Showing 108001 words to 111000 words out of 121208 words
kan kujera ita ma ta zauna. A bisa umurnin da babban jami'in ya ba mu daga ni har ita.
Sannan ya yi gyaran murya ya ce, "To maganar gaskiya, mun fahimci wannan lamari ƙarya ce kawai babu gaskiya a ciki. Don haka mun kori wannan case ɗin ku je ku sasanta kanku a gida. Amma kafin ku je, ya dace mu yi muku iyaka da juna, a matsayinmu na jami'ai. Daga yau kada wanda ya sake tayar da wannan magana, saboda mun kashe ta daga yanzu kuma mun binne ta a nan. Tun da daman can kun kai matsalar kotun ƙoli kuma ba a gama zartar da hukunci ba. To mu babu abin da za mu yi muku a nan, ku tashi ku je kuma ku tabbatar da an kashe wannan rigima daga nan."
Wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyata, cike da tunanin abin da ya sauya musu ra'ayi lokaci ɗaya kuma nan take. Wani ƙanen Mukhtar cikin zafin rai ya ce,
"Ranka ya daɗe haƙƙin ɗan'uwanmu muke so a ƙwato mana fa! Saboda ta ji masa a mazakutarsa yanzu haka yana ƙarƙashin kulawar likitoci."
"Mu dai mun kori case ɗin daga hannunmu, amma idan kun ga za ku iya kai wa wani wuri ƙofa a buɗe take."
Zancen babban jami'in kenan, sannan ya miƙe ya fice. Yaya Maimuna cikin ƙololuwar ɓacin rai ta ce,
" Rashin adalci dai ake ƙoƙarin yi mana, to wallahi Mukhtar ya gama zama da ke daga yau ɗin nan. Hamza miƙo mini takardar sakinta da ya ba mu sallahun a ba ta." Ta miƙa hannunta ga wani ƙanen Mukhtar, wanda tun da aka zo wurin bai ce komai. Takarda ya ciro daga aljihunsa ya miƙa mata, ta fisga cikin fushi ta wurgo mini tana faɗin,
"Ga shi nan! Daga yau Allah ya raba mu da masifa da bala'i!"
Cikin sauri Kawu Sale ya duƙa ya ɗauki takardar ya saka aljihu ba tare da ya duba ba. Umma ta miƙe tana faɗin,
"Masifa da bala'i kam yanzu kuka fara cin karo da ita! Kuma ku jira ku gani idan haƙƙi zai bar ku ku shaƙi iska mai kyau!"
Tana ƙare faɗar hakan ta ja hannuna muka fice, 'yar sandar muka ci karo da ita za ta shiga ɗakin. Umma ta nuna mata wuyanta da hannu alamun sai ta yanka ta, murmushi kawai 'yar sandar ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Kawu Sale ya biyo mu muka fito harabar wurin. MD na hango da babban jami'in suna ta hira har da dariya, sosai mamaki ya kama ni. Saboda walwalar da na hango kwance a kan fuskokinsu, kuma alamunsu ya nuna akwai kyakkyawar sanayya a tsakaninsu.
Ban bi ta kan shi ba daga ni har Umma, Kawu Sale ne kawai ya nufi inda suke, ina ji kafin mu yi nisa da su yana faɗa wa babban jami'in takardar sakin da aka ba ni.
Ban san ya suka yi ba, muka nufi hanyar gida a ƙasa ni da Umma jugum-jugum babu mai magana. Har mun yi nisa MD ya biyo mu tare da Kawu Sale a cikin motarsa.
Tsayawa ya yi daf da mu ya yi parking ya fito. Har ƙasa ya duƙa ya gayar da Umma kansa a duƙe. Umma ta amsa tana haɗe fuska ni ma na gayar da shi fuskata babu yabo babu fallasa, saboda har lokacin akwai busasshen hawaye a kan fuskar tawa.
"Mama ku zo na sauke ku gida!" Umma ta ce,
"Tafiyarka kawai mun kusa ƙarasawa kada mu wahalar da kai."
"Don Allah Habi ki shigo mu tafi! Saboda akwai maganar da za mu yi da shi idan mun je gida!"
Hannun Umma na ja muka shiga motar muka zauna, "Ai Habi wannan yaro; babu abin da za mu ce da shi sai godiya! Saboda shi ne ya kashe wannan gobara da ta turnuƙe. Ba don shi ba da yanzu ba mu san inda matsalar za ta tsaya ba, don haka mu gode wa Allah mu gode masa. Saboda waɗannan mutane da gaske suke yi sai sun nuna wa yarinyar nan iyakarta. Amma da yake ta Allah ba tasu ba, ga shi komai ya dakata ba tare da sun ci galaba a kanmu ba!"
