Showing 42001 words to 45000 words out of 116554 words

Chapter 15 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1292

"kar ki min kuka" gyada masa kae kawae tayi, ya dauko wani leda ya mika mata, kin karba tayi da farko, amma ganin ynda ya tsare ta da ido yasa ta sa hannu ta karba duk da bata san meye ba, ajiye mug din hannunsa yyi yace "xan koma kano" dago dara daran idanuwanta tayi tana kallonsa, a hnkli tace "to ngd sir Allah tsare hanya," yace "Ameen Zainab!" Kira min Amina, mikewa tayi ta nufi sama, tare suka sakko da Aminan ya mike yace "sae kin xo meenah, I will b on my way ynxu" Amina tace "kai yayana baxa ka jira Abban Fadil ba," yace "mun yi waya da shi, nace baxae same ni ba, beside mun ma hadu daxu da safe ae" Amina bata so hka ba a sanyaye tace "to shknn yaya ina xuwa" sama ta nufa, ya juya yana kallon Afeefah, murmushi yyi ganin ynda ta bata fuska, yace "me ya faru kuma?" Kmr xata yi kuka tace "ni ma wajen Mami na nake son komawa" dariya yyi yace "ae nn da few dayz xa ku koma sch," Amina ce ta sakko rike da leda ta mika masa tace "gashi yaya ka kai ma teemah" hararanta yyi yace "wa xa ki hada da kaya?" Marairaice masa tayi tace "ba jirgi xa ka bi ba yayana" karba yyi yace "shknn sae mun yi waya" Juyawa Zainab tayi ta haura sama da sauri, Dr Sharif yyi dariya yana kallon Amina yace "xa ki sha lallashi yau knn" dariya tayi tace "wae baxa ka tafi ba?" Yace "wae xata koma kano ita ma" dubu goma ya ciro ya daura kan fadil ya shafa kan yaron , yyi pecking dinsa yace "gudbye son" godiya Amina tayi masa ta raka yayan nata har gate, snn ta dawo cikin gida, dakin Afeefah ta shiga ta sameta xaune tana rusa kuka, dariya ssae abun ya bata, ta dake ta shiga lallashinta amma kmr dada tunxurata take hkn yasa ta bar dakin. Da yamma misalin Karfe biyar Afeefah ta bude ledan da Dr Sharif ya bata, waya iPhone 7 ta gani, tuni ta kwalalo ido a dan tsorace tana kallon kwalin wayar, mikewa tayi da sauri ta bude jakarta ta saka kwalin da ganinta kasan ba karamin tsoro ta ji ba.

After Magrib Ma'aruf ya tafi da Afeefah can gida, a hanya take gaya masa wayar da Dr Sharif ya bata, yace "iyye, lallai Aliyun nn na ji da ke, to kin gode, idan mun koma gida sae ki kirasa kiyi masa gdya, gobe sae in siyo maki sim" Afeefah tace "toh yaya"

ba karamin kunyar tambayar da dad ke mata Afeefah tayi ba, taki dago kanta don ji tayi da ma ta nutse wajen kawae, Ammi tayi dariya tace "ka bar ni da ita kawae Alhaji, xata gaya min gskya" dad yyi dariya yana kallon Afeefah yace "to tashi ki tafi" mikewa tayi kanta a kasa ta bar falon, dad yyi murmushi yace "Allah ya ji kan Umar ya gafarta masa," Ammi tace "Ameen ya Allah" snn ta mike ta bi bayan Afeefah, bedroom dinta ta kai ta ta xaunar da ita gefen gado tace "kar ki ji kunya ta dota, ki gaya min gskya kina son Aliyu wan matar yayan ki?" Afeefah ta sunkuyar da kai bata ce komae ba, sae da Ammi tayi da gske snn a hnkli ta gyada mata kai a kunyace, Ammi tayi murmushi tace "toh shknn tashi ki yi tafiyar ki" mikewa tayi da sauri ta bar dakin ta shige na su Ilham. A hanya xa su koma gida Afeefah ke ce ma Ma'aruf "yaya