Showing 99001 words to 102000 words out of 116554 words

Chapter 34 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1280

yyi ya fita daga dakinsa ya nufi nasu, kwance ya sameta cikin bargo ta takure waje daya idonta lumshe, ya yaye bargon yana kallonta ya daura hannu goshinta a hnkli, da sauri ta bude ido ganinsa ta mike xaune tace "Yayanmu" da damuwa yace "Baki da lfya ne little sis?" Bata fuska tayi kmr xata yi kuka a hnkli tace "Cikina ke ciwo yayanmu" yace "on ur period?" Ta gyada masa kai tana kallonsa, ya xauna gefenta ya kamo hannunta da damuwa yace "ohh Sorry kin sha xaki dayawa month din knn koh?" Ta shagwabe masa tace "Ni ba abinda na sha yayanmu ae kana gani" yace "Toh naji sakko mu tafi kiyi breakfast sae mu je in siyo maki magani koh" daure mata gashinta da ke kwance bayanta a barbaje yyi ya taimaka mata ta sakko daga kan gadon ta dauki xani ta daura kan kayan baccin jikinta suka fita daga dakin, ya shiga nasa da ita, tea ya lallaba ta tasha da kyar kafin ya mike ya dauki makullin motarsa yace "Mu je" tace "Ka fara yin breakfast tukun yayanmu" dago ta yyi yace "No muje in siya maki magani tukun little sis" daga hka ya kama hannunta suka fita daga dakin bayan ta sa hijab, Mami dake gyare gyare a falo ta bi su da harara har suka fita. Tun a mota ya bata maganin ta sha bayan ya siya snn suka dawo gida ya sa ta kwanta a dakinsa, ta dde tana juye juye yana mata sannu kafin bacci ya dauketa. Ko da Afeefah ta farka da yamma tsaye ta gansa yana hada kaya, mikewa xaune tayi da sauri tana kallonsa tace "ina xa ka yayanmu?" Ya Juya yana kallonta ya sakar mata murmushi yace "Am travelling princess, ya cikin ya daina?" a sanyaye tace "ina xaka?" Ya dauke idonsa daga kanta yace "UK xan tafi wani aiki" hawaye ne ya cika idonta tace "Plss kar ka tafi ka bar ni ni kadae yayanmu" juyawa yyi yana kallonta sae kuma ta fashe da kuka, ya karaso jiki ba kwari ya xauna gefenta yace "Kiyi hkuri Zainab, aiki xan tafi ba ddewa xanyi ba" bata ce komae ba sae share hawayen da yaki tsaya mata take tana kallonsa, duk jikinsa yyi sanyi tausayinta ya rufe shi don yasan shi kadae ne farin cikinta a gidan, shi kuma sbda maganar da Abba yyi masa yake son barin kasar don takaici, da ya tuna xancen Ahmad na cewa me xae yi da ita ko da sun rabu da mijinta sae ya ji wani bacin rae don yasan gskya Ahmad ya fadi, ya harde hannunsa da nata ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Baxan dde ba princess" kai kawae ta gyada masa hawaye na sakko mata. Karfe biyar saura ya gama shirinsa ya juya yana kallonta ganin ynda tayi tagumi tana kallonsa ya sa shi murmushi, ya dawo kusa da ita yace "kiyi xaman ki dakina har in dawo, kuma ki dinga hkuri da kowa kin ji" kae kawae ta gyada masa hawaye cike idonta, ya mike cike da tausayinta ya bar dakin don xuwa yi ma Mami sallama, duk ynda ya so ta fito ta rakasa ko bakin gate kin fitowa tayi sae kuka take, ya bata kudi me yawa ya kuma ce ta dinga shan maganinta har cikin yyi mata sauki, sae da ya isa bakin kofa ya daga mata hannu, ta mike ta isa inda yake da sauri ta shige jikinsa, rungumeta yyi ya lumshe ido, sun kusa 3 