Showing 45001 words to 48000 words out of 116554 words

Chapter 16 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1266

"Don Allah yayanmu kayi hkuri ka yafe min, baxan sa..." Kasa karasa tayi don tasan karya xata kuma yi masa, runtse ido yyi wani mugun sonta na fixgarsa, lkci daya hawaye ya taru idonsa, a hnkli ya janyeta daga jikinsa ya koma gefen gado ya xauna ya rike kansa da yyi masa nauyi, ta sulale nn kasa ta xauna tana rera kuka, sautin kukanta ne ya ishesa ba shiri ya sakko kasa yana facing dinta ya kamo hannunta a hnkli yana kallon fuskarta murya can kasa yace "tel me the truth little sis, kina son lecturan nn Dr Aliyu Sharif koh?" Kasa dago kai tayi bare ta basa amsa, ya dago kanta yana kallon idonta da ya rine don kuka, yace "tell me little sis" a hnkli ta shiga gyada masa kai, kura mata ido yyi ita ma hka, lkci daya ya kirkiri murmushi ya sauke idonsa daga nata, murya can ciki yace "shi ya siya maki waya koh?" Nn ma gyada masa kai kawae tayi, ya rike hannayenta gam yana kallonta, hkn yasa ta sunkuyar da kai a tsorace, murya can kasa yace "its OK little sis, I understand kina son shi sosae, dama wani abokina ne ke son ki tun kina karama shiyasa kika ga nake hanaki kula samari, but tun da kina son Dr Aliyu baxan kuma hanaki mu'amala da shi ba, amma ki kula da mutuncin ki na _'ya mace_ kin ji my princess, yhu knw I do alwayz have trust...." Kasa ci gaba yyi sbda tokarewar da muryarsa yyi lkci daya hawaye ya taru idonsa gudun kar ta dago ta gani yasa ya mike da sauri ya nufi kofa ta bisa da kallo har ya fita daga dakin, ta kusa minti goma xaune a dakin duk jikinta yyi sanyi, tana tunanin to waye wnn da yayanmu ke son hada ta da, mikewa tayi daga karshe ta fita daga dakin ta sauka downstairs, kwance ta samesa kan kujera a falo, ta karasa a sanyaye ta xauna kasa gefensa tana kallonsa, amma ta kasa cewa komae, hannunsa ta kamo xata yi magana sae kuma tayi shiru, a hnkli tace "yayanmu baka da lfya ne?" Gyada mata kai kawae yyi ya dafe kansa yace "am having headache" da damuwa tace "ka sha magani?" Yace "na sha!" Lumshe ido yyi hkn yasa tayi shiru bata kuma cewa komae ba, tana nn xaune har bayan minti ashirin snn ta daga kai tana kallonsa ta ga bacci yake, mikewa tayi tana kallon agogo ta ga har goma ya gota, gyaran gidan ta shiga yi tun daga shara har goge goge ta gyara ko ina fes, snn ta nufi kitchen don ganin ko akwae foodstuffs, gnin bbu yasa ta tafi sama ta shiga dakinsa ta dauki wallet dinsa dake gaban mirror ta bude ta ciro dubu uku snn ta rufe ta mayar ta ajiye, pen da jotter ta dauka tayi rub da ciki kan gado ta shiga list din abubuwan da xata bukata na girki, da ke suna xuwa kasu da su Jiddah duk tasan price din cooking stuffs din, tana gama list din ta mike ta fice daga dakin, gun mai gadi ta nufa tayi masa sannu da xama snn tace "dama baba Wanda xae je min kasuwa nake nema" mai gadin yace "toh bari in kira maki kanina yana can saman layi" Afeefah tace "toh" snn ta xauna ya tafi kiran kaninsa, ba a dau lkci ba suka dawo a tare ta mika ma kaninnasa list din da kudi tace "sae ka yi kudin mota cikin kudin" godiya tayi ma mai gadin snn