Showing 99001 words to 102000 words out of 121208 words
"Ni na rasa da me zan fassara wannan lamari. Duk da idan ɓera da sata daddawa ma da warinta. Maman Taufiƙ tana da zafin kishi sosai har na fitar hankali. Shi kuma mijinta yana da idon kallon mata ya ji sun burge shi. Idan ya yi laifi a kan ɓoye matan da ya yi, to laifinsa kaɗan ne nata ya fi yawa. Saboda ya fi kowa sanin zafin kishinta, yana gudun ya faɗa mata hakan ya janyo masa tashin hankali. Amma kuma da ya faɗa mata gaskiya sai ta fi jin sauƙin abin, da a ce ta ji labari kwatsam! Bayan aikin gama ya gama."
"Maza! Maza!"
Zancen Inna Kulu kenan tare da jinjina kai, kafin maganar Kawu Sale ta shigo dodon kunnuwanmu tun kafin mu gan shi.
"Me mazan suka yi?"
Murmushi na yi mai sauti ban ce komai ba, Inna Kulu ce ta yi ƙarfin halin faɗin,
"Tsohuwar bazawararka aka ce yaushe za ta kawo sadaki a ɗaura muku aure?"
"Ki rantse da Allah gaske kike yin maganar nan, ni kuma cikin satin nan a ɗaura na dinga zuwa gidanta dangana sanda."
"Idan da rabon sandar ta jingine ka gidan da ƙarar kwana ai sai ka je ga fili ga mai doki."
Zancen Inna Kulu kenan da Kawu Sale, tsam na miƙe ina dariya na yi ɗakin Umma. Kwance na yi, bayan na mayar da ruwa da kunun ayar da Maman Taufiƙ ta ƙi sha a furji. Ina ta juya abubuwan da suka faru a kwanyata bi-da-bi, har tunanin Sajida ya faɗo mini a rai zumbur na miƙe na fito waje. Inna Kulu na iske ɗakinta ina faɗin,
"Wai Inna ya aka yi da kuka kai Sajida gidansu?"
Inna Kulu fuskata babu yabo babu fallasa ta ce da ni,
"Lafiya lau na fito gidan, duk da Uwarta ta yi ta jifa ta da maganganu marasa daɗi. Bayan na ce ga 'yarta nan mun kawo mata kada ta tsine mata. Tun kafin na gama fitowa na ji tana faɗin, yau gidan mijinta za ta kwana ta gama kwana gidan har abada."
"Allah Sarki Sajida!"
Haka kawai na tsinci hawaye suna kwaranya a kan fuskata, saboda duk abin da aka yi mata sanadina ne. Domin a huce haushi na da ake ji a kanta, saboda ta nuna tana ƙaunata a fili fiye da kawunta.
"Akwai Allah! Kuma in Sha Allah sai abin ya zame mata alheri."
Zancen Umma kenan, wadda ke riƙe da labulen ƙofar ɗakin Inna Kulu. Kafin ta ɗora da faɗin, "Ke kuma Kulu idan ba ki daina zancen Bazawarar Sale ba, sai 'yan Amin su amsa ya tare can tun da ba za ki bar shi ya huta da magana ɗaya ba."
"Ai da yana iyawa da ya yi tun lokacin da take rawar ƙafa kansa. Idan kuma kun isa a yi auren cikin satin nan kamar yadda ya ce."
"To ba mu so, kuma Allah ya raba mu. Ke ma da kike zancen saboda kishi Allah ya ba ki ikon dainawa. Mace saboda jin daɗin aure da tsufanki ma sai kin yi kishin Salenmu! Amma duk kika motsa sai kin cika baki kamar gaske."
"Kyale ta Habi! So take yi na ɓanɓaro sabuwar budurwa ɗanya shataf!"
Zancen Kawu Sale ya sa na yi murmushi ban shirya ba, haka suka dinga wasar su kamar yadda suka saba na baro ɗakin. Zuciyata cike da tunanin. 'Kenan dai mace komai tsufanta idan ta ji daɗin aure tana kishin mijinta. Balle masu rangwamen shekaru waɗanda suke tsaka da cin ganiyar lokacinsu.'
****
Daren ranar bacci rabi da rabi na yi, saboda na yi ta kiran wayar Sajida domin na ji halin da take ciki. Amma duk kiran da na yi babu wanda na samu wayar kashe ake cewa.
Jiki babu kuzari muka shirya ni da yara kamar koyaushe, Najib ya kwashe mu ya ajiye su ni ma ya kai ni wurin aiki.
