Showing 51001 words to 54000 words out of 116554 words

Chapter 18 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1265

Mami tace "Maxa ki je ki shirya kayan ki" Mikewa Afeefah tayi ta fita daga dakin tana tunanin to ina xa su bayan ta ce xata bi yayanmu Abuja, hawaye ne ya cika idonta ta shiga dakinsu ta shiga hada kayanta a jaka, bata yi wani breakfast din kirki ba, shi kansa Aliyun bae yi ba, Karfe bakwae da kusan rabi suka kama hanyar Kaduna, Sae da suka yi nisa ssae snn Mami na kallon Aliyu ta madubi tace "Aliyu tare xa ku wuce Abuja da Zainab bana son mu je Kaduna tare da ita, amma yaushe xa ka komo kano?" Shiru Aliyu ya dan yi snn yace "xan kusa sati biyu ina jin Mami" Mami tace "To ku tafi idan yaso nn da sati ko motar haya ce sae ka sa ta ta dawo" to kawae Aliyu yace ma Mami, Afeefah kam wani farin ciki ne ya lullubeta, har U-rimi Aliyu ya ajiye Mami bakin gate din gidansu Ma'aruf, rana ta farko knn tunda Mami ta haifi Afeefah ta ji faduwar gaban barinta da Aliyu abinda bae taba samun ta ba, don har lgs tana barin ya tafi da Afeefah, Aliyu yace "Mun tafi Mami" murmushi kawae ta iya yi masa, Afeefah kuma ta daga mata hannu, kallonta kawae Mami ke yi har ya ja motar, ta bi motar da kallo har ya bar layin snn ta ja kafa da kyar ta shiga gidan yayan late mijinta.
Surutu kawae Afeefah ta dinga yi ma Ya Aliyu a mota shi dae bae tanka ta ba lkci lkci kuma yyi murmushi har suka shigo Abuja wajajen Karfe sha biyu na rana.

Eeshatullah Goni

πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya mace kyautar AllahπŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story


