Showing 54001 words to 57000 words out of 116554 words

Chapter 19 - Ya mace kyautar Allah complete hausa novel

Aaashmad   

24 Aug 2025

1277

murya yace "Baxan iya driving ba Zainab," Hawaye ta shiga yi a hnkli tace "to in kira Dr Sharif ya duba ka?" Dago idanuwansa da suka masa nauyi yyi yana kallonta.

Eeshatullah Goni😘😘

[5/22, 07:57] Umar Dalha: 'Ya mace kyautar Allah
A true life love story
By Ashmaad
56____58
A hnkli ya sauke idonsa daga kallon da yake mata, hawaye na ci gaba da sakko mata tace "Ka ji yayanmu" jin bae ce mata komae ba yasa ta mike ta nufi kofa xata fita ta ji ya kirata, dawowa tayi har lkcn tana kuka, murya can ciki yace "Dnt wrry I will be alryt in'sha Allah" juyawa tayi ta fice daga dakin ta nufi Wanda take, wayarta ta dauka ta shiga kiran Dr Sharif, katsewa yyi ya kirata, tana goge fuskarta a sanyaye tace "Sir ka xo ka duba shi" yace "OK Address fa?" Shiru tayi tunawa da tayi bata san Address ba da sauri tace "ina xuwa sir" katse wayar tayi ta fara tunanin Wanda xae gaya mata address din anguwar ga gidan ba mai gadi, jiki a sanyaye ta fita daga dakin, waje ta nufa tana isa gate ta bude a hnkli ynda yayanmu baxae ji ba, snn ta fita daga gidan. A manne ta ga address din layin da ma anguwar daga gefen gate, haddacewa tayi ta juya da sauri ta koma gidan, text Msge din address din ta tura masa, kiransa ne ya shigo wayar ta daga yace "OK I will b on my way ynxu" gyada masa kai kawae tayi ya katse wayar ta fita daga dakin ta koma dakin yayanmu, Ac'n dakin ta kashe ganin kmr sanyi yake ji, ta jima xaune gefensa tayi tagumi tana kallonsa shi dae bae bude ido ba, mikewa tayi daga karshe jin wayarta na vibrate ta fita falo, daga kiran tayi Dr Sharif yace "Ina kofar gida" gabanta ya fadi ta dae dake tace "To ina xuwa" dakin yayanmu ta nufa da sauri ta xauna gefensa ta janye bargon jikinsa ta shiga tashinsa, bude ido yyi a hnkli cikin sanyin murya yace "What again Zainab," hade rae tayi kmr me shirin kuka tace "Ya xo" mikewa yyi xaune da sauri yace "Wa?" A hnkli tace "Dr Sharif" wani kallo ya watsa mata yace "ya xo ina?" Kuka ta fashe da tace "ba duba ka nace ya xo yyi ba tunda baxa ka je asibiti ba," bacin rae karara fuskarsa yace "With whose consent, kina da hnkli kuwa" kuka ssae ta shiga yi tana kallonsa, lkci daya ya dafe kansa, cikin kuka tace "to bari in ce masa ya tafi kawae" tana fadin hka ta mike xata fita, cikin sanyin murya yace "Wait, kar ki ce ya tafi, ki je ki shigo da shi falo ku gaisa, sae kice ina bacci nothin more" yana kae wa nn ya koma ya kwanta, a sanyaye Afeefah ta fita daga dakin tana share hawayen fuskarta ta nufi kofar gida, tana bude gate taga motarsa ta karasa gun a sanyaye, kallonta kawae Dr Sharif yake don ba karamin kyau Bakar Abayan jikinta yyi mata ba har ta karasa kusa da motar bae daina kallonta ba ya sauke glass din motar, suna hada ido ta sunkuyar da kai da sauri, murmushi yyi yace "Don Yayanki bae da lfya sae ki xauna kiyi ta kuka Zainab" dan murmushi ta kirkira tace "Mu shiga ciki Sir" bude motar yyi ya fito, kallo daya tayi kasa ta dauke Kai ta fara tafiya don ba