Showing 114001 words to 116554 words out of 116554 words
kuma kunya ta shiga dawainiya da shi don bae ma san da idon da xae kalli Mamin ba, tana xaune daki Fadila durkushe gefenta alamar magana take mata, kmr munafuka Afeefah ta rabe jikin Aliyu, duk suka xauna k'asa, Fadila ta kalli yayanta da jajayen idonta ta gaishesa ya amsa kafin ta mike ta fita daga dakin, yana son tambayar kukan me take sae dae bae ce komae ba, ya gaida Mami kansa kasa, ta amsa masa a sake tana tambayarsa gida, Afeefah ma ta gaisheta a sanyaye ta amsa mata ita ma hka, rasa abun cewa suka yi gaba daya, shi kam har lkcn bae dago ba, Afeefah ta mike a hnkli ta isa gaban uwar tata ta durkushe gabanta cikin rawan murya tace "Don Allah Mami kiyi hkuri ki yafe min...." kuka ta saki a hankali, Mami na kallonta tayi shiru na kusan minti biyar, ganin ynda take kuka yasa tace "ya wuce Zainab, Allah yafe mana baki daya, sae dae ki nemi gafarar wanda kika cutan" kai ta gyada ma uwar tata hawaye na sakko mata, Mami ta kalli Aliyu da bae d'ago ba har lkcn tace "Kai kuma sinne kan me kke hka kmr munafuki" murmushi yyi sae dae bae iya ya dago ba, Mami ma tayi murmushin ta tabe baki tace "Allah kyauta" mikewa yyi yace "Abba na daki Mami" tace "yana ciki," yace "Bari in je gaida shi" daga hka ya juya ya nufi kofa, Mami ta kalli Afeefah dake durkushe har lkcn gabanta tace "Ki tashi ku je" mikewa tayi ta bi bayansa kanta a kasa. Sun dde xaune falon Abba bayan sun gaisa, sae dae shi din ma Aliyu bae iya daga kai ya kallesa ba, duk kunyan iyayen nasa yake, Abba na lura da hkn ya shashantar ya dinga jan Zainab da hira. Uku da 'yan mintuna suka fito daga bangaren Abba, Aliyu ya shiga dakin 'yan matan gidan don ganin Fadila ya ji kukan me take, kwance ya sameta idonta biyu kuma kuka take har lkcn, sae dae duk ynda ya so jin damuwarta kin gaya masa tayi tace ba komae, hka ma Afeefah tayi tayi da ita ta ki magana, juyawa yyi ya nufi dakin Mami ya sameta tana waya ya jira ta gama wayar kafin yace "Mami wae me ya samu Fadila?" Mami tace "Me ka ga?" Yace "Naga tana ta kuka," Mami ta dan yi murmushi tace "xata daina"
Da yamma misalin shidda Afeefah na kitchen tana taya su Jiddah girki Ya Aliyu ya shigo kitchen din, dab da ita ya tsaya yyi wrapping hannunsa a waist dinta ya kwanta bayanta, su Jiddah na ganin hka suka dauke Kai da sauri, suna ci gaba da abinda suke, Cire hannunsa ta shiga yi murya can kasa tace "Meye hka yayanmu, kaga fa su Anty Jiddah" saitin kunnenta ya kai bakinsa yace "Ki bar girkin nn hka mu tafi gidanmu yamma yyi" xata yi magana Mami ta shigo kitchen din, da sauri ya saketa ya koma baya, ita ko ji tayi kmr ta nutse, wani kallo Mami ta shiga yi masu ae da sauri suka fice kitchen din kmr munafukae, su Anty Jiddah suka dinga dariya, Mami tayi tsaki ta dauki abinda ya kawo ta ta fita. Basu suka bar gidan ba sae tara da wani abu, ta so su kwana amma yaki yrda wae baya son su kuma wani abun kunyan. Bayan sati biyu da xuwansu gida wanda ya kama watansu daya cur da aure da yamma bayan ya dawo aiki tana kwance jikinsa sanye da wani dan mini skirt da vest suna kallo ko kuma ince yana kallo don ita idonta lumshe yake, cikin 'yan kwanakin nn ba karamin soyewa suka yi ba, ta ga love gun Aliyu kmr xae hadiyeta, tun tana kunya har dae ta hakura ta ajiye, komae shi yake yi gidan kafin ya fita aiki, sae ran da yake sauri ne xae bar mata, yasan likes nd dislikes dinta kuma ya san halinta tsaf, don hka duk abinda xae bata mata rae gudunsa yake.
