Showing 120001 words to 121208 words out of 121208 words

Chapter 41 - ABOKIN AIKINA HAUSA NOVEL

24 Nov 2024

6394

Ƙirjina ya shiga bugawa da sauri da sauri, saboda ni ma wa'azin da tunatarwar da Alƙalin yake yi sun shafe Ni. Domin ɗabi'ar Mukhtar tuni ta yi naso a jikina, duk da ba ta zamar mini jiki kamar shi ba; amma dai Ina aikatawa lokaci bayan lokaci. Idan kuma har haka ne, ni ma ina cikin tsinuwar Allah da mala'ikunsa kamar yadda ya faɗa. Babu shiri hawaye suka dinga fareti a kan fuskata, tare da da-na-sani a kan biye wa ruɗin zuciya da kururuwar shaiɗan. Domin sun saka ni aikata abin da Allah zai yi fushi da ni, bayan kuma ya tsine mini.

Muryar Mukhtar na tsinkayo yana faɗin,

"Na gamsu da bayananka duka ranka ya daɗe! Kuma in Sha Allah zan gyara kuskuren da na aikata daga yau. Amma a yi mini haƙuri a yafe mini a janye zancen sakin nan, in Sha Allah daga yanzun nan zan shiga fafutukar neman magani domin na zamo kamar yadda take so!"

Alƙalin ya girgiza kai ya ce,
"Hukuncinku rubuce yake a cikin littafan addinin Musulunci irinsu; Minhajil Muslim, Muwaɗɗa Malik da sauran littafan da suka zo da bayani a kan matsalarku. Saboda Allah ya fi kowa sanin kalolin halittarmu 'yan Adam, dalilin da ya sa kenan aka bai wa mata damar neman wanda ya yi daidai da buƙatarsu. Saboda gudun su faɗa halaka ta sanadin wannan matsala. Saɓanin kai da kake namiji kana da damar auren mace fiye da biyu zuwa uku har huɗu ma. Ita kuma kai kaɗai ne take da shi, idan ba ka cire mata kwaɗayin wasu mazan ba; za ta iya fita waje nemansu ido rufe domin su yi mata abin da take buƙata, Wanda kai ka kasa sauke mata nauyinsa a cikin gidanka. Don haka an bai wa mata damar muddin mijinsu ba ya gamsar da su yadda suke so, ko kuma ba ya iya ɗauke ragamar buƙatuwarsu a duk lokacin da suka nema a wurinsa; su kai kotu a raba auren, domin su je su auri wanda ya yi daidai da halinsu da kuma ra'ayinsu. Saboda tsoron su faɗa halaka a ɓoye ba tare da an sani ba."

"Don Allah ranka ya daɗe kada a raba ni da matata wallahi ina son zama da ita!"

Alƙalin ya miƙa hannu tare da nuni a kan a ba shi takarda. Bayan an miƙa masa ya fara rubutu a jikin wata takardar yana cewa,

"Ka yi haƙuri! Idan da rabon za ku sake zama a gaba sai ku daidaita kanku. Saboda ka ci sa'a ba ka yi rantsuwar da na umurce ka da ita ba tun farko, don da a ce ka rantse tana zina ita ma ta rantse a kan ba ta yi; da ko ku kaɗai ne kuka rage a cikin duniyar nan ba za ku sake auren juna ba har abada. Amma yanzu idan har kuna da buƙatar sake zama, za ku iya sasanta kanku daga baya ku daidaita tsakaninku!"

