Showing 57001 words to 60000 words out of 116554 words

Chapter 20 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1278

da Asuban nn, ina xae je nemota? dakinta ya koma da sauri don dubawa ko wayarta na nn, ya ga bbu, dakinsa ya koma yana ganin jiri ya dauki tasa wayar ya shiga kiran layinta, jin yana ringing yasa ya runtse ido yana addu'ar Allah sa ta dauka, Afeefah dake xaune har lkcn cikin mota tana hawayen da bata san dalilinsa ba ta daga wayarta da sauri jin yana vibrate ganin me kiranta yasa tayi saurin mayarwa cinyarta gabanta na faduwa, har sae da ya katse snn tayi saurin kashe wayar gaba daya hawaye na xarya a kuncinta, Aliyu kam rike kansa yyi ganin bata dauka ba, da kyar yyi namijin kkri ya kuma kiranta don duk jikinsa rawa yake, jin wayar a kashe gaba daya ya sa shi fadawa kan gadon hawaye na gangaro masa, to ina Zainab xa ta batun bbu Wanda ta sani a Abuja, tunawa da yyi so tari idan abu ya hadasu idan ta xo gunsa a lgs sae ta hada kayanta ko baya nn tace xata tafi tasha ta koma gida, tuna hkn da yyi yasa ya mike da sauri, to amma wani tashar xae san ta tafi, ya fi minti goma ya rasa abun yi daga karshe ya yanke shawarar tafiya airport kawae ya yanki ticket ya koma Kano. Da kyar ya iya yin wanka ya wanke baki snn ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya dauki wayoyinsa da Atm ya fita, kulle gaba daya gidan yyi, ya taka har xuwa main road da kafa, snn ya tari taxi da xae kai sa Nnamdi Azikiwe international Airport, sae kusan Karfe takwas ya isa airport cikin rashin sa'a bae samu flight na farko ba sae na biyu kuma sae xuwa sha daya xae tashi, rike kansa yyi bayan ya samu wuri ya xauna xuciyarsa na bugawa, har xae iya jira kuwa, da xae iya driving da ya koma gida ya dauki motarsa kawae ya kama hanyar Kano, amma Sam hnklinsa baya tare da shi bashi da nutsuwa don hka bare iya driving din ba. Afeefah kam tun shidda da rabi motarsu ya tashi, tun kuma lkcn take karanto addu'o'i a xuciyarta ga shi har lkcn hawayenta ya ki tsayawa, da ta tuna abinda ya faru jiya da daddare sae gabanta ya fadi ssae, sae take ga abun kmr a mafarki. Karfe sha daya da rabi jirgi ya tashi bayan long waitin dat seems like dat of yrs to Aliyu. Karfe sha daya da kusan minti arba'in Afeefah suka isa Kano don motarsu ba karamin gudu yyi ba, jiki a mace ta fito bakin titi bbu ko sisi a hannunta sae wayarta ga wani jiri da take gani, duk tayi laushi ga gajiyar hanya, a dai daita ta tsayar da, da kyar ta iya ce masa "Jan bulo xaka kai ni" bata jira cewarsa ba ta shige, yace "ba nn nayi ba Hajiya" marairaice masa tayi tace "Don Allah ka taimaka bawan Allah na gaji da tsayuwa ne wllh" bae kuma cewa komae ba ya ja adai daitan ya nufi inda ta ce masa. Dai dai kofar gidansu tace ya ajiyeta, yana gama parkin ta fito da kyar tace "Nawa xan baka?" Yace "ki bada dari biyar" gun mai gadinsu ta nufa ta gaishesa ya amsa da fara'a yana tambayarta ya hanya, tace "Baba dari biyar xaka basa don Allah xa a kawo maka" ya amsa da to snn ya mike yyi gun Mae keken, ita kuma ta shige