Dago kanta yyi yace "Wae bacci kike da yamma baby, kin fasa fitan ne" ta bude ido a hnkli ta kallesa bata ce komae ba, yace "tell me wats wrong baby, kince min bbu inda ke maki ciwo gashi duk kinyi sanyi, naji jikin ki da dumi kuma" girgixa masa kai tayi ta kuma lumshe ido ta shige jikinsa, danna bell aka yi ya kalli kofar duk a tunaninsa drivern da ya aika siyo masu abinci ne, ya kwantar da ita ya manna mata kiss a baki ya shafa fuskarta kafin ya juya ya nufi kofar ya bude, su Anty Safiya da Baby ne tsaye bakin kofar, kallon mamaki yake masu don bae samu lbrin xuwansu ba, Safiya tayi dariya tace "Wnn kallon hka yayanmu, ko mu koma ne" murmushi yyi har lkcn bae basu hanya ba, Anty baby tace "Lallai yayanmu" daga hka ta raba ta gefensa ta shiga falon hka ma Safiya suka bar sa nn tsaye, mikewa xaune Afeefah tayi da sauri jin muryar yayyin nata, sama tayi niyar haurawa da sauri sbda kayan jikinta, amma tuni suka karaso cikin falon, cike da jin kunya ta mike ta rungume su, Anty Safiya tayi dariya hka ma baby sae dae basu ce komae ba, sae a snn suka gane abinda yasa ya ki basu hanya, rufe kofar yyi ya dawo cikin falon yace "Lallai ma yaran nn, xuwa bbu notice" Anty baby tace "wae mu nn surprise visit muka yi, ashe baxa mu burge ka ba ma, ae tun jiya na xo, ita kuma Maman iman yau ta iso" yace "Toh meeting din me xa ayi kuma ban sani ba" kallonsa duk suka tsaya yi da mamaki kafin Anty Safiya tace "Biki muka xo" ya dan yi shiru kafin yace "Bikin wa?" K'asa basa amsa suka yi, can dae Baby tace "Fadila," da mamaki yace "Fadila kuma?" Anty Safiya tace "Kai yayanmu, nufin ka baku sani ba" xaunawa Aliyu yyi yace "Joke apart, bikin wa ku ka xo?" Anty Safiya tace "Wllh na Fadila, kuma yau saura kwana biyar" har lkcn mamaki bae bar fuskarsa ba yace "Da wa xa ayi bikin" Anty baby tace "Tsohon mijin Zainab, Dr Aliyu" still Afeefah tayi tana kallonsu ko kiftawa bata yi, shi kansa Aliyu bae iya cewa komae ba sae kallonsu yake, Anty Safiya tace "Abba ne ya bashi, kuma ya biya masa sadaki," sunkuyar da kai Afeefah tayi a sanyaye, shi kam Aliyu Mamakin dalilin da yasa aka ki gaya masa kawae yake, a hnkli yace "Allah sa hkn shine mafi alkhairi" duk suka ce Ameen, Anty na kallon Afeefah tace "irin wannan kyan da da hske da kika kara yan matan yayanmu". Murmushi ta yi ta rufe fuskarta jikin kujera da sauri cike da jin kunya, duk suka yi dariya, yana kallonsu yace "Toh ku tashi ku gyara mana gida don dama bbu abinda muka yi yau bamu da lfya" dariya duk suka yi, ya jawo Afeefah jikinsa yace "Koh ba hka ba baby" ta kwace kanta ta mike a kunyace ta nufi sama da sauri da dan fingilallan skirt dinta, suka bi ta da kallo suna dariya.
🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
By Ashmaad
End.
kashe wutan dakin yyi, a hnkli ya mirgino ya dawo kusa da ita ya jawota jikinsa, cikin sanyin murya yace "Fadila" a hnkli tace "Um" bae kuma cewa komae ba jin ynda jikinta ya dau rawa, ya lumshe ido yace "Kiyi baccin ki Kinji" muryarta na rawa tace "Toh" tausayi ta basa ba kadan ba ganin ynda ta tsaya bbu gardama, suna nn a hka bayan kusan awa daya ya ji saukar numfashinta a hnkli alamar tayi bacci. D'aga wnn rana ya ji hkurinsa ya soma gazawa, duk irin juriyarsa ta bangaren nn ji yyi wnn karan bbu juriyar, ya so sae ta gama sec sch ko xae santa amma ya ga alaman baxae iya ba kuma gashi tausayinta yake, kullum cikin ciwon ciki yake me tsanani, ganin saura 'yan kwanaki su fara jarabawan waec yasa ya gwammace yayi ta wahalan don bae son abinda xae kawo mata cikas a jarabawarta, fadila ta lura bae jin ddi duk ta damu tace ko su tafi asibiti, yace yana shan magani, gani yyi yana neman hallaka kansa ranan ta shigo da daddare rike da coffeensa ta samesa kwance yyi rub da ciki, a sanyaye ta xauna gefensa tace "Uncle to ni ban ga magungunan da kke sha ba" da kyar ya Mike xaune yana kallonta yace "Ina sha mana" coffee dinsa ta mika masa ya karba ya ajiye ya mike da kyar ya nufi gaban mirrornsa ya dauko olive oil me kyau da cotton wool ya dawo ya xauna yana kallonta ya mika mata yace "Its gud, ki dinga inserting kin ji" sunkuyar da kai tayi da sauri da ganinta kasan ba karamin kunya ta ji ba, cikin sanyin murya yace "Karba" a hnkli ta sa hannu ta karba yace "Promise xa ki dinga yi, atleast thrice daily" k'asa cewa komae tayi sae gyada masa kai da take, yace "Toh tafi ki kwanta, gudnyt" da kyar ta Mike ta juya ta nufi kofa ta fita. Komawa yyi ya kwanta, yasan hkurin sa ya gama karewa kuma yyi hkn ne don bae son ya wahalar da 'yar baiwar Allahr, hkn da yace tayi xae rage mata wahalan ssae, duk da ya ga alamar bata da gardama xata basa hadin kai, da yawan mata na daukan 1st nyt so personnel, abeg its nt oo, a novel kadae ne ake maida shi hkn, don sae kinyi niyar wahalar da kanki xa ki wahala. Ana saura kwana hudu Fadila su fara jarabawa ya shigo bedroom dinta da daddare bayan ta sallamesa ta kai masa coffensa ta dawo tana karanta biology dinta, tayi Mamakin ganinsa don indae ta kai masa coffee da ya gama sha yake kwanciya, ya xauna gefen gadon cikin sanyin murya yace "Tafi ki yi alwala Fadila" a hnkli tace "Alwala" ya ce "Eh" mikewa tayi ta ajiye takardan hannunta ta nufi bayi, ba a dau lkci ba ta fito ya shimfida darduma yana kallonta yace nafila xa muyi, bata ce komae ba ya ja su sllhn, sun dde xaune yana addu'a kafin ya juyo ya kalleta ya dafa kanta ya lumshe ido ya shiga yi mata Addu'a. A hnkli ya mike ya d'ago ta ya xaunar da ita gefen gado ya cire mata hijab din jikinta yace "Kiyi kwanciyar ki" kwantawa tayi kmr ynda yace mata sae dae gabanta faduwa yake ba kadan ba, tana ji ya cire jallabiyan jikinsa ya kwanta gadon shi ma, kashe wutan dakin yyi, a hnkli ya mirgino ya dawo kusa da ita ya jawota jikinsa, cikin sanyin murya yace "Fadila" a hnkli tace "Um" cikin sanyin murya yace "Kin amince mu raya sunna daren yau Fadila?" Duk da ynda gabanta ke faduwa hkn bae hanata gyada kai kmr kadangariya ba, ya lura da irin bugun da xuciyarta ke yi a hnkli yace "baxan cuce ki ba Fadila, I promise" nn ma kai kawae take gyada masa hawaye na sakko mata, ya juyo da ita ya lumshe ido ya hade bakinsa da nata ranan kuma ce rana ta farko da ya fara yin hkn, romantically ya shiga kissing dinta ta tsaya bbu gardama, a wnn daren ya mayar da fadilarsa cikakkar mace, iyakar daurewa ta daure, ta bashi tausayi ssae, ya ji sonta ya karu xuciyarsa, Washegari garau ta tashi don ya bata duk taimakon da take bukata a daren, advantage din auren doctor knn Lol.