Ban yi wani aikin kirki ba ranar saboda ban da natsuwar zuciya, a ƙarshe ma tattara komai na yi na tura drowar teburina. Saboda ƙwaƙwalwata ta toshe ba na gane komai face tunanin Sajida da Maman Taufiƙ. Sai tashin hankalin da zai biyo baya ita da Amininta idan ta ji labarin yankan bayan da ya yi mata.
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi kiran Najib ya shigo wayata, duk da ban san me zai faɗa mini ba; sai da gabana ya buga da ƙarfi kafin na ɗaga wayar numfashina yana sama da ƙasa.
"Maman Haidar, na je makaranta tun ƙarfe ɗaya ban ga su Ummu Salma ba, gabana aka watse makarantar amma ban ga sun fito ba. Har maigadin na tambaya ya ce da ni wani ya zo ya ɗauke su da mashin. Na je Bafarawa Estate a can ma an ce ba su koma gidan ba."
Dam-dam-dum! Shi ne sautin luguden da zuciyata ke yi tamkar ta fasa ƙirjina ta fito. Ban san lokacin da na zabura na miƙe tsaye ina ta maimaita faɗin, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" A bakina ba.
Waya a kunnena na fito da gudu na yi bakin gate, ban ma san ya katse kiran ba har sai da wani kiran ya sake shigowa.
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wayyo Aunty wuta! Ki zo ki cece ni wuta! La'i'laha illallah Muhammadur Rasulullah! Shi kenan!!!! Ɗakin duka ya kama da wu..."
Muryar Sajida kenan da na ji a cikin waya, da wata sabuwar lambar da ban san ta ba, kafin kiran ya katse. A gigice, na durfafi saman titi idona a rufe ba na gane komai da kowa a lokacin, balle na hango abin da ke gabana. Odar mota na ji 'Ɗiiiiiiiiiiiiiii!' A cikin kunnuwana tamkar za a fasa mini dodon kunne. Cak! Na tsaya sai jin na yi an ture ni na faɗi gefen titin, daga ni har wayar mun ɗaiɗaya. Yunƙurin miƙewa na fara yi na ji an riƙa ni da hannu biyu na tashi, sai sannu ake jera mini ba tare da na shaida muryoyin mutanen ba sai ta mutum ɗaya waton MD.
Ruɗu da firgici ya sa na zama tamkar wata zararriya ina faɗin, "Yarana sun ɓata! Wuta ta canye Sajida! Don Allah ku taimaka mini zan mutu idan na rasa yarana da Sajida. Zan mutu idan na rasa yarana su ne rayuwata."
Hannuna na ji an ja ban tirje ba na bi, aka saka ni cikin mota sannan aka rufe. Fisgar motar aka yi da ƙarfi idona a rufe ina ta zunduma ihu, tare da kiran sunan Sajida da yarana tamkar wata mahaukaciya sabon kamu.
Hmmmmm! Laifin daɗi ƙarewa. A nan muka kawo ƙarshen ABOKIN AIKINA littafi na ɗaya. Idan Allah ya ara mana lokaci an yi sallah lafiya za mu ɗora da wani sabon salon kafcen. A cikin littafi na biyu mai tsayawa a zuciya. Ubangiji ya albarkace mu da ganin wannan wata mai tarin falala waton Ramadan.
Fatan alheri gare ku gabaɗaya luv u all😘
D. AUTA CE✍🏼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*AM BACK MY FANS.*
*ARBA'IN DA ƊAYA.*
'Ƙiiiii' Shi ne kalar birkin da MD ya ja, a daidai ƙofar gidan Kawu Sale. Saboda hanzarin fisgo ni da ya yi na faɗa jikinsa a haukace babu shiri, a dalilin bai gama tsayuwa ba na nemi ɓalle murfin motar na fice.
Kallon-kallo muka dinga yi wa juna, kafin na yunƙura kamar wata zakanya, na fisge daga riƙon da ya yi mini na fice motar aguje ina ƙwala wa su Umma kira. Gidan na faɗa a sukwane tare da faɗin,
"Umma! Umma ki zo an sace su Haidar! Wayyo Zuciyata za ta buga!"
A tsakiyar gidan na zube ina gunjin kuka cikin sauti tare da ɗaga murya. Inna Kulu da Umma har rige-rigen isowa wurina suke yi tare da jero mini tambayoyi. Ban bi ta kan tambayoyinsu ba, illa ihun kiran sunayen yarana da nake yi tare da Sajida a haukace.
Ruwa na ji Umma ta watsa mini a jiki da ƙarfi, na zabura ina ƙoƙarin ficewa gidan tamkar wata zautacciya. Inna Kulu ta damƙe ni Umma ta fara girgiza ni tare da faɗin,
"Ki dawo! Hankalinki! Na ce!"