amma don Allah kar a gaya ma su Mami, kasan Abbanmu karatu yake son muyi, ni sae na gama karatuna" kmr xata yi kuka ta kare mgnr Ma'aruf ya dan tabe baki yace "na ji" duk da kawae amsa mata yyi don shi ya ma fi son a aurar da ita da karatun hofin. Hka Afeefah ta karashi hutun ta a Kaduna duk ta kagu ta koma kano ta rasa dalili, ana gobe xata koma Abba ya sa ya saleem ya yankar mata ticket, tsaraba ssae Ammi tayi mata, hka ma Anty Amina, ya Ma'aruf kuma laptop ya siya mata, Saleem kuwa da ya tambayeta me take so kawae Ca tayi yar karamar Nokia xae siya mata, da yamma Ya Ma'aruf da Anty Amina suka rakata airport, suna nn har jirgin yyi take off snn suka koma gida. Adnaan ne ya tare ta a airport din kd, Afeefah tayi mmkin da ya Aliyu bae xo tarar ta ba as usual. Bayan sun kama hanya tace "ya Adnaan yayanmu fa?" Adnaan yace "yana gida" shiru tayi bata kuma cewa komae ba har suka isa gida, bata damu da murnar dawowanta da yan uwanta ke tayi ba ta nufi sama da sauri ta shige dakin ya Aliyu, yana tsaye waya na kare kunnansa alamar waya yake, da gudu ta rungumesa tsam cike da farin ciki tace "yayanmu" da farko dakewa yyi, tana dago dara daran idonsa ta daura kan nasa kawae ya kasa, lkci daya ya sakar mata murmushinsa Mae kyau ya ja kumatunta yace "Welcm" bata fuska tayi tace "shine baka xo daukana a airport ba ko yayanmu" ajiye wayar hannunsa yyi yace "kin gaya min xa ki taso yau?" Ta wara ido tace "yaya ka manta bnda waya" yace "na tuna," tace "amma ya saleem ya siya min yar karama bn fara amfani da shi ba" gyada mata kai kawae yyi, ta juya ta nufi kofa tace "bari in je in gaida Mami" bin ta yyi da kallo har ta fita. Tana fita dakinsu ta nufa da sauri ta bude jakarta ta ciro wayar da Dr Sharif ya siya Mata ta shige bayi da sauri ta shiga kiran layinsa, yana dagawa tace "Sir na dawo" yace "haba, yaushe kika dawo" tace "ynxun nn" yace "welcm dear, result din ku ya fito" xaro ido tayi tace "da gske sir? Ka duba min nawa?" Yace "yep na duba, Allah ya taimake ki a course dina kadae kike da carry over" dafe kirji tayi sae kuma ta saka masa kuka, yyi dariya ya katse wayar. Ta ci kukanta ta koshi ta fito daga bayin. Cikin jaka ta boye wayar da sauri. Da daddare Afeefah na fiddo da tsarabar su jiddah wayarta dake cikin jaka ya soma ring, xaro ido su Jiddah suka yi jin Ringtone din, da gudu Afeefah ta nufi jakar don mancewa tayi bata sa a cylnt ba, kashe wa tayi gaba daya ta mayar jakar, Jiddah tace "iPhone Afeefah? Wa ya siya maki" bata fuska tayi tace " ya Ma'aruf" bata jira cewarsu ba taje ta ci gaba da abinda take, Sadiya ta sauke ajiyar xuciya har da su Sumayya. Hka Afeefah ta dinga kaffa kaffa da wayar kar yayanmu ya gani, laptop kuwa da ma ta kai ma Mami tace Ma'aruf ne ya bata, wayar kuwa bata nuna mata ba sae wnda saleem ya siya mata, ana gobe xa su koma sch da daddare Afeefah na xaune ita kadae daki ta shige cikin bargo ta gama waya da Dr Sharif knn tana danne dannenta, ya Aliyu ya turo kofar dakin ganin tun yamma bata sakko falo ba, tsayawa yyi yana kallon bargon, ko kadan Afeefah bata san an shigo dakin ba, ya karasa kan gadon ya yaye bargon a hnkli