Showing 36001 words to 39000 words out of 116554 words

Chapter 13 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1271

bayanta ta mika mata ta karbesa ta fita daga kitchen din. Misalin sha daya Amina ta gama duk girke girken da xata yi ta bar kitchen din. Afeefah na kwance tana rungume da Fadil dake ta wasa a jikinta Amina ta bude dakin da sallama ta tsaya daga bakin kofa tace "bani shi xae ci abinci" mikewa Afeefah tayi ta kai Mata yaron ta karbe sa ta juya ta fice. Amina na fita Afeefah ta jawo wayar Ma'aruf dake gunta har lkcn, taga alamar private sim dinsa ne shiyasa bata ga an kira ba, nmbr Dr Sharif tayi dialing, yana dagawa ta gaishesa a hnkli, ya amsa yace "Kin tashi lfya Zainab?" Tace "um" yace "ina hanya fa" ta wara ido tace "da gske sir" yace "yea ko in koma" da sauri tace "A'a," yyi murmushi yace "to sae na xo" ita ma tayi murmushin tace "Allah tsare hanya" tana ajiye wayar jikinta yyi sanyi, to ya ma xata gaya ma ya Ma'aruf xata yi bako, ga matarsan nn da bata da kirki.

Mikewa Afeefah tayi daga kwancen da take jin har an tada sllhn Azahar ta nufi bayi tayi alwala ta fito, ko da ta idar da sllhn kayanta ta ciro don ita tsoron kwalliya ma take a gidan tun kayan baccin jiya ne jikinta duk da tayi wanka, ta dan yi shafe shafenta snn tasa wani gown dinta na material ta maka dogon hijab a kai ta koma ta kwanta, Amina ce ta bude kofar dakin tace "ki je ki dauki abincin ki kitchen fa" to kawae Afeefah tace mata, Amina ta rufe kofar, bayan minti talatin Amina ta kuma bude kofar dakin tace "baki sauka kin dauki abincin ba kuma" mikewa Afeefah tayi da sauri ta nufi kitchen a sanyaye, Aminan na biye da ita a baya ta nuna mata abincin nata da ta ajiye Mata kan faranti da drink da ruwa snn ta juya ta fita kitchen din. Plate Afeefah ta dauka ta bude shinkafar don ba iya cinye duka xata yi ba, ta dibi kadan ta bude miyar ta diba, kaji ta gani a daya kulan dake kan farantin ta dauki daya, coslow din ma bata diba ba ta dauki ruwa maimakon drink snn ta fita daga kitchen din ta haura sama. Kasa cin abincin tayi ta dan cakalkala ta mayar kitchen tana neman bolan xubarwa, bell din gidan aka danna sae da ta dan tsorata ta fito daga kitchen din da sauri rike da abincin don kar Amina ta gani, kallo daya Amina tayi mata ta nufi kofa tana rike da Fadil murmushi dauke fuskarta, Afeefah ta koma kitchen din kmr xata yi kuka, ita dae ta kawo kanta, da ta sani da bata fara bin ya Ma'aruf ba, Amina na bude kofar ta rungume yayanta cike da farin cikin gninsa, rankwashi Dr Sharif ya kai mata yace "kina ma da hnkli kuwa, kada ni xa kiyi" dariya ta kyalkyale da tace "kai yaya, kaga ynda ka canxa kuwa yayana, welcm big bro nah," murmushi yyi ya karbi yaron hannunta ta basa hanya ya shigo falon, Afeefah kam kasa kwakkwaran motsi tayi a kitchen din jin kmr muryar Dr Sharif take ji a falon, ga kamshin turare irin nasa da ya gauraye gidan, Amina kuwa baki har kunne ta ga yayanta da take bala'in so, Dr Sharif ya xauna yana rike da Fadil yace "ina Captain din?" Tace "wllh ya fita tun daxu yaya, amma nasan yana hanya ynxu," kitchen ta nufa da sauri sae ta ga Afeefah a tsaye, dauke kanta tayi ta dauki faranti da glass cup ta bude fridge ta fiddo drinks da ruwa ta daura kai ta fice daga kitchen din tana cewa "yaya ina momyna da fateema, meyasa ba ka xo min da teema ba" yace "suna gida, idan kina son ganinsu ae sae ki je kanon" tace "Ayya yaya dama wllh kila next wk xan tafi kanon sae ga shi kace min xaka xo" hiran yaushe gamo suka dinga yi da yayan