By Ashmaad

51___52
Cikin kuka Afeefah tace "Ni ma ban san sunan anguwan ba" Dr Sharif ya dan yi shiru snn yace "To wae kukan me kike ma, ba ke kika ce xaki bi sa ba" gyada masa kai tayi bata ce komae ba, bayan kusan second goma yace "Shknn sae anjima" kuka ta saki tace "Sir don Allah kar ka tafi ka bar ni pls" murmushin da bae yi niya ba yyi cikin sanyin murya yace "to ya kike son in maki Zainab" ta girgixa kai tace "Ni dae kar ka kashe wayar don Allah" yace "To naji, sae ki ban lbri coz I don't have anything to say" a hnkli tace "To wani irin lbrin kke so" yace "me ddi" ta wara ido tace "Sir ni fa bn ma iya lbri ba, ka gaya min wani iri kke so dae" shiru ya dan yi snn a hnkli yace "Tell me meyasa kike so na" Xaro ido tayi da sauri tace "Sir lbri fa kace in baka" yace "um wnn ma ae lbri ne" rufe fuska tayi da kujera tayi yar dariya tace "Sirrr" yyi murmushi yace "Ma!" Jin tayi shiru yasa yace "ina jin ki fa" cike da jin kunya tace "Tunani nake yi sir" yace "To gama" bayan kusan second sha biyar a hnkli murya can kasa tace "Sbda kana da kyau ssae" murmushi yyi yace "Haba!" ta dago kanta da sauri tace "Allah sir, kana da kyau ba kadan ba don duk kafi kanninka kyau, shi sa 'yan mata ke son ka a sch, snn bbu ruwanka yhu are so kind nd understandin, kuma ka iya lecturing ba kadan ba, yhu are vry educated Sir, snn ga shi kae Medical Dr ne, kuma kana da taimako ba kadan ba" tun da ta fara xancenta Dr Sharif yyi shiru yana sauraronta, jin shirun yyi yawa yasa a hnkli tace "Sirr" murmushi yyi shima a hnkli yace "Ma!" Rufe fuskarta tayi da sauri, yace "Uhm shknn abinda ya sa kike so na?" Gyada masa kai tayi tace "um" yyi murmushi yace "to ngd" murmushin ita ma tayi snn tace "to ni baka gaya min ba" yace "meye bn gaya maki ba?" Cike da jin kunya tace "Abinda na gama gaya maka" yace "uhm wae dalilin da yasa nake son ki?" Gyada masa kai tayi a hnkli, yyi murmushi ssae, kmr Mae rada yace "Sbda kukan ki da shagwaban ki yasa nake son ki Zainab," bata fuska tayi tace "ni tun yaushe na daina kuka Sir" dariya yyi yace "ynxu fa kika gama min kukan Zainab, kuma ni baxan so ki koya ma yarana wnn kukan da shagwaba ba" shiru tayi bata ce komae ba, amma kiris ya rage ta fashe da kuka, dariya yyi don sarae yasan fushi tayi, a hnkli yace "fararen idanuwan ki masu rauni da saurin xubda hawaye suka ja hnkli na gare ki Zee nah, snn dimple din nn naki guda daya me kyau ma is nt left behind, ga wnn dogon hancin ki kmr na balarabiya, da dan karamin bakin nn naki da kike tabewa idan xa ki fara kuka" Afeefah ta fashe da kukan karya tace "Wayyo sirr ni xagi na kawae kke yi" dariya yyi sosae yace "Da gske fa nake bby, da wnn tsayin naki kmr daren sllh kina tafe kmr iska xae hankade ki one side" bata fuska tayi tace "Bye bye" da sauri yace "ohh tsaya bby, wasa nake maki wllh, but get this dear _Yhu are so