Mukhtar ya fara roƙonsa cikin magiya cikin rawar murya, a kan kada a sake ni yana son zama da ni. Amma Alƙalin bai fasa ɗaga takardar da ya gama rubutawa ba yana faɗin,

_"A yau jumu'a uku ga watan biyar, shekara ta dubu biyu da goma Sha biyar 3/5/2015. Babbar Kotun jaha, ta aminta da miƙa saki ɗaya ga Zaituna Aliyu! Wadda ta zamo mata a wurin Mukhtar Mai Shadda, saboda tauye haƙƙin auratayya a tsakaninsu tsawon shekara huɗu."_

_"Ɗaga sa hannun Alƙali Muhammadu Jaɓɓi Falgore."_

Wani sanyin daɗi ya kwarara tun daga kaina har zuwa tafin ƙafata. Kafin na daidaita natsuwata na ji Alƙali ya kira sunana tare da ba ni umurnin na saka hannu a jikin takardar kotun. Na miƙe jikina yana rawa ina ji tamkar na kifa na karɓi takardar, hannuna yana kyarma na saka hannun a inda ya nuna mini. Sannan ya kira sunan Mukhtar a kan ya zo ya saka nasa hannun, ban juyo ba har sai da na zauna inda na tashi. Sannan na kai kallona inda yake ko gezau bai yi ba balle ya saka hannun kamar yadda aka umurce shi.
Sai da ya maimaita masa maganar sannan ya miƙa takardar ga magatardarsa, shi ya kai masa ita har inda yake sai da ya saka hannun sannan ya mayar wa Alƙalin takardar. Umma da Baba Ali ma duk sai da suka saka hannu sannan aka linke takardar bayan an buga stamp aka ba ni.

Murna har tsakiyar zuciyata, duk da wani gefen zuciyar ina jin kamar ba a kyautawa Mukhtar ɗin ba. Muryarsa na ji tana sarƙewa tamkar mai jinyar da numfashinsa ya yi ƙasa.

"Na yarda da hukuncin Kotu, Amma ina da buƙatar a ba ni yarana duka su dawo hannuna. Zan ci gaba da ɗawainiya da su don daman can ni Allah ya ɗora wa hidimarsu."

Kai-tsaye Alƙalin ya ce,
"An karɓi uzurinka, kuma Kotu ta mayar maka da yaranka a hannunka. Domin ka ci gaba da hidimta musu kamar yadda Musulunci ya shimfiɗa wa kowane uba."

"Ban aminta ba ranka ya daɗe!"

Zancen da na yi kenan jikina yana ɓari saboda tsabar tashin hankalin da na shiga. Bayan kaɗuwar da nake ciki a kan zancen Mukhtar ɗin da na Alƙalin duka. Domin sanin da gangan Mukhtar ya yi hakan don ya ƙumsa mini baƙinciki kamar yadda aka yi masa.

"Ki yi haƙuri ya fi ki iko a kan yaransa, duk da ke Musulunci ya bai wa damar riƙon su. Ko da ba kya duniya idan Mahaifiyarki tana raye ita ce a madadinki, a wani ƙaulin ma an ce har sai danginki sun ƙare kaf, sannan za a ba da yaran gare shi ko ga ahalinsa. Amma idan aka yi masa hakan a wannan lokaci an cutar da shi da yawa, duba da yadda aka raba auren yana da kyau a bar shi da yaransa. Domin su dinga ɗebe masa kewar rashin ganin ki a kusa da shi."

Idona a rufe na ce, "To idan har wannan sakin shi zai janyo a raba ni da yarana. Na aminta na yi ta zama a gidansa da aurensa har duniya ta ƙare a haka. Saboda yarana su ne rayuwata kuma su ne komai nawa a cikin duniya, ba zan iya rayuwa babu su ba!"







Yau ake yin ta🤭 uwa da ɗa sai Allah😢






Ƙarshen littafi na ɗaya kenan, idan Allah ya kai mu bayan sallah kuma ya ara mana lokacin. Za mu dawo bakin aiki kamar yadda muka dakata yanzu, in Sha Allah za mu ɗora labarin a inda muka tsaya. D. Auta taku ce kuma tana yi muku son so gabaɗaya😘




Masu neman lambata ga ta; 08022014771 fatan alheri gare ku duka. Bye😍








D.AUTA CE✍🏼


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login