Tsawar da ta yi mini sosai ta shiga jikina, cikin sauri na faɗa jikinta ina kuka na ce, "Haidar, Ummu Salma da Iman duka sun ɓace! Ita ma Sajida wuta ta ƙone..."
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Me ke shirin faruwa da mu ne haka?"
Zancen Inna Kulu kenan, kafin Umma ta ja hannuna mu fito gidan, motar MD na hango a inda na bar ta. Hakan ya sa na tuna ashe shi ne ya kawo ni gidan, har mun yi gaba ya biyo mu yana gayar da Umma. Fuskarta a haɗe ta amsa masa sannan ta ƙara jan hannuna muka yi gaba.
Biyo mu ya yi da motar yana roƙon Umma ta shigo ya kai mu inda za mu je, amma haƙuri kawai ta ba shi sannan ta tare mana wata adaidaita muka shige. Tafiya adaidaitar take yi ina sharɓar kukana mai ɗauke gunji kala-kala.
'Wuuuuuuummmmmh!! Ummmmmm!'
High Court Juduciary na ga an rubuta, a jikin bangon allon saman bakin babbar kotun da ke Sokoto.
"Kotu kuma? Me ya kawo mu kotu?"
Tambayar da na yi kenan bakina yana rawa. Yanayin da nake ciki bai hana ni kai kallona a kan fuskar Umma ba. Wadda ta ɗauke kanta kamar ba ta fahimci halin da nake ciki ba.
Kuɗi kawai ta ciro a jaka tana miƙa wa mai adaidaitansahun, na fito ina faman wara ido. Saboda ganin tsarin kotun da girman ta ya sa zuciyata ta hau bugawa, 'Ɓal-ɓal!' da sauri da sauri.
Duk da ba ranar ne karon farko da na taɓa ganin ta ba, amma wannan karon ya sha banbam da na saura. Saboda iyakaci na bi ta gaban gate ɗin kotun na wuce idan an biyo da ni ta Sama road, ko kuma idan na hau titin Hause of Assembly da ke gidan Gwamnatin Sokoto.
Umma tana gaba ina bin ta a baya har harabar kotun, bayan mun gaisa da masu gadin wurin sun yi mana wasu 'yan tambayoyi Umma ta amsa musu a taƙaice.
Kai-tsaye aka yi mana jagora har ofishin wani mutumi mai harɗaɗɗiyar fuska. Zama muka yi daga ni har Umma a kan kujerun da ke ofishin. Sai da ya gama rubuce-rubucen shi a jikin wani file sannan ya cire gilashi ya fuskance mu.
"Me ke tafe da ku?"
"Mijin 'yata na kawo ƙara!"
Zancen Umma kenan kanta tsaye ba tare da shayi ko rawar murya ba.
"A kan me kika zo?"
Mutumin ya sake jefo mata wata tambaya, sai da ta gyara zamanta sannan ta ce,
"Ina so ya sakar mini yarinyata, kuma ya ba ta yaranta da ya sace a makaranta."
Dam-dam! Shi ne bugun da ƙirjina ya yi, musamman sakin da na ji ta ambata, da kuma yarana da suka faɗo mini a rai.
"A kan me kike so a sake ta?"
"Saboda zaluncin da yake yi mata tsawon zaman da suka yi ba ta mori komai ba sai ƙunci. Domin tun da ta aure shi shekara goma sha uku har yanzu ba ta ji daɗin auren shi ba, balle ta yi farinciki da zama da shi."
Shiru mutumin ya yi na ɗan lokaci bai ce komai ba, sai daga baya ya nemo wani sabon file ya fara rubutu. Sunanta ya nema da sunana har da na Mukhtar duka, sannan ya tambayi yaranmu nawa duka ta faɗa masa.
Bayan ya ƙare rubutun ya sake cire gilashin idonsa ya ce,
"Kotu kike so a tura ku a yi shari'a? Ko kuma sulhu kuke so a yi bayan fage ba tare da kowa ya sani ba?"
"A shiga kotun kawai!"
Zancen da na yi kenan cikin sauri ba tare da na jira na ji cewar Umma da hukuncinta ba. Saboda yadda nake jin tsanarsa ta linku sosai a kan sace mini yarana da ya yi, domin tun da na ji Umma ta faɗi ya sace su zuciyata ta gamsu da shi ne ya ɗauke su.
Duba da yadda suka yi a lokacin da ta je ɗauko mini kaya ita da Sajida, domin ya ce ba zai sake ni ba sai an ba shi yaransa.