ta koma cikin gida ta haura sama don gyara bedroom, tana kwance dakin tana kallo bayan ta gama gyaran ta ji yayanmu ya kwala mata kira ta mike da sauri ta sauka kasa ta isa kusa da shi ta durkusa tace "yayanmu gani" idonsa lumshe yace "Check who's at d door" da sauri ta nufi kofa ta bude mai gadi ya mika mata kayan cefanen ta karba tayi masa gdya ya mika mata canjin, tace "A'a ka basa ya rike baba na gode" gdya shima yyi mata snn ta rufe kofar ta karaso cikin falo, ya Aliyu ya bude ido yana kallonta yace "wats dat?" Ta wara masa ido tace "cefane mana, girki xan maka yayanmu" ya dan yi murmushi ya kuma lumshe idonsa ta nufi kitchen, kiranta ta ji ya kuma yi bayan yan mintuna tana kkrin blendin tomatoes ta fito da sauri, yyi mata nuni da jakarta ta nufi jakar jin wayarta ne ke vibrate, da kyar ta iya ciro wayar tana kallon mai kiranta taga Dr sharif ne, kasa daga kiran tayi, hkn yasa a hnkli yace "pick ur call, Dr Aliyu koh?" Gyada masa kai kawae tayi kanta a kasa ta daga kiran ta kara a kunne tayi shiru, "Zainab!", Da kyar ta iya bude baki tace "Na'am, ina kwana sir" Dr Sharif yace "Me ya hanaki shiga lecture yau?" Shiru tayi har sae da ya kuma kiran sunanta snn a hnkli tace "Sir kaina ne ke min ciwo shi sa" yyi murmushi yace "shiyasa kika xauna karkashin bishiya knn kika hade rae kika ki shiga lecture kowa ya xo wucewa ki bi sa da harara daga karshe kika tafi gida koh?" Murmushi tayi ta girgixa masa kai tace "ni ba gida na tafi ba" yace "to ina kika tafi?" a hnkli tace "gidan yayanmu" "wani yayan naku?" Murya can kasa tace "Ya Aliyu" shiru Dr sharif yyi snn a hnkli yace "kina me?" Wara ido tayi tace "Am cookin for him he is sick" shiru Dr Sharif ya kuma yi na yan sakwanni snn yace "alryt, ayi girki lfya" lkci daya ya katse wayar, Afeefah ta dan yi stil kmr me naxari snn ta juya tana kallon yayanmu taga idonsa a lumshe, mikewa tayi a sanyaye ta koma kitchen, cikin minti arba'in ta gama hada lafiyayyen rice nd stew dinta da fried cow meat, ta yayyanke vegetables din ta ajiye gefe daya, snn ta shiga hada masa favourite drink dinsa na Ginger, jikinta ne ya bata ana kallonta ta juya da sauri ta gansa jingine jikin kofar kitchen ya rungume hannayensa yana kallonta, ta xaro ido ta isa gabansa da sauri tace " yayanmu ka tashi? Ya ciwon kan" jin yyi shiru yana kallonta yasa ta kamo hannunsa lkci daya ta sake da sauri tace "yayanmu jikin ka da xafi, har ynxu kan ne?" Kai ya gyada mata ya juya ya koma falo, bin bayansa tayi ta ga sama ya nufa, hkn yasa ta koma ta cigaba da abinda take, ta gama ta tsaftace kitchen din ta ajiye sauran kayan girkin da ya rage a deep freezer snn ta jera abincin a dinning, kwance ta samesa a daki yyi rub da ciki ta xaune gefensa tana kallonsa tace "yayanmu?" Juyawa yyi yana kallonta a hnkli yace "Zainab!" Tace "am through," yace "Weldon" tace "in kawo maka sama?" Yace "No sae anjima" tace "to ka siya maganin ciwon kan ne?" Gyada mata kai yyi, shiru tayi hkn yasa yace "ba lecturan ki ya kira ki ba daxu, may b kina da lecture ynxu, start goin to sch little sis" Tace "dama ynxu xan wuce yayanmu, amma xan dawo da yamma ka ji" Ya Aliyu