Showing 117001 words to 120000 words out of 121208 words
Kuma ina buƙatar a raba aurenta da shi, tun kafin baƙincikinsa ya sa zuciyarta bugawa. Saboda tun da ta aure shi take fuskantar baƙinciki da ƙuncin zuciya har yanzu da muke wannan maganar. Ƙazafi, sharri, cin amana, yaudara, ƙarya, munafurci babu kalar wanda bai ƙulla mata ba. Tun tana ɓoyo ba ta bari na sani har ta fara sanar da ni ina tausar ta. Da abin ya kai maƙura ta fara neman hanyar barin gidansa ina danne ta, saboda ba na so ta fita gidan uban 'ya'yanta ta bar yaranta a gantale. Amma yanzu ni da kaina na tsani zamanta da shi, saboda an yi zama babu adadi ana yi musu sulhu. Sai an gyara kwana biyu ya dawo ma halinsa, to mun gaji daga ni har ita, har masu zaman sulhun. Ya sallame ta ko kuma ku ku sallame ta idan ya ƙi bi ta hanyar lalama!"
Shiru ya ratsa tsakanin maganganun Umma kafin Alƙalin ya yi gyaran murya ya ce,
"Ina Zaituna!"
Na miƙe jikina yana rawa saboda idanuwan da aka zuba kaina.
"Mijinki yana ba ki ci da sha da sutura?"
"Ba ya ba ni ranka ya daɗe! Saboda lalurorina duka da na yarana a kaina nake ɗaukar su, tun lokacin da na fara aiki!"
"Subhanallah!"
Ita ce maganar da na ji wani ya faɗa wanda ban san lokacin da ya shigo ɗakin ba. Sannan muryar Mukhtar da na tsinkayo yana faɗin,
"Wallahi ranka ya daɗe ƙarya take yi!"
Alƙalin ya dakatar da shi da hannunsa sannan ya gyara zamansa ya sake jefo mini wata tambayar,
"Ɓangaren shimfiɗa fa! Yana sauke nauyin da Allah ya ɗora masa kanki?"
"Ba ya saukewa! a
Asali ma rabon da mu'amalar aure ta haɗa ni da shi shekara huɗu kenan!"
"Harka ta lalace!"
Zancen Baba Ali kenan, kafin Alƙalin ya yi magana, Mukhtar ya riga shi da cewa,
"Wallahi ranka ya daɗe ko ranar na faɗa maka ba ta yarda da ni, ko na zo ta ba ni haƙƙina sai ta ƙi amincewa da ni. Dalilin haka ma na yi wani aure saboda kullum faɗin take yi; ita ba matata ba ce! Babu aurenmu!"
"To ke saboda me kike hana shi haƙƙinsa? Kuma me ya sa kike faɗar ke ba matarsa ba ce babu aurenku?"
Jikina yana rawa, cikin ɗaga murya na ce,
"Ranka ya daɗe tun da na aure shi shekara sha uku bai taɓa gamsar da ni ba. Sannan hannunsa yake aure ba farjina ba!"
Idona a rufe na faɗi maganar, saboda zuciyata ta gama rufewa da takaicin ƙaryata nin da yake yi, bayan ya san gaskiya. Ɗakin ya yi tsit ana sauraron maganar Alƙalin bayan wadda na faɗa.
"Idan na fahimce ki da kyau, tun da yake saduwar aure da ke, ba ki taɓa gamsuwa da alƙalaminsa ba. Haka ne?"
Na ɗaga masa kai duk da nauyin maganarsa da na ji a cikin kunnuwana.
"To zancen hannunsa yake aure ba farjinki ba! Me kike nufi da hakan?"
Sai da na goge gumin fuskata, sannan na daidaita natsuwata saboda nauyin faɗar maganar da nake ji a bakina.