karamin kyau sky blue shaddan jikinsa yyi masa ba, da sauri yace "Wait Zainab" hkn yasa ta tsaya har ya karaso snn yace "Baki gaya min me ke damun yayanki ba? Ina son sanin me xan dauka a mota" Juyowa tayi ta kirkiri murmushi tace "Ae ya ma yi bacci, kuma ya sha magani yace min da sauki" da ganinta kasan kame kame kawae take, Dr Sharif da ya gane komae yace "OK then there is no need of me goin inside bari kawae in baki wani maganin sa karfin jiki ki basa ya sha" da sauri tace "A'a sir mu shiga mana" girgixa mata kae yyi kan yace komae ta bata fuska kmr xata yi kuka tace "to baxa ka sha ruwa ba Sir" dan murmushi yyi yace "to xan sha Zainab" bude motar yyi ya fiddo maganin ya mika mata ta dan risina ta karba snn tace "to mu shiga ka sha ruwa" bin bayanta yyi har suka shiga gidan tana gaba yana biye da ita, a hnkli yace "Baki sa Hijab ba yau ko?" Juyawa tayi da sauri ta kallesa sae kuma ta juya cike da jin kunya ta ci gaba da tafiya da sauri sae a snn ta tuna dan mayafin abayanta ne kawae a kanta gashi kusan fitted ne abayar, murmushi kawae yyi ganin ynda take sauri har ta isa kofa ta shige gidan da sauri, daki ta nufa ta dauko hijab ta sa snn ta dawo tayi masa iso cikin falo. Fridge ta nufa ta dauko masa soft drink da ruwa ta durkusa gabansa ta ajiye snn ta dago kai tana kallonsa, murmushi ya sakar mata, ita ma ta mayar masa a kunyace snn ta bude drink din ta xuba masa a glass cup ta dauka ta mika masa ya karba murya can kasa yace "Thanks dear" mikewa tayi tace "ina xuwa sir" snn ta nufi dakin yayanmu, xaune ta samesa gefen gado ya rike kai da hannu biyu, ta karaso da sauri tana kallonsa tace "ka tashi yayanmu" dago kai yyi yana kallonta da idanuwansa da suka kada ssae, kmr xata yi kuka tace "jikin ne yayanmu?" Girgixa mata kai yyi da kyar yace "Aa" shiru ta danyi snn ta marairaice masa murya can kasa tace "to yayanmu tun da ka tashi don Allah ka fito ku gaisa da shi kaga yana falo" tsare shi tayi da dara daran idonta masu rikitar da shi ya kasa daina kallonsu, kamo hannunsa tayi hkn yasa yyi saurin dauke kansa, ta kuma marairaicewa tace "Plss" kasa ce mata A'a yyi, da kyar yace "Tafi gani nn xuwa" cike da jin ddi ta mike tace "yauwa yayana," snn ta fita daga dakin. Kasan lallausan rug din tsakiyar falon ta xauna tana kallon Dr Sharif tace "Yayanmu na xuwa" yace "OK" Da kyar Aliyu ya iya Mikewa ya dauki shirt dinsa ya daura kan farin singlet din jikinsa snn ya fito falon da sallama, Dr Sharif ya daga kai yana kallonsa tare da amsa masa sallaman, Karasowa cikin falon ya Aliyu yyi ya basa hannu suka yi musabaha suka gaisa, Aliyu ya koma kujera ya xauna, Dr Sharif yace "Ya jikin" ba tare da Aliyu ya kallesa ba yace "Alhmdllh, am feelin much beta now" Dr Sharif yace "Ma'sha Allah, Allah kara lfya" mikewa Aliyu yyi yana kallon Afeefah yace "Baxa kiyi ma bakon naki girki ba" dariya tayi tana kallon Dr Sharif da ya dan yi murmushi tace "Ae shi baya cin abinci yayanmu, coffee kawae yake sha" murmushi Aliyu ya kirkira yace "Sae ki hada masa ae" excusing kansa yyi ya koma daki, Afeefah ta kalli Dr Sharif cike da jin kunya tace "Sir in hado maka?" Murmushi yyi ya girgixa mata kai yace "No am OK" kasa sakin jiki tayi a falon duk ta takure waje daya, ya lura da hkn ya mike yana kallonta yace "akwae inda xan tafi Zainab, tel ur brother I will b on my way" mikewa tayi ta nufi daki ganin idon ya Aliyu a lumshe yasa ta fito tace "Sir yyi bacci idan ya tashi xan gaya masa" yace "gud gwara da baki tashe sa ba," yana gaba tana biye da shi a baya suka fita daga gidan, ya jingina jikin motarsa yana kallonta yace "Naga kmr akwae damuwa a tattare da yayanki he looks pale," kmr xata yi kuka tace "nima bn san me ke damunsa ba" Dr Sharif yace "but na ga kun shaku da shi ssae, y nt ki tambayesa ko xae gaya maki" tace "To xan tambayesa in ga ko xae gaya min" yace "OK I will b on my way, make sure kin basa drugs din da na baki," gdya ta kuma yi masa ya shiga motarsa tana daga masa hannu har ya bar anguwar. Afeefah na shiga dakin yayanmu taga kmr bacci yake hkn yasa ta fita tana tunanin ynda xata lallabasa ya gaya mata damuwansa.
Da rana tana gama girka lunch ta shiga dakinsa da abincin, ajiye farantin hannunta tayi ta xauna gefensa ta shiga tashinsa, ba karamin xafi jikinsa yyi ba, ya mike xaune yana kallonta, hawaye ya gani idonta tace "yayanmu ka ki mu tafi asibiti kuma an xo duba ka a gida ka ki, ga shi jikin ka yyi xafi ssae ynxu" kincewa komae yyi hkn yasa ta mike ta shiga bayi ta debo ruwa a bowl ta fito snn ta dauki dan karamin tawul ta saka ciki ta dawo kusa da gadon ta ajiye tana kallonsa har lkcn hawaye take tace "Ur temperature is high," unbutton din shirt din jikinsa ta shiga yi a hnkli, kallonta kawae yake har ta cire shirt din ya ji bare hands dinta a jikinsa, wani irin tashi tsigar jikinsa yyi kmr Wanda aka hada da wayar wuta, tun da yake bae taba jin wani abu game da Afeefah ba sae ranan, shi dae yasan yana sonta ba kadan ba kuma so na aure, amma bae taba sha'awarta dae dae da na second daya ba sae yanxu da ya ji sa cikin wani bakon yanayi, da sauri ya dakatar da ita yace "Wait Zainab, xan tafi in watsa ruwa ynxu" mikewa yyi duk da jirin da yake gani ya shige bathroom da sauri. Tana nn xaune har ya fito daga bayin sae dae bata ga alamar ya watsa ruwa ba, tace "yayanmu har ka yi wankan?" Gyada mata kai kawae yyi ta bisa da kallo har ya xauna gefen gado snn ta shiga xuba masa abinci a plate. Da yamma ta shigo dakin da cup din tea sanin bae wani ci abinci ba daxu, xaune ta samesa yana rike da wayarsa da alama waya ya gama, ta karaso kusa da shi tace "ga tea na hada maka yayanmu" ya karba yace "thnk yhu" xama tayi gefensa tace "Mami ce ta kira ka koh?" Gyada mata kae kawae ya iya yi don duk sae ya ji sa uncomfortable da ta xauna kusa da shi, ga wani faduwa da gabansa yake, tana kallonsa tace "Yayanmu me xan dafa da daddare yau" cikin dubara ya xamo kasa ya xauna snn yace "Kar ki damu xan fita ynxu, idan ina dawowa xan siyo mana take away" tace "toh baxa ka tafi da ni ba?" Girgixa mata kai yyi yana kurban tean hannunsa yace "muna aiki ne kan wani case da colleagues dina" mikewa tayi tace "to shknn bari in kawo maka maganin da Dr Sharif ya kawo