Showing 93001 words to 96000 words out of 116554 words
lkci daya hawaye ya shiga sakko mata har da sheshsheka, wani message din ta kuma yi masa tace "Ka kula ni don Allah ba don ni ba yayanmu, reply me plss nah," daga hka ta ajiye wayar tana ci gaba da kukanta, duk abun duniya ya taru ya mata yawa, har sha biyu neman bacci tayi ta rasa, ta kuma jawo wayar ta bude whtspp ae ko ta ga ya mata reply da "Hm" wani mugun ddi ya lulubeta ta mike xaune da sauri kmr wanda ya mata maganar arxiki, ta tura masa reply kmr hka "Yayanmu me nayi maka baka son ka kula ni plss" ganin datan sa a kashe yake yasa ta kashe ita ma ta ajiye wayar cike da jin ddin d'an reply dinsa, daga hka bacci me ddi ya dauketa ta mance da damuwarta. Washegari Thursday ta tashi cike da farin ciki ita fa yayanta yyi mata reply, tana idar da sllh ta jawo wayarta da sauri ta kunna data ta hau whtspp, taga bae hau ba har lkcn, ajiye wayar tayi ta mike ta shiga wanka. har takwas saura bata ji fitar Dr ba gashi tana son sauka ta nemi breakfast don Karfe takwas da rabi take da lecture, mikewa tayi daga karshe ganin har takwas tayi ta sa hijab dinta ta fita daga dakin, kwance ta samesa falo yana kallo, kmr munafuka ta karaso cikin falon tace "Ina kwana sir" yace "Lfya lau" daga hka ta nufi kitchen ta dauki indomie daya a store, cikin 'yan mintuna ta fito daga kitchen rike da plate din indomie da kwae sae cup din tea, bin ta yyi da kallo har ta haura sama, ya girgixa kai ya ci gaba da kallonsa, takwas da rabi ta sakko rike da jakar makaranta ta shigo falon tana kallonsa tace "Sir in je gida gun Mamina d'aga sch yau?" Juyawa yyi yana kallonta kafin yace "No!" Ta hade rae tace "Sbda me sir" ba tare da ya kalleta ba yace "Nace baxa ki ba" juyawa tayi fuu ta fice daga falon kmr xata tashi sama, ya bi ta da kallo kafin yyi murmushi ya kauda kansa. Suna xaune da Maryam karkashin bishiya sun fito daga lecture ta fiddo wayar ta ta bude whtspp tana duba messages dinta, gnin message din yayanta da tayi ba karamin murna ya sa ta ba, ta bude da sauri taga kmr hka "Ykk" Maryam ta lura da yanayinta tace "Ko kudi sir ya tura maki acc wnn farin cikin" murmushi kawae tayi bata tanka ta ba, ta tura masa reply tace "yayanmu ka gaya min garin da kke plss" tana tura masa ta mayar da wayar jaka tana murmushi tana kallon Maryam tace "Me ma kika ce"
Daga wnn lkcn Yayanmu bae kuma hawa online ba, nn fa Afeefah aka dawo gidan jiya a damuwa, duk ta rasa me ke mata ddi gashi nmbrsa baya shiga as alwayz. Yau asabar tana kwance daki abun duniya ya isheta ga ciwo da cikinta yake alamar period dinta, Dr Sharif ya shigo dakin, tun Thursday rabonta da sa shi ido, ta mike xaune ya karaso ya xauna gefen gadonta yace "Frnds dina xa su xo anjima, nd am beggin yhu for d sake of Allah ki sakko ki tsaftace gidan ki Zainab" ta dan turo baki tace "To wa xae taya ni" shiru yyi yana kallonta kafin yace "OK xan taya ki taso mu je" tace "To" snn ta mike ta dauki kaya mara nauyi a wardrobe dinta ta shiga bayi don cire atamfar jikinta, bin dakinta ya shiga yi da kallo ko ina kyalli yake