Showing 39001 words to 42000 words out of 116554 words

Chapter 14 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1267

mata tun Afeefah na nonnokewa sbda kunya har ta sake, light make up tayi mata, ta sa mata jan bakin da tasan xae amsheta, snn ta mata daurin dankwali ya xauna das a kanta, wae ina ma xa a iya kwatanta irin kyan da Afeefah tayi don Amina sake baki tayi tana kallonta, wane ba indiya ko balarabiya, ita kanta Afeefah sae da taji kunyar don bata taba kwalliya hka ba, hotuna Amina ta mata snn tace "to tafi kuyi hira da Sir din ki" rufe fuska Afeefah tayi da sauri cike da jin kunya, can ta dauki hijab dinta xa ta sa, Amina tace "meye hka xan gani?" Afeefah ta sunkuyar da kai tace "sa wa xan yi" Amina tace "Haba sae kace warce xata fita kofar gida, falo fa xaki xauna" karbe hijab din Amina tayi tace "yi tafiyar ki hka" Afeefah kmr xata yi kuka tace "baxan iya fita hka ba Anty" Amina ta sake baki tana kallonta can tace "to wllh baxa ki fita da hijab ba, gwara ki dauko mayafi toh" Afeefah ta marairaice tace "ban xo da mayafi ba anty" Amina tace "bari xan baki nawa," jan mayafinta mai kyau ta fiddo mata ganin atamfar na da ratsin ja ta mika mata tana murmushi tace "to ga shi ki yafa" a kunyace Afeefah ta karbi mayafin amma ta kasa yafawa don ba sabawa tayi ba, Amina ta karba tana dariya ta yafa mata shi a shoulder dinta gefe daya, snn ta dauki turare ta fesheta da shi ta fiddo mata red flat shoe dinta ta bata tace "sa kiyi tafiyar ki" a hnkli Afeefah tace "ngdd," snn ta sa ta fita daga dakin. Da kyar Afeefah ta sauko downstairs don ji take kmr ta nutse tsabar kunya, juyawa Dr Sharif yyi don ganin me sakkowa, ya kafa mata ido ko kiftawa bae yi, wani mugun sonta na fixgarsa, ta sunkuyar da kai da sauri, tana harhardewa ta karaso falon ta rakube gefen kujera kanta a kasa a hnkli tace "Sir ya hanya?" murmushi Dr Sharif yyi murya can kasa yace "Zainab!" Ba tare da ta dago kai ba tace "um" ya nuna mata gefensa yace "dawo nn" kin tashi tayi sae da ya kuma kiran sunanta snn ta mike da kyar kanta a kasa ta dawo kusa da shi ta xauna kasa, kallonta kawae yake, ta dago a hnkli tana kallonsa da dara daran idonta, ya lumshe ido yace "kinyi kyau" rufe fuskarta tayi da sauri murya can ciki tace "ngd Sir" Amina ce ta sakko ta shigo falon tace "baxa ku xaga kaduna ba yayana, da kun dan fita outing" kallon kanwartasa yyi yana murmushi yace "Yayanta xae bari in fita da ita?" Amina tace "ehh mana, bari in masa mgna" juyawa tayi ta koma sama, Dr Sharif na kallon Afeefah yace "wae mu je yawo?