yana kallonta, a kidime ta mike xaune tana kallonsa, lkci daya ta shiga kkrin boye wayar hannunta, fixgewa yyi yana kallon wayar da mmki, kuka ta saki ta mike da gudu ta fice daga dakin ta shige dakin Mami, Mami da fitowarta daga bayi knn ta bi ta da kallon mamaki, kuka ta fashe mata da tace "wayyo Mami ki ce ma yayanmu dady ne fa ya siya min wayar" korarta Mami tayi daga dakinta a fusace, Afeefah tayi dakin Adnaan shi ma ta fashe masa da kuka tace "kaga ya Adnaan, dady ne ya siya min wayar fa" Adnaan yana kallonta da mmki yace "wani waya?" Cikin kuka tace "yana hannun yayanmu je ka gani kar yace ba shi ya siya min ba ya min duka" dariya Adnaan yyi ya mike ya fita ya samu Ya Aliyu dakin sa a kwance, kallon iPhone 7 din kan gadon Adnaan yyi ya karasa ya dauka yana dariya yace "Wae kaji dady ya siya mata tace" wani mugun kallo Aliyu yyi masa can yace "naji, ae ni bn ce mata komae ba kai mata wayarta" Adnaan ya fita da wayar ya kai Mata dakinsa, mikewa ya Aliyu yyi ya fice daga dakin ya nufi dakinsu jiddah, jakar kayan Afeefah ya nufa ya xuge ya shiga fiddo kayan ciki can kasan jakar ya ga kwalin wayar ya bude bae ga receipt ciki ba, kan farin envelope idonsa ya sauka ya dauki envelope din ya bude ya ga hotuna ne ciki, yana cikin fiddo hotunan aka bude kofar dakin ya daga kai suka yi ido hutu da ita ta shigo, mutuwar tsaye tayi bakin kofar cikin rawan murya tace "yayanmu" bae kuma kallonta ba ya ciro hotunan gaba daya yana kallo, mikewa Aliyu yyi da sauri ya dafa bango tsabar wani mugun jirin da ke neman kada sa daga durkushen da yake kansa na juya masa.

Eeshatullah Goni😘😘
?
?[5/23, 08:34] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya mace kyautar AllahπŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

44.....
Afeefah ta fasa ihu a tsorace ta durkushe wajen tana kallonsa lkci daya ta fashe da wani matsanancin kuka ta daura hannu a ka tana kiran Mami, da kyar Aliyu ya iya jan kafarsa ganin tsayuwar ya gagaresa ya koma can gefen gado ya rike kansa da yyi masa nauyi ssae, Adnaan ne ya shigo dakin da sauri ya kalleta snn ya kalli Aliyun, su Jiddah ma suka shigo suka yi cirko cirko a bakin kofa su kalleta su kalli Yayanmu, Mami ce ta shigo dakin ita ma tace "me ya faru? Wa ke min ihu a gida?" rasa me bata amsa aka yi, Afeefah kam sae kuka take daga durkushen da take, kallon Aliyu dake xaune gefen gado har lkcn yana rike da kai Mami tayi ta ja tsaki ta juya ta fice daga dakin, Adnaan ya karaso cikin dakin ya karasa kusa da Aliyu yace "me ya faru bro? Me tayi maka" ganin Aliyu bae da niyar tanka sa yasa ya juya ya fice daga dakin shima, su Jiddah suka bi bayansa. Mikewa Afeefah tayi ta fice ita ma da sauri jikinta na rawa, dakin Adnaan ta shiga ta xube gabansa cikin kuka tace "ya Adnaan ka taimake ni yayanmu xae kashe ni yau" Yace "me kika yi ne wae?" Muryarta na rawa tace "Ni ma bn sani ba" hka tayi ta xama dakin Adnaan taki fita sae kuka take. Ganin gyangyadi take daga xaunen da take yasa Adnaan yace "ki kwanta Zainab" bude ido tayi, tayi shiru tana kallon bakin kofa can ta mike kmr warce kwai ya fashe ma ta fice daga dakin ta nufi