gida da sauri, Dake su Sumayya ma na hutu duk suna gida, suka bi ta da kallon Mamaki jiddah ta Mike da sauri tace "Daga ina hka Afeefah" bata bi ta kansu ba ta haura sama da sauri don wani sabon hawayen ne ke taruwa idonta, duk suka mike suka bi bayanta, dakin Mami ta shige, ta sameta tsaye tana gyara kayan wardrobe dinta, juyawa Mami tayi don ganin Wanda ya shigo mata ganin Afeefah yasa ta yi still tana kallonta da mmki, xubewa nn tsakiyar dakin tayi ta shiga rusa wani kuka me tada hnkli tana kallon Maminta, Mami ta sake kayan hannunta ta karasa da sauri kusa da ita ta durkusa ta kamota a rude tana tambayarta me ya faru, kuka kawae Afeefah take har da shessheka, hnklin Mami yyi mugun tashi don har wani bari jikinta ya dau yi da kyar tana jijjigata ta iya cewa "ki min mgna Zainab ina Aliyun? Me ya faru" Su kansu jiddah da ke tsaye bakin kofa ba karamin tsorata suka yi ba, Afeefah ta rufe fuskarta jikin Maminta har lkcn Mami na tambayarta me ya faru kuma ina Aliyu a kidime, da kyar ta iya bude baki muryarta na rawa tace "yana Abuja" Mami tace "me ya dawo dake ke? Wani abu ya faru ne?" Duk a rude take watso mata tambayar, da kyar Afeefah ta saita kanta ta rage kukan da take tana kallon Mami hawaye na bin kuncinta, hnklin Mami yyi mugun tashi, ta shiga kallon 'yar tata daga sama xuwa kasa, a tsawace tace "ba magana nake maki ba, me ya faru nace" hawayen da Afeefah take suka fi na da, ta juya a hnkli tana kallon yayyinta da kanninta dake tsatstsaye bakin kofa hnkli a tashe, Mami da ta sha jinin jikinta ba kadan ba ta kalli yaran nata da kyar tace "ku fita ku ban waje" juyawa gaba daya suka yi suka bar dakin suka kullo kofar, Mami ta Mike gabanta na faduwa da kyar tace "Me ya hada ki da Aliyun?" ganin Afeefah bata da niyar cewa komae yasa Mami ta daka mata wani raxanannen tsawa ta dago ta tace "baxa ki min mgna ba? Me Aliyun yyi maki, ki bude baki nace ki min mgna don uban ki" ba karamin tsorata Afeefah tayi ba tana wani Sabon kukan jikinta na rawa tace "Mami.. Mami wae.. Wae yayanmu wae yana sona, yana son ya au...." Kasa ci gaba tayi don kuka ne ya ci karfinta, Mami ta xama kmr wata mutum mutumi tana kallonta 'yar tata, rungumeta Afeefah tayi cikin kuka tace "Ni baxan sake bin sa ba Mami, kar ki kuma cewa ya tafi da ni, ban san me ya samesa ba wae ni yake cewa xae aura in xama matarsa" kallon mugun Mmki Mami ke mata, lkci daya taji wani abu ya tsaya mata a xuciya ta runtse ido da kyar, ta janye Afeefah daga jikinta, idonta ya kada ba kadan ba murya can kasa tace "ki gaya min gskya Zainab, kar ki boye min komae, yyi maki wani abu ne?" Shiru Zainab tayi hawaye na bin kuncinta, hnklin Mami ya kuma tashi ba kadan ba, bude kofar dakin aka yi a hnkli duk suka juya suka ga Aliyu tsaye bakin kofar a sanyaye yana kallonsu, Afeefah ta fasa ihu a tsorace ganinsa taje can karshen gado ta rakube tana kuka tana kiran Mami, har wani bari jikinta yake, Mami kam mikewa tayi xuciyarta na bugawa da sauri da sauri fuskar nn tata a daure ita ma hawayen ne cike idonta ta nufesa.

