Showing 105001 words to 108000 words out of 121208 words

Chapter 36 - ABOKIN AIKINA HAUSA NOVEL

24 Nov 2024

6414

wuta."

"Ok! Ke ce Auntynta kenan? To karaso ina dakin nasu yanzu na zo ba su magani."

Maganarta cikin rashin cikakkiyar Hausa ya sa na gano yare ce ita, kuma ga dukkan alama matar ma'aikaciyar asibitin ce.
Da kuzarina na shiga dogon ɗakin, ina ta faman gayar da marasa lafiyar da ke kwance suna jin jiki, gwanin ban tausayi.
Na wuce ɗakin na faɗa wani sannan na hango Sajida a kan wani gadon da ke ƙarshen ɗakin. Wani sanyin daɗi ya shige ni saboda gani ɗaya da na yi mata na hango sauƙi. Duk da jikinta da fuskarta duka sun yi baƙi tamkar gawayi, da sauri na isa bakin gadon murmushi a kan fuskata ina jera mata sannu.
Gani na ya sa ta ƙi karɓar maganin da ma'aikaciyar jinyar ke miƙa mata, ta fashe da kuka tana faɗin,

"Aunty kin ga yadda na koma ko?"

"Daina kuka, karɓi maganinki ki sha. In sha Allah za ki ji sauƙi kwanan nan ki dawo yadda kike."

Da kaina na karɓi maganin na ba ta, ganin ta ƙi barin kukan, matar tana murmushi ta ce da ni,
"Kanwar nan naki, tana son ki sosai. Tun jiya take zancen ba ki zo ba, ta damu ta gan ki da yawa."
"Allah Sarki! To ga ni na zo. Me kike so na je na kawo miki?"

"Babu komai Aunty! Daman magana ce nake son mu yi ni da ke..."

"Babu wata magana da za ki sake yi da ita! Baƙar natau mai baƙin nacin tsiya. Macen da ta haɗa kai da ƙawarta suka nemi salwantar miki da rayuwa kike wani rawar jiki a kanta. To wallahi in dai ni ce na haife ki, na raba ki da wannan azzalumar matar, kilibabba, mai fuskar munafukan farko. Allah ya isa tsakaninmu da ke Zaituna, daga ke har Uwarki da ba ta san darajar surukuntaka ba. Wai har ita za ta saka hannu ta daki Mukhtar a gaban kuliya, kuma don an mayar da shi banza a ɗauki yara a miƙa miki. To wallahi ko giwa ta faɗi ta fi ƙarfin karnukan farauta ire-irenku azzalumai, ya ku haram, ya ku halas!"

Sakato na yi ina kallonta tamkar wata doluwa, saboda gaskiya ta sa ban san me zan faɗa wanda zai zo daidai da lafuzzanta ba. Jakata kawai na saɓa a kafaɗa ina murmushin yaƙe na ce da Sajida.
"Ni zan tafi! Ubangiji Allah ya ba ki lafiya."

"Idan ke kike da lafiyar ki hana ta."

Zancen da ta raka ni da shi kenan, har na yi gaba na dawo baya saboda ina so na san halin da Aminu yake ciki.

"Amm! Jikin Aminu fa? Shi ma da sauƙi ko?"

Sajida tana goge hawaye a kan fuskarta da ta sha baƙi tamkar an yi mata fentin gawayi ta ce,
"Yana ɓangaren maza, ya ƙone da yawa ba kamar ni ba."

"Ya Salam!"

Ita ce kalmar da na iya furtawa, ina ƙoƙarin juyawa idona a rufe na ci karo da mutum. Babu zato na ji saukar mari a kan fuskata,

'Tau!!!'

Gabaɗaya kallon mutane ya dawo kanmu. Daga ni har wanda ya yi gangancin saka kuturun hannunsa ya mare ni. Dafe da gefen da na sha marin nake kallon shi tamkar a ranar na taɓa ganin shi a rayuwata. Zuciyata cike da tunanin abin da zan yi na rama tozarcin da ya yi mini a cikin mutane.
Hannuna na ware iya ƙarfina na sauke masa nawa marin, sannan na duƙa a lokacin da zai dawo mini da wani marin, na kai wa jarumarsa kutuball da ƙafa.
Sai ga shi ƙasa dafe da gaban shi yana ihun na kashe shi, mutane suka yo kansa aka rirriƙe shi. Yayin da ni ma wasu mata suka fitar da ni cikin ɗakin ina ƙoƙarin tirjewa. A kan babu inda zan je sai na ga ƙarshen rashin mutuncin da yake taƙama da shi.
Muryar Yaya Maimuna na tsinkayo tana aiko mini zagi, tare da boren da take yi wa mutane a sake ta sai ta kashe ni.
Da ƙyar wannan ma'aikaciyar ta shawo kaina na amince zan tafi. Saboda na kafe a kan babu inda zan je sai Yaya Maimuna ta zo ta kashe ni, kamar yadda take ta ihun faɗa ana tausar ta.
Matar ta raka ni har compaund ɗin Asibitin inda ake ajiye motoci, sannan ta fara sauke numfashi tana faɗin,

