Showing 63001 words to 66000 words out of 116554 words

Chapter 22 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1275

tayi tace "Sir baxae min xafi ba?" "Idan kika rufe ido" yyi assure dinta, a hnkli ta mika masa right hand dinta ya karba, a tare suka dago kai suna hada ido duk suka yi saurin sunkuyar da kai, ganin ya dauki dan alluran ta saka kuka tana yarfe dayan hannun, wani yar kara ta saki ta fixge hannunta jin shigar alluran vein dinta, lkci daya ta saki kuka ta sakko da kafafuwanta kasa daga kan gadon tace "Wllh sir akwae xafi ni dae" hade rae yyi yace "Yhu are joking" kamo hannunta ya kuma yace "Ki fa tsaya Zainab ko mu tafi asibiti, yhu see m almost missin jam'i" runtse ido tayi jin alluran har cikin ranta ta dafa sa ta saki kuka, da sauri yace "Take ur hands off me" ba shiri ta cire hannun, har ya gama sa mata drip din bata daina kukan da take ba, ya mike yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Yhu are vry funny" bata ce komae ba sae shirin kwanciya da ta shiga yi, yace "Wait saura allura" xaro ido tayi tace "Ba ga shi ka yi min ba a hannu" ya girgixa kai ya dauko alluran ya nuna mata, tuni ta kuma marairaicewa tace "Sir don Allah ka xuba cikin drip din ae ana yin hka" murmushi yyi yace "Wnn ba a xuba wa drip Zainab" hawaye ya xubo idonta tace "To a ina xaka min alluran," da sauri tace "A hannu?" Rasa me xae ce mata Dr Sharif yyi, ya ajiye alluran ya juya yace "Bari in tafi masallaci" Bin sa da kallo tayi har ya fita, snn ta bi drip din hannunta da kallo, yana fita Momy da Su ilham suka shigo dakin, Suna mata ya jiki, duk da ita bata ji ko wani sauki ba a hnkli tace "Da sauki" Anty Jamila ta shigo dakin da tsire a plate da hollandia drink ta ajiye mata tace "Tashi ki ci Zainab," To kawae Afeefah tace, Momy dake xaune gefenta tace "Wnn me xae mata, in xubo maki shinkafa Zainab?" Afeefah ta girgixa kai tace "Na sha tea fa Momy" suna xaxxaune dakin dad yyi Sallama ya shigo dakin Dr Sharif na biye da shi a baya da saleem, Momy ta mike su Aneesah ma hka suka fita daga dakin, Dad yace "Sannu Ummi, ya jikin" sunkuyar da kai Afeefah tai tace "Da sauki dady" gaishesa tayi snn tayi masa sannu da dawowa, ya tambayeta ya hanya da su Abbanta duk tace "Suna lfya Abba" Godiya dad yyi ma Dr Sharif snn ya fita daga dakin, Saleem ya kalli tulin tsiren dake gefenta yace "tab, duk ke xa ki cinye wnn Zainab" hararansa tayi tace "Toh xa ka ci ne?" Dariya yyi yace "A'a ni yau bnyi kuka da ihu nace kai na na ciwo ba, na masu yin hkn ne" xaro ido tai kmr xata yi kuka tana kallon Dr Sharif tace "Sir ka gansa ko?" Juyawa saleem yyi ya fita yana dariya, Murmushi Dr Sharif yyi yace "yi hkuri shima xae xo kansa wataran, ya ciwon kan?" Tace "Sir yana min fa har ynxu" ya kalli ruwan yace "To baki bari an maki allura ba" xaro ido tayi tace "Kai fa kace xaka tafi mosque" Karasowa kusa da ita yyi ya dauki alluran ba tare da ya kalleta ba yace "Kin shirya" kmr xata fashe da kuka tace "Sir a ina xa ka min? A hannu" ya girgixa mata kai yace "Ba a yi a hannu" tace "To sae ina?" Dago kansa yyi yana kallonta, hkn yasa tayi saurin sunkuyar da kai, sun fi minti uku bbu Wanda yace komae, daga karshe tace "Sir" dago kai yyi ya kalleta, ta kuma sunkuyar da kai a hnkli tace "to ka min" yace "Kin shirya ynxu" gyada masa kai kawae tayi snn tace "Amma a lap fa xa ka min dae" yyi murmushi yace "OK" a dan kunyace ta daga dogon gown din jikinta har cinya ba tare da ta kallesa ba a hnkli tace "ka min sir" yana sauke idonsa kan cinyanta xumbur ta ga ya mike ya nufi drip din dake sakale jikin curtain ya juye alluran har biyu ciki, ba tare da ya kalleta ba yace "ki ci naman ki, ina xuwa" bae jira cewarta ba ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Misalin Karfe tara saura Dr Sharif na xaune kasa falon Dad, dad ya shigo falon yace "Ashe kana ta jira na Aliyu" Dr Sharif yyi murmushi bae ce komae ba, dad ya xauna kan kujera ya rage volume din News din da ake a tv snn ya maida hnklinsa kan Dr Sharif yace "Dad dinka ne ya kirani 2 dayz bck a kan maganar ka da Zainab wae kace xaka tafi course, wani course ne wnn da xae hana ka aure Ali," Dr Sharif ya sunkuyar da kansa bae ce komae ba, Dad ya dan yi murmushi ya ci gaba yace "Nasan yhu are nt sayin the truth, irin iyayenta can kano sun nuna maka karatu take shi ne xaka bullo min da hka koh? To mahaifiyarta da kanta ta xo nn shekaranjiya, kuma mun yanke magana da gwaggwo na, ko ba kai ba ina da 'ya yan abokai da yawa da xan iya hada Zainab da, kuma willingly xa su amince duk da ba neman kai nake da ita ba" Dr Sharif ya dago kai a sanyaye yana kallon Dad sae dae bae ce komai ba, da kyar daga karshe yace "Ba hka bne Dad ban son tauye mata karatun ta ne tun da ta nuna tana so" Dad yace "dama aure na hana karatu? To ynxu dae ga shi mahaifiyarta ta turo min ita in yi duk ynda naga ya dace, kuma in ka ga Zainab ta bar gidan nn to gidan mijinta xa ta don in less then three wks xan hada ta da yayyinta duk in aurar da su" Dr Sharif yace "Toh shknn Abba, kayi hkuri xan turo idan Allah ya yrda."

