasa mu dace" sosae Mami ta daure ta cire ma kanta damuwar Aliyu ta fuskanci mutanan da suka xo taya ta farin cikin aurar da 'yar ta, don yyi mugun tsaya mata a rae ga wani nauyin 'ya yanta da take ji kuma ynxu, tun ana saura kwana biyar bikin dama wata kawar Mami ke ta aikin gyara Zainab ciki da waje, tayi wani kyau me daukar hnkli fatar ta sae sheki yake, bbu wani abinda xa'ayi sae yinin biki don ango baya k'asar kmr ynda ake cewa, sae dae xa a hada duk occasions din da xa ayi da na su Ilham can Kaduna, Karfe biyar aka soma Shirye shiryen tafiya da amarya, aka shirya ta cikin wani dan karensun lace maroon me adon silver takalmin silver hka ma gyalenta da xa a iya kiransa da fari Anty Zainab ta sa mata sarkanta na gwal da dan kunne da awarwaro wanda momy ta siya mata nata gudunmawar, duk wanda ya kalleta sae ya kuma kallonta tsabar haduwa duk da lip da lip gloss kadae aka shafa mata a jajayen lebbenta sae kwalli da yar powder don ko gira ba a ja mata ba, fararen hannunta sun sha hyena baki da ja hka ma kafafunta, falon da Abba da dad suke aka nufa da ita suka yi mata nasiha ssae me kashe jiki sae dae wa enda suka rakota kadae ne suke jin abinda iyayen Maza ke cewa har ya kashe jikinsu ita kam tayi nisa tunanin Aliyu, in ka ga ynda take kuka sae ka rantse nasihar ce ke shigar ta, nn ko kukanta na daban take don bata ma san me suke cewa ba, gun kakar ta da ta haifi ubanta wato Mahaifiyar dad aka kai ta daga nn, ita ma tayi nata tana yi tana tsokanarta har ta gama snn aka tafi da ita gun Mami da momy. Gnin ynda Afeefah ke kuka yasa Momy ta ja ta gefe suka xauna tace "wae kukan me kike hka Zainab," Afeefah ta share hawayen da ya ki tsaya mata muryarta na rawa tace "Ni ban ga yayanmu ba" Momy ta dan yi shiru snn tace "Yayan ku xae xo, kuma har gidan ki xae je ya ganki, kiyi hkuri Kinji" daga hka ta dinga lallashinta tana bata baki har masu tafiya da ita suka shigo dakin, Wasu kawayen Mami biyu, sae 'yan uwan mahaifinta biyu da yayyinta Anty Safiya da Anty baby, da Anty Zainab su ne yan Kai ta. A cikin mota su Anty Safiya suka ajiye fushin da suke da ita suka shiga lallashin 'yar kanwar tasu don kuka take bakin rai. Shidda da 'yan mintuna suka iso gidan wato gidan Alhaji Sharif don nn xa a ajiye ta kafin ta tare can gidan Dr idan ya dawo, cikin sakin fuska da girmamawa aka tarbe su gidan, aka yi masu iso har dakin da aka gyara masu Anty Amina da bakinta har kunne ita ce kan gaba gun tarban sirkanta, ita dae Afeefah fuskarta na lullube cikin mayafi Anty Zainab ta xaunar da ita gefen gado a lafiyayyen dakin da aka ajiye ta, Ko kafin su Anty Safiya su idar da sllhr Magrib har an jera masu abinci kusan kala hudu akan lallausan carpet din da ke tsakar dakin, bayan sun idar duk suna xaxxaune Ummi da kawayenta biyu suka shigo dakin aka gaisa cike da mutunta juna snn suka fita, Anty baby ta juya tana kallon Afeefah da har lkcn kanta ke rufe tace "Baxa ki yi sllh ba" girgixa mata kai kawae tayi, Anty Zainab tace "Bata yi ae" daga hka Anty Safiya ta fara xuxxuba ma iyayensu abincin da suke ra'ayi snn ta juya tana kallon Afeefah tace "In xubo maki" girgixa mata kai kawae Afeefah tayi cikin mayafi daga hka ta fara xuba masu su ma. Bayan isha suka soma shirin tafiya gida, a nn ne Afeefah ta cire mayafin fuskarta xata fara masu hauka Hajiya binta kawar Mami tace "A'a ke kuma Zainab ba ga Sajida xata tsaya da ke ba, wnn ae shashanci ne" ta fadi hkn tana nuna 'yar kanwar Mami, hkn bae hana Afeefah kuka kmr ranta xae fita ba har dae shessheka, duk suka watse cike da tausayinta suka bar ta daga ita sae Sajida bayan sun kuma yi mata nasiha kan xamanta kewar aure. Sae bayan barin su gidan teemah ta shigo dakin da kawayenta don ganin amaryar yayan nata, Afeefah tayi saurin boye fuskarta har dae suka gama xamansu suka fita, Anty Amina ce ta shigo da abinci ta ajiye tana murmushi tace "Sannu Anty Amarya, ni ma baxa ki bude min fuskar ba" kin cewa komae Afeefah tayi bare ta sa ran xata ga fuskarta, Amina tayi dariya tace "Toh shknn tun da rowan fuskar kike mana, ga abinci nn ku ci" ta fadi hka tana kallon Sajida snn ta fita. Karfe goma saura kanwar Ummi ta shigo dakin tana kallonsu Afeefah tace "Kun dae ci abincin koh" Sajida tace "uhm mun ci" duk da ita kadae ta ci Afeefah ta ki ci, Matar tace "Toh gun kwanciyar yyi maku koh" Sajida tace "Yyi Mama" Matar tace "Toh shknn" snn ta juya ta fita. Sajida ba mai magana bace don hka tuni tayi kwanciyarta ta fara bacci, Afeefah kam bnda kukan da ita kanta bata san dalilinsa ba bbu abinda take, kafin sha biyu shigowar Anty Amina yyi biyar duk don ta tabbatar basa bukatar komae, Karfe sha biyu da 'yan mintuna ta shigo dakin da rigan bacci sabo ta karasa gun Afeefah tace "Ga nighty ki canxa kin ji" a hnkli Afeefah ta sa hannu ta karba, Anty Amina tace "Xaki yi wanka ne" girgixa mata kai kawae tayi, tace "Toh shiga bayi ki canxa" ba musu ta mike jiki ba kwari ta shiga bayan ta canxa ta fito yafe da mayafinta, Anty Amina ta rage masu Ac bayan Afeefah ta kwanta snn ta kashe wutan dakin tayi mata sae da safe ta fita. Washegari hka Afeefah taki sakin jiki gidan surkan nata gashi abinci ma sae Anty Amina ta tilasta ta take ci, Ummi kam mugun kunyarta take don duk ta shigo dakin rasa sukuni take, da yamma driver ya maida Sajida gida, Afeefah ta ci kukanta ta koshi duk da ba hira suke ba amma sae taji kewanta ssae, ranan teemah ce ta taya ta kwana, ita ma teemah ba mai magana bace tsakaninsu idan sun hada ido teemahn ta sakar mata murmushi wani lkcn ta mayar mata wani lkcn kuma ta sunkuyar da kai, da Anty Amina kadae ta dan sake a gidan sae d'an ta Fadil da take yawan raino. Washegari lahadi Afeefah na daki da yamma misalin biyar da Fadil na jikinta tana masa wasa, xuwa ynxu ta rage kukan da take ta dan sake amma fa da Anty Amina kadae, sae dae bata minti talatin Aliyu bae fado mata hka kawae ba, sanye take cikin atamfar England an mata riga da skirt da ya xauna dass jikinta, Anty Amina tayi mata dauri me kyau snn ta gyara mata fuska ta fesheta da turare, duk daga can gida aka kawo mata kayanta, ita ko damuwa da rashin ganin mijin nata bata wani yi ba, tana kwance ta daura Fadil kafar ta tana masa lilo yana ta kyalkyala dariya aka bude kofar dakin, duk a xaton ta Anty Amina ce don ta fi kowa shigowa dakin, jin shiru yasa ta juya tana kallon kofar ta gansa tsaye yana kallonta, wani mugun faduwa gabanta yyi ta ajiye Fadil da sauri ta mike xaune tana waige waigen inda xa ta ga mayafinta, cikin rashin kuzari ya karaso dakin ya durkushe gabanta yana kallonta
Eeshatullah
Hmmm
[6/29, 06:24] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya Mace kyautar Allah👩🏻🌸
By Ashmaad
76...