dakinsu, su Jiddah na shirin kwanciya Afeefah ta shigo dakin ta nufi kan gado a sanyaye, duk suka bi ta da kallo, sae da ta kwanta snn Jidda ta karasa kusa da ita ta xauna tace "Afeefah me kika yi ma yayanmu" hawaye ne suka gangaro mata bata ce komae ba, daga karshe ta kauda kanta, mikewa jiddah tayi ta bar wajen. Har asuba Afeefah bata wani rintsa ba, ta rasa me ke mata ddi a duniyar, tasan a da ko da wasa bata tsallake duk umarnin da yayanmu ya bata amma tun da ta fara higher institution take disobeyin dinsa ta rasa dalili, sae da su Jiddah suka dawo daga gaida Abba snn ta mike jiki ba kwari ta fita don xuwa gaishesa, Abba na xaune falonsa ya Aliyu ma na xaune falon daga kasa gefensa, Afeefah ta karasa a sanyaye ta xauna daya gefen Abba murya can kasa tace "Ina kwana Abba" Abba yace "lfya lau mamata, kin tashi lfya" gyada masa kai kawae tayi kanta a kasa, Abba yace "an koma makaranta yau ko?" Kai ta gyada masa nn ma, yace "to Ma'sha Allah, sae a maida hnkli kin ji mamata" tace "toh Abba" juyawa yyi yana kallon Aliyu da ya sunkuyar da kansa yace "yauwa ina jin ka Ali" Afeefah ta tsura masa ido lkci daya hawaye ya taru idonta, dago kai yayanmu yyi suka hada ido da ita, ya dauke kai da sauri, da kyar ta iya bude baki tace "ina kwana yayanmu" Ba tare da ya kalleta ba cikin sanyin murya yace "lfya lau" kallon Abbansa yyi yace "dama Abba ina son xan koma can gida na ne, sbda Akwae wani case da muke dubawa ni da abokai na kafin in koma lagos, so we have to stay togeda don mu yi aikin tare" Abba yace "toh shknn Allah ya taimaka" yace "Ameen" snn ya mike ya fita daga falon, bin sa da kallo Afeefah tayi snn ita ma ta mike a sanyaye tace "Abba na tafi" Abba yace "bbu matsala dae koh" kai ta gyada masa tace "bbu Abba" ya sallameta ta fita. Hawaye ne suka shiga bin kuncinta ta nufi dakinsu ta fada kan gado ta dinga rusa kuka, kukanta ya tsananta jin fitar motar Aliyu, su jiddah dae na ta shirin sch abunsa bbu Wanda yace mata komae, gajiya tayi da kukan ta mike daga karshe ta shiga bayi ta wanke bakinta tayi wanka ta fito, duk sae ta ji kmr xaxxabi na neman rufeta, ta fiddo da kayanta da kyar ta sa bayan ta shafa mai ta koma kan gado ta kwanta, Mami ne ta shigo dakin tace "wato Zainab ni kike jira in shigo in gaida ki koh" mikewa tayi da kyar don kanta yyi mata nauyi a sanyaye tace "Mami kaina ne ke min ciwo" Mami tace "ki sakko kiyi breakfast sae ki sha magani" saukowa tayi daga kan gadon ta daura dankwalinta ta bi bayan Mami, tea kadae ta iya sha, Mami ta dauko Mata magani ta bata ta sha snn ta koma falo ta kwanta kan kujera, Driver ne yyi horn alamar yana jiransu, Jiddah da sadiya suka dauki jakarsu suka yi ma Mami sallama, Afeefah ta mike da kyar tace "Anty jiddah don Allah ki dauko min jakata da hijab a sama" Mami tace "kina da lecturen safe ne?" Afeefah ta gyada kai tace "Umm" Mami tace "ki bari kawae su tafi ko da rana sae ya kai ki tunda baki jin ddi" girgixa kae Afeefah tayi ta mike da sauri tace "A'a ni xan tafi ynxu Mami" sama ta nufa ta dauko hijab da jakarta ta sakko tayi ma Mami sallama suka bar gidan. Driver na ajiye su ko wannensu ya nufi