Daga ni har Umma tsit muka yi ba tare da mun ce komai ba, Kawu Sale kawai yake ta zuba shi kaɗai har muka kai ƙofar gidansa.
Bayan mun fiffito ne Kawu ya fara yi wa MD godiya Umma ma ta yi masa godiyar ta shige gida. Kawu ya ƙaraso inda nake yana faɗin,
"Ki gode wa Allah ki gode masa. Don shi ne ya yayyafa wa wutar ruwan sanyi ta kwanta, kuma babban jami'in ya tabbatar mini da duk inda suka kai ƙara a cikin garin nan; sai sun sa a kore su."
Hawaye mai sanyi na ji ya zubo mini a kan fuska, da sauri na goge sannan na kalli MD na ce,
"Na gode maka sosai! Ubangiji ya jiƙan magabata!"
Ina gama faɗar hakan na yi cikin gida na bar shi a nan tare da Kawu Sale. Muryar Umma na tsinkayo a lokacin da na kutsa kaina gidan tana cewa,
"Ni fa Kulu wallahi ba na son mutumin can yana manne wa Zaituna. Haka fa shekaranjiya ko da muka fita mun gan shi a ƙofar gidan nan. Haushi ya sa ban bi ta kansa ba a lokacin da yake roƙon mu zo ya kai mu inda za mu je."
Kaina a tsaye na isa inda suke tsaitsaye suna maganar na ce,
"Shi ya cece ni a lokacin da mota ta tashi kaɗe ni bayan na fito ma'aikatarmu a ruɗe. Hakan ya sa ya kawo ni gida, kuma shi ne dalilin da ya sa kika gan shi kenan bayan mun fita, saboda wayata da ke hannunsa yana son ba ni. Don jiya bayan mun dawo daga kotu, Inna Kulu ta ba ni wayar da ya kawo a ajiye mini. Yanzu ma ni ce na tura masa saƙo a lokacin da 'yan sandan suka zo tafiya da ni. Kuma kin ji abin da Kawu ya ce ba don shi ba da ba mu san inda matsalar za ta tsaya ba!"
Shiru kawai Umma ta yi ba ta ce komai ba, illa butar da ta ɗauka ta shige bayi. Inna Kulu ce kawai ta fara jinjina abin tana faɗin Allah ya saka masa da alheri. Kawu Sale ya shigo gidan yana yabon kirkin MD tare da nuna jin daɗinsa a fili, dangane da halin girman da ya nuna mana.
Takardar sakin ya ciro daga aljihunsa ya miƙo mini yana faɗin,
"Allah ya raba ki da alaƙaƙai. Ubangiji ya kawo miki kyakkyawan sauyi a nan gaba."
Hannu biyu na saka na karɓi takardar zuciyata fes! Sai dai ganin rubutun ya sa annurin fuskata ɗaukewa. Domin a kallon farko na gane ba rubutun Mukhtar ba ne a jikin takardar, kenan dai har yanzu tana ƙasa tana dabo tsugunne ba ta ƙare ba.
"Yawwa! Bari na je yanzu na nemo mana motar da za ta kwaso miki kayanki." Zancen Umma kenan da ya sa na ɗauke kallona daga saman rubutun sakin da su Yaya Maimuna suka yi mini. Domin ganin rubutun ya sa na yi tantamar bai san wainar da suke toyawa ba.
Umma ta fice na ja ƙafafuwana na shige ɗakinta na kwanta ina cizon takardar a bakina. Saboda tunanin maganar da Mukhtar ya sha faɗa a kan ba zai taɓa sakina ba, a haka zan ƙare cikin gidansa a wulaƙance, gudun ya sake ni wani mai kuɗi ya aure ni.
"Hmmmmm! Akwai Allah!"
Kuma ba ya barci balle gyangyaɗi😢
D. AUTA CE✍🏼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ARBA'IN DA HUƊU.*
_'Komai za ki yi yanzu; aikin gama ya gama sai haƙuri. Kuma zama da ni yanzu kika fara, don wallahi babu wata kotu ko alƙalin da zai sakin ki ba tare da amincewa ta ba. Yadda muka fara rayuwa tare haka za mu ƙare ta, saboda babu ɗan iskan ƙaton da zan bari ya aure ki bayan ya gama bibiyar ki da aurena, ba tare da ya yi duba da illar ɗaukar wa kansa kaya a dalilin auren da ke saman kanki ba.'_
Zancen Mukhtar kenan da ya faɗo mini a zuciya, tamkar a lokacin yake furta mini shi a cikin dodon kunnuwana. "Hmmmmm!"