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba lkci daya ya Aliyu ya fado mata hka kawae ta ji gabanta ya fadi. Amina ce ta kuma sakkowa tana murmushi tace "yayanta yace xa ku iya fita amma kar ku dde" juyawa tayi tace "ina xuwa" snn ta kuma komawa sama, ba a dau lkci ba ta dawo falon tace "Anty ki tafi yayanki na kira a sama" Afeefah tayi murmushi ta gyada mata kai alamar ta ji, farantin Drinks din dake falon Amina ta dauka ta nufi kitchen, Afeefah ta Mike a hnkli don xuwa kiran ya Ma'aruf, rasa inda xata bi da Dr Sharif baxae bita da kallo ba tayi, don wani kunya take ji idan yana kallonta, tana fara tafiya mayafin jikinta ya xame kafin ta ankara har ya kai kasa, ta xaro ido da sauri ta durkushe wajen kmr xata yi kuka tana kallonsa, Dr Sharif ya kauda kansa yana murmushi, mikewa tayi da gudu ta nufi stairs rike da mayafin a hannu bin ta da kallo yyi yana murmushi, ba a dau lkci ba Ma'aruf ya sakko Afeefah na biye da shi a baya yana kallon Dr Sharif yace "amma fa baxa ka dde min da kanwa a waje ba Dr" Dr Sharif yyi murmushi yace "In'sha Allah" makullin mota Ma'aruf ya basa yace "ga aron mota" dariya Dr Sharif yyi ya karbi makullin yace "thanks frnd" Ma'aruf yyi masu Allah kiyaye hka ma Amina suka koma sama, yana gaba tana biye da shi a baya ya nufi parkin lot, juyawa Dr Sharif yyi yana kallonta a hnkli yace "koma ki dauko hijab din ki Zainab" Afeefah ta juya ta koma cikin gidan ta ajiye mayafin ta dauki hijab dinta, Amina tayi dariya tace "lallai ma yaya" murmushi Afeefah tayi kawae ta fita ta samesa cikin mota yana jiranta.


Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

41.....
Sae da suka hau main road ba tare da Dr Sharif ya kalleta ba yace "Ina kike son in kai ki Zainab?" Shiru tayi bata ce komae ba, can kuma a hnkli tace "nima bn sani ba" yace "Ma'aruf bae taba fita dake bne duk xuwan ki hutu kd?" Ta girgixa masa kai tace "ae shi ba nn yake ba" Dr Sharif yace "yea hka ne na manta, bari mu je to ki ga state university din kaduna, da polytechnic dinsu, ko kin taba xuwa?" Girgixa masa kai tayi, ya nufi hanyar unguwar rimi, har cikin kasu ya shiga da ita, sae a snn Afeefah tace "Sir wae nn ne?" Dariya yyi yace "da fa, ga dayan a gaba shima xan shiga dake" tabe baki tayi tace "ko kyau, North west din mu ya fi kyau!" Dariya yyi ssae yace "kai bari yan Kaduna su ji ki bbu ruwana" dariya tayi tace "to ni ina ruwana da su daga na fadi gskya?" xagawa da ita cikin kasu yyi gaba daya, sae tabe baki take, ita a dole bae mata ba daga karshe tace "ni dae sir na gani, mu tafi kawae" yyi murmushi yace "to mu je tudun wada ki ga polytechnic dinsu na science?" Tabe baki tayi tace "ni bn san wajen ba" yace "ae nuna maki xan yi" tace "tohm mu je" polytechnic din art dake unguwan rimin ya fara nuna mata yace "akwae wani a barnawa ma, but ynxu na tudun wada xa mu" suna isa junction road yace "kalli can ki ga stadium dinsu" juyawa Afeefah tayi da sauri tana kallon inda yake nuna mata ta xaro ido tace "wnn dan wurin sir?" Dariya yyi ssae yace "don baki shiga bne" ta tabe baki tace "um ni dae dan karami ne" kwafa