maka" bin ta kawae yyi da kallo har ta fita snn ya sauke ajiyar xuciya tare da lumshe idonsa. Har bakin mota ta rakasa yace "idan kin koma ki rufe kofar da key ina da spare key, in kuma aka dauke wuta ki kunna inverter" tace "To Allah kiyaye yayanmu sae ka dawo" murmushi kawae yyi mata ya tada motar ya fita daga compound din ta rufe gate snn ta dawo cikin gida tayi kwanciyarta bayan ta rufe kofa da key, Karfe Takwas da wani abu Aliyu ya shigo gidan, kwance ya sameta kan dogon kujera alamar sllh ta idar ta kwanta, karasawa yyi ya duka yana kallonta, lkci daya ta bude ido ya sakar mata murmushi yace "Bacci kike?" Girgixa masa kai tayi ta mike xaune, abincin hannunsa ya ajiye ya nufi kitchen ya dauko plate, yace "sakko ki ci abinci" ba musu ta sakko ya shiga xuba mata abincin a plate. Afeefah na gama cin abincin ta mike ta nufi dakin da take ta bar sa xaune yana kallo. Karfe goma saura ya shigo dakinta ya sameta kwance tayi rub da ciki idonta lumshe tana waya, ko ba a gaya masa ba yasan da Wanda take wayar ya juya da sauri ya fice daga dakin xuciyarsa kmr xae fashe. Mikewa xaune tayi bayan ta katse wayar sae kuma ta mike ta bi bayansa, kwance ta samesa yyi rub da ciki ta karasa kusa da shi tace "yayanmu!" Banxa yyi mata, hkn yasa ta kuma kiransa nn ma ya share ta, mikewa tayi a sanyaye ta fice daga dakin don idonsa biyu, shi kam wasu hawaye ne suka xubo masa ya Mike xaune da sauri ya rike kansa dake Sara masa. Afeefah na shiga daki kuka ta dinga yi ta kasa daga kiran da Dr Sharif ke mata, da kyar daga karshe ta mike ta shiga bayi don yin wanka bayan ta gama cin kukan nata. Ta fito daga wankan tana tsaye gaban madubi daure da xaninta Aliyu ya shigo dakin, karasawa yyi kusa da ita ganin yanda ta dauke kai ya sa ya tsaya yana kallonta murya can kasa yace "Zainab!" Jin bata tanka sa ba yasa ya jawo ta jikinsa don fara lallashi kmr ynda ya saba a ko da yaushe, wani yarr ya ji tun daga tsakiyar kansa har yatsansa kafarsa kmr Wanda wuta ya ja yyi saurin saketa ya koma baya, ta fashe da kuka ta juya tana kallonsa muryarta na rawa tace "ni bn san me na maka ba yayanmu," kasa jure kukanta yyi ya runtse ido ya kuma jawota jikinsa gabansa na faduwa, jin Afeefah a jikinsa ba karamin rikita sa yyi ba sabanin da da bae taba jin komae ba, kasa daukansa kafafuwansa suka yi ya nufi kan gado da ita, ya xauna ya wani kankameta jikinsa ya runtse ido muryarsa na rawa ya shiga cewa "No! no Plss Zainab kar ki guje ni, plss plss plss, ki tausaya min i i i just can'ttt do with... without yhuuu, I love yhu" kmr wani xautattce hka ya koma don har wani rawa jikinsa yake, Afeefah tuni ta daga kai da mamaki tana kallonsa lkci daya ta shiga tura sa tana cewa "yayanmu" bude idonsa da ya kada yyi yana kallonta lkci daya hawaye ya shiga xuba a idonsa, tsorata tayi ba kadan ba, ta shiga kkrin kwace kanta daga jikinsa, bata ankara ba sae jin bakinsa tayi a wuyarta a rikice yake cewa "I just love yhu Zainab, son ki a jini na yake ki tausaya min ki xama matata pls, Marry me Zainab kar ki guje ni" wani matsanancin kuka ta fashe da a tsorace jikinta na wani mugun