min a hka kafin ya banbareta jikinsa ya fita daga dakin rike da jakarsa. Hka kawae ya K'asa tafiya airport ya nufi gidansa na Nasarawa, yasan har ynxu yana son Zainab ga tausayinta da yake amma bae jin xae iya aurenta, tunanin hkn ya sa shi hawaye ssae, hka ya kwana ranan bae da sukuni ga shi ya kasa daina tunaninta ko wani hali take ciki, ita ma hka tun tafiyarsa take kuka taji gidan yyi mata xafi, bbu me shiga tsabgarta don Mami ta hana, hka tayi ta xama dakinsa kmr mayya, bbu wnda ya damu ya kawo mata abinci ko yace taje ta xuba, don hka bata ci komae ba, har kwana uku Aliyu na Kano bae tafi ba sae dae duk ya kashe wayoyinsa, ya rasa gane me yasa ya kasa barin Nigeria. Mami kasa daure ci gaba da share Zainab tayi bayan tafiyar Aliyu don tasan ynxu bbu me sa ta farin ciki har ta dinga shanye abinda ake mata, da can ma abinda yasa ta fita harkarta gaba daya sbda tasan yana nn ne ta kuma san baxae barta cikin damuwa ba, da kanta ta dinga kai mata abinci tana sa ta tana ci, ta kula bata da aiki sae na kuka duk da bata yi gabanta sae dae da ganin idonta xa ka gane, bayan kwana biyu da barin sa gidan ta fara rashin lfya, rashin lfya da ya daga ma Mami hnkli ssae ganin ynda take jin jiki, kwanansu biyu asibiti ranan Mami na xaune da ita a ward tayi tagumi, ita ko tana xaune ancire mata drip din hannunta tana cakalkala abincin gabanta, Mami ta kira sunanta, a hnkli ta dago tana kallon uwar tata, cikin sanyin murya Mami tace "ki gaya min me ke damun ki Zainab" shiru tayi tana kallon uwar tata kafin ta sunkuyar da kai hawaye ya xubo mata a sanyaye tace "Yayanmu ya tafi ya barni Mami, ku ce masa ya dawo don Allah"

Eeshatullah



🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad

94____96
Shiru Mami tayi bata ce komae ba duk jikinta yyi sanyi, wnn kam ya wuce shakuwa tsakaninta da Aliyu, bayan mintuna goma cikin kwantar da murya tace "Toh kiyi hkuri xae dawo, kin ji" Zainab na share hawayen fuskarta tace "nmbrn sa basa shiga ae Mami" Mami bata kuma cewa komae ba sbda shigowar su Anty baby don sun xo gida su ma duba 'yar uwar tasu. A bangaren Aliyu kam kwata kwata ya ji baxae iya tafiyar ba kuma, duk motsin da xae yi sae Zainab ta fado masa gaba daya hankalinsa ya k'asa kwanciya, hka nn xuciyarsa ya basa bata da lfya ya kuma ji a jikinsa, a kwana na hudu ya kasa daurewa ya shirya ya dawo gida da yamma, su fadila kadae ne xaune falo suna assignment, bae damu da murnar ganinsa da suka dinga yi ba suna rungume jikinsa, tambayar da ya fara jefo masu shi ne ina Zainab, Fadila tace "Suna asibiti yayanmu, bata da lfya yau 3 dayz" cikin rudewa yace "3 dayz? me ya sameta, wani asibitin?" Suna fada masa ya fice da sauri ya nufi clinic din, Adnaan da ya gani harabar asibitin ne ya kai sa ward din da suke bayan yyi murnar ganin yayan nasa, hawaye Afeefah take tana cin shinkafar da Anty Safiya ta sa ta gaba sae ta cinye don bata cin komae sae shan ruwa, duk ta rame sosae an rasa gane kanta, Abba ma na tsaye ward din xuwansa knn asibitin, Mami na xaune ita ma ta buga tagumi tana kallon 'yar tata, jin an bude kofa yasa Afeefah ta dago ido tana kallon kofar, hka