Showing 111001 words to 114000 words out of 116554 words

Chapter 38 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1290

xae kalli Mami ba, dakinsa ya shiga ya same Afeefahr kwance, ya karasa da sauri ya xauna gefenta ya dago ta yace "Ya jikin princess?" Shiru yyi jin har lkcn jikinta da xafi ga idonta da ya kumbura, cike da tausayinta yace "jikin ne har ynxu princess? Kin yi breakfast kuwa?" Bata basa amsa ba sae hawaye, duk ya rikice ya rungumeta yace "ina ke maki ciwo, Mami bata baki magani bane?" Girgixa masa kai kawae tayi, yyi shiru yana kallonta, mikewa yyi ya fita daga dakin, ba a dau lkci ba ya dawo da cup din tea, ya dago ta yace "Tashi ki sha sae mu tafi asibiti kin ji" karba tayi ta shiga sha a hnkli tana jikinsa, tana gamawa ya daga ta ya dauki makullin motarsa, da kyar yaga take tafiya, tausayinta ya rufesa a sanyaye yace "Sorry Princess, kin shiga ruwan xafi kuwa" bata ce komae ba ya rike hannunta suka fita daga dakin, dai dai nn Mami ta fito daga bangaren Abba, daga ita har shi ji suka yi kmr su nutse barin shi, ko kallonsu bata yi ba ta shiga bedroom dinta. Dae dae stairs din karshe Zainab ta ji muryar Dr Aliyu Shariff falon yana amsa gaisuwan yayyinta cikin sanyayyan muryarsa, shi ma shigowarsa knn ta dalilin kiransa da Abba yyi yana nemansa daxu, ji tayi kmr ta koma sama da gudu sae dae tuni suka yi ido hudu da shi, ta sunkuyar da kai da sauri tana kkrin buya bayan ya Aliyu sbda ynda take tafiya.


🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad

104.....
Har suka karasa cikin falon tana bayan ya Aliyu, Aliyu ya basa hannu murmushi dauke fuskarsa suka yi musabiha suka gaisa, sae dae cike yake da Mamakin ganinsa, though bae nuna ba, sae a snn Afeefah ta gaishesa kanta a k'asa, Dr Sharif ya amsa murmushi dauke fuskarsa yana kallonta, d'aga hka ya maida hankalinsa kan Tv, barin falon Aliyu yyi tana biye da shi a baya sae dae sauri take ta shige gabansa sbda yanayin tafiyar ta, kmr ance ta juya ta ga idon Dr Sharif kanta, suna hada ido yyi murmushi ya dauke kansa, ji tayi kmr ta nutse sbda kunya, Allah dae ya sa ba ganewa yyi ba ta fadi a xuciyarta, don tasan shi kmr maye yake. Tun da Abba ya sauko falo Dr Aliyu ya k'asa kallonsa, tuni su Jiddah suka bar falon, har lkcn bae d'ago ba ya gaida Abba da ladabi, Abba ya amsa da fara'a murmushi dauke fuskarsa yace "Ya aiki Ali" yace "Alhmdllh Abba" Abba yace "Toh Madallah" shiru ne ya biyo baya kafin Abba yace "Dama na kira ka ne in kuma baka hkuri Ali, hausawa sun ce wanda aka cuta ake ba ma hkuri, lallai kayi abinda ba ko wani namiji bne xae iya a wnn xamanin da muke ciki, na yaba da hankalin ka da juriyar ka da uwa uba hkurin ka Ali, Allah yyi maka albarka, kuma duk wanda ya rufa ma wani asiri Allah xae rufa masa nasa in'sha Allah, Allah ya jibanci al'amuran ka, ka nuna kai namiji kwarae" Dr Sharif bae dago ba har lkcn cikin sanyin murya yace "Ameen, ngd Abba" Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Amma ka gaya me xuciyarka ke raya maka game da Fadila?" Da sauri Dr Sharif ya d'ago yana kallonsa, sae kuma ya mayar da kansa k'asa bae ce komae ba