Sunkuyar da kai tayi da sauri, cikin sanyayyan muryarsa yace "Zainab" kin amsawa tayi, hkn yasa ya mike ya xauna gefenta yana kallon kyakkyawar fuskarta ya dago kanta a hnkli, tayi saurin rufe idonta, murmushi yyi gnin ynda kirjinta ke bugawa ya sake ta ya mike ya fita daga dakin, tana jin fitarsa ta fada kan gado tana maida ajiyar xuciya, lkci daya hawaye shiga xiraro mata. Karfe shiddah Anty Amina ta shigo dakin tana kallonta tace "Anty Amarya ki tashi ki shirya xa ku tafi gida da Dr" Afeefah taji gabanta ya fadi ssae ta fashe da kuka tana kallon Anty Amina tace "Don Allah ni a bar ni a nn Anty" Anty Amina tayi dariya ta xauna gefenta ta kamo hannunta tace "Gidan mijin ki xa ki Anty, ke da gidan nn kuma sae in kun xo gaida Ummi" gnin ynda take kuka yasa Amina ta rungumeta tana rarrashinta, wanka tasa ta fara yi kafin ta shirya ta fiddo mata da wani material me kyau da aka mata dinkin doguwar riga tace ta sa, bayan ta bata turarurruka kala kala ta shafa masu ddin kamshi, make up vry light tayi mata snn ta shafa mata jan bakin da tasan xae fi dacewa da jan lebbenta, ta sharce mata dogon bakin gashinta da ya sha mai sae walkiya yake tayi mata dough da shi, jewelries ta sa mata snn ta dauki mayafinta ja, ratsin kayan jikinta ta lullube ta da shi, ta fiddo mata flat shoe me kyau shi ma ja ta bata rasa, ta fesheta da turarruka masu tsada. Duk ynda Afeefah ta so danne kukan ta kar Amina ta gani kasawa ta yi har Amina ta lura sae dae bata hanata ba illah tausayinta da taji ssae don ta san hka yake ga ko wace 'ya mace. Hannunta ta kama fuskarta a rufe suka nufi dakin Ummi, Ummi na xaune kan gado shi kuma yana xaune daga kasa, Afeefah ta ki barin jikin Anty Amina sae shisshige mata take, Ummi tayi murmushi shi kam sae kallonsu yake, Anty Amina ta xauna kasa tare sa Afeefah tace "Ga ta Ummi" Ummi ta kalli Dr Sharif tace "Toh Aliyu ga amanar Zainab, ka riketa amana kmr ynda iyayenta suka damka maka ita sbda sun aminta da kai Haiydar, kai ne gatan Zainab a ynxu, in kuma ka kasa rike amana kai da Allah, Allah kuma ya taya ka riko, ke kuma Zainab ki bi mijin ki sau da kafa don aljannar ki na tafi kafarsa kin sani, Allah yyi maku albarka ya baku xaman lfya da xaman Hkuri, ya axurta ku da xuri'a dayyaba," tana kai wa nn tace "sae ku tafi ku sallami Abban ku" Dr Sharif da ya kasa dago kai yace "In'sha Allah Ummi" Afeefah kam bnda kuka jikin Anty Amina bbu abinda take, Anty Amina ta daga ta bayan Dr Sharif ya Mike ya sallami umminsa ya fita daga dakin, shi ma Abban yyi masu tasa nasihar daga nn Anty Amina da teemah suka rakasu har mota ta bude mata gidan gaba ta shiga da kyar tana kuka ta rufe kofar cike da tausayinta, shi ma da ganinsa kasan a sanyaye yake, ya tada motar Amina ta daga masu hannu tana murmushi tace "Toh yaya sae mun xo" murmushin kawae ya mayar ma kannin nasa ya ja motar suka fita daga gidan. Ana kiraye kirayen Magrib ya