"Na fa'imci kuna da masala a sakaninku. Saboda tun jiya ita yarinyar nata take ta zancenki ita kuma tana ta zagin ta. Dun Allah kada ki daina kula ta wallahi tana kaunar ki da yawa. Mamar ce kawai ke da masala amma ita ma za ta daina ne ki yi akuri."

Zaman jakata kawai na gyara tare da ɗaga mata hannu na fice Asibitin zuciyata tana ƙuna. Saboda zagin da Yaya Maimuna ta yi wa Ummata na shanye albarkacin Sajida ban rama ba. Da kuma takaicin marin lusarin maza, namijin ho-ti-hon da ya yi wa mazan duniya rakiya a tsugunne.




Shin wane ne wannan? 🤔🥲 Yaya Maimuna dai ta hana mu ji maganar da Sajida take son faɗa wa Zaituna🙁😟





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*AM BACK MY FANS.*


*ARBA'IN DA UKU.*

Ban iya zuwa wurin aiki a lokacin, sai gida na koma saboda babu kuɗi a jakata. Kuma ban ce da Najib ya jira ni ba sannan ba na so na kira shi, gudun na katse masa uzurin da yake yi. A ƙafa na yi tattaki tun daga cikin asibitin har zuwa har bakin gate, dalla-dallan motocin alfarma suna ta shiga da fice a cikin Asibtin tamkar ana gasar gwadin ranttsun motocin da suka ji gishiri.
Idan na ga mace da mijinta cikin mota suna hira ko dariya sai na ji sun burge ni. Saboda rabon da na yi hirar arziƙi da Mukhtar mu yi raha da dariya har na manta. Kullum faɗa masifa ne yake haɗa ni da shi mu yi doguwar magana, ba ya shawara da ni, ban san komai a kansa ba duniya, idan ba shi da nake gani da ido ba.
Shigarsa fitarsa duka bai damu da sanar da ni ba, domin wani lokaci ba na sanin ya shigo gida kuma ba na sanin fitarsa. Matuƙar ba ina tsakar gida ko falo ba, wanda babu yadda za mu yi dole mu ga juna ko ba ma so.

Da tunanin na shiga gidan Kawu Sale, na karɓi kuɗin mai adaidaitasahu na kai masa sannan na dawo. Tun kafin na zauna Inna Kulu da Ummata suka fara jefo mini tambayoyin.
"Lafiya kika dawo yanzu?... Ko yau ba a aikin ne?"

Wuri na samu a kan kujerar tsugunno na yi tagumi, sannan na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi na ce da su.
"Asibiti na fito ban je wurin aikin ba."

"Ya jikin Sajidar? Allah dai ya sa lafiya?"

Tambayar Inna Kulu kenan, na amsa mata cikin yaƙe na ce,
"Ita kam da sauƙi, amma mijin nata ne aka ce ya ƙone da yawa. Na so zuwa duba shi na manta shaf sai bayan na fito asibitin na tuna."

"To Allah ya ba su lafiya duka, kuma ya ƙara tsare gaba."

"Amin" na ce, sannan na ciro wayata na fara neman lambar Maman Taufiƙ, duk da cikakken sanin da nake da shi a kan da wuya na same ta. Haka na yi ta jera mata kira kamar wadda aka saka dole, saboda duk kiran da na yi sai an sanar da ni a kashe wayar take.

"Wai wa kike kira?"

Umma ta jefo mini tambaya tana sheƙa ruwan sanyi, a cikin kunun zaƙin da take ƙoƙarin haɗawa.
"Lambar Maman Taufiƙ ce nake gwadawa ko za a dace ta shiga."

"Ke ma dai kin fiye saka abu a ranki wallahi, ki bar ta kawai, daman gyaɗa idan ta ji zafi ita ke fitar da mai da kanta ba sai an matsa ba."

