Showing 66001 words to 69000 words out of 116554 words
in gansa mana" hawaye na bin kuncinta ta karasa maganan, Ma'aruf yace "To sae kin yi alkawarin baxa ki je ki daga ma mutane hnkli da kukan ki ba" da sauri tace "Allah" Ma'aruf ya kama hannunta yace "To muje" binsa kawae take har suka fita daga ward din, da ganinta kasan bbu karfi jikinta, A hnkli Ma'aruf ya turo kofar dakin ya shiga tana biye da shi a baya, yana kwance idonsa a lumshe ga drip a hannunsa, a hnkli yake numfashi, Mami ta gani xaune gefensa da saleem, kallo daya Mami tayi mata ta dauke kanta, Afeefah ta karasa bakin gadon a sanyaye hawaye na bin kuncinta tana kallonsa, wani kuka ne ya xo mata Ma'aruf ya janye ta daga jikin gadon yace "Hka muka yi da ke" girgixa masa kai ta shiga yi da sauri, yace "To mu tafi ae Kinga bacci ya ke" cikin kuka tace "A'a kayi hkuri Allah ban gama ganinsa ba" Ma'aruf xae yi magana Dad ya shigo dakin, murmushi yyi ganinta ya karasa kusa da ita ya dafa kanta yace "kin tashi mamata, bbu inda ke maki ciwo koh" kai kawae ta gyada masa hawaye na bin kuncinta, ya kama hannunta suka fita daga dakin xuwa can harabar asibitin, ya samu wasu kujerun roba biyu suka xauna, nn ya shiga lallashinta yana assuring dinta jikin Aliyu da sauki ssae, bacci kawae yake, muryarta na rawa tace "Amma aman jini fa yake yi dady" dad yace "Nace ki kwantar da hnkli mamata ae baxae sake ba, xuwa anjima xa ki ga ya tashi" suna nn xaune har mota ta shigo haraban asibitin, yana gama parkin ya fito, ganin dad yasa ya nufi inda suke xaune dad yace "Har ka dawo Ali" Dr Sharif yace "Eh na dawo Abba," Dad yace "Nawa maganin yake" Dr Sharif yyi murmushi yace "Dubu sha biyar ba dari biyar" Dad ya sa hannu a aljihu yace "Ina da kudi a nn, bari in baka" wani murmushin ya kuma yi yace "Ka bar shi Abba" Dad ya hade rae yace "Kai bana son hka ba ni na aike ka ba wae, gashi" juyawa yyi ya bar wajen yace "Allah ka bar shi Abba" duk ynda dad ya so ya dawo kin dawowa yyi har ya shiga cikin asibitin.
Har Karfe tara da kusan rabi Aliyu bae farka ba, Dr Sharif yyi assuring dinsu sae xuwa can eleven xae tashi, bae kai Karfe goma a asibitin ba yyi ma Dad sallama ya tafi tare da Ma'aruf, gnin har goma da rabi ya kusa yasa dad yace saleem ya mayar da su Momy da Mami gida shi xae kwana asibitin, Momy da Mami na fita dakin dad ya kalli Afeefah dake xaune har lkcn kusa da Aliyu yace "Mamata tashi ki bi su ku tafi gida ki huta gobe sae ku dawo" marairaicewa tayi tace "Wayyo dady ka bar ni nima in kwana nn plss" Dady yace "A'a ku tafi kawae gobe ae xaku dawo da safe" Saleem ne ya kama hannunta gnin har idonta ya cicciko yyi ma dady sallama suka fita don shi xae mai da su Momy gida. Karfe sha daya da minti arba'in dad ya ga Aliyu na jujjuya kai, mikewa yyi daga xaunen da yake da sauri ya karasa kan gadon yana kallonsa, gnin yanda yake rike da kirjinsa yana jujjuya kai yasa dad ya nufi kofa da sauri don xuwa kiran nurse, ji yyi yana ambaton sunan Allah can kasa, dad ya juya da sauri yana kallonsa, lkci daya ya ga ya bude ido ya mike xumbur kmr Wanda aka tsikara lkci guda ya shiga kiran