Showing 87001 words to 90000 words out of 116554 words

Chapter 30 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1287

tausayinta yace "Srry Wife me" turo baki tayi ta ci gaba da kukan tana cewa "Wayyo ni xafi yake min sirrr" bata rufe baki ba taji dumin bakinsa a yatsan nata dake jini har lkcn, ta xaro ido tana kallonsa ta ga idonsa a lumshe yake, jin ynda yake tsotsan yatsan yasa a hnkli tace "Sir" ya kusa minti bakwae bae cire bakinsa ba kafin ya bude rinannun idanunsa a hnkli yana kallonta, ta sunkuyar da kai da sauri yyi murmushi cikin kasalalliyar murya yace "Ya daina?" Kai ta gyada masa ya mike ya xauna gefen gadon kusa da ita har suna jiyo numfashin juna yana rike da yatsan yace "in dan sa maki spirit kadan?" Xaro ido tayi tana dan komawa baya tace "A'a xae min xafi" ya kuma matsawa dab da ita ya shiga share d'an hawayen fuskarta cikin sanyin murya yace "me sa baki son muyi rayuwa ynda mata da miji suke yi Zainab," gabanta ne ya fadi lkci daya ta hade rae ta wani tsuke baki, murmushi yyi ya rungumeta a hnkli ya daura fuskarsa kan wuyarta tare da lumshe ido yana shakar da'ddadan kamshin jikinta, murya can kasa yace "Ki daina tsorona plss Zainab, Allah kadae yasan irin son da nake maki, love me same sweetheart, ke kadae ce macen da na fara yi ma kallon soyayya a rayuwata Zainab, am blindly in love with yhu" a hnkli ta shiga turasa gabanta na faduwa ganin muryarsa ya soma canxa salo, amma ya ki saketa, lkci daya ta tsorata da shi ta fashe da kuka tace "Ni ka bar ni in ci gaba da girkina sir" gnin abinda yake mata yasa ta rudewa ba kadan ba jikinta ya dau rawa, ranan ma yayanta da ta kira ne kadae ya ceceta, don turata yyi ya mike ya shige bayi kmr ana hankada sa, daga hka da ta samu ta dauki dankwalinta ko Zip bata tsaya rufewa ba ta fice da gudu daga dakin ta shige nata ta kulle ta dinga rusa kuka, bata son irin abinda yake mata ita dae. Har Washegari bata fito daga dakinta ba ga shi da yunwa ta kwana ga assignment din da bata yi ba, Karfe bakwae da wani abu ta sakko da shirin makaranta, ya samesa xaune falo shima yyi shirin fita office yana sip din coffee yana kallon news. K'asa Karasowa cikin falon tayi kanta a kasa, juyawa yyi yana kallonta, lkci daya yyi murmushi ya ci gaba da shan coffeensa, hawaye ne ya shiga bin kuncinta ta juya da sauri xata koma sama ya kirata.
Eeshatullah.