har sae da Abba yace "Ka yi shiru Ali" Dr Sharif ya dan yi murmushi yace "Xumunci muke Abba" Abba ma yyi murmushi yace "ka je kayi shawara da magabatan ka, duk da nasan abu ne me wuya su kuma yarje maka neman aure gidan nn, amma xan so hkn don ina son hada xuri'a da kai, ni me baka Fadila ba ko sisin ka ne Ali, a ra'ayina sae 'ya ya na mata sun kare karatu nake aurar da su, sae dae in har ka amince da auren fadila ni me baka ita ne ko nn da sati daya ne ka bukaci hkn, duk da kasancewarta auta gidan nn warce ko secondary bata kare ba, don ynxu sauran mata shekara daya ta gama. Duk sbda yabawa da hankalin ka da nayi nake son baka ita" Dr Sharif ya k'asa cewa komae har lkcn kansa na kasa, bayan kusan second ashirin ya d'ago a hnkli yace "Shknn Abba ngd, xan yi shawara da iyayena" Abba yace "Toh shknn, Allah maka albarka, kiran knn dama" Dr Sharif ya kuma yi masa gdya, snn ya mike yyi masa sallama ya fita falon duk jikinsa yyi sanyi, bakin gate ya hadu da Fadila ita da Rahma sun dawo kasuwa kasancewar ranan asabar ce ba boko, sanye take da hijab har kasa navy blue da ya haska farar fatan ta ba kadan ba, ba karamin kama suke da Afeefah ba har tafiyar sae dae ta fi Afeefah haske ssae, kallonta kawae yake hkn yasa ta ji kunya ba kadan ba ta sunkuyar da kai tun kan ya karaso inda suke, a kunyace tana fidgeting fingers dinta tace "Ina yini uncle" murmushi yyi yace "Lfya lau" Rahmah ma ta gaishesa ya amsa mata da murmushi kafin ya maida dubansa ga fadila, juyawa tayi da sauri ta nufi cikin gida Rahmah tayi masa sallama ta bi bayanta, sae ta basa dariya ya juya ya fita daga gidan.
Yana rike da hannunta suka shiga office din likita, ya taimaka mata ta xauna, likitar tayi murmushi tana kallonsu tace "Nyc couple," don da ganinsu kasan yes couples ne, Aliyu yyi murmushi suka gaisa kafin yyi mata bayanin Matsalar Afeefah, magunguna ta rubuta masu bayan ta duba ta, snn tace "Sae ta dinga shiga ruwan xafi a kai kai, kafin kwana biyu xata warware in'sha Allah, a kuma daga mata kafa ko na sati daya ne, Allah bada xaman lfya" ta karasa maganar tana murmushi, dariya Aliyu yyi yana kallon Zainab da ta sunne kai tana turo baki ita kunya, yyi ma likitar godiya ya mike ya dago Afeefah ganin ta ki tashi, likitar tayi dariya tace "Allah ya sauwake amarya" kin cewa komae tayi kanta a kasa ya kama hannunta suka fita. Sae da suka bar harabar asibitin ba tare da ta kallesa ba tace "Ina xa mu yayanmu?" Ya kamo hannunta yana tuki da hannu daya yace "Xamu je in ba Abba hkuri Princess, fushi yake da ni" bata fuska tayi cikin muryar shagwaba tace "Ni mu tafi gida yayanmu, wani tym sae mu je" murmushi yyi, yyi pecking hannunta yace "Shknn love" ta kauda kai ita kunya. Yana gama parkin a parkin lot din gidansa ya bude mota ya fito ya xaga ta inda take ya bude mata, ya dauke ta ya rungumeta kmr baby ya nufi cikin gida da ita, bae tsaya ko ina da ita ba sae bedroom dinsa ya direta kan gado, ta mike xaune tana turo baki, jawota jikinsa yyi ya lumshe ido yana murmushi yace "Ina sonki Zainab," lumshe ido ita ma tayi ya daura kanta kan kirjinsa, cikin sanyin murya yace "Am confuse