"Wallahi Umma ban ji daɗin abin da ta aikata ba, don na san ita ma abin zai dame ta muddin hankalinta ya dawo jikinta." Na ƙare maganar cikin sanyin jiki da na murya, Inna Kulu da ke wanke shinkafa a bakin makwarara ta ce,

"Kishi masifa ne kam! Amma wani kishin ya wuce haddin musulunci. Haka kawai ka cinna wa kishiya da mijinka wuta saboda tsabar hauka?"

"Ba ta san halin maza ba ne shi ya sa! Duk kishin da zai sa a salwantar da rayuwaka rashin imani ya shiga ciki ya zauna. Haka fa na taɓa ganin wani labari da daɗewa a tashar talabijin ta RTV Sokoto, kuma na ji an maimata shi a gidan Radio BISHIM FM ana hira da wanda abin ya faru da shi. Wata ce ta cinna wa mijinta wuta, tare da yaronta da ke kwance kusa da shi yana barci, don kawai zai yi mata kishiya. Da ƙyar ya samu ƙofar tsira ya diro ta taga tun daga saman bene ya karairaye. Wutar ta canye yaron ƙurmus kuma bayan ya gama jinya ya yi aurensa, ita kuma ya sake ta. Yanzu wannan wa gari ya waya?"

"Ita!"

Na ba ta amsa a gajarce saboda sanyin da jikina ya yi, Inna Kulu ta ƙara da cewa,
"Kuma idan ba Allah ya tsare ba, ita da aure a nan duniya sun yi hannun riga. Saboda duk wanda ya ji tarihinta ba zai taɓa auren ta ba, don ko an so yin jahadi dangin mutum ba za su bari a auro musu annoba ba."

Jiniyar motar 'yansanda da muka jiyo ta karaɗe unguwar, hakan ya sa muka yi shiru dukanmu muna sauraro. Sai ga Kawu Sale kamar an jefo shi ya faɗo gidan yana gyara zaman babbar rigarsa yana faɗin,

"Ke duniya ina za ki da mu?"

"Lafiya!?" Tambayar da muka yi masa kenan, buta ya ja da gudu ya faɗa bayi. Dukanmu muka bi shi da kallo, kafin mu ji dirin mota a ƙofar gida, ana rafka mana sallama. Cikin tashin hankali Umma ta zari Hijabi ta yi waje ni ma na bi bayanta da sassarfa ƙirjina yana bugawa.
Ganin 'yansanda reras a ƙofar gidan, hakan ya sa na gwalalo ido waje cike da matsanancin tsoro. Bayanin da na ji wani ɗan sandan yana yi wa Umma; ya sa hantar cikina kaɗawa, 'yan hanjina suka murɗa na koma cikin gidan da gudu. Hannuna a kai ina salati, wanda sai na kamo shi ya kufce na ƙara janyo wani.

Jikina yana rawa na fara tura wa MD gajeren saƙon da bai fi layi ɗaya da rabi ba. Saboda shi kaɗai ne mutumin da ya faɗo mini a rai a daidai lokacin, kuma shi nake da cikakken tabbaci a kan zai fitar da ni matsin rayuwa duk rintsi.
Umma ta shigo gidan cikin matsanancin tashin hankali bakinta yana rawa ta ce da ni,
"Shirya mu je da kaina zan kai ki. Babu wata motar 'yansanda da za ki shiga, don ba kisan kai, ko sata kika yi ba."

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"

Ita ce kalmar da muka haɗa baki wurin faɗa daga ni har Inna Kulu da Kawu Sale da ke ƙoƙarin fitowa bayi.
"To mu tafi gabaɗayanmu a rufe mu ɗan makulli ya ɓace."

Zancensa kenan sannan ya yi gaba cikin ƙunar zuciya muka bi bayansa ni da Umma. Duk da matsanancin tsoron da nake ciki, amma hakan bai hana ni bin Umma ba cikin sauri 'yan sandan suka bi mu da motarsu.
Adaidaitasahu muka shiga mu duka uku, tare da wani ɗan sanda a gaban da mai adaidaitasahun. Ƙirjina ya hau bugawa fal-fal tamkar zuciyata ta ɓalle ta fito waje. Babu wanda ya ce komai har aka kai matattarar 'yansanda da ke polo.
Yaya Maimuna na fara hangowa sai wasu daga cikin danginsu maza. Fuskata na cure saboda jikina ya ba ni da wuya a kwashe ta daɗi, musamman ganin fuskokinsu babu alamun rahama balle sassauci.
Ankwa aka saka mini ina kuka Ummata tana yaɓa wa su Yaya Maimuna maganganu masu zafi, tare da kira musu Allah ya isa ta fi cikon kwando Kawu Sale yana tausar ta.
Gaba wani ɗansanda ya saka ni Ummata ta riƙe ni tana faɗin, "Babu inda za a je mini da yarinya, a tsaya gaban kowa a yi magana idan abin ya ƙi a tura mu babbar kotun ƙoli, don daman can case ɗinmu yana hannunsu."