Zainab yana kkrin sakkowa kasa, da hanxari Dad ya koma ya rikesa yana kiran sunansa, girgixa Kai kawae yake yana rike da kirjinsa da yake ji kmr xae tsage ya daura kansa kan kafadar Dad, dad na pat din bayansa a hnkli, sae da ya nutsu snn dad ya dago kansa yana kallonsa yace "Sannu Ali" kasa cewa komae Aliyu yyi sae bin dakin da ya shiga yi da kallo kmr me son tuna abu, lkci daya ya kuma xabura dad ya mayar da shi xae kwantar don ya fita kiran likita, ya rike dad da sauri hawaye ya shiga gangarowa idonsa yana girgixa Kai kmr me son yin mgna amma ya kasa, dad da hnklinsa ya tashi ssae yace "Bari in kira likita ynxu Ali, am coming" kin sake sa still Aliyu yyi muryarsa na rawa yace "Abba, Zainab" da mmki dad yake kallonsa don a iya saninsa he was unconscious ko da Zainab ta suma daxu, dad yace "Zainab kuma, Me ya sameta? Daxun nn suka wuce gida har da Mamin ka Ali" girgixa kai kawae Aliyu ke yi hawaye na sakko masa yace "Abba kar a raba ni da ita don Allah, Abba a tausaya min a bani Zainab, Abba....." Kasa ci gaba yyi ya dafe kirjinsa da ke masa azaba da hannu biyu ya runtse ido, kallon mamaki da confusion Dad ke masa baki bude, wani kara Aliyu ya saki da karfi yana girgixa kai yana rike da kirjinsa da yaji na neman tsagewa, a rikice dad ya mayar da shi ya kwantar da sauri ya nufi kofa xae fita ya ci karo da likita da nurses guda biyu, hanya ya basu suka shigo dakin, kasa tsayawa dakin dad yyi ya fita a sanyaye maganganun Aliyu na masa yawo a ka, me knn? Dad ya fi minti sha biyar a corridor din wards din jingine jikin bango duk jikinsa yyi sanyi likita ya fito yana kallonsa yace "Alhaji mu je office" binsa Dad yyi har suka shiga office din, likitan ya ajiye stethoscope din hannunsa yace "Alhaji wacece Zainab?"
Eeshatullah Goni
Ku dinga hkuri dani pls uxururruka ne suka yi yawa but after gobe in'sha Allah xa ku dinga samun typn ssae.
[5/22, 07:59] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸
By Ashmaad
66......
Shiru dad yyi yana kallon likitan, gnin jiran amsarsa likitan ke yi yasa ya sauke ajiyar xuciya yace " 'yar uwarsa ce Zainab" likitan ya jinjina kai yace "Shawara ce xan baku, in ma hanasa ita aka yi to a bashi in har kuna son lfya da kwanciyar hnklinsa" Dad ya share wani xufa da ke keto masa da kyar yace "Ce maka yyi yana sonta?" Likitan yace "Ae ba sai ya gaya min ba Alhaji, na fahimci komae" Dad ya dau fiye da second ashirin yana kallon likitan daga bisanni ya jinjina kai yace "Toh shknn ngd likita, xan iya shiga in gansa koh?" Likitan yace "Xa ka iya shiga amma idan ka tarar yana bacci kadda ka tashe sa" Dad yace "Toh ngd" snn ya mike ya fita daga office din rae a dagule, ya dde tsaye jikin bango yana mmkin lamarin daga karshe ya nufi ward din da Aliyu yake. Kwance dad ya samesa idonsa lumshe ya karasa gefen gadon yana kallonsa cike da tausayinsa, to amma me yasa tun farko bae fito yace yana son Zainab ba sae da ya bari aka karbi sadaki da kaya, Dad ya jinginar da kansa jikin kujerar da yake xaune ya shiga tunanin ynda xa'a bullo ma lamarin. Da asuba dad na dawowa daga masallaci ya sami Aliyu xaune ya