Karfe goma saura Dr Sharif ya shiga dakin da Afeefah take ya sameta kwance idonta a lumshe, karasawa yyi kusa da gadon ya tsura mata ido, a hnkli ta bude idon suna hada ido ta mike xaune da sauri ya sakar mata murmushi yace "Ya kan ya daina" murya can kasa tace "Ya daina" yace "Ma'sha Allah, me sa ba ki ci namanki ba" girgixa masa kai tayi tace "Ni bana son yaji, kuma momy ta kawo min shinkafa na ci" xaunawa yyi yace "Toh ae shi xae gyara maki bakin ki" dauko naman dake rufe da takarda yyi ya dauki toothpick ya dauki daya yace "Bude bakin toh" kmr xata yi kuka tace "sir yaji" hararanta yyi, hkn yasa ta bude bakin a hnkli ya sa mata naman yana kallon cikin idonta, a kan idon Anty Jamila da shigowarta dakin knn, dariya tayi ssae tace "Lallai Dr, kai da kanka, amma fa da wani ya gaya min baxan yarda ba," murmushi yyi ya dauke kai, Afeefah kuma ta boye fuskarta cikin pillow cike da jin kunya.
A gidan Dr Sharif ya kwana ranan Sbda yasan sae can dare drip din xae kare, throughout nyt din operating din laptop kawae yake a dakin Ma'aruf, dake yace Aneesah ta bar wayarta kusa da ita xe kira, Karfe daya da kusan rabi ya kirata, bugu uku ta daga, yace "Srry Neesah na tashe ki koh, ruwan ya kare?" Aneesah tace "lah ba komae Dr" mikewa xaune tayi tana kallon ruwan tace "Saura dan kadan Dr" yace "xae kai minti nawa?" Tace "toh ka shigo mana ka duba Dr" yace "toh gani xuwa" mikewa tayi ta dauki hijab dinta ta sa snn ta lullube Afeefah da ke ta baccinta, da sallama ya shigo dakin yace "Am srry Aneesah na tashe ki" dariya tayi tace "Kai Dr bbu komai" duba ruwan yyi yace "in less than 15 mins xae kare anjima xan dawo" tace "toh shknn" snn ya fita daga dakin, Aneesah ce ta kirasa ganin ruwan ya kare, yana shigowa dakin ya nufi kan gadon yana kallon Afeefah, lkci daya Afeefah ta farka jin an kama hannunta, ta mike xaune tana kallonsa, ya sakar mata murmushi snn ya shiga cire drip din, yana gamawa yace "ki kwanta" ba musu ta koma ta kwanta, yyi ma Aneesah sae da safe snn ya fita dakin.