'Waton suna wurin Barira?'
Tambayar da na yi kenan, kafin na tsinkayo muryar Umma tana faɗin, "Ba sai an shiga kotu ba! Ko iya sulhun aka yi ya wadatar. Matuƙar zai sake ta, kuma zai bar ta da yaranta."
Rubutu mutumin ya sake yi sannan ya ce da Umma, ta faɗi sunan unguwar da yake za a tura masa takardar sammaci.
"Runjin Sambo, kusa da layin gidan Hassan Ɗangote!"
Bayani ta yi tiryan-tiryan aka rubuta a jikin takarda, sannan aka tayar da manzo takanas a kan ya zo tare da yaran ana buƙatar ganin shi. Sannan mutumin ya miƙe ya ce mu jira shi ya sanar wa Ogansa, ya fice bayan ya rufo ƙofa na sauke ƙatuwar ajiyar zuciya.
Umma ta ɗora kallonta a kaina tana faɗin, "Duk abin da kika sani ki faɗa, tun daga farkon aurenku har zuwa yanzu."
Kai na ɗaga mata ba tare da na iya furta ko kalma ɗaya ba, har mutumin ya dawo ya ce da mu mu biyo shi. Yana gaba muna bayansa har wani babban ofishi, wanda tun da muka jefa ƙafafuwanmu sanyin A.c ya fara bugar mana fuska.
Wani kamilin farin tsoho na gani a kan kujera, fuskarsa a sake saɓanin wanda muka fara gani. Wuri ya nuna mana muka zauna, sannan ya sallami wanda ya kawo mu a kan ya tafi idan Mukhtar ya zo a kai shi ɗakin sulhu.
Idonsa ƙur a kanmu ni da Umma sannan ya ce, "Me ke faruwa tsakaninki da mijin naki?"
Zama na gyara sannan na fara zayyano masa tun farkon aurenmu har zuwa lokacin da ya sayar mini da kayan ɗaki. A nan ya ce na tsaya ya ci gaba da rubuce-rubuce a jikin wasu takardu sannan ya ce na ɗora, bayan an gabatar mana da lemu mai sanyi ni da Umma da ruwan gora guda biyu.
Bayani tiryan-tiryan na shiga yi ko waƙafi babu balle aya, har na gangaro inda ya sa aka zubar mini da cikina. A nan ma dakatar da ni ya yi bayan ya rintse idonsa yana jijjiga kai. Shiru ya ratsa tsakani sai ga sallamar mutumin da ya kawo mu ya dawo, bayani ya yi masa a kan ga Mukhtar can a ɗakin sulhu tare da yaran duka.
Zumbur na miƙe tun kafin a ba ni umurni na nemi ƙofar ficewa, farin dattijon ya ce,
"Ina za ki je?"
Kunya ta kama ni a lokacin da na yi ido biyu da Ummata, saboda kallon da take yi mini ya sa na ji kaina ya zama ƙatoto. Dawowa na yi na zauna sai da dajjiton ya ba mu umrnin mu je can kafin ya zo sannan muka fice ni da Umma.
Ɗakin sulhun babba ne mai ɗauke da kujerun roba farare za su kai guda ashirin. Tun daga nesa na hango su Umma Salma makure tamkar a ce 'kyat' su arce da gudu.
Suna hango mu suka zo da gudu suka rungume ni dukansu suna kuka. Tsabar tausayinsu ya sa na fara kukan ina dudduba fuskokinsu ina share musu ruwan hawaye. Umma Salma ta sake ni ta yi wurin Umma ta fashe da kuka. Saboda ni kaina na hango hawayen da Ummata take sharewa da gefen hijabinta. Hakan ya sa ta nemi kujera ta zauna ba tare da ta ce ƙanzil ba.
Ta gefen ido na saci kallon Mukhtar zaune a kan kujera fuskarsa a haɗe yana kallon bangon ɗakin. Yarana na ja muka yi kan kujeru muka zauna ina ci gaba da rarrashinsu a kan su daina kukan da suke yi.
Mun ɗauki minti goma kafin farin dattijon ya shigo, tare da wasu da ke take masa baya, cikinsu har da mutumin da ya kai mu wurinsa.
Zama ya yi a kan kujerar da ke fuskantarmu ya yi gyaran murya sannan ya ce,
"Mukhtar Sa'adu mai shadda!"
Sunan da farin dattijon ya faɗa kenan da ƙarfi, wanda na gama tantance shi ne alƙalin babbar kotun. Mukhtar ya fara zarar ido tare da faɗin,