"Tun da na aure shi, idan aka cire farkon aurenmu da yake nema na sosai. Yana kwashe wata biyu, uku, har zuwa biyar, shida bai neme ni ba. Idan ma ni na neme shi kai-tsaye yake nuna mini bacci yake ji. Wani lokaci kuma idan ana sanyi, yana cewa da ni asuba yake son tashi kuma ba ya son yin wanka sanyi yake ji. Tun ina neman haƙƙina a wurinsa yana hana ni, har ta kai idan na matsa masa ya yi mini kamar an yi masa dole. Yana ɓata fuska yake haiƙe mini babu wani ɗan saƙo, sannan minti biyu ya yi masa yawa ya zubar da ruwansa ya bar ni haka nan! Na sha kuka a kan wannan matsalar a ɓoye ba tare da ya sani ba, da na ga bai damu da damuwata ba na fito fili na sanar da shi ya nemi magani. Saboda na fara gundura da halinsa kuma shi ya ƙi ya gano matsalar domin ya gyara. Idan na yi masa zancen neman magani sai ya ce da ni, ai duk namijin da ya saba da amfani da maganin maza; to kullum ba ya iya komai sai ya yi aiki da shi zai moru. Zancen da yake yi mini kenan koyaushe, da ya ga na matsa masa, a kan dole ya nemo magani islamic center don na gaji; Sai ya je ya nemo maganin amma ko ya yi amfani da shi babu wani canjin da ake samu. A ƙarshe ma sai ya bijiro mini da zancen an ce asiri ne wani mai sona ya yi masa. Saboda ya hana mu zaman lafiyar aure, a cewarsa. Bayan kuma ya sha sanar da ni abin da yake yi yana gusar da sha'awarsa ba tare da ya neme ni ba. A ƙoƙarin shi na kare kansa daga neman matan da nake zarginsa da shi, saboda ganin rashin kulawar da yake yi wa haƙƙin auratayy..ar..mu."
Numfasawa na yi, saboda muryata da ta fara rawa alamun damuwa ƙarara a cikinta. Ɗakin ya yi tsit ban da ƙarar fankokin da ke kaɗawa a cikin ɗakin babu mai motsin kirki. Kallona na kai gefen da Mukhtar yake tare da su Yaya Maimuna, na hango shi yana goge gumi da gefen rigarsa. Da abin da ya kai masa maƙura ya cire hular kansa yana fifita.
"Me ya sanar da ke yana yi? Wanda ke gusar masa da sha'awarsa ba ya neman haƙƙinki da ke wurinsa?"
Ajiyar zuciya na sauke, sannan na furzar da iska mai sauti a bakina na ce,
"Amfani yake yi da hannunsa domin ya gamsar da kansa, a taƙaice dai Istimna'i a Musulunce. Dalilin da ya sa ba ya nema na kenan duk tsawon watannin da za mu ja ba ma tare, tun abin yana damuna na shige toilet na yi kuka a ɓoye, na dawo yi a gabansa ba ya bi ta kai, har ya ƙone mini zuciya na tattara shi duka na watsar. Saboda ganin kukana ba ya damunsa, na fara neman saki a wurinsa ba tare da kowa ya sani ba. Saboda wata magana da ya taɓa faɗa mini muna tsaka da hira watarana, inda ya sanar da ni shi da za a zare masa aure a rayuwarsa, da ya ji daɗi. Saboda zai iya tsare kansa ba tare da ya zauna da mace ba. Hakan ya tunzura ni na ga ni zaman me nake yi da shi. Na fitittike masa sosai a kan dole sai ya sake ni, amma ya rufe idonsa ruf! A kan shi ba zai iya sakina ba sai dai na yi haƙuri. Na rufe maganar ban taɓa faɗa wa kowa ba, saboda ba na so na zubar masa da mutunci a idon mutane. Duk da ni kullum burinsa kenan ya yi mini ƙazafi da sharri, saboda ganin ina raba dare ina chartting da mutane kafin na fara zuwa aiki. Allah ya sani ban da saurayi ko wata macen banza da nake hira da ita a waya. Amma akwai wasu groups da ake hira har biyun dare ba a yi bacci ba. A can nake biye matan group ɗin ana hira har dare ya raba, wadda duk rabin hirar a kan topic ne idan admins ɗin group sun turo a bai wa juna shawara. Sosai group ɗin yake ɗauke mini kewar rashin Mukhtar, sannan na yi sabo da mutanen sosai. Idan ba a gan ni ba har nema na ake yi a waya. To ire-iren hakan ne idan sun kira ni a waya cikin daren, ko kuma ya gan ni ina chatt ɗin ya ce da maza nake yi. Na sha faɗa masa, da a ce yana ba ni lokacinsa ya sauke haƙƙina da ke wuyansa, da na daina chatt ɗin dare gabaɗaya na ba shi lokacina, domin mu faranta wa juna. Amma shi zai kwashe lokaci mai tsawo a waje bai dawo gidan ba, wani lokaci har sha biyu da rabi na dare, ko ɗaya saura duka yana kaiwa waje bai dawo ba. Amma yanzu Alhmdulillah! Tun da na fara zuwa aiki na daina hira group ɗin, asali ma ba na samun damar chatt kamar yadda nake yi a can baya. Saboda haka don Allah ina so ya sauwaƙe mini, domin ina jin tsoron na faɗa muguwar rayuwa a sanadin aurensa!"
"Bayan ƙaton da kike tare da shi kuna sheƙe ayarku a wurin aikin, har wata muguwar rayuwa kike gudun faɗawa cikinta saboda aurena? Wallahi Allah sai ya saka mini a kan duk ƙazafin da kika yi mini don kawai kina so na sake ki!"