tsabar gyara amma ta bar masa falo duk kura, yasan kitchen ma darajar tana girki cikinsa yasa take tsaftace shi, gnin bata fito daga bayin har kusan minti goma knn yasa ya mike ya nufi bayin ya tura kofar, tsaye ya ganta gaban mirror daga ita sae undies tana kkrin daure gashinta guri daya amma ta kasa sbda cikansa, xaro ido tayi a tsorace ganinsa ta durkushe wajen kmr xata yi kuka tace "Meye hka sirrr" shigowa bayan yyi ya jingina da kofa ya rungume hannayensa yana kallonta, ta saka kuka tana cewa ita dae ya fita, karasawa kusa da ita yyi ya dago ta, ta fasa masa ihu, kasa daina kallon kyakkyawan suran jikinta yyi ga ta fara ssae, tuni jikinta ya dau rawa tana kare kirjinta ganin kallon da yake mata, ya hade ta da bango lkci daya yanayinsa ya canxa, ta fashe da kuka tace "Don Allah ka tafi sir ka ga kayana xan sa plss ynxu xan fito" rungumeta yyi ya dago kanta a hnkli ya hade bakinsa da nata, duk haukanta yau ba sarara mata, baya ma gane abinda take cewa kawae, ganin abinda ke sakkowa kafarta yasa ya ji wani takaici don bae yi niyar kyaleta yau ba, da kyar ya saita kansa bayan ya dakatar da abinda yake mata ya mike yyi saurin ficewa da bayin. Ita kanta bata san me yasa ya kyaleta ba jikinta na rawa ta mike, sae snn ta ga abinda ya gani, wato period dinta ne ya xo mata. A sanyaye ta gyara jikinta ta fito daure da tawul, ta xauna gefen gado har lkcn jikinta na faduwa. Ta kusa minti talatin xaune kafin ta mike ta dauki kayanta ta sa tana kallon agogo ta ga sha daya da rabi, sae bayan Azahar ta fito daga dakinta jiki a sanyaye har lkcn bbu kowa falon, hkn yasa ta nufi kitchen ta dauko sweeper da mop da bucket dinsa ta fito falon, shara ta soma yi, ta share ko ina na babban falon kafin ta fara mopping din falon, kusan awa daya ya dauketa kafin ta gama snn ta soma goge gogen kayan wutan falon, ko ina ya dawo sae sheki yake gwanin sha'awa, dakinta ta tafi ta dauko burner da turare ta dawo falon ta kunna, tana durkushe kusa da turaren ya sakko downstairs cikin kananan kaya, tsayawa yyi jikin stairs din ya rungume hannayensa yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Ko ke fa Matar Dr" k'asa kallonsa tayi don wani mugun kunyarsa taji tana ji, ya karaso cikin falon ya durkusa gabanta ya dago kanta yace "Sannu wife, Allah maki albarka" murmushi kawae tayi bata ce komae ba, ya mike yace "xan je can gida, xuwa anjima xa mu dawo tare da frnds din nawa" kai ta gyada masa yace "Kin ci abinci?" Tace "Ynxu xan ci" yace "OK sae na dawo" daga hka ya nufi kofa ya fita. Afeefah na gama aikin ta shiga kitchen ta daura girkin jollof snn ta koma sama. Wayarta ta dauka ta kwanta ta bude whtspp tana dubawa ko ya Aliyu ya hau, kmr a mafarki ta dinga kallon message din da yyi mata yace "Kin fi kowa sanin garin da nake Zainab, ya su Mami da Abba" ddi kmr ya kasheta ta mike xaune da sauri tana kallon lkcn da yyi Mata message din taga ko awa biyu bae yi ba, reply tayi masa hannunta na rawa tace "Don Allah yayanmu ka dawo we are missing yhu plss," ta tura masa hade da emoticon din kuka, ga mamakinta sae ta