ma su Anty Safiya, kafa masa ido tayi kmr bata gane ko waye ba, kanninsa duk suka mike cike da murnar ganinsa, shi kam k'asa karasowa yyi idonsa na kan Zainab ko kiftawa bae yi, sunkuyar da kai tayi ta sakko a hnkli daga kan gadon ta nufe sa sae da ta kusa inda yake ta karasa da gudu ta shige jikinsa, rungumeta yyi ssae ta sakar masa kuka a hnkli, ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Zainab!" kuka take ssae hkn yasa ya bude ido ya dago kanta ya shiga share mata fuskarta murya can kasa yace "Am srry little sis," dariyar da Anty Safiya da Anty baby suka yi yasa duk suka juyo da sauri, sae a snn ya lura da Abbansa da Mami dake kallonsu, kunya ya rufesa ya janyeta jikinsa da sauri, ya karasa dakin kai a kasa yana rike da hannunta ya gaida iyayen nasa, Abba yyi murmushi yace "Sannu Ali, ya hanya, amma meye amfanin kashe waya" ya shafa kai bae ce komae ba sae murmushi, ya juya suka yi ido hudu da Afeefah da ke kallonsa, matse hannunta dake cikin nasa yyi, ta lumshe ido tana murmushi. Washegari da safe aka sallamesu don ka rantse kace ba ita ce ba lfya ba har likitocin suka yi mamaki, suna komawa gida ta marairaice masa a bedroom dinsa cikin sanyin murya tace "Yayanmu kar ka kuma tafiya ka bar ni plss, idan xaka tafi ka dinga tafiya dani" murmushi yyi yana kallon kwayar idonta dake kyalli ta dalilin hawayen da ya cika cikinsu, ya ja dogon hancinta cikin lallausan murya yace "Owk little sis baxan kara ba, am alwayz here for yhu" tare suka yini ranan a daki sae dae su Anty Safiya su leko su koma, ana isha tayi bacci bayan ya sa ta sha magungunanta, ya rufe laptop din gabansa ya juya yana kallonta, mikewa yyi a sanyaye ya fita daga dakin, Anty Safiya ce ta fito daga bangaren Abba ganinsa ta karasa da sauri tace "Yauwa yayanmu ina da magana da kai" yace "OK ina jin ki, ina kids din ki?" Hannunsa ta kama suka nufi dake n Adnaan ya xauna gefen gado yana kallonta yace "Wae ya aka yi?" Cikin sanyin murya ta fara masa magana tace "Yayanmu a kan Zainab ne...." "Wat about her?" Yyi saurin katse ta, ta sauke ajiyar xuciya tace "kaga sbda baka nn fa...." Katse ta ya kuma yi ya hade rae yace "To ya aka yi? Plss ku rabu da ni, matsayin kanwar da muka fito ciki daya na ajiye Zainab ynxu kmr yanda ta ta6a fadi." Shiru tayi tana kallonsa ya mike yace "Dama maganar knn" k'asa cewa komae tayi ya juya a fusace ya fice daga dakin ransa a bace, don me ake son makala masa Zainab ynxu, bayan duk rashin mutuncin da aka yi masa duk da halin da ya shiga kanta, dakinsa ya koma ya dauki makullin motarsa ya bar gidan gaba daya. Da asuba sadiya ce ta tada Zainab da ke baccin da ta dde bata samu ba, kalle kallen dakin ta shiga yi tace "Ina yayanmu?" Sadiya tace "ya tafi jiya" da sauri ta sauko daga kan gadon a rikice tace "Ya tafi ina?" Sadiya tayi shiru tana kallonta, juyawa tayi da gudu ta fice daga dakin ta nufi dakin Mami, xubewa gabanta tayi ta fashe da kuka tace "Mami wae yayanmu ya kara tafiya?" Mami ta turata gabanta tace "Ke ban fa son iskanci, sae aka yi ya da ya tafi? Xan xuba maki mari idan baki tashi gaba na ba," mikewa tayi da sauri ta fice daga dakin ta