Showing 33001 words to 36000 words out of 121208 words
ba ya tayar da mu daga ni har yaran, balle zuwa ya ga tashin mu idan safiya ta waye."
Ajiyar zuciya Inna Kulu ta sauke sannan ta ce, "Ni wannan zama naku Zaituna, ban taɓa ganin irin shi ba sai gare ku. A ce ko kaɗan babu jituwa tsakanin mace da mijinta; to ya ya za ku fahimci juna balle ku nemo hanyar gyara domin ku gyara zamantakew...?"
"Ita ma ai tana da matsala, babbar matsalar Zaituna a rayuwa bai wuce kafiya ba. Da tana bin shawarar da muke ba ta da tuni ta zauna lafiya mu ma ta bar mu mun huta. Amma duk abin da kika ce ta yi sai ta nuna miki ta fi iyawa. To zama da Mukhtar ya zama dole ko don 'ya'yanta, tun da tun farko ba ta bayyana mana matsalar shi da wuri ba. Balle a taro tun kafin ta yi tsanani, har sai da komai ya lalace sannan ta faɗa bayan ta fara tara zuri'a da shi."
Maganar Umma kenan da muka ji a sama ba tare da mun ji shigowar ta ɗakin ba, sai da ta ja numfashi sannan ta sake cewa,
"Na sani Mukhtar bai yi mata halacci ba mu ma bai yi mana ba, amma babbar matsalar shi ne yaran da ke tsakaninsu. Mahaifiyar shi ba ta duniya balle a miƙa mata yaran, domin ta san yadda za ta yi da su, shi kuma ba ɗa ba ne balle a ce za a bar masa su hannun shi. Sannan kaf dangin shi babu mai zuciyar riƙa masa 'ya'ya tsakani da Allah balle a kai musu su karɓa, saboda zuri'arsu kaf babu haɗin kan taimakon juna balle a share wa ɗan'uwa kuka. Babbar matsalar ita ce a cikin gidan ma tarbiyyar yaran za ta fara gurɓacewa ba sai an je nesa ba. Domin idan kin manta na tuna miki, sau nawa suna neman 'ya'yanki da lalata Allah yana tsarewa kafin ki baro gidan?"
Ta ƙare maganar a fusace cikin ɗaga murya, saboda fuskarta ta nuna kai wa ƙoluwar ɓacin rai. Kafin na ba ta amsa ta ƙara da cewa,
"Lokacin da kika daka yaji kika zo gidan nan, watanki biyu ana faɗi-tashi da yaran, nawa Mukhtar ya kawo mana domin mu ciyar da su ko a yi musu wata lalura? To a haka kike so na kawo ki gidan nan ke da yaranki ya bar mu ciyar da ku da sauran laluro, shi ya rungume hannun shi ya zuba mana ido? To ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa. Sawunki a likkafa ki ɗauki jakarki ki koma tun kafin wankin hula ya kai ki dare, baƙincikin ɗa namiji ba a kanki aka fara ba kuma ba za a ƙare kanki ba. Kula da tarbiyyar yaranki ya fi miki alkhairi da neman wani matsugunnin da kike yi. Saboda inda kika sani kin raina shi, shi kuma inda za ki je an raina ki."
Tana ƙare faɗar hakan ta fice, mintuna a tsakani na ji tana magana a waya. "A kawo yaran nan idan ta tashi ta koma tare da su. To idan sun dawo a kawo mata su."
Daga ni har Inna Kulu babu wanda ya yi motsin kirki balle mu samu kuzarin cigaba da bitar maganganun. Domin har zuciyata na gamsu da zancenta ɗari bisa ɗari, saboda ta tunanar da ni wasu abubuwan da na manta a baya. Hakan ya sa na yi ammana da Mukhtar ne ƙaddarata a cikin duniya, wanda ban da ikon gyara ƙaddarar ta dawo mini daidai yadda nake so; har sai ranar da Allah ya kawo mini sassauci da mafita a cikin rayuwata da ta 'ya'yana.
Inna Kulu ta tashi ta fice, mintina a tsakani ta dawo ɗauke da kofin kunu da ƙosai a ƙaramin faratin silba. Gabana ta ajiye tana faɗin,
"Ɗauki ki karya sannan ki bar wa Allah lamarinki, in Sha Allah za ki ga haske a gaba muddin kika cusa wa zuciyarki dangana, kuma kika bi abin da Mahaifiyarki take so."