yace "ki ci abinci to kafin ki tafi" shiru ta dan yi snn tace "sae dae in tafi da shi yayanmu" yace "OK bude wallet ki dauki transport," tace "nagode yayanmu" mikewa tayi ta bude wallet din ta dauki transport tace "byee yayanmu" binta yyi da kallo har ta fita snn ya maida kansa kan pillow ya runtse idonsa. Kitchen Afeefah ta nufa ta dauki kula ta xuba abinci ta debi ginger drink snn ta samu leda ta saka su ciki ta fito falo ta dauki handbag dinta ta fice daga gidan. Ana kiran Azahar ta shigo sch, masallaci ta nufa ta fara yin sllh ana idarwa ta yi ma yayanmu addu'ar Allah basa lfya snn ta mike ta fice, bin ta Maryam tayi tace "Wae na maki laifi ne Zainab, naga yhu are ignoring me" Afeefah tayi murmushi tace "ni baki yi min komae ba Maryam, daxu kaina ke ciwo shi sa bn shiga lecture ba" Maryam tace "To Allah sauwake, ynxu sae 4 kuma muke da lecture, mu tafi cafeteria sae in baki handouts ki duba abinda muka yi yau" Afeefah tace "to ki je can ki jira ni akwae inda xan tafi ynxu" Maryam tace "OK" snn ta nufi cafeteria, Sae da Afeefah ta daina ganinta snn ta nufi office din Dr Sharif da sauri, kwankwasa kofar tayi a hnkli, sae da ta kwankwasa har sau uku Snn yace "Come in!" A hnkli ta tura kofar ta shiga da sallama, yana xaune ya jinginar da Kai jikin kujera ya sauke kafarsa daga kan table dinsa ya gyara xaman sa, ta Karaso cikin office din, ido ya kafa mata ta cikin farin glass din idonsa, kanta a kasa ta karaso table dinsa tace "ina yini sir?" Yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "Har kin gama girkin knn Miss Chef?"

Eeshatullah Goni๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜

[5/22, 07:57] Umar Dalha: ๐ŸŒธ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป 'Ya mace kyautar Allah๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป๐ŸŒธ

A true life love story

By Ashmaad

46___48
Shiru Afeefah tayi tana kallonsa, sae kuma tayi murmushi tace "Um na gama" ledan hannunta ta ajiye ta fiddo kulan ciki da drink da plate da spoon tace "I brought this for yhu sir" bata jira cewarsa ba ta bude kulan abincin, dauke kai yyi ya shiga danna wayarsa yace "Abincin yayan naki xa ki kawo min?" Ta girgixa kai tace "ae da yawa na dafa sir" ganin xuba masa take son yi a plate ya dakatar da ita da sauri "No! ni am OK" tsayawa tayi tana kallonsa, yyi kmr bae san tana yi ba, can ta rufe kulan ta mayar da shi cikin nylon da plate din snn ta dauka ta nufi kofa, bin ta yyi da kallo har ta fice ta rufo masa kofar sa. Cafeteria ta nufa ta samu Maryam xaune da drink a gabanta, Maryam tace "har kin dawo?" "Um" kawae Afeefah ta ce mata, Maryam tace "ina ce office din sir kika tafi" hade rae Afeefah tayi tace "hka nace maki" bata jira cewarta ba ta bude leda ta fiddo abincin tana kallonta tace "Bismillah" Maryam ta dan yi murmushi tace "A'a ni na koshi" Afeefah tace "OK" diban abincin tayi cikin plate ta dauki spoon ta fara cin abun ta, jin wayarta na vibrate a jaka ta bude jakar ta fiddo wayar, jiddah ta ga ke kiranta, ta daga Jiddah tace "wae ina kika je yau Afeefah?" Afeefah tace "wajen yayanmu" Jiddah tace "shine kika ki shiga lecture?" Afeefah ta