[6/29, 06:29] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad

80___81
Tsayawa tayi sae dae bata juyo ba ya mike ya karaso inda take yace "Kin tashi lfya" kai ta gyada masa ba tare da ta juyo ba, yace "Kina da lecture da safe ne yau" girgixa masa kai tayi kawae, ya juya ya koma falon, ita kuma ta nufi kitchen, indomie ta dafa ta koma sama, duk da yunwan da take ji kasa cin indomien tayi sae cakalkala shi take, bude kofar dakin yyi ya shigo yana kallonta yace "Driver na waje idan xa ki tafi sae kiyi masa mgna since ba ynxu kike da lecture ba, ni xan wuce" yana fadin hka ya ajiye mata five k a gaban mirror yace "Am off," mikewa tayi da sauri kmr xata yi kuka tace "Sir assignment din fa" ya dan yi shiru kafin yace "Kawo in ga" jakarta ta nufa ta fiddo handout din ta karasa kusa da shi ta mika masa ya karba yana kallon takardar, ya kusa minti biyar yana dubawa kafin ya karasa cikin dakin ya xauna gefen gado yace "Dauko pen da calc" daukowa tayi ta mika masa ya nuna mata gefensa ta xauna snn ya shiga mata bayanin topic din da ynda xata yi assignment din, ta shagwabe fuska tace "Ni dae Sir ka rubuta min plss ba ganewa xanyi ba" kunnenta ya ja yace "ke knn kullum kice baxa ki gane ba, C'mon take this pen" kukan shagwaba ta saki har da buga kafa tace "Sir plss ni dae ka min" kallonta ya tsaya yi, kafin yyi murmushi ya fara rubuta mata ta mike xata bar wajen ya fixgota yace "Ina xa ki, watch wat am doin" ta turo baki tace "kitchen xan kai plate, saketa yyi ya ci gaba da rubutun ta dauki plate din ta fita, da cup din sauran coffee dinsa ta dawo tana kallonsa tace " Sir in shanye," yace "Kina so ne?" Tace "Ae baka hada min toh" yace "OK xan dinga hada maki" daga hka ta shanye sauran coffeen ta dawo gefensa ta xauna tana kallon ynda yake ta solving mata questions din, ta dan yi tagumi tana kallon farin hannunsa dake dauke da kwantattcen bakin gashi, a xuciyarta tace kmr na yayanta, cikin kankanin lkci ya gama assignment din gaba daya ya tsaya yana cross checking, shafa takardan tayi tace "Ina son kalan rubutun ka sir" kallonta yyi ya kwaikwayi muryarta yace "Da gske" rufe fuskarta tayi da sauri tana dariya, don kanta ta xame hannun, ya tsaya kallon idonta da ya dan kumbura yace "Me ya sami idonki" dago kai tayi ta sa hannu tana shafa idon tace "Nima bn sani ba" yace "Kinyi kuka dae" ta turo baki xata dauke kai ya rike habarta tayi saurin rufe idon ita kunya, dan karamin jan bakinta ya tsura ma ido, ya lumshe ido ya kuma bude su, a hnkli ya kai bakinsa, jin lips dinsa kan nata yasa ta bude ido a tsorace, kwantar da ita yyi ya shiga shan bakinta idonsa rufe, kasa kwakkwaran motsi tayi sbda irin rikon da yyi mata, wnn karan sume masa ta kusan yi don kukan ma k'asawa tayi sae numfashinta dake sama sama, gnin hka yasa ya kyaleta ya mike da kyar bae ma ganin gabansa ya fice daga dakin, ta kusa minti goma kafin numfashinta yyi dai dai ta mike xaune da sauri ta ja bargo jikinta na rawa ta rufe kanta ta dinga rusa kuka kmr ranta xae fita, bayan minti kusan talatin ta ji fitowarsa daga bangarensa, sae kuma ta ji fitar motarsa, da kyar ta mike ta cire ragowar kayan jikinta ta nufi bayi, wanka tayi ta daura towel ta fito ta dauki wani kayan ta sa, snn ta nufi kan