yyi yace "bbu ruwan sir dae, bari yan kd su ji ki su kama ki" dariya tayi tace "ni ina ruwana da su" ta sardauna crescent ya shiga sbda traffic, ta ce "Sir Dubi fa titin mu ma ya fi nasu girma da kyau ssae" yyi murmushi yace "eh mana" cikin mintunan da basu wuce goma ba suka isa poly road, Afeefah ta xaro ido tace "Sir nn ne polyn nasu?" Yace "yea" tace "kai shine yayanmu ke wani cewa makarantun kd sun fi namu ashe ba hka bne" dariya kawae Dr Sharif yyi ya nufi main gate din k.p.t, ya karbi gate pass ya shiga, dariya kawae Afeefah ta dinga yi ita a dole ta raina polyn, Dr Sharif ya girgixa kai yace "kin san shekaran polyn nn nawa?" Ta girgixa kai, yace "uhm ki bar raina sa, babban makaranta ce yarinya," tace "bn yadda ba, ka gaya min shekaran sa nawa!" Yace "this polytechnic was founded in 1956! Ki lissafa shekarunsa ki ga tun kan Independence, ya fi north west din nn naku da kike brag da iyakacinsa shekara biyar, kin manta slogan din kadunan ne wae? 'Center of education! Let me remind yhu" Afeefah ta saka dariya tace "kai Sir" murmushi yyi ya xaga da ita cikin polyn gaba daya snn suka fita ya shiga da ita ostrich bakery dake wajajen ya siya mata snacks kala kala, suka kama hanyar U.rimi, ya juya yana kallonta yace "its almost 6 pm da mun shiga gamji in ji cmmnt din ki, nd beside ma it's nt decent mu shiga da yamma" Shiru tayi bata ce komae ba, murya can kasa ba tare da ya kalleta ba yace "Mu je muyi hoto?" Shiru tayi kmr me naxarin abinda yace, sunanta taji ya kira, ta dago manyan idonta tana kallonsa a hnkli yace "Mu je studio muyi hoto nace?" Dauke kanta tayi, sae kuma tayi murmushi ta gyada masa. Hadadden studio ya nufa yana gama parkin ya juya yana kallonta yace "mu je" bude kofar tayi ta fito shima ya fito, yana gaba tana biye da shi suka shiga studio din, Afeefah taji baxata iya hoton ba bayan Sun shiga sbda kunya, ma'aikatan wajen duk a tunaninsu pre wedding pics suka xo yi, Dr Sharif yyi murmushi yace nml pic suka xo dauka, da kyar Afeefah ta iya tsayawa suka yi hoto da Dr Sharif tsabar kunya sae wani rurrufe fuska take, kala hudu kawae suka yi ya biya kudin suka ce su dawo gobe su karba bayan sun tura ma Dr Sharif a wayarsa, kasa kallon Dr Sharif Afeefah tayi har suka shiga mota, Eatry taga yyi parkin ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar ya mika mata ledan hannunsa, ta karba ba tare da ta kallesa ba, ya tada motar suka nufi gida, Dr Sharif na gama parkin bayan sun isa gida Afeefah ta bude motar ta riga sa fita da sauri tayi cikin gida, Amina dake kitchen ta fito tace "sannun ku da dawowa" Afeefah tayi murmushi kawae ta ajiye ledan hannunta tace "ina Fadil Anty?" Amina tace "tare mu ke girkin a kitchen ae, gashi can cikin kekensa" dariya Afeefah tayi ta mata sannu da aiki ta nufi sama da sauri kafin Dr Sharif ya shigo.