Ban musa ba na sauko daga kan gadon na fara shan kunun, domin shi kaɗai nake jin zai iya shiga cikina. Ko shi saboda yunwar da nake ji maƙoshina har ya fara bushewa.
Kasancewar yaran sun je makaranta, bai kawo su ba har sai da aka gama sallar juma'a. Sannan suka shigo da gudu suna ihun murna tare da ƙwala mini kira, tarbon su na yi fuskata ɗauke da mayalwacin murmushi. Jikina suka faɗo dukansu suka rungume ni, ni ma na rungume su ƙam-ƙam. Nan take damuwa ta ziyarce ni har ta bayyana kan fuskata.
Saboda kukan da Ummu Salma da Iman suke yi. Jan su na yi muka ƙarasa cikin ɗakin ina faɗin,
"Ya isa, ku daina kukan haka."
Haidar riƙe da hannuna ya ce, "Mama wai da gaske kin ce ba za ki sake zama gidan Abbanmu ba?"
Kallo na ƙura wa fuskar shi kafin na ce, "Wa ya faɗa maka?"
"Abbanmu ne ya ce dama mun daina kuka don kin ce ba za ki sake zama da mu gidan ba, shi ya sa da dare kika tafiyar ki kika bar mu."
Amsar da Ummu Salma ta yi hanzarin ba da ni kenan tun kafin Haidar ya faɗa.
Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce, "Ko ma dai mene ne ina tare da ku abadan in Sha Allah! Ku je ku gayar da Umma." Har sun fice Iman ta dawo tana goge hawaye ta ce, "Abbanmu yana wurin Umma da Baba Sale suna magana."
Zumbur na miƙe saboda na san sharri da ƙage irin na Mukhtar, abu kaɗan zai iya juya shi zuwa babba. Balle ganin da ya yi mini tare da MD komai zai iya faɗa domin ya jaza mini wani sabon tashin hankali na daban.
"Wallahi Umma da idona na gan ta tare da shi a ƙofar wani gida, kuma a gabana ta shiga motar shi suka tafi tare da 'yansan..."
"Ban katsi hanzarinka ba Mukhtar! Amma mutumin nan ya faɗa mini duk abin da ya faru a lokacin da ya kawo ta gidan nan. Asali ma ban da shi; da tuni an cutar mana da ita saboda sakacinka. Kada ka ga ina zuba maka ido kana zaluntar mini yarinya ka ɗauka ba na son ta. Wallahi duk girman mutuncin da kake gani ina yi maka albarcin 'ya'yanka kake ci. Domin ni ba ki yi mini halacci ba kuma ba ka yi wa Zaituna adalci ba. Saboda ta nuna maka ƙauna kuma ta yi maka rufin asirin da a tara mata dubu ba za su iya yi maka irin shi ba. Mutumin da kake aibatawa kuma, mahaifiyar shi ya kai asibiti a daidai lokacin da taƙadarun suka biyo ta. Saboda ciwon asma gare ta wanda tashin shi cikin daren ya yi sanadin ceton Zaituna. Domin ba don ta ya fito ba, kuma ita ma ba wurin shi ta je ba, amma idan har ba ka yarda da zancen ba; kana da damar ɗaukar mataki daidai da laifin da kake ganin ta yi maka."
Maganganun da na ji kenan a lokacin da na durfafi ɗakin Kawu Sale, saboda a can ne mahaɗarmu a duk lokacin da aka zo sansancin rikicinmu ni da shi.
Hawayen daɗi na goge a fuskata na sha jinin jikina a bakin ƙofar, saboda ba ƙaramin farinciki zancen Ummata ya saka ni ba.
'Ashe har yanzu Umma tana so na.'
Zancen zucin da na yi kenan kafin na ji ɗaci ya ziyarci kan harshena, a sanadiyyar muryar Baba Sale da na ji yana faɗin, "Ke Habi ba haka ake sulhu ba, yadda ya kawo ƙara ya dace ki tsaya a saurari ta bakin..."