Washegari Dr Sharif bae boye ma Afeefah yanda suka yi da dad ba, ya kuma yi mmkin ynda bata nuna ta damu ba, hkn yasa yace "Dad yyi maki magana ne?" Girgixa masa kai tayi alamar A'a, ya dan yi shiru snn a hnkli yace "ynxu kin ban go ahead mu yi ynda dad yace?" Sunkuyar da kanta kawae tayi bata ce komae ba, murya can kasa yace "Zainab!" Tace "Uhm" yace "kin yi shiru" a hnkli tace "Naji sir" yace "kin amince?" A kunyace "Ta gyada masa kai," dawowa kusa da ita yyi ya kamo hannunta yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Thanks love" Murmushin ita ma tayi a kunyace ta janye hannunta, yace "No more headache ynxu koh" ta gyada masa kai tace "ya daina ynxu" wara ido tayi tace "Sir ina abu me ddin da kace xaka kawo min?" Shima ya wara manyan idonsa yace "Ae na kawo maki" tace "toh ina yake" murmushinsa me kyau yyi mata yana kallonta ya kashe mata ido ya nuna mata pink lips dinsa yace "I had wanted giving yhu a kiss idan na xo jiya, ko in baki ynxu" xaro ido tayi ta Mike da sauri ta bar falon da gudu har tana tuntube, ya bi ta da kallo yana dariya.

Bayan kwana biyu magabatan Dr Sharif suka kawo sadakin Zainab dubu dari biyar da akwatunan lefe saiti Shidda sau biyu, abun ba a magana sae mutum ya gani, don duk kayan akwatunan bbu na bnxa, murna wajen Momy kam ba a magana duk da 'ya yanta nasu ma ba laifi amma ko kadan basu sami shigen na Zainab ba, duk ynda Anty Amina ta so ganin Zainab don har da ita aka kawo lefen kin fitowa tayi daga bayi har suka bar gidan bayan Azahar, bbu abinda Afeefah take tun lkcn sae kuka ta rasa dalilin kukan nata, don ita dae tasan tana son Dr Aliyu Sharif ba kadan ba, sae dae tun daga lkcn da ya kirata ya sanar da ita xuwan iyayen nasa ta kasa samun kwanciyar hknli. Washegari da ya kasance Saturday tana kwance ita kadae daki aka bude kofar dakin, Wanda ta gani tsaye bakin kofar yasa ta saurin mikewa a tsorace.