Eeshatullah

[5/22, 07:57] Umar Dalha: ?????? 'Ya mace kyautar Allah??????


A true life love story


By Ashmaad

60.....
Tagwayen Mari masu lfya Mami ta kai masa, ta cakume kwalarsa hawaye na xubo mata tana girgixa kai tace "Da abinda xa ka biya ni knn Aliyu, is this the end result of d trust I had in yhu, is this my reward? ka gaya min me kama 'ya ta? Me kayi mata" Shiru kawae Aliyu yyi hawaye na sakko masa a hnkli, duk ynda Mami ta so ya bata amsan tambayoyinta kin cewa komae yyi, hkn yasa ta sake sa ta bude kofar dakin ta nuna masa waje alamar ya fita har lkcn hawaye take ssae, kansa a kasa ya juya ya fita daga dakin, Mami ta koma gun Zainab dake rakube jikin gado ita ma tana kukan, dagota tayi ta xaunar da ita gefen gado, da kyar tace "nace kar ki boye min komae Zainab, ki gaya min me yyi maki" tana share hawayenta a sanyaye tace "Mami ni bae min komae ba, kawae ce min yyi wae don Allah in yarda in auresa" sunkuyar da kai tayi tana kai wa nn, Mami tace "Sae aka yi ya?" Afeefah ta dago kae wasu sabbin hawayen na sakko mata a hnkli tace "Sae na gudu na shiga bayi na kulle, ban bude ba har asuba, ina jin ya tafi masallaci sae na fito da sauri na bar gidan," Shiru Mami tayi tana kallonta snn tace "Me ya kawo xancen?" Afeefah tana kallon uwar tata a sanyaye tace "Dama tunda muka je bashi da lfya" nn ta labarta ma Mami duk abinda ya faru har xuwan Dr Sharif gidan, sae kuma da daddare da ya shigo ya ganta tana waya da Dr Sharif ya fita da kuma ynda ta je dakinsa ya shareta, har xuwa san da ya dawo dakinta da maganganun da ya dinga gaya mata, ta karashe maganar tana kuka ssae tana kallon Mami, Mami tayi shiru tana kallonta, can ta mike tsaye ta share guntun hawayen fuskarta tace "ki tafi kiyi wanka" tana kai wa nn ta fita ta kulle kofarta ta waje, downstairs ta sauka ta nufi kitchen ta hado tea ta koma sama ta bude dakinta ta ajiye ma Zainab dake xaune har lkcn bakin gado tace "ki fara shan tean sae ki tafi kiyi wanka" kai kawae Afeefah ta gyada mata, Mami ta dauki wayarta ta fita ta kuma kulle kofar ta, su jiddah kam basu samu fuskar tambayarta abinda ya faru ba, ta nufi bangaren mai gidanta ta xauna falonsa, layin Safiya ta fara kira tana daga wayar bayan sun gaisa tace "Safiya ina son ki nemi izini gun mijinki ki taho Kano gobe" Safiya da hnklinta ya tashi tace "lfya Mami? Me ya faru" Mami tace "ina sauraran xuwan ki" tana kai wa nn ta katse wayar, ta shiga neman na 'yar ta ta biyu, tana daga wa ita ma tace tana son ta taho kano gobe, ita ma hnklinta ya tashi ba kadan ba, Mami ta katse wayar snn ta jinginar da kanta jikin kujera. Yinin ranan Afeefah bata fita daga dakin Mami ba, kuma Mami bata bar kowa ya shiga dakin ba, tunawa Afeefah tayi wayarta a kashe yake hkn yasa ta mike ta nufi gaban madubin Mami ta dauki wayar ta kunna snn ta koma ta kwanta, ko minti goma bata yi da kunna wayar ba kiran Dr Sharif ya shigo, mikewa tayi a sanyaye ta dauki wayar ta koma ta xauna, cikin sanyin murya ta gaishesa, shima ya amsa mata hkn, ganin tayi shiru yasa yace "me ya samu wayar ki, I've been tryn reachin yhu tun jiya" da kyar ta iya cewa "Bbu charge ne" yace "OK, ya jikin yayanki, yhu seem worried, is he nt gettin beta" shiru ta dan yi sae kuma tace "Da sauki sir" shima ya dan yi shirun snn yace "Are yhu sure?" Ta gyada masa kai tace "Um," yace "to shknn, my regardz to him, am leaving Abuja ynxu" tace "Toh Allah tsare hanya sir" yace "Ameen tnx dear" sallama yyi mata ta katse wayar. Ta koma ta kwanta a sanyaye. Mami na gama abincin Dinner bayan su Jiddah sun gama jerawa a dinnin, ta dauki wani kula daban ta xuba abincin ta ba Fadila ta kai ma Aliyu ganin ko abincin rana bae sakko ci ba, Adnaan da ke xaune falo yace "Ya dawo ne Mami?" Ba tare da Mami ta kallesa ba tace "Ehh" da mmki yace "Ban sani ba wllh, bae je masallaci ba kuma" Mikewa yyi ya bi bayan fadila suka nufi dakin Aliyu, xaune ya samesa kan darduma ya idar da sllh kansa a kasa, Karasowa cikin dakin yyi, fadila kuma ta ajiye abincin hannunta ta fita, Adnaan ya xauna daga kan gado yana kallonsa yace "Ashe ka dawo bro ban sani ba" da kyar Aliyu ya iya dago kansa da yyi masa nauyi yana kallon dan uwan nasa cikin sanyin murya yace "na dawo" kallonsa Adnaan ya tsaya yi ganin ynda idonsa ya kada ssae, da damuwa yace "Me ya faru bro, me ya sami idonka" Aliyu ya nuna masa kansa kawae, Adnaan ya sakko kasa kusa da shi yace "ciwon kai? Kaje clinic kuwa" Aliyu ya gyada masa kai yace "Na je." Adnaan yace "Allah ya sauwake, ga abinci sae ka ci kasha magani" da kansa ya dauko abincin ya xuba masa a plate ya ajiye masa gabansa yace "Eat plss bro, sae ka sha magani" misalin Karfe tara jiddah ta samu ta faki idon Mami ta shiga dakinta, ta samu Afeefah kwance tana game da wayarta, da ganinta kasan Akwae damuwa ssae tattare da ita, Afeefah na ganinta ta mike xaune ta ajiye wayar, jiddah ta karaso da sauri bayan ta kulle kofar ta xauna kusa da ita da damuwa tace "Wae me ya faru Afeefah?" Afeefah ta yi shiru tana kallon yar uwar tata, lkci daya hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta da sauri, Jiddah xata yi magana aka bude kofar Mami ta shigo, wani arnen kallo ta shiga yi ma Jiddah da ta mike da sauri jikinta na bari ta fita da sauri, Mami tayi kwafa ta karaso cikin dakin tana kallon Afeefah tace "kada in kuskura in ji bakin ki" kai kawae Afeefah ta gyada mata ta juya ta fita. Ko Abba Mami bata gaya ma abinda ya faru ba, bae kuma san Zainab na gidan ba har Washegari da ya kasance ran lahadi.