Zainab, I met yhu a virgin, me hkn ke nufi princess, yhu were married for six month, are yhu tryn to say bbu abinda ya shiga tsakanin ki da tsohon mijin ki" jin ta ki cewa komae ya sa ya d'ago kanta, ya ga hawaye ne fuskarta, ta kuma shigewa jikinsa muryarta na rawa tace "Ni ban san kai nake so ba yayanmu" shiru yyi yana sauraranta, a hnkli ta ci gaba hawaye na sakko mata tace "Sbda kai naki barin Dr Aliyu yyi min komae, amma duk da hka yake xaune da ni kuma bae canxa min fuska, har lkcn da na fara kiran ka da daddare, a wnn dalilin ne ya sake ni ba wae don ina gudunsa ba," kallonta kawae Aliyu yake jikinsa yyi sanyi sosae, tana kuka tace "Ka taya ni rokon gafararsa yayanmu, nasan na cucesa ba kadan ba, gashi Mami ma fushi take da ni ynxu, kuma tace min sae alhakin sa ya kama ni, shi yasa bana son mu koma gida, ka rokon min Dr Aliyu Sharif ya yafe min don Allah yayanmu, ban san ba shi nake so ba sae da na yrda da aurensa, ni baxan iya rashin ka ba shiyasa na gane kai ne abokin rayuwata ba Dr ba" ya runtse ido ya rungumeta tsam yana jin maganganunta kmr a mafarki, da kyar ya iya bude baki cikin sanyin murya yace "Ina son ki Zainab, ina son ki" sun fi minti sha biyar a hka kafin ya dago kanta yana kallonta yace "bari ki shiga ruwan xafi Kinga baki iya tafiya har ynxu" boye fuskarta tayi da sauri ya kwantar da ita ya mike ya shiga bathroom, ba a dau lkci ba ya fito ya karasa inda take ya dago ta xaune ya cire mata hijab din jikinta, yana kkrin cire mata kayan jikinta ta sa masa kukan shagwaba tace "Ni ka bari xan yi da kai na" ya wara ido yace "Sbda me?" A hnkli tace "Ni ina jin kunya" ya kai bakinsa saitin kunnenta murya can kasa yace "Kin manta abinda ya faru jiya da daddare ne baby, ae kunya ta kare kuma," boye fuskarta tayi da sauri jikinsa tace "Wayyo yayanmu" yyi dariya ya shiga cire mata doguwar rigar jikinta, tana rokonsa ya bari bae kulata ba har sae da ya cire gaba daya, kare kirjinta ta shiga yi tana kukan shagwaba don bata sa komae ba, ya dauke abarsa ya nufi bathroom da ita yace "ashe yau princess dita xata ga karshen jin kunya"

Dr Sharif bae samu courage din gaya ma iyayensa ynda suka yi da Abba ba don yasan da wuya su goyi bayansa, ko sanin xuwansa gidan ma ba su yi, shi dae baxae ce yana son Fadila ba sae dae tana burgesa sbda nutsuwarta da wayonta ga respect, ga kokari both ilimin addini da boko, sae dae bae jin yana da ra'ayi na aurenta, yasan sun gano abinda Afeefah tayi shi sa Abba ya kirasa ya kuma basa hkuri. Bayan sati biyu da xuwansa kiran Abba mahaifinsa Alhaji Shariff ya kira sa falonsa, ya dde xaune yana jiran jin abinda mahaifin nasa xae ce, kafin Alhaji Sharif na kallonsa yace "Ya ku ka yi da Alhaji Mahmoud, ina nufin sirkin ka a da, wato mahaifin tsohuwar matar ka" Shiru Dr yyi yana kallon dad din nasa, Alhaji Shariff yace "Kayi shiru Aliyu" shafa kansa yyi a sanyaye yace "Dama kirana yyi ya kuma ban hkuri kan abinda ya faru, yake kuma nuna xae ban kanwarta in yi shawara da ku in ji ta bakin ku, nasan kuma da wuya ku ban goyon baya shi sa na bar xancen kawae" Alhaji Shariff ya sauke ajiyar xuciya yace "Kai