Eeshatullah Goni
[5/22, 07:58] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸


By Ashmaad

64....
Kasa tashi Afeefah tayi daga xaunen da tayi kan gado tsabar rudewa ga wani rawa da jikinta yake, gnin ya nufota yasa lkci daya karfi ya xo mata ta mike da gudu xata shiga bayi yyi saurin rikota, kuka ssae ta saki jikinta na rawa ta shiga cewa na shiga uku, sun fi minti uku a tsaye amma bata bari sun hada ido ba, bbu abinda take sae kuka har lkcn jikinta na bari, da kyar muryarta na rawa tace "Don Allah kayi hkuri ka kyaleni" kallonta kawae Aliyu yake a sanyaye, kan gado ya nufa da ita suka xauna gefen gadon har lkcn idonsa na kanta, nn ma sun fi minti biyar a xaune a hka, daga karshe ta dago kanta a hnkli tana kallonsa, kallonta shima yake suna hada ido gabanta yyi mugun faduwa barin ynda ta ga ya rame ba kadan ba, ya daura hannunsa me dumi kan shoulders dinta yana girgixa mata kai lkci daya idonsa ya kada ssae, mgna yake son yi amma ya kasa, hkn yasa ya rungumeta ssae ya runtse idonsa, kuka ta shiga yi a hnkli ta kasa janye jikinta daga nasa, saukan hawayensa ta ji a bayanta, ta koma baya da sauri ta daga kai tana kallonsa, gnin hawayen idonsa ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "Yayanmu" kamo hannunta yyi yana girgixa mata kai da kyar yace "Kar ki guje ni Zainab, don't plss, da son ki nake rayuwa, son ki a jinina ne, I can't afford loosin yhu, be mine plss ko baxa muyi xaman aure ba na amince just to have yhu by my side I just can't...." kasa ci gaba yyi, ta fada jikinsa tana kuka a sanyaye, ya kankameta muryarsa na rawa yana ci gaba da yi mata magiya, da karfi tace "No! Kai yayana ne ka daina cewa kana sona plss yayanmu, it sound awful ni fa kanwar ka ce, ka manta ni ce little sis dinka, kmr ynda baxa ka iya ce ma su Anty jiddah kana sonsu ba nima kar ka iya ce min hka plss, knn ba daya muke da su ba ko yayanmu," kuka ne ya ci karfinta, shima hawayen yake, duk jikinsa yyi sanyi, janye jikinta tayi daga nasa ta Mike da gudu ta shige bayi tana kuka me tsuma xuciya, Aliyu ya rike kansa da ke juya masa, ya kusa minti biyar xaune daga dakin daga karshe ya Mike da kyar yana ganin jiri ya bar dakin. Ya kusa minti goma a corridor ya kasa sauka downstairs tsabar jirin da yake gani, da kyar daga karshe ya saita kansa ya shiga sakkowa stairs din a hnkli kmr me kirga steps dinsa, har lkcn Momy na falon da wasu kawayenta biyu suna ta shawaran abubuwan da xa suyi biki na gabatowa, Jamila kadae ce a gidan tana girki, su ilham sun fita kai ma kawayensu IV, da kyar ya karaso falon ya xauna, Momy ta bi sa da kallo tace "Har ka fito Ali, sae da ka tasheta koh?" Murmushi ya kirkira ya girgixa mata kai yace "A'a idon ta biyu ma" Momy tace "ta tashi knn, bari Jamila ta fito ta kai ka daki ka ga kayan lefen nata da aka kawo jiya" Aliyu ya daga kai yana kallon Momy kan yace komae Momy tace "Ae Alhmdllh Zainab tayi goshi Ali, nayi xaton yau Zuwairan xata xo ma, don jiya da safe aka kawo, akwatuna goma da kit biyu Ma'sha Allah, sadaki kuma dubu dari biyar ina fatan ka sani" kallonta kawae Aliyu yake lkci daya yana processing abubuwan da take gaya masa, sae da ya daukesa lkci kafin ya gama fahimtar ta, wani irin bugun da xuciyarsa bae taba yi masa ba yaji, lkci daya ya kuma jin kmr an soka masa mashi, dafe kirjin yyi da hannu biyu tsabar axaba da yake masa, Momy ta mike da sauri tana tambayarsa lfya, lkci daya Yaji wani abu me dumi ya taho masa ya shiga kwararowa nn kasa, ba momy ba har bakin nata dake xaune falon a rude suka mike suna salati gnin Aman jini yake, tun kan ya kai kasa momy ta rikesa a rikice tana kwala ma driver da masu gadi kira, Jamila ta fito da sauri jin ana salati da kiran driver ta shigo falon, ihu ta fasa a tsorace ita ma tana kallonsa, lkci daya tayi waje da gudu a rikice, a bakin gate ta ci karo da Saleem jikinta na rawa ta gaya masa abinda ke faruwa da gudu ya nufi cikin gidan ta bi bayansa tana kuka, Afeefah kam na bayi har lkcn duk da ta ji fitarsa amma ta kasa fitowa sae kuka take, jin ihun da Jamila tayi yasa ta fitowa da sauri daga bayin ta sakko downstairs, abinda ta gani yasa ta fasa wani ihu da karfi ta karaso falon da gudu jikinta na rawa dae dae lkcn da su Saleem suka shigo falon a rude, bata kai ga karasawa inda yake ba ta ji kafafuwanta sun kasa daukanta lkci daya wani duhu ya mameta kawae ta sulale nn inda take ta fadi kasa da karfi, kawayen Momy ne suka yi kanta da sauri hnkli tashe.