Wani ɗan sanda na ga ya yi wa wani ƙus-ƙus sannan aka zare mini ankwa suka ce mu shiga daga ciki. Dogon benci muka zazzauna yayin da wasu suka zauna ƙasa. Babban jami'in da muka taras kan kujera shi ya fara yin magana, bayan ya kira Yaya Maimuna a kan ta ƙara yin bayanin abin da ya kawo su wurinsu.

"Haƙƙin ɗan'uwanmu muke nema a bi mana ranka ya daɗe. Saboda har asibiti ta je a gaban kowa ta kai masa harbi da ƙafarta. Kuma tun da ya faɗi ƙasa har yanzu bai tashi ba yana can gadon asibitin, ana ta ƙoƙarin shawo kan matsalar da ta haifar masa amma abin ya ci tura."
"Waiii! Sannu Zita azurari uwar zuba! To ba gadon asibiti ba ko cikin ƙabari ne; Mukhtar ya cancanci fiye da haka a hannun Zaituna."
Zancen Umma kenan kafin wani jami'in tsaron ya katsa mata tsawa, a kan ta yi shiru kada ta sake magana har sai an ba ta umurni. Umma ta yi muƙus tana harare-harare bakinta yana mui-mui.

"To yanzu dai kun ji abin da suke nema a yi musu. Don haka za mu ajiye ta a nan, har sai an yanke mata hukuncin da ya dace da ita, sannan ku dawo mu san yadda za a shawo kan lamarin."

"Tsakani da Allah ranka ya daɗe ba a yi wa yarinyar nan adalci ba! Mun ji ta yi masa ba daidai ba. Amma bai dace a ce za a riƙe ta a nan ba, don wannan rigima ta cikin gida ce bai dace a ja ta da tsauri haka ba. Saboda faɗa ne tsakanin mata da miji kuma kowa ya sani ana samun matsala."

"Za ka koya mana yadda ake aiki ne!?"

Wani ɗansanda ya yi wa Kawu Sale magana cikin ɗaga murya, shi ma ya ba da amsa cikin kwantar da kai ya ce,
"Ba haka ba ne ranka ya daɗe! Amma dai don Allah a duba lamarin da kyau yarinyar marainiya ce!"
"Mu ma dukanmu nan marayu ne... Kofur Musa!"

"Yes ser!"

"Kai ta ɗakin ajiya, idan kuka shirya sai ku dawo a yi magana."

Zumbur Umma ta miƙe tare da riƙe ni tana faɗin,
"Don girman Allah ranku ya daɗe kada ku rufe mini yarinya. Wallahi shi ya janyo ta yi masa abin da ta yi, don kowa ya san babu ruwanta shi ne da matsala."

"Idan ma kowa ya sani mu ba mu sani ba! Kofur Musa je da ita kawai."

Umma ta ƙara damƙe ni ina ta kuka na ƙanƙame ta, wanda aka kira kofur Musa ya zo zai taɓa ni Umma ta buge masa hannu tana faɗin,
"Wallahi sai dai a kashe mu daga ni har ita! Amma ba zan bari ku rufe mini yarinya ba!"
Wata 'yarsanda mace aka kira ta saka kulki ta fara dukan hannun Umma, amma ta kasa raba ni da ita kamar yadda take so. Ana tsaka da haka wani jami'in ya shigo ya sara wa babban jami'in ya ƙame, sannan ya yi masa ƙus-ƙus suka fice ofishin tare. Bayan ya ce da 'yar sandar ta dakatar da dukan da take yi wa Umma, a ƙoƙarinta na son ta ɓanɓare ni daga jikinta ta ƙarfi.

Mintuna a tsakani muna maƙale ni da Umma, 'yan sandan suka dawo suna murmushi suka ce da matar ta fice ta bar mu. Ta fice tana aika mana harara tare da yin ƙwafa, Umma ta ja ni ta zaunar da ni a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login