gadon jiki ba kwari don har lkcn gabanta bae bar faduwa ba, ta dauki wristwatch dinsa da necktie ta fita daga dakin ta nufi bangarensa, kan kujera a falonsa ta ajiye masa snn ta fice da sauri ta koma dakinta, wani sabon babin kukan ta bude ta dinga yi kmr warce aka yi ma mutuwa dama ga ta gwana, har lkcn leccan ta yyi bata mike ba kuma bata da niyyan yin hkan, daga karshe bacci ne yyi awan gaba da ita. Tun daga wnn incident din ta fara wasar 'yar buya da shi har na sati daya, in dae tasan yana gidan bata fitowa shi ma kuma baya shiga inda take, driver ne ke kai ta sch duk Safiya snn ya koma ya dauko ta da yamma, tana lura da karfe bakwae da rabi yake fita, don hka karfe takwas take fitowa driver ya kai ta makaranta, girkin ma da take ajiye masa daina ajiyewa tayi ynxu, kulli yaumin ta dawo daga makaranta sae ta tabbata baya gidan take sakkowa falo tayi abinda xata yi, duk da ta lura sae bayan Magrib yake shigowa gida ynxu, ba karamin rama tayi ba don taki kwantar da hnklinta ko da yaushe cikin tunani take, babban damuwar ta ita dae tasan ko ya Aliyu ya dawo, kusan kullum sae ta je department din su Anty jiddah ta tambaye su ko ya dawo sae su ce A'a, bbu ranan Allahn da xae wuce bata yi tryn numbobinsa ba amma duk switch off. Yau laraba Karfe biyu ta koma gida don lecturer su bata xo ba, driver na gama parking ta kalli inda Dr Sharif ke ajiye mota ta ga bae dawo ba, ta fito ta nufi cikin gida, wanka ta fara yi ta saka wata yar riga mara nauyi na kanti tayi kwanciyarta tana tunanin me xata girka, danwake taji take sha'awar ci ganin tana da komae a kitchen yasa ta mike ta fita xuwa kitchen, ta gama hada flour din danwaken tana kkrin bude ruwan da ta daura kan gas taji ance "Kama ta" a tsorace ta koma baya ta bar wajen tare da juyowa, ta gansa tsaye bakin kofa y rungume hannayensa, hade rae tayi ta juya masa baya da sauri, ya karaso cikin kitchen din yace "Kin gama hide nd seek din ki" bata tanka sa ba sae gaishesa da tayi ba tare da ta juyo ba, yyi murmushi yace "Kin dae san hukuncin duk macen dake gudun mijinta Zainab ba sae na tuna maki ba" turo baki tayi bata ce komae ba, ya karaso bayanta ya juyo da ita, tayi saurin sunkuyar da kanta, murmushi yyi yace "Me kike girka wa" murya can kasa tace "D'an wake" ya wara manyan idonsa yace "Meye hkan?" Ta juya tace "Idan na gama xaka gani" flour din da ta kwaba cikin roba ta dauka ta nufi gun tafasasshen ruwan xafin dake kan gas, ya bi bayanta yana kallon roban yace "Meye wnn kuma" juyowa tayi ta wara masa manyan idonta kmr nawa tace "Watch nd see" ya langwabar da kai yace "Ok" sae da ta kuma wanke hannunta snn ta fara saka dan waken, dariya yyi yace "Da hannu kuma, y nt ki sa spoon, its kinda odd" xaro masa ido tayi tace "Hka ake yi a gidanmu" bae kuma cewa komae har tayi rabi snn ta juyo tana kallonsa tace "Baxa ka taya ni ba?" Yace "Ae bn iya ba" tace "Ynda ka ga ina yi hka xaka yi" yyi murmushi yace "A'a ki dae gama ni dae bn iya ba" yana tsaye yana kallonta har ta gama ta wanke hannunta ta wanke roban ta debo ruwa ta dawo, ta kwashe danwaken da ke ta tafasa, ta sa man gyada a kan gas din ta yanka albasa, murmushi yyi yace "tab! Aiki" ta juya tana kallonsa tayi murmushi snn ta kunna wani gas din ta