nata don sun kusa shekara ba su hadu ba, mikewa tayi tace "bari in hado maka coffee yayana, nasan kuna tare har ynxu" murmushi yyi ta nufi kitchen, wnn karan da mmki take kallon Afeefah dake tsaye har lkcn a kitchen, a dan fusace tace "wae ke me kike yi a kitchen a tsaye ne" bata jira cewarta ba ta shiga yin abinda ya shigo da ita kitchen din, hawaye ya cika idon Afeefah, Amina na fita daga kitchen din ita ma ta fita a sanyaye tana rike da plate din abinci har lkcn, assuring kanta ta shiga yi cewar ae da Dr Sharif ne ya xo Kaduna da ya kirata tasan Mae irin muryarsa ne kawae, tana fitowa daga kitchen din suka yi ido hudu da shi, sake plate din shinkafar hannunta tayi a kidime ta juya da sauri xata koma kitchen din sae kuma ta nufi stairs da gudu kmr munafuka, ya bi ta da kallon mamaki, Amina ta mike da mugun mmki ita ma ta bi ta da kallo snn ta maido da dubanta kan shinkafar kan tiles tace "anya yarinyar nn na da lfya ma kuwa, ba da ni ba wllh" wayarta ta shiga nema don kiran Ma'aruf, murmushi kawae Dr Sharif yyi yana shafa kansa yace "wa xa ki kira?" A fusace tace "Baban Fadil xan kira mana, do ni bnsan ko tana da iskokai ba yarinyar bbu ruwana, Dubi fa abinda tayi ynxun nn" Dr Sharif da har lkcn yana murmushi yace "Uncle dinta ne mijin naki" tace "ni bn san ynda suke ba, jiya ya kawota" Dr Sharif yace "kira min ita" bata fuska Amina tayi tace "tayi maka me yaya, ka rabu da ita ina jin ba ita kadae take ba" hararanta yyi yace "nace ki tafi ki kira min ita" sama ta nufa ba don ranta ya so ba ta shiga dakin da Afeefah take, ta sameta xaune tana rusa kuka bakin ranta, mamaki ne ya cika Amina, sae abun ma ya kusa bata dariya, ta dake tace "me aka maki kike kuka?" Afeefah ta girgixa mata kai da sauri muryarta na rawa tace "gida xan wuce Anty" Amina tace "to sakko a mayar da ke" mikewa Afeefah tayi da sauri ta dauki jakar kayanta, Amina tace "A'a bar jakar xa a biyo ki dashi daga baya sakko kawae" ba musu ta bi bayanta kmr munafuka ita dae har lkcn bata yarda Dr Sharif ta gani xaune falon ba, suna shigowa falon Afeefah ta shiga rufe fuskarta da Hijab dinta ta nufi kofa da sauri, har ta kusa ba Amina dariya, Dr Sharif yace "Zainab!" Juyowa Afeefah tayi da sauri tana kallonsa har lkcn fuskarta a rufe, kuka ta saki ganin shi din ne, Amina ta shiga kallon yayanta da mmki jin ya kira sunan Afeefah, mikewa yyi ya karasa inda Afeefah take yana murmushi yace "sauke hijab din" saukewa tayi ta sunkuyar da kanta da sauri, ya tsura mata ido snn a hnkli yace "baki son ganina ne kuma" muryarta na rawa tace "ina so" Amina ta kwalalo ido da mugun mmki tana kallonsu, yace "toh share hawayen ki" a hnkli ta shiga share fuskarta yace "follow me," ba musu ta bi bayansa suka koma falon ya xauna kan kujera ita kuma ta xauna kasa gefensa har lkcn taki dago kanta, da mmki Amina tace "yaya kasanta ne dama wae?" Yace "ehh nasanta, student dita ce" Amina ta xaro ido tana kallon Afeefah, murya can kasa Dr Sharif yace "kuma budurwata! koh Zainab?" Afeefah ta rufe fuskarta da hijab da sauri ta daura kanta bisa gwiwanta, Amina ta fashe da dariya tace "kai yayana, wae da gske kke don Allah" murmushi yyi yana kallon Afeefah da ke jin kmr ta nutse wajen, yace "karya nayi Zainab?" Kin cewa komae Afeefah tayi ya sakko nn kasa gefenta ya xauna yana kallonta a hnkli yace "Zainab" murya can kasa tace "um" yace "wae ke ba budurwata bace?" Kin dago kanta tayi, yace "shknn bari in tashi in tafi since yhu re denying me" dago kanta tayi da sauri a kunyace tace "Sirr"