Bayan isha Ma'aruf yace da Dr Sharif "ya mgnr daxu Dr, mu tafi gun dad din ne ynxu? naji kace gobe xa ka koma!" Dr Sharif yace "to mu tafi frnd" takwas da kusan rabi suka isa can gidan, Dr Sharif yace "look captain kunyan dad nake wllh, just go in and explain to him" Ma'aruf ya hade rae yace "kaga matsala ta da kai koh" Dr Sharif ya marairaice masa yace "don Allah ka rufa min asiri kai ka shiga I just cnt go in" tsaki Ma'aruf yyi ya bar sa cikin motar ya nufi cikin gidan, ba karamin farin ciki dad yyi da xancen da Ma'aruf ya xo masa da ba, dad yace "ae wnn ba matsala bne in har uwar tawa tana so, kaga sae a hada da nasu jamila kawae, ka xo min da ita gobe mu ji ta bakinta" Ammi dake xaune falon tayi shiru dae tana kallonsu bata ce komae ba, dad ya juya yana kallonta yace "ko ya kika ga Uwar gida?" Sauke ajiyar xuciya tayi tace "Amma kuma Alhaji naga ae yana da kyau a fara jin ra'ayin iyayenta na kano ka ga ba wajen mu take ba bare kayi saurin yanke hukunci hka!" Dad ya hade rae yace "ji wani xance don Allah, da nan da can din ba daya ba mne, kuma nasan baxa su ce don me ba, don duk abinda na yanke tamkar su suka yanke ne" Ammi tace "To Allah rufa asiri, amma Dr Aliyu kam mutum ne, Allah dae ya xaba abinda ya fi alkhairi" Dad yace "yauwa xancen knn, Ameen ya Allah" Ma'aruf ya sallami iyayen nasa ganin ya bar Dr Sharif a waje snn ya bar gidan, Yana shiga motar ya sakar ma abokin nasa murmushi yace "In'sha Allah kmr ka samu Zainab frnd" murmushi Dr Sharif ya mayar masa yace "I trust yhu captain" goma saura suka isa gida, Amina tayi masu sannu da xuwa snn ta dauko masu abinci ta ajiye masu tsakiyar rug din falon ta nufi sama, Afeefah na shirin kwanciya Amina tace "kaddai har xa ki kwanta" Afeefah tayi murmushi tace "um bacci xan yi" Amina tace "to baki tafi kin ma Sir sae da safe ba yace baxae kwana nn ba" Afeefah ta kauda kanta a hnkli tace "toh" dariya Amina tayi ta fita daga dakin, Afeefah ta mike ta sa hijab dinta har kasa snn ta fita daga dakin ta sauka downstairs. Xaune ta samesa da Ma'aruf, ta karaso cikin falon kanta a kasa ta xauna daga kasa, cike da xolaya Ma'aruf yace "kin sakko fira knn" bata fuska tayi tace "A'a" yyi dariya ya mike yace "bari to in baku waje." Sae dae Ma'aruf ya haura sama snn Dr Sharif ya juya yana kallon Afeefah yace "har kin gama jin Kunyan" rufe fuskarta tayi da sauri yyi murmushi yace "to dawo nn" bata masa musu ba kanta a kasa ta dawo gefensa ta xauna daga kasa. Wayarsa ya mika mata yace "kin ga hoton da kika ki gani daxu" murmushi tayi ta karbi wayar tana kallon hoton nasu, ba karamin kyau suka yi ba barin Dr Sharif, tace "um bayan ka fini kyau!" Yace "kin dae fini" sunkuyar da kanta tayi tace "bn yarda ba" Ma'aruf ne ya sakko downstairs ya shigo falon da sallama yana mika ma Afeefah waya yace "ga yayanki" ba karamin faduwa gabanta yyi ba, ta karbi wayar da kyar, juyawa Ma'aruf yyi ya koma sama, sarae Dr Sharif ya lura da halin da Afeefah ta shiga, wayar na soma ringing ta daga a sanyaye tace "yayanmu!"