daura kwae uku, cikin kankanin lkci ta hada lafiyyan danwakenta da ya ji kwae da albasa a plate tasa yaji gefe daya, ta juya tana kallonsa murmushi dauke fuskarta tace "Xaka ci" xaro ido yyi da sauri yace "Nop na ci abinci" hade rae tayi tace "Allah sae ka d'an d'ana ni dae" ya langwabar da kai bae ce komae ba, ta fita daga kitchen din ya bi bayanta, tsakar falo suka xauna gaba daya, duk ynda taso ya ci danwaken kin ci yyi wae ya koshi, ta dauki daya a spoon ta kai masa baki ya kauda kai da sauri ya matsa yace "Wllh na koshi Zainab" ta hade rae ta fara juya abun ta xata ci, murmushi yyi ya matso kusa da ita ya jawo ta jikinsa ya lumshe ido yace "Oya srry xan ci amma kwaya biyu, kin ga bn iya ci ba Billah" kukan shagwaba ta saki tace "Sbda nayi jagwalgwalo koh? Shknn" shiru yyi yana kallonta don dariya ma take basa, ya kwantar da murya yace "Naga dae ba don ni kika girka abun ba wife, ni da kike play din hide nd seek da for d past one wk ma" turasa tayi xata bar wajen ya hadeta da jikinsa ya rungume, kuka ta saki tace "Sir ni ka kyale ni" cikin sanyin murya yace "Tell me wat's ur prblm Zainab, daman yhu are only deceiving me ba sona kike ba koh" kin sauraransa tayi sae kwace kanta take neman yi daga rikon da yyi mata, kamshin jikinta ya sa shi lumshe ido, daga hka kuma ya canxa salon rikon da yyi mata ya juyo da ita tana facing dinsa, abinda take tsoro ya soma yi mata, kan kace me ya dawo kmr ba shi ba, kokuwa ta shiga yi da shi amma ya gwada mata ya fi karfinta, ba karamin tsorata tayi ba gnin da gske yake, muryarta na rawa ta shiga rokansa tana hada sa da Allah, amma kmr tana tunxura sa, Mami ta dinga kira daga nn kuma ta koma yayanta, kmr wanda aka tsikara ya turata daga jikinsa, mikewa tayi jiki na rawa xata gudu ya fixgota yana huci, idon nan nasa yyi ja, yana mata mugun kallon da ya kada 'yan hanjin cikinta, cikin kaushin muryar da bata san sa da shi ba yace "Kadda ki kuma kiran min wani gardi daga yau gidan nn" a tsawace yace "Clear?" Bnda rawa bbu abinda jikinta yake, ya turata ya mike kmr wani xaki ya haura sama, ta kusa minti goma a falon tana kuka daga bisanni ta mike da kyar ta haura sama ta shige dakinta. Har dare bata sakko ba duk da irin yunwar da take ji, daga karshe fridge dinta ta bude ta dauki hollandia drink ta sha, Karfe goma ta yi wanka ta shirya ta kwanta, sae dae har sha biyu k'asa bacci tayi ga wani mugun ciwo da kanta ke mata, a hnkli ta mike ta dauko wayar dake gaban madubi ta dawo gefen gadon ta xauna ta shiga trying line din ya Aliyu har Karfe daya tana abu daya amma switch off, ta fada kan gado ta dinga rusa kukanta na tsiya, a hka bacci barawo ya sace ta. Washegari kusan da xaxxabi ta tashi, hka ta daure ta yi shirin makaranta don takwas da rabi take da lecture, tana jin fitar motarsa ta mike da kyar ta fita daga dakin sanye da hijab tana rike da jakar makarantar ta sakko falon, tsaye tayi tana kallon plate din d'anwaken jiya dake tsakar falon har lkcn, a sanyaye ta karasa falon ta duka ta dauke plate din ta nufi kitchen ta bude kofar kitchen din ta xubar cikin waste bin snn ta rufe kofar ta wanke plate din ta fita daga kitchen din. Drivern dake xaune da mai gadi yana ganinta ya mike ya tafi fito da mota dafa garage.