"Dakata Malam Mukhtar!"
Zancen Alƙalin kenan bayan maganarsa. Ya yi shiru yana aika mini harara tamkar idonsa su faɗo, bayan ya yi ƙwafa mai ƙara wadda ke nuna zallar ɓacin ran da yake ciki.
"Shin ka yarda da zancen da ta yi a kan Istimna'in da ta ce kana yi?"
Alƙalin ya jefo masa tambayar da ta so gigice shi, domin kuwa miƙewa ya yi taku ɗaya biyu kamar zai bar wurin, sannan ya koma kujerar da yake kai ya zauna yana zarar ido.
"Ƙarya take yi mini ranka ya daɗe!"
"To idan haka ne! Za mu ba ku ƙur'ani dukanku ku yi rantsuwa da shi, saboda ka ce tana zina, ita kuma ta ce ba taɓa yi ba. Shin ka yarda ka amince za ka rantse da alƙur'ani, domin ka kare kanka da duk abin da ta faɗa a kanka, wanda ba ka gamsu da su ba duka?"
Turka-turka! Ku hasko mana idon Mukhtar🤭
D. AUTA CE✍🏼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ARBA'IN DA BAKWAI.*
*Book 1 ending.*
"Rantsuwa da Al'ƙur'ani kuma!?"
Tambayar da ya yi wa Alƙalin kenan yana zarar ido, tare da miƙewa tsaye dafe da ƙirjinsa. Alƙalin bai yi magana ba illa ɗaga masa kan da ya yi alamun tabbatarwa. Sannan ya gyara zamansa ya ce da shi,
"Kwantar da hankalinka ka zauna!"
Mukhtar ya koma kan kujerar da yake kai ya zauna. Alƙalin ya ɗan muskuta bayan ya yi gyaran murya ya ce,
"Abin da ya sa ka ji an sako zancen rantsuwar! Saboda ka ce ƙarya ce take faɗa a kanka ba gaskiya ba. Amma idan ka gamsu da bayananta dole a jingine rantsuwar gefe. Daman ita ana yin ta ne kawai saboda a kore shakku, ko kuma kokwanton da ake yi a kan wani abu a yayin Shari'a. Don haka idan ka yi rantsuwar shi kenan za mu gamsu da zancenka. Ita kuma za mu ƙaryata zancen da ta yi a matsayin sharri ko ƙazafi, matuƙar ita ma ba ta karɓi rantsuwar ba."
"Ranka ya daɗe! Don Allah a bar zancen rantsuwar nan! Saboda na yi sau ɗaya kuma ba na fatar Allah ya sake kama ni da laifinta."
Mukhtar ya ƙare maganar yana goge gumin fuskarsa da gefen rigarsa. Alƙalin ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce,
"Me kake zance a kansa, na ka yi sau ɗaya?"
"Rantsuwar ranka ya daɗe!"
"To fa! Kenan dai ka gamsu da dukkan bayanan da ta yi?"
"Na gamsu da wasu, amma wasu ƙarya ce kawai take yi mini ranka ya daɗe kamar yadda na faɗa tun farko."
"Wace magana ce ƙarya? Kuma wace ce gaskiya a cikin abin da ta faɗa yanzu?"
In da-in da ya fara yi sannan ya ce, "Zancen da ta yi a kan na ce dama an cire mini aure ba gaskiya ba ne! Amma abin da ta ce ina yi wannan gaskiya ne tun ina saurayi. Saboda ba na so na faɗa sana'ar zinace-zinace, shi ya sa nake yin hakan musamman a lokutan da ta ƙi ba ni haƙƙina."
"Kenan ka tabbatar da kanka; kana yin hakan ba ƙarya ta yi maka ba?"
"Haka ne ranka ya daɗe!"
"To ma Sha Allah! Daman abin da nake so ka amsa kenan da bakinka. Kuma Alhamdulillah! Ka tabbatar da hakan a gaban kowa ya ji."
Shiru ya ratsa tsakani bayan maganar Alƙalin, babu wanda ya yi ko dogon motsi balle wani ya yi yunƙurin cewa wani abu. Sai da ya ja ɗan lokaci sannan ya sake magana cikin wata kalar murya ta daban, ba irin wadda ya yi wa Mukhtar tambayoyin da ita ba. Domin wannan muryar sabuwa a kame take sosai kuma harɗe, saɓanin ta farkon da yake haɗawa da murmushi yayin maganar.