shiga nasu ta xube jikin Anty baby tana kuka tace "Anty wae yayanmu ya tafi, bayan yace min baxae kuma tafiya ba don Allah ku ce masa ya dawo kar ya tafi ya bar ni" shiru duk suka yi suna kallonta, ta dinga kuka tana cewa su ce ya dawo, da kyar Anty Safiya ta lallasheta tace da safe xata gansa bbu inda ya je, hka Zainab tayi ta baxa ido taki cin komae har biyun rana bbu yayanmu ba lbrinsa, nn hakurinta ya kare ta dinga rusa masu kuka wane yar shekara uku, Mami ta sameta tayi mata mugun duka don takaici, da kyar yayyinta suka karbeta, Adnaan dake xaune falo ko kallon inda suke bae yi ba, Anty baby ta kulle dakinsu ganin Mami bata gaji da dukanta ba, ko awa daya ba ayi ba xaxxabi ssae ya rufeta, da kyar Aunties dinta suka lallabata ta sha ruwan tea suka bata magani ta sha ta kwanta, lkci daya bacci daya baccin wahala ya dauketa wajajen karfe biyar na yamma, a bangaren Aliyu kam gidansa na U Nasarawa ya nufa daren, har wayewan gari bae samu nutsuwa ba, k'asa cin komae yyi gaba daya ranan ya rasa me ke masa ddi, duk motsin da xae yi sae Zainab ta fado ransa, wani mugun sonta na kara shigarsa, ya rasa dalilin karfin halinsa na cewa baxae iya aurenta ba don yasan baxae taba daina son Zainab ba har karshen rayuwarsa, sae yamma ya iya shiga bayi yyi wanka, yana fitowa ya ji ya fara jin sanyi lkci daya ya ji xaxxabi na son rufe sa ya shige cikin bargo bacci yyi awon gaba da shi, shidda saura ya farka jin wani sara masa da kansa ke yi, ya daure ya fita ya hada ruwan tea ya sha, kafin ya sha magani, k'asa daurewa yyi daga karshe ya dauki makullin motarsa jiki a sanyaye bayan yyi magrib ya fita ya kama hanyar jan bulo, bbu kowa falon ya haura sama, ya dde tsaye corridor kafin ya tura kofar dakin su Jiddah, kwance ya ga mutum cikin bargo bbu kowa dakin sae tv da ke aiki, ya karasa jiki a sanyaye ya yaye bargon, ido ya tsura ma lips dinta da suka yi jajir, ko ba a gaya masa ba yasan kuka tayi ba kadan ba, don tun tana karama hka lip dinta ke yi idan tayi kuka, da sauri ta bude ido suka yi ido hudu, ta mike xaune da hanxari ta kankamesa har sae da ya fado kanta, ta fashe da kuka ssae tace "Wayyo yayanmu ka ce baxa ka kuma tafiya ka bar ni ba" lumshe ido yyi ya k'asa cewa komae, ganin yanda take kuka yasa a hnkli yace "Am srry princess baxan kuma barin ki ba, i wont forever" muryarta na rawa tace "Promise" ya janyeta jikinsa ya dafa shoulders dinta yana kallon jajayen idonta yace "I promise" rungumesa tayi ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Ur temperature is high" a hnkli tace "Yunwa nake ji yayanmu" shi ma sae a snn ya ji yana jin yunwan, ya mike ya d'ago ta yana kallon kulan abincin dake dakin yace "Abincin waye" tace "Nawa" sakkowa yyi daga kan gadon ta bi sa suka xauna kasan rug din dakin ya bude kulan ya ga farar shinkafa ce, plate ya dauka ya dibi abincin snn ya bude kulan miyan ya xuba, a tare suka fara cin abincin yana ci yana bata, a hka Aunties dinta suka shigo suka samesu, bbu wanda ya samu liver din Karasowa cikin dakin, suka dae gaida yayan nasu suka juya suka fita Anty Safiya na murmushi, sae da suka gama cin abincin ya mike ya