cire drip din hannunsa ya dafe kansa, dad ya karaso da sauri yana kallonsa yace "Ya aka yi Ali? Ka tashi?" Da kyar ya dago kansa yana kallonsa da idanuwansa da suka sauya kala cikin sanyin murya yace "Sllh xan yi" Dad yace "Xaka iya kuwa?" Kai kawae ya gyada masa ya sauko daga kan gadon ya nufi bayin dake ward din yana gnin jiri. A ward din dad ya shimfida masa darduman da ya karbo, duk sae da Aliyu ya rama sallolin da ake binsa duk da jirin da yake gani, snn ya juya yana kallon dad dake ta kallonsa, ya sunkuyar da kai ya gaishesa cikin sanyin murya, Dad ya amsa yana murmushi yace "Ya jikin Ali" yace "Da sauki Abba" Dad yace "To Ma'sha Allah, Allah kara afuwa" Aliyu xae yi magana aka bude kofar dakin Mami ta shigo rike da flask din ruwan xafi da leda dauke da kayan beverages da Bread, murmushi ne ya bayyana fuskarta gnin Aliyu xaune kan darduma ta karaso ta ajiye abin hannunta tana kallonsa tace "Sannu Ali, ya jikin" duk da yyi mmkin ganinta bae nuna ba, ba tare da ya kalleta ba yace "Da sauki" mikewa yyi ya koma kan gado ya xauna ta bi sa da kallo snn ta karasa kan gadon.
Karfe sha biyu saura aka yi discharging dinsu don jikin nasa Alhmdllh, sae dae har lkcn jin xuciyarsa yake kmr ba tasa ba, duk da dad yaso ko da xuwa yamma ne a kuma gnin jikinsa amma Aliyu ya nuna shi ya ji sauki a sallamesa kawae, ssae likitan ya kuma jad'da'da ma Dad muhimmancin bayanin da yyi masa daxu a office, dad da duk tunanin ynda xae bullo ma lamarin ya damesa yace "In'sha Allah xa a kiyaye Dr" Saleem ne yyi driving dinsu ya maida su gida, kwanciya Aliyu yyi kan kujera a falo ya lumshe ido. Afeefah da sakkowarta falon knn ita da Anty Jamila da su Ilham xa su je asibiti don tun da asuba ta ishesu da kukan ita a kai ta gun yayanta, Aliyu ta gani kwance falo, ba tare da tayi wani tunani ba bata kuma damu da wa enda ke falon ba ta karasa wajensa da gudu ta fada kansa ta fashe da kuka ssae tana kallonsa, shima kallon nata yake ya kasa cewa komae, da kyar ta iya bude baki muryarta na rawa ta daura kanta bisa kirjinsa tace "yayanmu" lumshe ido yyi ya hade hannunsa da nata, cikin sanyin murya shima ya kira sunanta, mikewa dad yyi cike da damuwa don komae ya dagule masa ya fice daga falon, toh shi kam ya xae yi da Dr Aliyu da mahaifansa kar su daukesa karamin mutum, a balcony ya hadu da Dr Sharif da Ma'aruf suna kkrin shigowa, har kasa Dr Sharif ya durkusa ya gaishesa, dad ya amsa masa yana kirkiran murmushi, Ma'aruf ya gaida dad din nasa shi ma, snn suka tambayesa jikin Aliyu, dad yace "jiki Alhmdllh yana ciki" Mami kam tun shigowar Afeefah falon dama ta kasa daga kai daga karshe ma dad na fita ita ma mike ta haura sama ba tare da ta kallesu ba. Da sallama Dr Sharif ya shigo falon da Ma'aruf, Momy ta kalli Afeefah dake jikin Aliyu har lkcn bayan ta amsa masu sallaman tace "To Zainab ae sae ki daga sa hka nn, Kinga jikin sa ba kwari" dai dai nn Dr Sharif ya sauke ido kan Zainab dake jikin Aliyu har lkcn idonta rufe, sunkuyar da kai yyi sae dae kasa karasawa cikin falon yyi sae murxa makullin motar dake hannunsa yake, Ma'aruf yace "Bismillah mana