Years ltr.
Dr Aliyu Shariff ne yyi parkin a parkin lot din dake gidansa ya fito, dai dai lkcn da Afeefah ma ta bude back sit ta fito daga motar ta shiga kkrin fiddo kids dinta, Karasowa yyi ya taimaka mata ya sauko da boyz din daga cikin motar su hudu, Arshaq dan shekara shidda me sunan late dad dinta wato umar ne ya dinga jan mayafin jikinta kmr xae yi kuka yake cewa "Mommy ni ban ga daddy ba, he left us and go, tell him to come back plss," Dr Sharif yyi murmushi ya dafa sa yace "C'mon big boy, tot yhu said yhu were hungry or ain't yhu any more, mu je momy ta baka noodles daddy na xuwa vry soon, d'an daddy" Afeefah ta tabe baki tace "Kai ma ka kula sa Dr" Sir Haiydar me sunan Dr Aliyu d'an shekaru takwas a duniya tuni yyi gaba ya bar su tsaye gun kmr ya san Inda xa shi din nn tsabar miskilancin yaron, halinsa tsaf na Dr Aliyu Sharif, bbu abinds ya mance bae dauka ba na halin me sunan na shi, so so gentle, smart nd brilliant, Afeefah ta bude baki tace "Ji min Yaro, ina kasan xa ka, C'mon come back" dariya Dr Sharif yyi yace "ji min Mata, Mutum da gidansa kice bae san inda xa shi ba, ko kin manta gidansa ne nn din" dariya ita ma tayi tana kallon dan baturen d'an nata da ya juyo yana kallonsu kamanninsa sak babansa. Fadila ce ta fito daga balcony ta taho da sauri ta rungume yayar tata cike da farin cikin ganinta tace "Wayyo Antyna har na gaji da jiran ku, sannun ku da xuwa" Afeefah tayi dariya tace "A'a ni dae kar ki kada ni" Fadila tace "Ina yayanmu fa" Afeefah tace "Xae shigo anjima" kama hannun Ashraf me sunan Abbansu wato Mahmoud tayi tana rungume da yayarta har lkcn suka nufi cikin gida, Dr Shariff ya bi bayansu rike da Arshaq da Sudais me sunan Abban kaduna, saukansu knn Abuja daga Lagos, Aliyu xae xo wani aiki ta takura sa sae ya taho da su don tana son ganin 'yar uwarta, Dr Sharif ne yaje dauko su airport, Aliyu kuma ya tafi yin abinda ya kawosa, in ka ga Zainab ka rantse kace ba ita bace, duk ta ajiye yarinta da kuruciya ta xama babban mace uwar maxa, bbu mai jin kansu da yayanta rabin ranta, suna xaune lfya cike da kaunan juna da 'ya yansu maxa, shekaran da ya wuce ta kare karatun ta na Bio chem, sae dae Aliyu bae yrda tayi aiki ba, bata kuma damu ba don bbu abinda ta rasa gun mijinta sirrinta, Fadila ma 'ya yanta uku ynxu 'yan biyu maxa da mace takwarar Zainab, ita ma suna xaune lfya da mijinta me sonta me kaunarta kmr ransa, Abba kam 'ya ya matan da yake ki a da duk sun cika masa gida da jikoki maxa, don Jiddah ma duk 'ya 'yanta maxa ne, hka ma Rahmah, Mami kullum cikin gode Allah take da ya axurtata da 'ya 'ya mata, Gasu duk xaune gidan maxajen su hankali kwance, so da yawa ta xauna in ta tuna wahalar da tayi a baya sae kwalla ya kawo mata tayi murmushi tace 'ya 'ya mata Rahamah ne.
Da hka nake kara maimaita cewa Duk _'YA MACE KYAUTAR ALLAH_ ce ga wanda bae sani ba.
Alhamdulillah a nan na sauke littafi na me taken 'ya mace kyautar Allah, kuskuren da nayi a ciki Allah ya yafe min.
Story $ Editted by My humble Khaleesat Haiydar (Miss Perfect) Lol
Written By Ashmaad (Eeshatullah Goni) my greetings goes to our fanz round the globe. We love yhu ol.
Mun sadaukar da littafin nn xuwa ga ko wace 'Ya mace round the globe.
Copied by Umar Dalha
Compiled by Princess Aysha Muhammad