Sautin ajiyar zuciyar da na sauke da ƙarfi kenan, saboda na yi amanna da cewa Mukhtar ba zai sake ni ta daɗin rai ba, ko kuma cikin ruwan sanyi irin haka ba. Wannan shiri ne daga hannun su Yaya Maimuna.
'Shin ta ya ya zan faɗa wa Umma har yanzu ina ɗauke da auren Mukhtar a saman kaina?'
'Ki ƙyale ta kawai a kwashe miki kayanki. Don ko kin bar su ba za ki koma zama gidansa ba!'
Zancen da wata zuciyar ta yi mini kenan cikin ƙwarin gwiwar da take ƙara mini, a kan rabuwa da gidan Mukhtar ta wannan hanyar. Kiran sallar Zuhur ya sa na miƙe jiki babu kuzari na yi arwala. Ina tsaka da sallah yara suka shigo da gudu Haidar yana faɗin,
"Yeeee! Ni na riga ku shigowa."
Shigowar su ɗakin daidai da shigowar Inna Kulu da kulolin abincinmu a hannunta. Ajiye mana namu ta yi a gabana tana faɗin,
"Ga abincinku nan, kuma don Allah ki daure ki ci kafin ta dawo mu je mu kwaso kayan."
Rungume ni yaran suka yi dukansu suna faɗin,
"Mama mun dawo!"
Murmushin yaƙe na yi wa Inna Kulu ina ƙoƙarin zare jakar makarantar da ke bayan Haidar. Sannan na ce da ita,
"Mun gode sosai Inna!"
Haidar ya fara ƙoƙarin buɗe kular abincin Umma Salma ta dungure masa kai tana faɗin,
"Kai dai ka sha haushi! Tun da ba za ka bari sai an ba ka ba!"
"Ƙyale shi je ku cire kayanku! Kai ma tashi sai ka cire uniform ɗinka sannan ka zo ka ci abincin!"
Yana turo baki ya miƙe yana hararar Umma Salma da ta janyo na hana shi cin abincin ba tare da ya cire kayansa ba.
Tare da su muka ci abincin babu laifi na ci da ɗan dama kafin na zare hannuna. Saboda jin da nake yi kamar zan yi amai muddin na ci gaba da cusa shi kamar yadda nake ta ƙoƙari.
Ko da Umma ta dawo gidan, gabaɗaya alamun jigata ya bayyana kan fuskarta. Amma a hakan ta ce da ni na tashi mu je a ɗebo kayan saboda na fi ta sanin kayana, gudun a haɗo da na Barira kuma hakan ya zamo wani sabon tashin hankali.
Inna Kulu ce ta ce da ita ta ci abincin tukunna idan ta yi sallah sai mu je. Ta ce ta yi wa mai motar kwatancen gidan wataƙila ma sai ya riga mu zuwa.
Dole ba don ta so ba ta zauna zaman cin abincin a gurguje ta yi sallah, saboda kiran da mai motar yake ta yi mata a waya yana faɗin ita yake jira. Zuciyata babu wata walwala muka fito gidan, bayan na bai wa su Ummu Salma umurnin su yi sallah da wanka kafin mu dawo.
Tun da muka doshi ƙofar gidan na ji ƙirjina yana dakan luguden uku-uku, saboda har raina ba na farinciki da kwashe kayan da muke ƙoƙarin yi. In da ta ni za a bi sai an jira idan ya sake ni sannan a kwashe kayan, duk da ba na zaton zan sake zama gidan amma kuma ba na so mu yi wahala a banza.
Kasancewar ina da makullin gidan a jikin na ɗakina, da na ƙofar falo tare da wadrobe ɗin da nake ajiyar wasu kayana a kitchen. Hakan ya sa ba mu sha wuyar shiga gidan ba duk da yake ƙargame, alamun masu gidan ba su ciki.
Da mamaki muka isa tsakiyar gidan, saboda ganin komai kaca-kaca tamkar an yi yaƙi. Ko'ina kwanoni da kofuna warwatse bayan tukunyoyin da aka jera kowace an yi girki da ita an ƙi wankewa.