gansa online, bayan kusan minti biyar ya bude message din ya kuma dau lkci kafin ya mata reply da "OK" bata fuska tayi gnin reply din, daga hka kuma ta ga ya sauka, a sanyaye ta ajiye wayar ta kwanta hawaye cike idonta. Bayan la'asar tana kwance tayi nisa tunaninta taji shigowar motar Dr Sharif, gyara kwanciyarta tayi bayan minti biyar ya shigo dakinta yace "Sakko ku gaisa da frnds dina" turo baki tayi bata ce komae ba ya juya ya fita, hijab dinta ta dauka ta sa ta sauko falon ta samesu su kusan biyar xaune falon, biyu kadae ta sani cikinsu don lecturers dinta ne, cike da jin kunya ta duka har kasa ta gaida malaman nata da abokansu, suka amsa da fara'a suna tambayarta ya gida, Malam Nasir yace "Student din mu sarauniyar kuka knn," murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, sauran duk suka yi dariya, daya malamin nata yace "A'a ni bn taba ganin tayi kuka ba, Zainab is among our best student or rather in ce mine, don ban san ko kuma hka ba ne a gun ku" Murmushi Dr Sharif yyi yana kallonta yace "Lallai kam, gwara da ka gyara sentence din ka" Malam nasir yyi dariya ssae yace "Ka ga mijinta ya karyata hkn don yasan waye matar sa, bnda kuka da shiga cafeteria bbu abinda ta iya fa, sae in iya irga shiganta aji na nawa duk don ina bada assignment" dariya kawae Dr Shariff da malam nasir suke, ita kuwa rufe fuskarta tayi cike da jin kunya, ganin va daina tsokanarta xa su yi ba yasa ta mike ta bar masu falon ta shiga kitchen ta dauki faranti ta dauro glass cup da drinks da ruwa ta fito ta ajiye masu, ta nufi gun Dr ta durkusa kusa da shi kmr me rada tace "In xubo masu abinci sir?" Kallon abokan nasa yyi yace "Wae a xubo maku abinci" duk suka ce Alhmdllh drinks din ma ya isa, daga hka ta haura sama ta shiga daki tayi kwanciyarta. Da suka tashi tafiya misalin biyar da rabi ya shigo dakinta ta xo tayi masu sallama, ko wannensu ya bata kudi me yawa sae dae bata amsa ba sae ajiye mata suka yi kan centre table, gdya tayi masu a kunyace kafin su fita ya rakasu. Tana komawa daki wayarta ta dauka don duk ta kasa samun kwanciyar hnkli kan ya Aliyu, tana bude chat ta gansa online ta tura masa message kmr hka "yayanmu" bayan kusan minti goma taga bae mata reply ba tayi masa whtspp cal ya ki dagawa, can yyi mata reply yace "Little sis" xaro ido tayi lkci daya tayi murmushi ta mayar masa reply "Don Allah yayanmu ka kira ni da nmbrka ynxu xan gaya wani abu" ba a dau lkci ba ya maida Mata yace "Me xa ki gaya min?" Tace "Ka kirani in gaya maka plss" "Hm" ya mayar mata kafin ya sauka, ta xuba ido ta ga kiransa amma shiru, tafi minti talatin tana jira amma shiru still, kmr xata yi kuka ta kuma logging ta tura masa emoticon na fushi, taga ya ma kashe data, kuka ta saki kmr karamar yarinya kafin ta tura wayar daga kusa da ita. Washegari Sunday ta tada fitinan ta ita gida xa ta, ya share ta bae tanka ta ba, daga karshe bangarensa ya koma ya bar ma ta falon, ta bi bayansa tana hawaye, a falonsa ya kwanta yana ganinta yace "Yhu are disturbing me Zainab, let me rest plss" cikin kuka tace "To ni nace maka xan je