hade rae tace "to wae wa ya gaya maki bna sch? Ni ynxu ma ina nn kusa da dept dinmu," katse wayar Jiddah tayi Afeefah ta mayar jakarta, Ba tare da ta kalle Maryam ba tace "ke kika ce ma Anty Jiddah bn shiga lecture ba?" Maryam tace "No!" Afeefah na gama cin abincin gabanta ta mayar da plate din da spoon cikin leda ta kalli agogon cafeteria ta ga har biyu, mikewa tayi tace "Baxan iya jiran lecture har 4 ba, ni na tafi gida" Bin ta da kallo kawae Maryam tayi har ta fice abun ta, ta kama hanyar main gate. Afeefah na isa gida ta bi ta kofar kitchen ta lallaba ta wanke kulan abincin hannunta snn ta dauki ginger drink ta nufi sama, dakin Mami ta shiga Mami tace "har kin dawo, ina su Jiddah?" Afeefah tace "basu gama lecture ba su" gaisheta tayi Mami tace "ya ciwon kan?" Afeefah tace "Da sauki Mami" juyawa tayi ta fita daga dakin ta shiga nasu tayi kwanciyarta, biyar saura Mami ta kirata ta sakko kasa ta taya ta girka Supper, Afeefah na slicing Pumpkin leaves tace "Mami xa kiyi abinci da yayanmu koh?" Mami tace "a ina kika ga yayanku?" Afeefah tace "Ba yana gidan sa ba" Mami tace "to gidan nasa xan kai masa abincin" a hnkli tace "Kinga Mami bashi da lfya fa" Juyawa Mami tayi ta kalleta tace "shi ya gaya maki bae da lfya?" Afeefah ta gyada Mata kai, Mami tace "Adnaan baya nn ban san Wanda xae Kai masa ba sae dae ya xo ya karba da kansa," Afeefah kmr xata yi kuka tace "Mami ba sae ni in kai masa ba, bashi da lfya fa" harara Mami ta watsa Mata tace "idan naki ba ki fa?" Shiru tayi bata ce komae ba, Mami ta ci gaba da abinda take, Mami na kwashe tuwo Afeefah ta juya xata bar kitchen din ita a dole fushi take baxa a kai ma yayanmu abinci ba, Mami tace "ina xa ki? Ni xan wanke maki kwanukan can" kmr xata yi kuka ta nufi sink ta soma wanke kwanukan da suka bata, tana gamawa ta bar kitchen din ta haura sama. Wayarta dake jakarta ta ciro dae dae lkcn da ya fara vibrate, Dr Sharif ta ga ke kiranta, da kmr baxata dauka ba har ya kusa katsewa sae ta dauka tayi shiru, tana jin yyi murmushi snn yace "Dama mutum na cin abincin da ba da sunansa a girka ba Zainab?, ae kwadayi knn" Shiru tayi bata ce komae ba, yace "Zainab" murya can ciki tace "Na'am" yace "yhu ran away frm my lecture yau koh? Nasan maganin ki" turo baki tayi bata ce komae ba yace "Gidan yayan naku kike koma knn!" Girgixa masa kai tayi tace "gida na dawo" a hnkli yace "Toh am srry dear in dan ban ci abincin ki bne, am just nt hungry a lkcn coz i finished drinking coffee kika shigo office," Shiru tayi bata ce komae ba yace "kin hkura?" Dan murmushi tayi yace "Gud almost tym 4 sallat will call yhu ltr" katse kiran yyi dae dae lkcn da su Jiddah suka shigo, Jiddah tace "ke dae ki daina abinda kike Afeefah, kwata kwata yau ba ki shiga aji ba wllh" Afeefah ta Mike fuuu ta fice daga dakin, a stairs suka hadu da Mami tace "ki shirya ke da Sumayya ku kai ma Aliyu abinci" ta wara ido tace "toh Mami" snn ta juya da sauri ta koma daki, Wanka ta shiga tana fitowa ta dauki kaya mara nauyi ta sa snn ta saka hijab ta dauki wayarta ta fice daga dakin, falo ta tadda Sumayya na jiranta, Mami tace "saura in yi biyan bashi da