Dr" sae a snn Afeefah ta dago da sauri suka yi ido hudu da Dr Sharif, a hnkli ta xamo daga jikin Aliyu ta dawo kasa tana kallonsa, sunkuyar da kai yyi ya karaso cikin falon, ya xauna nn kasan rug din falon cikin sanyin murya ya gaida mum, ta amsa tana murmushi hade da ce masa ya gajiyan jiya, Murmushi kawae yyi a sanyaye yana kallon Aliyu da ya kafa masa ido yace "Ya jikin" Aliyu ya gyada masa kai cikin sanyin murya yace "Alhmdllh," Dr Sharif yace "Allah kara afuwa" Ma'aruf yace "Sannu barrister, Allah kara lfya" murmushi kawae Aliyu ya iya masa, Afeefah kam tun shigowar Dr Sharif falon ta kasa dago kanta, har sae da Ma'aruf yace "Ina kwana Anty Zainab" snn ta dago a hnkli tana kallonsa ta kirkiri murmushi tace "Ina kwana yaya" Ma'aruf yyi dariya yace "A'a ki dae ce min lfya kawae, na bar maki yayan" Momy tayi dariya tace "Ae ka bar ta ynda ka ganta yau bbu wnda ta gaisar gidan nn, tunda ta dare kan yayanta ko waigo mu bata yi ba" Murmushi tayi snn ta kalli Dr Sharif dake kallonta har lkcn, cikin sanyin murya tace "Ina kwana sir" Sauke idonsa yyi daga kallon nata a hnkli yace "Lfya lau" mikewa yyi yana kallon Momy yace "sae xuwa anjima momy, xan tafi" Momy tace "breakfast fa Aliyu?" Yace "Mun yi momy" Aliyu dake kallonsa har lkcn ya kalla yace "Allah ya kara afuwa barrister" Aliyu yace "Ameen ngdd" Ma'aruf ya juya yana kallo yace "Captain sae xuwa ltr" bae jira cewarsa ba ya fice daga falon da sauri Afeefah ta bi sa da kallo a sanyaye, Mikewa Ma'aruf yyi ya bi bayansa, tsaye ya samesa ya hade kansa da motarsa, Ma'aruf ya dafa sa yace "Ya aka yi Dr" dagowa Dr Sharif yyi da kyar yana rike da kirjinsa da hannu daya yace "Bana jin ddi ne" Ma'aruf yace "Subhanallah, to ina xa ka ynxu" a takaice ya basa amsa yace "Hotel, xanje in sha drugs" bae jira cewarsa ba ya bude mota xae shiga don wani jiri yake gani, Ma'aruf ya riko sa da sauri ya karbi makullin motarsa yace "Let me drive yhu"
Eeshatullah.
[5/22, 07:59] Umar Dalha: 🌸👩🏻'ya Mace kyautar Allah👩🏻🌸
By Ashmaad
67......
Dad ne xaune falonsa da yamma Mum ta shigo tare da Mami kmr ynda ya aika Aneesah kiransu, dad ya nisa bayan sun xauna yana kallon Mami yace "Hajiya Zuwaira dama kinsan akwae magana a kasa kika sa na karbi kayan mutane, ynxu ya kike son inyi fisabillilahi " Mami ta daga kai ta kallesa kmr bata fahimce sa ba tace "wace mgnr kke nufi Alhaji" kallonta kawae dad yake don sarae yasan ta san mgnr da yake nufi, can ya girgixa kai yana kallon Momy, da ganinsa kasan ransa ya baci, Mami kam ko a jikinta, a nutse ya shiga yi ma Momy bayanin abinda ya faru jiya da daddare a asibiti, bnda salati bbu abinda momy take tana kallon mai gidan nata. Suna isa hotel din da Dr Sharif yyi lodge ya fada kan gado yyi rub da ciki tare da lumshe ido, kallonsa kawae Ma'aruf yake, can yace "Toh maganin da xaka sha fa?" Bae tanka sa ba kuma bae bude idonsa ba, hkn yasa Ma'aruf ya xauna gefen gadon, sun fi minti goma a hka, can ya kuma kallonsa yace "Kaga since yhu are nt OK ka tashi mu tafi gidana Dr," Ba tare da Dr Sharif ya bude ido ba yace "I wil b fine frnd, yhu can leave, Bacci xan