gidanmu" mikewa yyi ya bar mata falon ya shige bedroom, ta bi sa da sauri, bude baki yyi yana kallonta, ta rungume hannayenta tana kuka, murmushi yyi ya jawo study desk dinsa ya dauki medicated dinsa ya sa kafin ya dauki wani babban text buk yasa gaba yana dubawa. Ta fi minti ashirin a tsaye har sannan a dakin, ya mike kmr xae dauki abu a gaban mirror ya fixgota, ta xaro ido tace "Don Allah kayi hkuri xan tafi wllh" bakinsa ya hade da nata, da kyar ta samu ta kwace kanta ta fice da gudu. Da yamma kmr wasa tace bari tayi tryn kiran Aliyu da nmbrsa ta UK da sabon sim dinta don a shi kadae take da airtym, ga mmkin ta taji ya shiga, ta xaro ido ta mike xaune gabanta na faduwa, ya dan dau lkci kafin ya daga, cikin sanyayyan muryarsa yyi sallama, amma ta kasa amsawa tsabar murnar jin muryarsa kuma tana tsoron kadda ya katse idan yaji ita ce, yace "Hello" nn ma ta ki cewa komae ya dan yi jim kafin ya katse wani tsalle ta doka cike da jin ddi dae dae nn Dr Sharif ya shigo dakin ya kalleta gnin mood dinta yace "Duniyar ta maki ddi knn koh?" Turo baki tayi bata ce komae ba, yace "ki shirya sae ina kai ki gidan amma baxa ki dde ba" mikewa tayi tace "Toh" wasu kayan ta fiddo ta nufi bayi ya bi ta da kallo har ta shiga ta sa key, murmushi yyi ya juya ya fita daga dakin. Grocery suka fara biyawa ya siya fruits da za su kai can gidan kafin su kama hanyar gidan, Karfe biyar suka shigo falonsu ya xauna kan kujera ta haura sama don bbu kowa falon, dakin Mami ta shiga, ta sameta ita da su jiddah ta rungume ta cike da jin ddin ganinta, Mami tace "Daga ina kike?" Tace "Shi ya kawo ni Mami yana falo" Mami tace "Sannun ku da xuwa" tace "Mami yayanmu fa?" Mami ta mike tace "waye kuma yayanku?" Kmr xata yi tace "Ya Aliyu mana" hararanta Mami tayi ta dauki hijab tace "Baki lura da shi a bayana ba knn" tana kai wa nn ta fice don xuwa su gaisawa da sirkin nata, Afeefah tuni har hawaye ya cika idonta tana kallonsu jiddah tace "Anty jiddah kuna waya da shi?" Jiddah ta girgixa kai tace "A'a amma yana UK, kuma muna chat da shi" jin hka ta warce wayar jiddah da sauri ta fice daga dakin ta shige nasu tuni jiddah ta mike tana cewa ta bata wayarta, Afeefah ta sa key a dakin kafin ta bude wayar ta hau whtspp da sauri, chat din ta shiga dubawa tun daga farko, ssae ta ga yake chat da 'yar uwar tasa kusan kullum, ga mamakinta sae ta ga kusan kullum din sae ya tambayi Jiddah ko sun hadu da ita a sch, jiddah tace suna haduwa kuma ko da yaushe tana tambayarsa, murmushi ya tura mata yace tana masa text ko da yaushe amma bae fiye mata reply ba yana daurewa yyi ignoring dinta, tambayarsa jiddah tayi "Sbda me" ya mayar mata yace "Sbda tana fama min ciwon da yaki warkewa a xuciyata, I just can't bear it sister, i alone knws wat am going through ynxu, all d same ina jin ddi idan na ga text dinta, it soothe me, jiddah ta tura masa fuskar tausayi tace "Kawae kayi blockn dinta yayanmu xae fi" yace "Koh?" Ta mayar masa tace "Allah kuwa" yace "OK I will giv dat a try" jikin Afeefah yyi sanyi ssae, lkci daya hawaye ya cika idonta, A chat din