pretty Zainab_ Allah ya maki baiwa da dama da baxan iya lissafo maki ba Zainab, I just love yhu Zee nahh, ina son ki da yawa, kullum addu'ata Allah ya mallaka min ke a matsayin matata uwar 'ya 'yana" rufe fuskarta tayi da sauri a hnkli tace "Thnk yhu sir" yace "ni baxa ki ce kina so na ba Zainab" a hnkli tace "I love yhu more" murmushi yyi yace "To yaushe xa mu hadu, ko yayanki baxae bari ba?" Ta dan yi shiru snn tace "idan na gaya masa xae bar ni, ae shi ba ruwansa" gate taji an bude ta wara ido tace "Sir kaga ya dawo ynxu" Dr Sharif yace "OK, shknn sae gobe knn" gyada masa kai tayi tace "Uhm Allah ya kai mu" a sanyaye yace "ki kula da kan ki Kinji Zainab" tace "To sir ngdd" kai kawae ya iya gyada mata ya katse wayar, ta kashe fitilar da ke kunne har lkcn da sauri kan ya Aliyu ya shigo, duhu ya gauraye falon, ta rakube jikin kujera inda baxae iya ganinta ba ta hade kai da gwiwa. Bude kofar falon ya Aliyu yyi gnin duhu falon ya ciro wayarsa ya kunna fitila ya shiga bin ko ina da kallo, kiranta ya shiga yi, ta ki dago kai bare ta amsa, ya karaso cikin falon yana kalle kallen inda xae gnta, ya ajiye ledan hannunsa da jakar kayanta da ya dauko a mota snn ya kunna Invertern falon nn da nn haske ya gauraye ko ina, ya ganta xaune jikin kujerar har lkcn kanta na hade da gwiwa, Karasowa yyi ya tsugunna gabanta ya dago kanta yana murmushi, kuka ta fashe masa da sae dae ba hawaye tana buge hannunsa, dariya yyi yana rike da fuskarta yace "Kiyi hkuri little sis, bn san xan dde hka ba wllh" juya masa baya tayi tace "Ni gobe xan wuce gida yayanmu na fasa hutun" murmushi yyi ya dago ta yace "Haba princess kiyi hkuri bn san xan dde bane" hawaye ne ya gangaro mata tace "ba sae da nace xan bi ka ba kaki kulani" yace "Gun abokan aiki na na tafi shi sa bn je da ke ba kiyi hkuri plss baxan kara ba" share mata hawayen ya shiga yi snn ya dago ta ya shigo tsakiyar falon da ita ya xaunar da ita shima ya xauna, ledan da ya ajiye ya jawo ya bude, ya fiddo drink din ciki da gasassun kaji, da kansa ya je kitchen ya dauko plates da cup, ya dibar mata nata ya ajiye mata gabanta, murmushi tayi tace "tnxx yayanmu" snn ta fara ci, shima ya diba nasa, ita ta fara tura sauran kajin gabanta tace "Yayanmu na koshi" yace "je ki sa a fridge," mikewa tayi ta nufi fridge ta ajiye ta dawo falon yace "baxa ki sha fura ba" ta girgixa masa kai tace "Na koshi" yace "to kinyi sllh?" Ta gyada masa kai, yace "Go nd brush ur teeth idan xa ki yi wanka kiyi sae ki kwanta ni ma bacci xan je in yi ynxu, kin gyara dakin da xa ki kwanta ko?" tace "Ehh na gyara" yace "Gud ki tafi da kayanki ciki" sae da safe tayi masa ta nufi dakin da xa ta kwanta rike da wayarta da jakar kayanta, Bakinta ta fara wankewa snn tayi wanka ta fito ta bude jakar ta fiddo rigar baccinta ta sa bayan ta dan yi shafe shafenta, ta kwanta knn wayarta ya