yi kawae, I only need rest" Ma'aruf ya jima xaune yana kallonsa daga karshe ya mike yace "toh shknn anjima xan dawo" fita yyi ya kullo masa kofa. Aliyu na xaune dakin Saleem ya tsura ma laptop din kafarsa ido duk da bbu abinda yake da shi amma yyi nisa tunanin da yake, Afeefah ta shigo da sallama dauke da farantin abinci da drinks, kallonta kawae yake har ta karaso kanta a kasa ta ajiye farantin hannunta, cikin sanyin murya tace "Yayanmu ga abinci" jin bae ce komae ba yasa ta dago kai tana kallonsa, kallonta taga yana yi, da sauri ta sunkuyar da kanta ta fara kame kame, can ta bude kular abincin ta dauki plate ta shiga dibar masa shinkafar, snn ta sa masa miya da kaji biyu, murya can kasa ba tare da ta kallesa ba tace "yayanmu yyi?" Hannu yasa ya karbi abincin ya ajiye kan bedside drawer, ta mike da sauri ta nufi kofa xata fita taji ya kirata cikin sanyin murya, still tayi bakin kofar ba tare da ta juyo ba tace "Na'am" jin bae ce komae ba yasa ta juyo a hnkli tana kallonsa, dauke idonsa yyi daga kanta yace "Lipton xa ki dafa min pls" tace "Toh" snn ta fice da sauri.
Tun da dad ya fara magana Ma'aruf ya saki baki da hanci yana kallonsa da mmki, har dad ya kai aya, gnin Ma'aruf ya ki cewa komae ya sa dad yace "Kayi shiru Ma'aruf" Ma'aruf ya shafa kansa lkci daya ya ciro handki dinsa ya goge xufan goshinsa, da kyar daga karshe yace "Dad amma.... toh ni ban ma san me xance ba wllh" dad yace "A'a shawarar ka fa na nema don hka ka samo abun cewa" Ma'aruf ya girgixa kai yace "Toh Dad da can sun san da hka don me basu maka bayani ba, tsakani da Allah bbu dattako cikin abin da kke shirin yi Dad" dad yyi shiru yana kallonsa lkci daya ya sauke ajiyar xuciya yace "To Ma'aruf ya kke son in yi ynxu, duk laifin Zuwaira ne don bata min bayanin komae ba duk da ynxun ma bata san abinda nake shiryawa ba, kawae na kira Baban Aliyun mun yi mgna ne daxu yake min wnn bayanin, ko kadan bata kyauta masu ba kuma ni ta ban mmki wllh," Shiru dad ya dan yi snn ya ci gaba "wani kusan yafi wani kusan Ma'aruf, don hka baxan iya hana Aliyu Zainab ba da kunya ssae, dubi ynda ubansa ya riketa tamkar 'yar cikinsa Haba haba" Ma'aruf ya dan tabe baki don shi Sam bae gamsu ba, "Dad ya xaka yi da iyayen Hydar da shi kansa ynxu" ya fadi hka yana kallon dad din nasa, dad ya nisa yace "Alhaji Sheriff mutum ne Mae fahimta, nasan xae fahimce ni ssae, snn ba wae xa'a mayar masu da kayansu bne, A'a sae a basa daya daga yayyin Zainab, shima nasan xae fahimce ni Aliyun don yana da hnkli" Ma'aruf yyi wani irin murmushin takaici yana girgixa kai kmr xae yi magana sae kuma ya fasa yace "Allah sa hkn shine mafi alkhairi" Dad na kallonsa yace "Ameen" duk da yasan d'an nasa bae gamsu ba, mikewa Ma'aruf yyi ya fice daga dakin. Afeefah na kwance daki ita kadae da yamma Dr Sharif kadae ne a ranta don tun da safe da ya tafi bae kuma dawowa ba gashi har Ma'aruf ya dawo, mikewa tayi a sanyaye ta dauki wayarta ta shiga kiran layinsa, har ya gama ring bae daga ba, hkn yasa ta kuma kira nn ma ba a daga ba, ajiye wayar tayi ta koma ta kwanta jiki ba kwari, Aneesah ce ta shigo dakin