rawa tace "Meye hka yayanmu, na shiga uku, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ihu ta fasa a gigice ganin yana kkrin saka bakinsa cikin nata, wani karfi ya xo mata ta hankadesa ta mike da gudu ta fada bathroom ta sa key, sae a snn hnklin Aliyu ya dawo, ya mike da sauri yana kiran Allah a xuciyarsa, bayin ya nufa ya shiga bubbugawa yana kiran sunanta jin irin ynda take kuka amma kmr da da tunxurata yake, dakinsa ya koma don dauko spare key amma tsabar rudewa yasa ya rasa inda ma ya ajiye ya dawo ya ci gaba da yi mata magiyan ta bude kofa amma taki sae kuka take tana kiran Mami a tsorace, a takaice dae a bayi ranan Afeefah ta kwana kuma ynda ta ga rana hka ta ga daren gashi ta ci kuka har ta gode Allah, shima Aliyu a xaune dakin ya kwana duk ya fice hayyacinsa, kiran sllh yasa ya koma dakinsa a sanyaye yyi alwala ya wuce masallaci, Afeefah na jin fitarsa ta fito jikinta na rawa ta saka abayanta da hijab, ta bude hand bag dinta ta dauki dubu uku da wayarta kan kace me har ta fice daga gidan da gudu, har ta bar layin bata daina gudu ba duk da bata san takamaiman inda xata ba ga ko ina duhu, tana isa main road ta tsayar da adai daita sahun da ta gani bata basa amsar tambayar da yake mata ba ta shige da sauri sae a snn tana mayar da numfashi tace "Tasha xa ka kai ni"
Xa ku ji ni shiru kwana biyu ta dalilin jarabawar da nake da shi sisters, srry for the inconvenience dat will cause.
[5/22, 07:57] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad

59.....
Afeefah da tayi xurfi cikin tunanin da take muryar mai adai daita ya dawo da ita tayi Firgit tace "Na'am" dan tsaki ya ja yace "Mun kawo tashar" a sanyaye ta shiga bin wajen da suke da kallo hkn yasa yace "daga ciki xa ki shiga" gyada masa kai tayi tace "Xan samu motar Kano a nn?" Mai adai daitan yace "Kwarae kuwa" fitowa tayi daga adai daitan tace "Nawa ne kudin ka?" Yace "ki bada dari bakwae" shiru tayi tana kallonsa, can ta marairaice tace "baka yarda dari biyar ba don Allah, kudin bbu yawa hannu na" dan tsaki ya kuma ja yace "Bani" mika masa tayi hade da yi masa gdya ya ja kekensa ya kara gaba, cikin tashar ta shiga ta nufi gun da taji ana kiran Kaduna, Kano, tana isa ta tambayi nawa ne kudin motar kano aka ce dubu biyu da dari biyar, shiru tayi kmr me shirin kuka ganin shknn kudin hannunta ya kare, mika masa kudin tayi daga karshe ya yankar mata ticket ta shiga ta samu waje daga jikin window ta xauna don passenger ba su fi hudu ba cikin motar ba. Aliyu kam yana dawowa daga masallaci ba karamin tashi hnklinsa yyi gnin gate din gidan a bude ba, ya nufi dakin Afeefah da sauri ya bude ya ga kofar bayin a bude, hkn yasa ya dan tsaya gabansa na faduwa yana kallon kofar, bayin ya nufa da sauri ya shiga ya ga bbu kowa, ya fita dakin da sauri ya komo falo nn ma ya gama dube dubensa bbu ita bbu alamar ta, rike kansa da ke juya masa yyi yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un, da kyar ya xauna gefen kujera ganin tsayuwar ta gagaresa, wasu hawaye suka xubo masa yana tunanin ina Zainab xa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login