Eeshatullah Goni😘😘

[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

39.....
Dariya kawae Amina take tana kallonsu, Dr Sharif yyi murmushi yana kallon Afeefah yace "to gaya min me ya sa ki kuka?" Shiru tayi bata ce komae ba, ya kuma yi mata tambayar, ta daga kai a hnkli tana kallon Amina, sae kuma tayi saurin sunkuyar da kanta, kallon Aminar Dr Sharif yyi yace "ke kika sa ta kuka knn?" Da sauri Afeefah tace "A'a sir bata min komae ba" Amina ta yo waje da ido ta dawo kusa da su ta xauna tana dariya tace "wllh yaya bn mata komae ba tun jiya da ta xo ta ki sake jiki fa," Dr Sharif ya galla mata harara yace "ke din? Kin sake mata fuska ne bare ta saki jiki?" Amina ta xaro ido ta kuma ta saka dariya tace "Ayya yayana ka tambayeta wllh bn mata komae ba jiyan ma da suka xo ban jin ddi ne" hararanta kawae Dr Sharif yake, Afeefah kam murmushi tayi ta sunkuyar da kai a hnkli tace "ni bata min komae ba kawae gida nake son wucewa" Amina ta yi dariya tace "to ka dae ji, in ma na maki wani abun kiyi hkuri Anty Zainab" sae a snn Dr Sharif yyi murmushi, Afeefah ma tayi murmushin cike da jin kunya, Amina ta mike tace "bari in kawo maka abinci big bro" kallon Afeefah kawae Dr sharif yake har lkcn taki dago kanta, Amina ta dawo falon ta dire kulan abincin ta koma ta dauko sauran, da kanta ta shiga xuba masa a plate, daga kai yyi ya kalleta yace "ita ta ci ne?" Amina tace "bata wani ci na kirki ba, breakfast ma ina kula da ita bata yi na kirki ba" spoon ya dauka ya sa a abincin da Amina ta xuba masa ya dauko ya ajiye gaban Afeefah yace "oya start eating ynxu" murmushi tayi hade da girgixa masa kai tace "Um na koshi sir" hararanta yyi yace "C'mon" bata kuma yi masa musu ba, ta dauki spoon din a hnkli, Amina ta xuba masa wani tana murmushi tace "bari in baku waje sir" daukar Fadil tayi tana dariya ta haura sama. Kasa cin abincin Afeefah tayi tsabar yanda yake kallonta ga wani mugun kunyarsa da taji tana ji, murya can kasa yace "Zainab!" Ba tare da ta dago ba tace "um" yace "kunya ta kike ji ne wae?" Gyada masa kai tayi, yyi murmushi ya soma cin abincin sa, ganin taki ci ne yasa yace "to tafi sama ki je ki ci" da sauri ta mike ta dauki abincin ta nufi stairs ya bi ta da kallo. Fitowa Amina tayi jin Afeefah ta bude dakin da take ta shiga dakin tace "har kin gama cin abincin" murmushi Afeefah tayi tace "a nn xan ci" dariya tayi tace "kunyar sir din naki kike" sunkuyar da kai Afeefah tayi da sauri, Amina ta ajiye Fadil kan gado tace "ga Fadil nn toh" juyawa tayi ta fita daga dakin ta koma gun yayanta, kallo ta samesa yana yi tace "yaya ae abincin xae huce" yace "eh jira nake ya huce dama" tace "wae da gske yayana budurwar ka ce Zainab" ba tare da ya kalleta ba yace "gashi na fada gaban ki" murmushi tayi tana kallonsa don har tayi aure bata taba jin yyi maganan mace ba don cewa yake ba su ne gabansa ba, lallai Zainab tayi sa'a, jin tayi shiru yasa Dr Sharif ya daga kai yana kallonta, tayi masa murmushi tace "na taya ka murna yayana, Allah baka Zainab! don yarinya ce me hnkli daga jiya na lura da hkn ga sanin ya kamata" murmushi yyi yace "Ameen ya Allah"