department dinsa, Afeefah kam karkashin bishiya ta samu ta xauna duk da tasan tana da lecture din safe, gaba daya tunaninta na gun ya Aliyu, duk ta rasa sukuni, Muryar Maryam ta ji a bayanta tana cewa "uhm Afeefah me kirki ko kira" Afeefah tace "ae ke naga kin yi kiran" murmushi Maryam tayi tace "wayata ce ta lalace, amma ai na shigo duba mana result, nayi niyar karbar lambarki gun Dr sharif ranan amma na manta," Afeefah tace "hka yace maki yana da nmbr na" Maryam ta dan yi murmushi tace "tashi mu shiga lecture an kusa shiga" girgixa mata kai Afeefah tayi tace "akwae abinda nake jira, ki shiga kawae" Maryam tace "toh" snn ta nufi lecture hall, Afeefah na nn xaune har bayan kusan awa daya ta hango Dr Sharif yana tahowa da wani student, dauke kai tayi da sauri har suka karaso, ta dan sata kallonsa suka hada ido don shima kallon nata yake, sunkuyar da kanta tayi har suka wuce. Mikewa Afeefah tayi da sauri ta bar wajen don bata ma son ya dawo ya ganta, rasa inda xata tayi lkci daya hawaye ya cika idonta ta nufi gate kawae, tsaye tayi tana share hawayenta ta tsayar da adai daita, shiru tayi duk da taji tambayar da yake Mata na cewa ina xata, a hnkli ta samu kanta da cewa "Nasarawa G.r.a xa ni" bata jira cewarsa ba ta shiga adai daitan.
Suna isa nasarawan tayi masa kwatancen inda xata, dai dai bakin gate din gidan ya ajiye ta ta fito ta bude jakarta ta mika masa duba daya ya bata canjin dari biyar, bata damu ba ta nufi gate din ta gaida mai gadin dake xaune kan benci a sanyaye tace "yana ciki" yace "ehh yana nn" tura gate din tayi ta shiga gidan, sae da ta isa bakin kofar shiga gidan taji gabanta na faduwa, kmr tana tsoron handle din kofar ta murda a hnkli ta ji shi a rufe, tsoron danne bell ta ji, kawae ta nufi back yard, kofar kitchen ta murda ta ji a bude ta shiga snn ta rufe ta nufi falo, bbu kowa falon sae Ac da plasman dake aiki, a sanyaye ta nufi stairs ta haura sama, ta dde tsaye bakin kofar dakin daga bisanni ta tura a hnkli tare da yin sallama can ciki ta shiga.

Eeshatullah Goni
😘😘
[5/23, 08:34] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya mace kyautar AllahπŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

45....
Mikewa xaune ya Aliyu yyi daga kwancen da yake ya cire bargon jikinsa yana kallonta, ta karaso cikin dakin a sanyaye tana kallonsa xata yi magana ya girgixa mata kai ya nuna mata kofa cikin sanyin murya yace "Leave! immediately" kuka ta sakar masa ta durkushe nn inda take tsaye ta hade hannayenta muryarta na rawa tace "don Allah don Annabi yayanmu kayi hkuri plss ina rokon ka" rike kae yyi a raunane yace "me ya kawo ki nn Zainab, meye na biyo ni, Let me be Zainab, just let me be plss leave..."kuka take a hnkli tana kallonsa, ya dago kansa a hnkli yana kallonta da idanuwansa da suka sauya launi, ya runtse ido ya mike cikin tsawa yace "leave Zainab" a tsorace ta mike hawaye na sakko mata, ganin ta nufosa yasa da sauri yace "kar ki karaso kusa dani, ki fita nace" bae ankara ba sae ganin ta rungumesa tsam yyi, ta kwantar da kanta kirjinsa muryarta na rawa tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login