"Babu abin da zan tsaya sauraro daga gare shi Sale, don magana ta gaskiya kai kanka ka san Zaituna ta sha wahalar auren shi. Kuma ba wai mun rasa inda za ta zauna ba ne ko abincin da za mu ba ta, balle ya zargi neman kai muke yi da ita shi ya sa muke tauye ta zama da shi koyaushe. Don haka idan har ya gaji babu dole ba sai ya yi ta ɗora mata ƙazafi ba, ya sake ta kawai gari da yawa maye ba zai ci kan shi ba wallahi. Amma ba ita ba ni kaina na gaji da matsalolin shi, idan bai gyara ba a wannan karon; to zan bai wa Babanta Ali dama ya raba auren kowa ya huta. Don daman can ni na hana da yanzu duk mai sha ta sha komai ya zama labari. Miji goma ai ba Uba goma ba ne."
Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi tamkar an sauke mini ƙaton dutsi a saman kaina, domin yau kaɗai Umma ta tabbatar mini da lalle ita ce ta haife ni. Saɓanin baya da nake tantamar hakan a duk lokacin da ta ɗauki gaskiya ta miƙa wa Mukhtar. Ko idan ta kawar da kai ga duk matsalolin shi idan na rattaba mata, a matsayin kare kaina daga wani laifin da ya ƙaƙaba mini ban ji ban gani ba, ko faɗan da take yi mini a kan boren da nake yi wa auren lokaci bayan lokaci.
"Wallahi Umma ban san ta fita ba, sai bayan na farka tsakar dare na ga ƙofar gidanmu a buɗe. Kuma na yi ta kiran lambarta ban samu ba, haka ma sai da na biyo sawunta kafin na sake rufe gidan. Ke ce kawai ban yi tunanin kira ba sai da safe gudun na tayar miki da hankalin."
"Ai da zafi-zafi ake bugun ƙarfe ba sai ya huce ba, domin da ka kira ni a lokacin dole mu fita neman ta mu da muka san zafinta. Saɓanin kai da rashin ganin ta bai hana ka komawa gidanka ka rufe ba, saboda ba ka da asara ko mutuwa ta yi akwai mata da yawa a gari har waɗanda suka fi ta."
Cikin kakkausan sauti na ji Umma ta ba shi amsa mai harshen damo. Babu shiri na maka wa ƙofar harara saboda maganar da na ji yana faɗi daga bakin shi cike da yaudara da daɗin baki,
"Yanzu dai don Allah Umma ku yi haƙuri, in Sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba. Domin Wallahi gabana har faɗuwa yake yi a duk lokacin da na ji ana zancen sakin nan. Saboda ko maƙiyina ba na fatar ya saki matar shi balle ni na aikata. Kada Allah ya nuna mini ranar da zan furta wannan mummunar kalmar daga bakina zuwa ga Zaituna."
To ni ma dai ga tawa harara🙄haɗi da tsaki😼 zuwa ga Muntari😂
D. AUTA CE✍🏼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*LAMBA SHA BAKWAI.*
Shiru na ji ya ratsa tsakani bayan maganar Mukhtar, sannan na ji muryar Kawu Sale yana faɗin, "Yanzu ke Habi tun da ya gano laifin shi, yana da kyau a ƙara ba shi wata dama. Idan har ya kiyaye abubuwan da ke janyo musu rikici shi kenan matsala ta kau, saboda haka ki zubar da komai a daina bitar abin da ya wuce. Kai kuma tsakani da Allah matuƙar ba ka gyara halinka ba, to duk abin da ya ƙara tasowa a gaba kada ka ga laifin kowa kai ka janyo. Abu na ƙarshe kuma ka daina zargi, domin muddin ka tsayu a kan zargin matarka to ba za ka taɓa jin daɗin zama da ita ba. A wani ƙaulin Malamai ma an tabbatar da cewa zargi yana ɓata aure."
"Ni a wurina komai ya wuce Kawu, amma maganar gaskiya aikin nan da take zuwa, ko kaɗan ban da natsuwa da shi. Saboda mutumin nan babu komai a ran shi face buƙatar kashe mata aure domin ya aure ta."
Maganar shi nan take ta saka idona rufewa, ta yadda ban san lokacin da na yi wuf na faɗa ɗakin ba. Cikin ƙunar zuciya na fara nuna shi da hannu ina cewa,
"Kai dai baƙin munafuki ne ƙarshen bugun lamba. To wallahi ko za ka mutu ba zan fasa zuwa aik..."
"Yi mana shiru Zaituna!" Babu shiri na gantsara saboda tsawar Baba Sale da carbin da ya watsa mini a jiki, na durƙushe ƙasa ina sosa wurin tare da aika wa Mukhtar harara ta gefen ido. Kafin Baba Sale ya ci gaba da magana cikin fushi tamkar ya dake ni.