fara vibrate ta duba ta ga Mami ce ke kiranta, dagawa tayi tare da yin sallama, Mami ta amsa tace "kin kwanta ne?" Afeefah tace "Ehh Mami" Mami tace "Ina Aliyun?" Afeefah tace "Yana falo" Mami tace "OK, kina jina?" Afeefah tace "Ehh ina ji" Mami tace "meyasa da aka tambayeki kina son malamin nn naku kika ce kina so?" Shiru Afeefah tayi bata ce komae ba, Mami tace "wato ke aure kike so ynxu ko Zainab?" A sanyaye Afeefah tace "wllh bnce ina son aure ba Mami Allah" Mami tace "Aa hka ne mana, da bakya so da baxa ki ce masu kina sonsa ba," Shiru Afeefah tayi lkci daya hawaye ya cika idonta, Mami tace "Shknn tunda hka kike so, sae a aurar da ke yayyinki ba su yi auren ba, don baxan kuma ja ma kai na bakin jinin da nayi ba a da, duk ynda suka yi da ke iyayen ki ne" kuka ta fashe da tace "Mami ni fa karatu nake," Mami tace "kinsan da karatun kika amsa masu kina sonsa sha sha sha kawae," Mami na kai wa nn ta katse wayar, Mami na katse wayar dama Aliyu ta kira don masa bayanin ynda suka yi da mutan Kaduna, Kuka Afeefah ta shiga yi a hnkli, jin wayarta na vibrate ta dauka don a tunaninta Mami ce, Dr Sharif ta gani da kmr baxata daga ba sae kuma ta daga a sanyaye don bata iya kin daga kiransa, cikin sanyin murya yace "ba kiyi bacci ba" "um" kawae tace masa, yace "kina ina ynxu?" A hnkli tace "bedroom" yace "kinyi kuka knn koh? Me aka maki?" Kukan ta sakar masa tace "Mami ce tace wae aure xa a min" shiru Dr Sharif yyi snn a hnkli yace "ke kuma ba kya so koh?" Ta gyada masa kai kawae, yace "Wa xa a aura maki?" Cikin muryar kuka tace "wae kai" shiru ya kuma yi snn cikin sanyin murya yace "kuma baki so na ko?" Girgixa masa kai tayi tace "A'a karatu nake son inyi ne Sir" yace "ki kwantar da hnklin ki Zainab, dama mgnr da nake son muyi knn jiya a sch kika wuce gida, Kinga ni ma is just of recent na ji abinda dad din Ma'aruf ke shiryawa don ba da ni yyi magana ba da Abba na yyi, but ki kwantar da hnklin ki, I will tel dem am nt ready ynxu don ko nace masu kina karatu a bari ki kare nasan ba lallai su yarda ba, sae in ce masu xan tafi course waje, hkn yyi ae koh?" Murmushi tayi a hnklk tace "Uhm ngd" yace "yauwa Zainab but make a promise to me plss" a hnkli tace "wani promise sirr?" A sanyaye yace "Dat no matter wat baxa ki taba ki na ba, promise me dat yhu will b my wife Zainab" shiru ta dan yi lkci daya tayi murmushi cikin sanyin murya tace 'I promise Sirr" yace "kar ki manta Zainab, alkawari kaya ne fa" a sanyaye tace "Na sani sir" murmushi yyi yace "To ngdd Zainab Allah baki ikon rike alkawari," a sanyaye tace "Ameen sir," yace "Gud nyt, kiyi addu'a kafin ki kwanta, ki kuma kula da kanki Zainab, ki kuma ji tsoron Allah a duk inda kika kasance" ta gyada masa kai cikin sanyin murya tace "Toh sir ngdd" katse wayar yyi, ta mike ta nufi socket xata yi plugging wayarta Aliyu ya shigo dakin.