Suna xaune da
Maryam a cafeteria bayan sunyi azahar kafin su shiga lecture, hira kawae Maryam ke mata amma gaba daya hnklinta baya kan hirar tayi xurfi a tunanin da take, jin Maryam tace Xata sa rana ta xo gnin gida ya sa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, tayi mata murmushi tace "Toh ina xuba ido sae kin xo" daga hka Maryam tace su tafi aji, suka mike suka fita daga cafeterian, tunani ta shiga yi ko dae ta tafi gida tun da yau kusan watan ta daya da aure, ta kalli agogo ta taga biyu ya kusa, yanke shawarar tafiya gidan kawae tayi ta kalli Maryam tace "kin ga Maryam ni fa gida xan tafi kawae, sae mun hadu gobe sae ki ban handout" da xolaya Maryam tace "Xa ki je ki yi ma sir girki knn" murmushi kawae Afeefah tayi ta mata sallama ta nufi gate da sauri. Cike da murnar ganinta kofar gidansu ta sauka daga adai daita ta basa kudinsa ta shige gida da sauri, bbu kowa falonsu ta haura sama, dakin ya Aliyu ta fara budewa da saurinta ta shiga, sae dae bbu kowa falon kuma bata ga alamar ana amfani da dakin ba don ya dan yi kura, hawaye ne ya cika idonta ta fito a sanyaye, dai dai lkcn da Mami ta fito daga dakinta, da mmki ta tsaya kallonta tace "Zainab? Daga ina hka?" Afeefah ta karasawa da sauri ta rungume uwar tata, Mami tace "Ikon Allah, daga ina kike?" Tace "Daga makaranta" Mami tace "Shi yace ki xo?" Turo baki tayi tace "Nayi kewarku ne Mami shi sa na xo, yayanmu fa?" Mami ta hade rae tace "Ban san baki da hnkli ba sae yau Zainab, to maxa juya ki bar min gidana sha sha sha kawae a ina aka taba hka" shiru tayi jiki a sanyaye tana kallon Mami, lkci daya hawaye ya taru idonta tace "Ae ba dde wa xanyi ba Mami, yayanmu fa?" Mami tace "Ki bar min gida Zainab tun ban bata maki rae ba" hawaye ya shiga bin kuncinta tace "To Mami xan tafi, amma yayanmu fa?" Mami tace "Ban sani ba ki kama hanyar gidanki" kuka ssae take tace "Don Allah ki gaya min Mami Allah xan tafi ynxu, ni shi na xo gani wllh" Mami tace "Baya nn to" a sanyaye tace "Ina ya tafi Mami, me sa layinsa basa shiga idan na kirasa" Mami tace "Me xae maki kike kiransa," tace "Ina son in ji muryarsa Mami nayi missing dinsa, idan ya canxa layi ne ki ban plss" Mami da ta dan fara shan jinin jikinta tace "Ke ban fa son shashanci baya Nigeria kiyi tafiyar ki gida, idan ya dawo ae xae je ya gan ki" kuka ssae ta dinga yi tana girgixa ma Mami Kai tace "Mami ina yace xe tafi, kuma yaushe xae dawo" wani tsawan da ya raxanata Mami ta daka mata tace "Fice min a gida kada ki ja ma kanki duka Zainab" tana kuka ta juya da sauri ta sauka ta fita falon. Karfe uku ya wuce ta shigo gida, ko kallon drivern ta da ke tambayar ta ya bata kira sa ba bata yi ba don wani duhu duhu take gani ga kanta dake neman rabewa biyu, last strength dinta tayi amfani da ta shiga falon kafin duhu ya mamayeta ta xube nn bakin kofar falon a sume, Dr Sharif dake kwance falo yana kallon wani American Movie ya mike da sauri ya karasa bakin kofar, durkusawa yyi gabanta ya dago ta a sume, mikewa yyi da sauri ya dauketa ya nufi sama da ita ya shiga part dinsa, kan gado ya kwantar da ita ya shiga bata taimakon da ya kamata. Can Karfe takwas na dare yana xaune kan darduma ya idar da isha ya ga tana juye juye har ya mike xae karasa kusa da ita jin sunan wanda take kira yasa ya koma yyi xamansa, ta kira yayanmu ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login