kana da ra'ayin koma masu knn, kuma it doesn't make sense in anyway ka saki yaya ka koma wa kanwa, sam ko kadan abun ba tsari, bae ma kamata ba, shi ma Alhaji Mahmoud din da yyi wani naxari kafin ya bullo da hkn" shiru Dr yyi don ya gano inda maganar mahaifin nasa ya dosa, kawae dae yana kame kame ne bae son fitowa fili, a hnkli yace "Ae Abba bbu abinda ya taba shiga tsakani na da ita na auratayya" Shiru dad dinsa yyi yana kallonsa fuskarsa dauke da mamaki, Dr Sharif ya ci gaba a sanyaye yace "Shine ma yasa ya bullo da hkn" Mahaifin nasa bae kuma cewa komae ba, bayan kusan minti biyar yace "Toh Allah shi kyauta, amma baka ji ddin ta ba sae kanwarta?" Dr Sharif ya sunkuyar da kai yace "yayansu take so, shi yasa ta ke min hka, ni kuma na sauwake mata don raba ta da xunuban da take kwasar ma kanta a kullum, kuma ga shi ynxu ta auri wanda take son" Alhaji Sharif yace "toh ban baka shawarar kuma koma masu ba Ali, ita kanwar Ca tayi tana son ka da har ake neman lika maka ita" a sanyaye yace "Yarinya ce Abba, baxata wuce 16 ba, koh secondary bata gama ba" Alhaji Sharif yace "Toh Allah bada sa'a, tashi ka je, sae dae duk abinda xa ka kuma fuskanta bbu ruwana, ban kuma yarje maka da saki ba, tun da kai ka ga xaka iya." Jikin Dr Sharif yyi sanyi ssae, sae dae bae kuma cewa komae ba.

🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad

105....
A week ltr

Tsaye tayi bakin stairs sanye da rigar baccinta da bae wuce gwiwa ba tana kallonsa, mopping yake bae ma lura da ita ba, mika tayi ta karasa saukowa, sae a snn ya a ganta, ya langwabar da kai yana kallonta, ta turo baki tace "Me sa baka tashe ni in taya ka ba" karasawa yyi kusa da ita ya jawo ta jikinsa a hnkli yace "Yau fa xa mu je gida baby" xaro ido tayi ta bata fuska tace "Me xa mu yi a can" yace "Xamu je gaida su Mami" shiru tayi bata ce komae ba sae kuma a hnkli tace "Yayanmu ni tsoro nake ji" ya hade rae yace "nace ni ba yayanki bne ynxu ki canxa min suna" dariya tayi tace "Toh xan dinga ce maka Brother!" Matse ta yyi jikinsa, tayi 'yar kara tace "Wayyo babyna" sae kuma ta boye fuska jikinsa da sauri, yyi dariya ya shiga kissing wuyanta tana shigewa jikinsa romantically. Karfe sha daya saura ta fito daga wanka daure da towel yana xaune yana danna laptop, ta nufi gaban mirrorn sa ta xauna cikin shagwaba tana kallonsa ta madubi tace "yayanmu" kallonta yyi kafin ya dauke kai ya ci gaba da abinda yake, ta kuma kiransa bae tanka ba, bata fuska tayi tace "Toh babyna" sae a snn ya kalleta yana murmushi yace "Ya aka yi" tace "Kaga lotion dina da spray suna can dakin fah," mikewa yyi ya nufi kofa yace "Toh bari in dauko maki" ba a dau lkci ba ya dawo rike da lotions har biyu da sprays kala kala, ya dire mata su gaban mirror ga su ki xaba, ta shagwabe tace "Yayan..." Da sauri ta rufe baki sae kuma tace "Babynah saura kaya" ya langwabar da kai yace "Toh ae ban san wanda xaki sa ba" tace "Kaje ka kakkawo min sae in xaba" yace "Toh!" Ya juya ya fita sae ga shi ya dawo da kaya saiti hudu, biyu atamfa daya lace, daya shadda, kmr xata yi kuka ta karbi kayan tana duba su kafin tace "kasan me? xa ka