su na jiya ne taga Jiddah na tambayarsa lkcn da xae dawo don Allah, ya mayar Mata yace "Xan dawo amma sae nn da shekaru bakwae idan Allah ya yrda, kafin nn No pain, no scar a xuciyata, yea duk sun goge in'sha Allah, but tsakanina da ke ne wnn kar ki gaya ma ko Mami" Jiddah ta tura masa emotion na rashin jin ddi tace "Kayi hkuri yayanmu, kar kace har seven years Plss, just forget ur pass nd face future plss ka kaddara dama Zainab ba matar ka bace a rubuce, Allah xae maka musanyar alkhairi, kila ma ita din ba alkhairi bace gare ka shi sa Allah bae baka ba, Allah xae baka Wacce ta fita, plss yayanmu ka dawo gida, its high time kai ma kayi auren ka ynxu kayi settle down, Zainab ta xama past tense gare ka tunda tana xaune gidan mijinta lfya ynxu" ya mayar mata yace "tnx sister, sae ki xaba min matar da kika ga ta dace da ni, I wil accept don ban san ta inda xan fara neman mata ba ynxu" wurgi da wayar Afeefah tayi kan gado ta dinga rusa kukan bakin ciki, bnda bubbuga kofa bbu abinda yayyin nata suke suna kiranta amma ta ki budewa sae kara sautin kukan ta da tayi, muryar Mami da taji ita ma tana kiranta yasa ta mikewa tana kuka ssae ta bude kofar, Mami tace "Lfya me ya same ki?" Rungume Maminta tayi tana kuka ssae tace "Mami kina ganin Anty jiddah take ce ma yayanmu a chat ni ba alkhairi bace gare sa shi sa bae aure ni ba, wae ya manta da ni yayi blocking dina, kuma yyi aurensa kawae" muryarta na rawa ta kare maganar cikin kuka ssae, daga sadiya har Mami suka juya suna kallon jiddah da hanjin cikinta ya kada, Mami tace "Toh sae me, sa ji da munafurcinsu daga ita har shi," wani mugun kallo Mami ta shiga yi ma Jiddah tace "Algunguma kawae munafuka, dole ku nuna mata ba ubanku daya ba, nasan akwae rana irin ta yau da xae xo" daga hka ta ja hannun Zainab suka fice daga dakin tana kuka, ta nufi dakinta da ita ta shiga lallashinta, da kyar ta hadiye kukan, Mami ta Mike ta fita daga dakin bayan ta tabbatar tayi shiru, kwanciya tayi kan gadon Mami tana sauke ajiyar xuciya. Bayan isha Dr Sharif ya dawo tafiya da ita, tana xaune dakin Mami bayan ta dan cakalkala tuwon gabanta Mami ta shigo tace "Tunda baxa ki ci ba tashi ki wanke hannun ki ku tafi mijin ki ya dawo" bata fuska tayi tace "Ni a nn xan kwana Mami" wani kallo Mami ta watsa mata tace "Kin tashi ko sae nayi kwallo da ke, ki kwana ki min me" mikewa tayi hawaye cike idonta ta shiga bayi ta wanke hannu ta fito, Mami tace "Ki tafi ki sallami Abban ku, sae ki deban maku abinci a kitchen" wayarta da jaka da hijab ta dauka fuu ta fice daga dakin ta nufi falon Abba, xaune ta samesa da Dr Sharif, ta sallame Abban suka fito tare da Dr Sharif din, sae da suka sakko downstairs snn fuskarta daure tace "wae xaka ci abinci" girgixa mata kai kawae yyi suka fita daga falon. Tara saura suka isa gida bayan ya biya ya siya gasassun kaji da fura, yana gama parkin ya juya yana kallon jajayen idonta yace "Kukan me kike?" Kmr jira take ta fashe da wani kukan tace "kaga sir ko ba Anty jiddah bace take ce ma yayanmu ta whtspp wae ni ba alkhairi bace gare sa shi sa bae aure