Ganin murhu da itace ajiye tsakar a gidan, hakan ya sa na gano da shi Barira take girki. Falon muka kutsa kai babu shiri na zaro ido waje, saboda ganin an dawo da kujeruna inda aka ajiye na Barira. Sannan babu nata ko ɗaya a falon sai nawa da aka maye gurbin nata da su.
Kasancewar mai motar tare yake da waɗanda za su taimaka masa, na ba su umurnin su fitar da kujerun waje su saka mota. Sannan na buɗe ɗakina Inna Kulu tana faɗin,
"Ita wannan amarya halan ɗiyar wane hamshaƙi ce a garin nan?"
"Me kika gani?"
Tambayar da na yi mata kenan ina tura ƙofar ɗakina da na buɗe ina 'yar dariya.
"Na ga gidan kamar ba ta san miye shara ba balle wanke-wanke!"
Ɗakin muka shiga ina faɗin, "Matar so ai ba za a auro ta don wahala ba. Da dai a ce shi ɗin ba son jiki ne da shi ba, da sai ya dingà gyara mata komai su huta da ƙazanta."
"Ikon Allàh!"
Inna Kulu ta faɗa tana ƙoƙarin cire labulen ɗakin, na yi 'yar dariya sannan na ce,
"To wallahi in dai Mukhtar ne har tsutsotsi sai kayanta sun yi ba tare da ya ɗaga su daga inda suke ba, balle ya kawar da su a ji daɗi. Saboda duk lokacin da na je Kebbi, na sha dawowa garin nan na tarar da kwanonina ko wata kulata da tsutsotsi suna gwazarniya. Saboda ba ya iya ɗauke kwano a inda ya ci abinci, haka ma ba ya iya wankewa sai dai ya nemo wani ya ƙara ɓatawa. Gidan nan kuma tamkar an yi yaƙi a cikinsa don komai sai na gani, tsakanin kwalayen tabar da yake Sha, gwangwanin maltina da ledodin ruwan pure water. Wasu ma an sha rabi an ajiye, wasu kuma ajiya ta sa sun fashe da kansu, sai tarin takardu da mujallun da yake bita tamkar wani furofesa."
"Cabɗijam!" Inna Kulu ta faɗa tana riƙe da gemunta, fuskarta cike da mamakin maganganun da na faɗa. Umma tana fito da kayan wadrobe ɗita ta ce,
"Ai duk wanda ya zauna da Mukhtar dole ne a yi masa sannu, kamar yadda ake yi wa mara lafiya idan an je ganin sa. Don zama da shi babban ciwo ne mai zaman kansa, wanda babu maganinsa matuƙar ba rabuwa aka yi da shi ba!"
Ina dariya na ce, "Wallahi ko kashi ya yi ba ya flooshing Umma, haka zai cika masai abinsa ya wanke jikinsa ya fito. Tun ina zuba ruwa cikin mutunci ba na damuwa har na fara jin haushinsa ina masa ƙorafi. Amma wallahi bai daina ba, don sai ya gama wankansa ya fita idan na shiga toilet ɗin na taras da kashin zanƙare cikin kwalbar masan. Dole ba don na so ba nake zuba ruwa na wanke toilet ɗin ina gunguni. Allah bai raba ni da matsalarsa ba har sai da muka dawo gidan nan."
"Wannan ai ƙazanta ce wallahi! Amma idan kika gan shi fes-fes da shi kamar bai san wani abu ƙazanta ba." Cewar Inna Kulu kenan suna ƙoƙarin ɓalle gado bayan an fitar da katifu. Dariya na fashe da ita ina faɗin,
"To wallahi Inna har da majina yake kaftawa ƙasan toilet ɗin sai na zo takawa na ji santsinta ya kwashe ni. Sannan ko a gidan nan haka yake duk da ɗakinsa daban nawa daban, amma warin da toilet ɗinsa yake yi wani lokaci har cikin falon nan gabaɗaya gamewa yake. Saboda ba ya flooshing tsawon kwanaki, warin kashin ya haɗe da warin tabarsa wuri ɗaya, ana tura kai ɗakinsa dole sai an fito ana toshe hanci. Da ƙyar na samu ya daina rashin zuba ruwa ko shi sai da na fara yi masa gorin; a gan shi a hanya tsaf-tsaf! Ɗakinsa kamar shekar ɓeraye. A haka nake ta jifar sa da maganganun da zai suke sa yana jin haushi har ya gyara dolensa. Saboda na yi iya ƙoƙarina wurin ci