Karfe takwas saura na sapiyar y Anty Safiya ta shigo gida da dukkan alama flight ta biyo, hnkli tashe ta shigo falon, Jiddah da Sadiya dake ta goge goge a falon suka nufe ta da sauri suka rungumeta cike da farin cikin ganinta, sae a snn hnklinta ya kwanta don duk tunanin ta mutuwa aka yi, Abba ta fara tambaya snn yayyinta Maza sae kanninta duk Jiddah tace suna sama, Sumayya da Fadila dake tsaftace kitchen suma suka fito jin muryarta suka rungumeta cike da farin cikin ganinta, sama ta nufa ta fara shiga dakin ya Aliyu ganin kmr bacci yake yasa ta fita ta shiga dakin Adnaan, shima yyi farin cikin ganin 'yar uwar tasa, snn ta shiga dakin Mami, Mami na ta gyaran daki Afeefah kuma na xaune gaban madubi tana shafa mae da alamar daga wanka ta fito, mikewa tayi da sauri ta rungume yayarta da murnar ganinta, Anty Safiya tayi dariya tace "Zainab sarkin kuka, kina nn kina yi ko kin bari?" Afeefah ta boye fuskarta tace "Wllh Anty na bari tambayi Mami" Anty Safiya tayi dariya tace "A'ah naga alama" Safiya ta rungume Mami dake kallonsu tana murmushi, tace "kai Mami Dubi ynda kika daga min hnkli wllh nayi xaton wani ne ba lfya, kuma duk na kira su jiddah suka ce min lfya, bn yarda ba sae da na gan ni gida" Mami murmushi kawae tayi tayi mata sannu da xuwa, Dakin Abba Safiya ta nufa don xuwa gaida sa shima. Ko minti talatin Safiya bata cika a gidan ba sae ga Anty Ummi ma ta shigo da yaranta kanana biyu, kmr ynda Anty Safiya ta shigo hnkli tashe hka ita ma ta shigo, sae da ta ga kowa lfya snn hnklinta ya kwanta. Sae da Mami ta ga 'ya yan nata snn ta shiga dakin mai gidanta don yi masa bayanin abinda yasa ta bukaci su taho kano, bata boye masa komae ba tun daga jiya da Afeefah ta dawo gida da abubuwan da ta gaya maya da kuma biyo ta da Aliyu yyi da yanda suka yi da shi, duk ta gaya masa, Abba yyi shiru yana kallonta da gani kasan shi ma ya dan girgixa da jin lamarin, Mami ta kara da cewa idan anyi breakfast duk xa a xauna kowa ya ji matsayin Zainab a gidan nn, bbu wani boye boye kuma, hawaye ne cike idonta ta karashe maganar tana kai wa nn kuma ta mike ta fice daga dakin da sauri, Abba ya bi ta da kallo daga karshe ya jinginar da kansa a hnkli jikin kujera ya lumshe ido don yasan shine sanadin faruwan komae, he never wished for a day like this a rayuwarsa.