Eeshatullah Goni 😘😘

πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya mace kyautar AllahπŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

54.....
Juyawa Afeefah tayi tana kallonsa har ya karaso cikin dakin shi ma yana kallonta, mikewa tayi daga inda take durkushe tace "baka kwanta ba yayanmu" gefen gado ya xauna yace "Ehh! Mami ta kira ki?" Kmr xata yi kuka ta xauna gefensa tace "Yayanmu wae tace aure xa a min inji Dadyn Kaduna" kallonta kawae Aliyu yake ita ma hka, hkn yasa ta kirasa a hnkli, yyi saurin sauke idonsa kasa daga kallon da yake mata cikin kakkausar murya yace "Kina son auren kuma koh?" Xaro ido tayi tace "Yayanmu ni da nake karatu kuma" mikewa yyi jiki ba tare da yace mata komae ba jiki ba kwari ya fice daga dakin ta bi sa da kallo. Ta fi minti goma xaune duk jikinta yyi sanyi daga karshe ta gaji ta kwanta jiki a mace ta rufa da bargo, ba a dau lkci ba bacci ya dauketa. Washegari kiran Dr Sharif ne ya farkar da Afeefah, ta na idar da sllh ta shiga gyara dakin da ta kwanta snn ta shiga bayi tayi wanka ta wanke baki ta fito, Abayar ta baki ta sa bayan ta shafa Mae da turare ta sa eye pencil snn ta kanannade dan mayafin abayar a kanta ta fito falo, share falon tayi ta goge ko ina snn ta koma daki ta kwanta ganin har lkcn bakwae bae yi ba, bacci ne ya dauketa bata farka ba sae kusan Karfe tara da wani abu, mikewa tayi daga kan gadon ta fita daga dakin ta nufi dakin ya Aliyu tana Mamakin dalilin da ya hanasa tashinta da asuba tayi sllh don its vry unusual of him, da sallama ta shiga dakin ta samesa kwance har lkcn cikin bargo, karasawa dakin tayi ta xauna gefen gadon tana kallonsa tace "Yayanmu baka tashi ba" a hnkli ya bude idonsa ya sauke kanta, murya can kasa yace "Na tashi" cire bargon jikinsa tayi hannunta ya sauka kan nasa hannun taji xafi, da damuwa tace "yayanmu jikin ka da xafi baka da lfya ne" mikewa xaune yyi da kyar ya rike kansa yace "xaxxabi nake Zainab" kmr xata yi kuka tace "ciwon kai?" Ya girgixa mata kai tayi shiru tana kallonsa kmr me shirin kuka, makullin motarsa dake gaban mirror ya nuna mata yace "Ki je ki bude mota xa ki ga wasu food stuffs na siyo jiya ki shigo da su sae ki hada breakfst," ba musu ta mike ta nufi gaban madubin ta dauki makullin motar ta fita, cikin dan kankanin lkci ta kwashe kayan abincin ta nufi cikin gida da su ta dire a kitchen, snn ta bude ledan Irish ta dibi Wanda xae ishesu ta shiga ferewa, cikin yan mintunan da baxa su wuce ashirin ba ta soya dankalin da kwae sae plantain, snn ta dafa ruwan Lipton ta hadasu a faranti gaba daya da kayan beverages snn ta daura bread ta nufi dakinsa, kwance ta kuma samunsa, ta ajiye trayn hannunta da damuwa ta karasa gadon tace "yayanmu ka tashi kayi breakfast sae ka sha maganin xaxxabi" to kawae yace mata, ganin bae da niyar mikewa yasa ta kuma cewa "plss ka tashi mana" da kyar ya mike xaune, ta xauna kasan dakin tana kallonsa da damuwa, bayi ya mike ya nufa ya wanke bakinsa ya fito ya xauna gefenta yana kallonta, jawo cup tayi ta shiga hada masa tean tana gamawa ta ajiye masa gabansa snn ta dibar masa dankalin da kwae ta ajiye masa tace "kaci yayanmu" fork din ya dauka ya shiga cin dankalin a hnkli sae dae Sam bae da appetite, da kyar ta lallabasa tana yi masa kmr xata yi kuka har ta samu ya dan ci dankalin snn ya dauki ruwan tea ya shiga sha, shi ma kadan ya iya sha ganin ta takura sa sae ya shanye yasa yace "Amae xanyi Zainab" hkn yasa ta kyalesa ya mike ya koma kan gado ya kwanta, sae a snn ita ma ta karya snn ta fita da farantin, ko da ta dawo dakin a lumshe ta tarda idonsa hkn yasa ta fita ta nufi dakin da take, wayarta ta dauka ta ga mis cals din Mami da Dr, Mami ta soma kira bayan sun gaisa ta shiga tambayarta inda ta shiga, Afeefah tace "ina hada breakfast ne a kitchen Mami, yayanmu bae da lfya ma" Mami tace "me ya samesa?" Kmr xata yi kuka tace "Wae xaxxabi yake, ko abinci fa baya ci, kuma jikinsa xafi" Mami tace "Subhanallahi, bari in kirasa" da sauri Afeefah tace "A'a Mami bacci yake ynxu ki bari anjima" Mami tace "toh shknn xan kira anjima" tana kai wa nn ta katse wayar, Dr Sharif Afeefah ta shiga kira yana gama ringing ya kirata, ta daga ta gaishesa a sanyaye murya can kasa, yace "Dnt tell me yhu just finish crying" girgixa masa kai tayi a hnkli tace "A'a bnyi kuka ba sir" yace "to me ya faru?" Shiru ta danyi snn kmr me rada tace "yayanmu ne bae da lfya?" Yace "Subhanallah, wat's wrong with him?" kmr xata yi kuka tace "nima bn sani ba amma yace min xaxxabi yake" yace "Eyya Allah ya sauwake, if its OK da sae na xo na duba sa," dan xaro ido tayi snn tace "ban san ko xae ce to ba" Dr Sharif ya dan yi shiru snn yace "OK ki tambayesa, ko kuma ku tafi clinic" tace "to Sir, bari in tambayesa" tana ajiye wayar ta nufi dakin ya Aliyu, wnn karan gani tayi ya lullube har kansa da bargo, xaunawa tayi ta yaye bargon tana kallonsa tace "yayanmu," bude ido yyi yana kallonta, hannu tasa a goshinsa taji xafi ba kadan ba, kmr xata fashe da kuka tace "yayanmu mu tafi asibiti mana jikin ka da xafi" girgixa mata kai kawae yyi, hkn yasa ta fashe masa da kuka tace "Ni xan kira Mami in ce mata baka son mu tafi asibiti," cikin sanyin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login