"Me ya kawo ki nan balle ki saka mana baki? Ko kin ji an kira ki da za ki zo kina yi wa mutane hauka? Wannan rashin mutuncin naki yana daga cikin abin da ke ƙara lalata muku zaman lafi..."
"Wallahi ko a gaban yara haka take yi mini ba ta shayin komai. Na sha faɗa mata duk abin da za ta yi mini zan jure matuƙar ba gaban wasu ko 'ya'yana ba. Domin yanzu silar hakan har yaran sun fara yi da ni a tsakaninsu. Ko yau da safe ina jin Haidar yana faɗin; shi ya gaji da kukan da nake saka Mamarsu, Idan ban bari ba shi ma zai rama mata a kaina. Ka ga a nan ta yi ƙoƙarin cusa musu ƙiyayyata tun kafin su mallaki hanka...'"
"Wannan kuma ba laifinta ba ne kai ka janyo. Don a irin halinka babu abin da 'ya'yanku ba za su yi ba, matuƙar aka biye doron da kake ajiye tsarin gidanka a kan shi. Yana da kyau ka fahimci matsalar taki ce duka ba ta mutum guda ba, yadda kake da laifi ita ma tana da shi. Don haka ku taru ku gyara dukanku ko don tarbiyyar yaranku. Ke kuma ki ji tsoron Allah ki daina cin zarafin mijinki don komai lalacewar shi miji miji ne, kuma yana sama da ke ko babu auratayya balle aure ya haɗa da 'ya'ya a tsakani."
Zancen Mukhtar da Ummata kenan a lokacin da ya so goga mini laifi, ta yi hanzarin toshe komai ta hanyar ankarad da shi domin ya hankalta.
Daga ni har shi suka rufe mu da faɗa, a kan mu zauna lafiya mu daina raba wa kanmu abin faɗa. Da nufin a bar wanda aka yi baya a matsayin ya wuce a fuskanci gaba, sannan batun aikina ma ba a hana ni zuwa ba kamar yadda yake da buƙata. Sai dai sun tunantar da ni abubuwan da baƙinciki ya sa nake ƙoƙarin aikatawa, ba don na manta da hukuncin laifi ba a musulunce ko a al'ada ba.
Sannan aka tashi zaman sasancin da zummar da dare zan koma gidan shi, bayan an saka ni dole sai da na ba shi haƙuri ba don na so ba.
Ina gunguni na fito ɗakin saboda ko kaɗan hukuncin bai yi wa zuciyata daɗi ba. Domin ni a rayuwata ban da wani buri a lokacin; face ya tsinke igiyon aurensa da suka yi mini mugun ɗaurin talala a jiki. Saboda ina so na kasance free babu aure ko da zan mori sauran rayuwar da ta rage mini a duniya. Domin na yi nagartacciyar ibada irin wadda zan samu natsuwar zuciya, saboda ina so na daina aikata alfashar da nake yi a ƙoƙarin kaucewa zinar zahiri.
Inna Kulu ta dinga ba ni haƙuri domin na rungumi ƙaddarata har zuwa lokacin da Allah zai kawo mini ƙarshenta. Sauraron ta kawai nake yi, amma ba don babu abin da take faɗa mini zai yi tasiri a zuciya ba, matuƙar ba za ta goya mini bayan rabuwa da auren Mukhtar ba.
Ƙarfe huɗu da minti goma na rana, bayan na gama sallar Asr ina kan sallaya da carbi a hannuna ina ja. Na jiyo sallamar Amina a tsakar gidan. Tana tambayar inda nake tare da yi wa su Umma bayanin ni ta zo dubawa, har da yi musu ya jikina suka amsa mata tamkar da gaske ciwon nake yi. Inna Kulu ta fara shigowa ɗakin sannan Amina a bayanta har inda nake zaune.
Murmushi muka yi wa juna ni da Amina sannan ta zauna tana faɗin, "Kai matar nan, ashe ma ciwon da sauƙi MD ya tsorata mu da cewa ciwon ya sa aka dawo da ke gida. Wataƙila ma lamɓo ne kawai gidan kika yi marmari, shi ya sa kika dawo don ki saka su Umma aiki."
Murmushi na yi mata da jajayen idanuwana, waɗanda har lokacin ba su gama washewa ba a kan kukan da na sha. Baki har kunne na ce da ita, "Ciwon kaina ne ya motsa,