Eeshatullah

🌸👩🏻 'Ya Mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

61....
Karfe sha daya saura duk yan gidan suka hallara a falon Abba, Aliyu kadae ne baya falon duk da kiran da Jiddah taje tayi masa, bayan kusan minti biyar kowa ya nutsu a falon, Mami ta kalli Adnaan tace "ina Ali?" Mikewa yyi ya fita, ba a dau lkci ba Adnaan ya dawo falon yace yana xuwa, da sallama can ciki Aliyu ya shigo falon yana sanye da jallabiya milk colour ya nemi gefen Safiya dake ta binsa da kallo ganin ynda yayan nata ya rame, ba ita ba duk kanninsa kallonsa suke hka ma Abba, Abba ya fara gaidawa snn Mami duk kansa a kasa don tunda garin Allah ya waye bae fito ba sae ynxu, Afeefah kam na xaune kasa daga gefen Mami, ita kadae Aliyu ya daga kai ya kalla suka hada ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ta boye fuskarta jikin Mami, ya kuma sunkuyar da kansa kasa, Adnaan ne ya bude wajen da Addu'a bayan 'yan mintuna Mami ta fara magana kmr hka "Na so ace, ko kuma ince na sha fatan kadda Allah ya nuna min rana irin ta yau da ma abinda nake shirin fada ma kowa ynxu, sae dae am mistaken, ya xama dole in bude ma kowa wnn sirrin yau, Da farko dae ina san ku san na shigo gidan Mahaifin ku a shekara ta 1986, lkcn Aliyu na da shekaru uku a duniya, ran da na cika shekara daya a gidan aka haifi Adnaan kuma a ranan Allah yyi ma Mahaifiyar su Aliyu rasuwa, Wanda hkn yasa rikon marayun ya dawo hannu na, na kwashi shekaru fiye da uku ban haihu ba, daga karshe Allah ya bani 'ya ta ta fari Safiya, bayan shekara biyu na haifi Ummi, daga Ummi kuma na haifi Suhaila warce Allah yyi ma rasuwa ran da na haifi kanwarta Sadiya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login