ga wani lace gold colour da milk ka kawo min," juyawa yyi ya fita ya kuma dawowa da lace din ta karba yace "Takalmi da mayafi fa?" Tace "Toh kawo min har da kayan make up" tana shafe shafenta ya dawo ya ajiye mata su, kafin yace "Toh kawo in shafa maki man" ta hararesa tace "Uhm nasan wayo xaka min bana so xan yi da kaina" ya marairaice mata yace "Allah shafa maki kawae xan yi, Kinga wanka nima fa nake son inyi" daukota yyi ya xaunar gefen gado ya dauki lotion din ya shiga shafa mata a hnkli jikinta yana kallonta, ae shafa lotion sae da ya daukesu fiye da awa daya, don wata duniyar daban ya lula da ita, daga karshe daukar abarsa yyi suka nufi bayi ganin ynda take masa kukan shagwaba ita wllh bata son irin hka, wanketa ya kuma yi tass, ya bar ta tayi daya wankan kafin ta bar masa bayin da gudu yana kkrin kamota don bata yrda yyi wanka gabanta, ko kafin ya fito har ta shirya tana durkushe tana busar da gashinta da hand dryer, yyi dariya yace "Ae da ki jira in kuma shafa maki lotion din" turo baki tayi ta kashe socket din don ta gama ta mike, ita ta fito masa da shadda sky blue da hularsa tace "Wnn xae ma kyau yayanmu" ta fito masa da takalmi da agogo ma ta ajiye masa gefen gado, yace "Toh baxa ki shirya ni ba baby" ta wara ido ta ce "ba gashi na fito maka da kayan ba" yace "Amma ae kin aike ni na je maki daxu, shine ni baxa ki min abinda nake so ba koh" marairaice masa tayi kafin ta tabe baki tace "Toh naji" ta dauki lotion da stool din gaban mirror ta xauna gabansa ta karbi towel din da yake goge gashin kansa da shi ta shiga goge masa sauran ruwan kafarsa da ma jikinsa gaba daya, nan ta shiga shafa masa lotion din tana kallon kwantattcen gashin jikinsa, kallonta kawae yake yana murmushi, ta turo baki ta ci gaba da abinda take har ta gama ta dauki farar singlet dinsa ta mika masa, ya bata fuska yace "Toh baxa ki sa min ba" ita ma ta hade rae xata yi magana ya fixgota jikinsa, ae da kyar ta kwace kanta ta fice da gudu daga dakin. Ba su suka bar gidan ba sae bayan Azahar, sae a snn mood din Afeefah ya canxa wae ita tsoron Mami take, ya dinga kwantar mata da hnkli har suka iso gida, yana rike da hannunta kmr xata yi kuka suka shiga falon, Adnaan kadae ne xaune falon, yyi murmushi ganinsu ya mike ya gaida yayan nasa, Aliyu ya amsa masa yana murmushi shi ma yace "Kwana biyu aiki ya boye ka," yace "Wllh kuwa, ynxu ma anjima xan koma tun jiya nake nn, har da nake shirin xuwa gaida ka can gida ashe kuna hanya" Aliyu yace "Sae mu koma tare, ya baka gaida Zainab ba" kallon Afeefah yyi ya tabe baki yace "Lallai yaya ni xan gaisheta, tana wani kallo na da ido kmr owl" ya karashe maganar yana hararanta, ta bata fuska tace "Toh ba jira nake in gaisheka ba" Aliyu yyi dariya yace "Sae ma nace ka dinga ce mata Anty Zainab xaka gane" dariya ssae Adnaan yyi, Afeefah ta turo baki tace "Ina kwana ya Adnaan" yace "Ban kwana ba" Aliyu yyi dariya yace "Kada Allah yasa ka kwanan mana" daga hka ya ja hannunta suka nufi sama ta juya tana masa gwalo. Dakin Mami suka nufa, sae dae gabanta faduwa yake ssae, shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login