ku" Afeefah tace "ae baxa mu dde ba" a dai daita sahu suka samu a bakin titi, suna isa Afeefah ta basa kudinsa tace ma Sumayya ta karbo canji ta nufi cikin gidan, bbu kowa falo hkn yasa ta haura sama ta bude dakinsa da sallama ta shiga, Yana xaune gefen gado da wani abokinsa dake rike da mug din tea yana sha, fadawa kansa tayi tace "yayanmu ya jikin" wani tsawa abokin ya daka mata yace "ke dalla ja can, baki iya sallama bne xaki fado ma mutane daki hka" daga kai tayi tana kallonsa lkci daya ta hade rae, Aliyu ya juyo fuskarta ya sakar mata murmushi yace "Da sauki little sis daga ina da magrib hka?" Mikewa tayi tana hararan abokin ta gefen ido ta fice daga dakin da sauri, Aliyu ya juya yana kallonsa yace "kaga ba fa na son hka khabir," khabir yace "ae ni haushi take bn tunda har ta kasa gane sonta kke 4 ol dis while, toh wae ma ni 4 God sake meye amfanin boye ma wnn yarinyar the truth abou everything, she is matured enuf, a fada mata matsiyinta a gidanku ka fito fili kace sonta kke, hka kawae tun yarinya bata san kanta ba kke wahala da ita kawae daga karshe duk abun nn ya tashi a aikin bnxa, ni in ma baxa ka iya gaya mata ba sae ni in mata bayani wllh" girgixa Kai Aliyu yyi yace "akwae dalilin da yasa ake boye mata ba hka nn kawae ba, its a long story yhu knw" mikewa Aliyu yyi ya fita daga dakin dae dae bakin kofa ya hadu da Sumayya rike da basket din abinci ta gaishesa tace "yayanmu Mami tace mu kawo maka," yace "to ngd shiga da shi daki" dakin ta shiga shi kuma ya sauka kasa ya samu Afeefah xaune a falo kiris ya rage ta fashe, ya karaso kusa da ita yana murmushi ya xauna gefenta ya jawota jikinsa tun kan yace komae ta fashe masa da kuka har da shessheka tace "yayanmu ni bna son wnn abokin naka ka gaya masa bbu ruwansa dani ya daina min mgna idan ba hka ba xan gaya sa da Abba" murmushi Aliyu yyi yace "yi hkuri Zainab, amma me yasa ba kiyi sallama ba" cikin kuka tace "Allah nayi kunnensa dae ne bae ji ba" Aliyu yace "toh ya isa hka nn princess xan ja masa kunne" shiru tayi ya shiga share mata hawayen fuskarta tace "Nace ma Mami baka da lfya shine ta ba mu tuwo mu kawo maka ni da Sumayya," murya can kasa yace "to ngdd little sis" a hnkli tace "ya ciwon kan yayanmu?" Ya dago kanta yace "Alhmdllh ya daina" tayi murmushi tace "Allah ya sauke," yace "Ameen" saketa yyi ya Mike yace "tashi ki je kiyi alwala mu xamu tafi mosque" tace "to yayanmu" snn ta mike. Suna idar da sllh ya Aliyu yace su xo su tafi tunda dare yyi, ba dan Afeefah ta so ba ta sa hijab dinta ya basu kudin transport snn ya rakasu har bakin titi suka hau a dai daita ya koma gida. Hka rayuwa ta ci gaba da kasancewa kullum son Afeefah na kara wahalar da Aliyu amma bnda abokinsa khabir bbu Wanda yasan halin da yake ciki, ko kaninsa Adnaan bae sani ba, a hka ya karaci kwanakinsa a kano kullum cikin tunanin Zainab har ya koma Lagos bakin aikinsa, Afeefah kam shakuwarsu ya 'da da karfi da Dr Sharif, har Maryam da take boye ma sarae tasan soyayya suke da Dr Sharif kai hatta 'yan ajin gaba daya sun dago don duk ran da xae shigo masu lecture ya ga bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login