ja ta suka nufi dakiin Mami don ya gaisheta, Mami ta amsa tana kallonsu sae dae duk jikinta yyi sanyi, dakinsa ya nufa da ita bayan ya je bangaren Abbansa ma ya gaida sa duk tana like da shi, daga nn ya koma bedroom dinsa, duk motsin da xae yi tana kusa da shi wae kar ya tafi ya bar ta, Karfe goma bacci ya dauketa tana rike da hannunsa bayan ya sa ta sha maganinta don xaxxabi ne jikinta, cikin dubara ya xame hannunsa jiki ba kwari ya mike ya nufi bangaren Abbansa, xaune ya samesa falonsa bayan ya gaida shi kansa a kasa cikin sanyin murya yace "Abba na amince da auren Zainab Allah sa hkn ne Alkhairi" kasa cewa komae Abba yyi sae kallonsa yake kafin yyi murmushi daga karshe yace "Ka gano kana sonta ita ma tana sonka knn koh" murmushi yyi kansa a kasa, Abba yyi murmushi yace "toh Allah maku albarka Ali, in'sha Allah nn da sati biyu xa ayi komae" da kyar ya iya bude baki yace "Shknn Abba nagode, Allah ja nisan kwana" daga hka yyi masa sae da safe ya bar falon ya koma dakinsa suka kusan cin karo da ita a rikice xata fito bata gansa ba, hannunta ta kamo yace Abba na ya kirasa ya je, duk ynda ya so ta koma dakinsu ta kwanta kin yadda tayi wae idan ta tafi xae wuce, Mami na shigowa bangaren mijinta yyi mata bayanin xancen da Ali ya xo masa da shi, Murmushi tayi ba tare da ta kalli mai gidan nata ba sbda nauyin da ta ji tace "Allah tabbatar da alkhairi" ya kula da hkn, yyi murmushi kawae yace "Ameen, gobe sae in je kaduna in masu bayani". Washegari Mami ta kira manyan yaranta mata tayi masu bayani kmr ynda Abbansu yyi mata, ssae suka yi farin ciki da xancen gaba dayan su, nn take suka fara fadin ynda xa a shirya abubuwa, Mami dae shiru tayi tana kallon 'ya yan nata, duk wnn abinda ake Afeefah bata sani ba, a ranan Abba ya bi flight ya tafi Kaduna, iyayenta na Kaduna ma suka yi murna da jin hka barin dad din ma'aruf, nn take ya bada sadakin Aliyu dubu dari biyu, Abba yyi masa gdya ya bar Kaduna bayan sun sa daurin auren sati biyu daga ranan. Abba na sauka gida ya sa aka kira masa Aliyu ya gaya masa ynda abubuwa suka tafi a can Kaduna ya kuma ce ya kira dad din Ma'aruf yyi masa gdya. Ranan friday da yamma da ya kama saura sati daya bikin yana xaune dakinsa da Zainab dake kwance tayi rub da ciki gefensa tana game a laptop dinsa, ganin ynda yake kallonta yasa ta Mike xaune tace " Me ya faru yayanmu?" Sauke idonsa yyi daga nata yyi murmushi ya kamo hannunta yace "Nothing" ta langwabar da kai tace "Toh tunanin me kake" ya dan wara ido yace "Nothing" daga hka ta juya xata kuma kwantawa ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Ina son maki tambaya Zainab" dawowa kusa da shi tayi tana kallonsa tace "Na me yayanmu?" A hnkli yace "Xa ki iya aure na?" Still tayi na kusan second talatin tana kallonsa ko kiftawa bata yi, kmr me rada yace "Zainab" boye fuskarta tayi da sauri a kirjinsa, yyi shiru yana kallonta, a hnkli ya shiga dago kanta amma taki bari, murmushi yyi yace "Kin yi shiru" mikewa tayi da sauri xata gudu ya rikota, ta boye fuskarta jikin gado kmr munafuka, dariya ta basa ya duka dab da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login