Har karfe uku suna hira da yayanta ya Ma'aruf ya shigo falon, yana dariya yace "Dama ana ganin ka bokan turai, baka da kirki Haiydar ko kira bbu fisabilillah" Dr Sharif yace "ae kai naga kana kiran, ba dae mun baka mata ba dole ka mance mu" dariya Ma'aruf yyi yace "ka ji gori koh, ke Amina kira min Zainab shi ma in basa Kanwata ko xan samu sakat" dariya Amina tayi tace "to ae budurwarsa ce Zainab din" Ma'aruf yace "kai Haba a ina ya san ta? Wae da gske Dr" Mikewa Dr Sharif yyi yana murmushi yace "wnn ba Matsalar ka bace" excusing kansa yyi ya fita don amsa wayarsa, Amina tayi dariya tace "a kano ya san ta" bayani tayi ma Ma'aruf ynda suka hadu da Afeefah, Ma'aruf yyi dariya yace "to in ji kin daina kishi da ita ynxu dae koh? Don kinsan ko ina son Zainab ynxu ya xama dole in bar ma wnda ko auren ma bae taba ba sbda halaccin da yyi min" dariya Amina tayi ta kai masa duka tace "kai dear! hka nace maka ina kishi da ita" yace "ahaf sae dae idan ba Aminar da na sani bace" tayi dariya tace "uhm ae ynxu Zainab ta xama Anty"

Ko da Dr Sharif ya dawo mikewa Amina tayi ta bar masu falon ta haura sama, Ma'aruf yana kallon Dr Sharif yace "ashe dae Kanwata kke so, ya xama dole in maka halacci in sa a baka" Murmushi Dr Sharif yyi yace "Allah sa ku banin dae" Ma'aruf yace "Serious in har da aure kke son ta an gama" Dr Sharif yace "Da aure nake sonta mana" Ma'aruf yace "ka shirya auren ne ynxu?" Dr Sharif ya shafa kansa yace "Ae karatu take ynxu, it won't b fair in katse mata karatun ta" Ma'aruf yyi murmushi yace "ka manta Amina na karatu ku ka bani ita" Dr Sharif yace "hka ne but bn san ko xa ayi mata aure ynxu ba, naga yayyinta mata ma basu yi auren ba" Ma'aruf yace "kai dae ynxu kke son auren ko ba ynxu ba?" Dr Sharif yyi shiru yana kallonsa snn yace "idan xa a bani" Ma'aruf yace "kar ka damu, aurensu ilham nn da 'yan watanni ne, xan yi convincing Abba ya hada gaba daya idan har yhu re jet serious coz nasan halin ka Haiydar" Sauke ajiyar xuciya Dr Sharif yyi yace "wllh da aure nake son Zainab, amma bari in maka tambaya daya, ya ku ke da Zainab? kuma ka gaya min gskyan wani irin dangantaka ne tsakaninta da Aliyu, tace min dad dinsu daya, hka ne?"

Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

40.....
Shiru Ma'aruf yyi yana kallon Dr Shariff snn yace "Hka tace maka dad dinsu daya?" Dr Sharif ya gyada masa kai, Ma'aruf ya dan tabe baki yace "I wonder y they are still hiding things for the innocent girl, ba dad dinsu daya da Aliyu ba but don't tell her dat" kasa ce masa komae Dr Sharif yyi, can dae da kyar yace "to ya suke da shi? Nd y are they hiding it for her? Kana nufin shi ba dan gidan bne knn?" Ma'aruf yace "No! Ita ce ba 'yar gidan ba, ynxu dae mu bar xancen nn, ka bn go a head in yi ma dad maganan?" A sanyaye Dr Sharif yace "Baka gaya min ynda ku ke da ita ba" Ma'aruf yace " yar Kanin dad dina ne, her father is late" da mmki Dr Sharif yace "bn gne ba, make me understand plss, then wat is she doin in kano, mum dinta fa, kana nufin ba iyayenta bne a kano?" Ma'aruf ya sauke ajiyar xuciya yace "Ka ga da mu bar wnn xancen kawae Dr, she knw nothin about ol dis dat am sayin, infact duk gidansu bnda Aliyun da Adnaan sae yayyinta mata biyu da suka yi aure bbu wnda yasan ba yar gidan bace ita, kuma baxan so ta ji a bakina ba ko a gidana, in dae kana son Zainab da aure da gske ka kwantar da hnklin ka am there for yhu, ltr xa mu je mu samu dad am sure he will b vry happy don shi indae mace ta fito da miji aure yake mata bae jiran sae ta kare karatu kmr ynda dad dinsu Aliyu ke yi, tashi mu tafi masallaci, almost tym 4 sallat" har suka dawo daga masallaci Dr Sharif was nt him self, dama yasan ba biological brothern Afeefah bne Aliyu, ya ga alama da ddewa, Ma'aruf ya haura sama ya bar sa nn xaune yana ta sake sake, he is afraid of loosin Zainab, yasan tun daga randa ya fara sauke idonsa ya ji sonta, abinda bae taba faruwa da shi ba, da farko he was thinking tausayinta kawae yake don yaga alamar tana da rauni ga saurin hawaye, daga baya yaga ba hka bne don duk randa bae daura ido kanta a sch ba bai jin ddi, nd he is matured enuf ba sae wani ya gaya masa ya fada tarkon son Zainab ba, sauke ajiyar xuciya Dr Sharif yyi don yasan Ma'aruf will Neva let him down. Amina ce ta shigo dakin da Afeefah take ta ganta kwance tana bacci, tada ta tayi tace "lallai ma Antyn nn sae ki xo kiyi kwanciyar ki a nn kina bacci ki bar bakon ki a falo" mikewa xaune Afeefah tayi tana mitsika ido, Amina ta mata murmushi tace "to tashi ki kara shiryawa ki je ku yi hira, yace min sbda ke ma ya xo kano" Kai Afeefah ta gyada mata kawae ta juya ta fita, Afeefah ta mike ta shiga bayi, wanka ta kuma yi tayi alwala ta fito tayi la'asar, snn ta yi shafe shafenta, ta fiddo da wani riga da skirt dinta na atamfa ta sa, ba karamin kyau kayan yyi mata ba, tana kkrin sa Hijab Amina ta shigo dakin, xaro ido tayi tace "ko yar powder baxa ki shafa ba" murmushi kawae Afeefah tayi bata ce komae ba, Amina ta kama hannunta tace "xo mu je dakina ki shafa" bin bayanta Afeefah tayi suka shiga bedroom din Aminar ta xaunar da ita gaban madubinta, kwalliya ta shiga rangada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login