"Istimna'i abu ne mai hatsari ga lafiyar mutum, sannan ƙololuwar zunubi a wurin Allah da addininmu na Musulunci. Saboda ko babu laifi a cikinsa yana haifar da matsalolin da za su zamo barazana ga lafiyar mai yin sa. Bayan ɓangaren wasu cututtukan, da kan iya zama barazanar da za ta shafi lafiyarsa da imaninsa, domin yana rage ƙarfin gani, kuma yana haifar da ƙuncin zuciya da yawan bugun ƙirji da na zuciya. Idan abin ya kama jikin mutum sosai yana haifar masa da taɓin ƙwaƙwalwa. Taɓin ƙwaƙwalwar kuma ba irin ta hauka ko doke-doke ba. A tsaye za a dinga ganin mutum lafiyayyensa amma ba ya aiki irin na masu cikakken hankali. Sannan an yi ittifaƙi a kan duk mai aikata irin wannan ɗabi'ar ta biya wa kai buƙata, musamman namiji; ba zai taɓa zaman aure da matarsa ba. Saboda zai rasa kuzarinsa na mazakutar ɗa namiji gabaɗaya, kuma zai iya komawa tamkar wani mata-maza ba tare da ya sani ba. Domin zai dinga abubuwa irin na mata, wanda idan aka yi rashin sa'a wata macen ma sai ta fi shi kuzari. Saboda ba zai iya ɗaukar lokaci yana saduwa da iyalinsa yadda ake so ba. Dalilin kuwa ya saba wasa da al'aurarsa, mintuna kaɗan ya zubar da ruwansa ya huta. Kuma shi kenan buƙatarsa ta gama biya daga hakan, saɓanin saduwar aure wadda ko ga mai kuzarin gaske sai ya yi da gaske. Domin a lokacin da maniyinsa yake gangar fita, ita kuma macen a lokacin sha'awarta take fara tashi. Shi ya sa masu dabara sai sun tabbatar da gamsuwar matansu; sannan suke zubar da ruwansu saboda gudun cutar da su, ba tare da sun sauke musu nauyin da ke rataye a kawunansu ba."
Shiru na ji Alƙalin ya yi kaina a duƙe, kunya kamar ta kashe ni. Saboda bayanin da yake yi cikin raina; ina jin ina ma ƙasa ta tsage na shige cikinta na ɓoye, saboda muguwar kunyar da ta lulluɓe ni.
Shirun da ya yi, ya bai wa kowa damar tagumi da nazartar maganganunsa. Duba da yanayin fuskokinsu da na saci kallo a fakaice ɗaya bayan ɗaya.
"Mukhtar ba za ka iya zaman aure da wannan baiwar Allah ba, idan ma kun ci gaba da zama; to kai ma za ka ci gaba da cutar da ita ne kamar yadda ka yi a baya. Don haka kotu za ta sauwaƙe mata, domin gudun ta faɗa halaka ta sanadin wannan ɗabi'ar da ta auri jikinka. Kai ma akwai damar gyara gare ka har yanzu tun da kana da sauran numfashi, saboda duk mai irin wannan halin, daidai yake da masu ɗabi'ar neman jinsi. Ma'ana mace ta nemi 'yar'uwarta mace ko namiji ya nemi ɗan'uwansa namiji, domin su biya wa juna buƙatunsu kuma su kawar wa da juna sha'awa. Kuma Allah da kansa ya tsine wa mai irin wannan halin har sau uku, inda masana sun ce babu wani laifi da bawa yake aikatawa na saɓo a nan doron duniya; wanda Ubangiji ya tsinewa mutum har sau uku jere da juna, sai masu aikata irin wannan ɗabi'ar. Kuma hukuncin neman jinsi ya yi kamanceceniya da biya wa kai buƙata. Wanda ake ɗaukar hannu ko wani abun da za a dinga wasa da azzakari ko farji, domin a biya wa kai buƙata ko kuma a gusar wa da juna sha'awa, ta wannan haramtacciyar hanya abin ƙyama. Saboda ɗabi'a ce irin ta dabbobi, shi kuma ɗan'adam Allah ya bambanta shi da dabba don ya mallaka masa hankalin da bai bai wa dabbobin ba."
Sai da ya numfasa, sannan ya sauke ajiyar zuciya ya sake cewa,
"Abin da kowa ya sani zina saɓon Allah ce, ya saka haramci a cikinta kuma ya ce mu nisance ta. Amma tana da sauƙi a kan wannan mummunar ɗabi'ar ta maɗigo, luwaɗi da biya wa kai buƙata. Kuma duk masu irin wannan halin, suna cikin tsinuwar Allah da mala'ikunsa koyaushe. Sannan muddin suka mutu a cikin wannan halin ba tare da sun tuba ba, to tabbas za su dawwama a cikin wutar jahanna da azaba marar yankewa."