Eeshatullah Goni
[5/22, 07:58] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar👩🏻🌸

By Ashmaad

65.....
A hnkli Afeefah ta bude idonta ta sauke kan Ma'aruf dake xaune kan kujera kusa da gadon da take kwance, mikewa yyi lkci daya ya sakar mata murmushi ya kama hannunta yace "Kin tashi Zainab" kkrin mikewa xaune ta shiga yi hkn yasa ya taimaka mata ta xauna, ta shiga bin ward din da kallo kmr me son tuno abu, xumbur ta shiga kkrin sauka daga kan gadon ya riketa da sauri yace "Ina xa ki?" Kuka ta saki a rikice tace "Ya Ma'aruf ina yayanmu?" Ya kwantar da murya cikin lallashi yace "yana lfya wllh, Kinga bacci yake ki bari...." Kuka ta kuma fashewa da tace "A'a ni wllh ka kai ni wajensa in gansa don Allah don annabi" ya hade rae yace "baki ji me nace maki bne, shima ae yana nn asibitin, kuma nace maki bacci yake" xata yi magana aka bude kofar dakin Saleem ne ya shigo da sallama Dr Sharif na biye da shi a baya, hadiye sauran maganar tayi ta sunkuyar da kanta sae dae har lkcn hawaye na bin kuncinta, Saleem ya karaso yana murmushi yace "Kin tashi Zainab?" Kai kawae ta gyada masa ba tare da ta kallesa ba, ya karaso bakin gadon ya daura hannunsa a goshinta yace "hope bbu inda ke maki ciwo koh?" Gyada masa kai tayi nn ma, a hnkli ta dago kai tana kallon Dr Sharif dake tsaye daga gefen Ma'aruf, murmushi ta sakar mata cikin sanyi murya yace "Sannu, ya jikin" sunkuyar da kanta kawae tayi, a hnkli tace "Da sauki" ya karaso bakin gadon ya dan rage gudun drip din snn ya juya ya fita. Duk irin ynda Zainab ke ta damun Ma'aruf da Momy a cire mata drip din hannunta a kai ta taga yayanmu kin bari a cire mata suka yi wae sae ya kare, hkn yasa ta dinga hawaye, sae bayan maghrib drip din hannunta ya kare, ana cire mata kuwa ta sakko daga kan gadon wani jiri ya debe ta, Ma'aruf yyi saurin rikota, Momy tace "To ina xaki ji karfin jikin ki kin ki cin abinci, jamila hado mata wani tean" Afeefah ta girgixa kai da sauri tace "Allah momy na sha dayawa daxu don Allah a kai ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login