Eeshatullah Goni😘

🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

42___43
Shiru Afeefah tayi jin ya Aliyu bae ce komae ba, can ta kalli screen din wayar ta ga bai kashe ba kuma, a hnkli ta kuma cewa "yayanmu!" Yace "ina jin ki, ykk" jin yanayin muryar tasa yasa da damuwa tace "baka da lfya ne yayanmu?" Yace "lfyata qlau, I called daxu ma'aruf yace kin fita da matarsa" Afeefah ta gyada kai da sauri tace "uhn!" Yace "Shknn gud nyt, just called to say hi" murmushi tayi murya can kasa tace "am missin yhu yayana" shiru ya dan yi sae kuma a sanyaye yace "No yhu are nt Zainab! nasan haushi na kike ji ynxu kina ga kmr ina takura ki koh? Kiyi hkuri with tym xa ki gane meyasa nake maki hka kuma xan daina kin ji" shiru Afeefah tayi ita ma jikinta yyi sanyi, kmr xata yi kuka tace "yayanmu wllh ni bna fushi da kai, kaga ae bn da waya ne ynxu shi yasa bana kiran ka" ya Aliyu yyi shiru bae ce komae ba, a hnkli tace "Allah nayi missing dinka yayanmu, I missed yhu a lot" dan murmushi yyi bae dae ce komae ba, kmr xata yi kuka tace "ka ji!" Murya can kasa yace "naji! Kina son gani na to?" Xaro ido tayi da sauri tana kame kame tace "Lah ae to kila ma na kusa dawowa ko yayanmu, mun kusa komawa sch ka tambayi su Anty jiddah" yace "toh shknn, Allah dawo da ke lfya" a sanyaye tace "Ameen yayanmu" katse wayar yyi lkci daya, duk sae ta ji ba ddi abinda ta ce masa, da da ne kullum cikin kiransa take in ta xo kd wani lkcn ma har cewa take ya xo ta gansa, amma wnn karan har bata son ya kira, juyawa tayi a sanyaye tana kallon Dr Sharif taga kallonta yake, dauke kai yyi da sauri, ita kuma ta sunkuyar da kanta, ya mike ya karbi wayarsa a hannunta yace "je sama ki ce masu xan tafi" tace "har xa ka tafi sir" yace "yea" mikewa tayi a sanyaye ta nufi sama. Ma'aruf ne ya sakko tare da Amina yace "wato dae da gske baxa ka kwana nn ba ko Dr" Dr Sharif yace "abokina na jira na tun daxu, so I have to go," Amina tace "to amma yaya don Allah ka xo kayi breakfast a nn" yace "xan xo in'sha Allah" Makullin motar Ma'aruf ya dauka yace "da motar ka xan tafi, gudnyt" juyawa Ma'aruf yyi yana kallon Afeefah da ke tsaye yace "Baxa ki masa rakiya ba" Amina tayi dariya tace "to kai kaji ya mata sae da safe shi din?" Dariya Ma'aruf yyi yace "wae nn kunyar surikinsa yake" juyawa Afeefah tayi da sauri ta nufi sama, Amina tayi dariya tace "Ina kuma xa ki Anty yana fa jiran ki ne a waje" sae da Ma'aruf ya sa baki snn Afeefah ta sakko a kunyace ta nufi kofa ta fita. Har Dr Sharif ya tada motar ta karasa kanta a kasa tace "Sae da safe sir" yace "Allah ya kai mu" bae kuma jiran jin abinda xata ce ba ya ja motar ya bar wajen, jikinta yyi sanyi ta bi sa da kallo, juyawa tayi da sauri tun kan ta fara hawaye ta nufi cikin gida da gudu ta haura sama ta shige daki, sae a snn ta fada kan gado ta fashe da kuka, tayi mai isarta daga karshe bacci ya dauketa nn kwance. Washegari misalin Karfe sha daya Afeefah na kwance daki kmr mayya taki fitowa har Amina ta gaji da xuwa cewa ta sakko ta kyaleta, bude kofar dakin aka yi ta daga kai don ganin waye, Amina ce ta tsaya daga bakin kofa tace "to ae kya fito ynxu tun da sir ya xo koh?" Murmushi kawae Afeefah tayi, Amina ta juya ta bar dakin, mikewa Afeefah tayi da kyar ta sa hijab dinta ta fita daga dakin fuskarta a daure, yana xaune falo yana shan coffee, ta karasa kanta a kasa ta xauna kan rug din falon, kin cewa komae tayi shi ma hkn, can dae a sanyaye tace "ina kwana sir" yana kallonta yace "lfya Zainab," har yyi shiru sae kuma yace "wat made yhu cry?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, ya ci gaba da shan coffeen sa, mikewa tayi xata bar wajen yace "ina kuma xa ki?" Girgixa masa kai kawae tayi sae ga hawaye, dauke kai yyi ya dauki envelope karami dake kusa da shi ya mika mata yace "ga hotunan! ur copies" risinawa tayi ta karba murya can kasa tace "ngdd" "sit" yyi instructing dinta, ba musu ta xauna, yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login