Showing 114001 words to 117000 words out of 121208 words
naka naka ne komai muninsa. Ke za ki iya canza miji amma ita ba za ta iya canza uba ba! Idan kuma kika matsa ke ma zan ce ki koma Birnin Kebbi don nan ba gidan ubanki ba ne."
"Yanzu Umma a kanta za ki yi mini gorin gida?"
"ke a tunaninki kin fi ta matsayi a wurina ne?"
"Ai ni kika haifa ba ita ba!"
"Abin cikin ƙwai ya fi ƙwan daɗi. Don haka daga yau kada na sake jin kina yi mata faɗa don ta nuna damuwa a kan mahaifinta. Saboda ko mu ba shi muke ƙi ba halinsa ne ba ma so, amma tun da zuri'a ta haɗa dole ne mu yi haƙuri da duk abin da za mu gani."
Haka Umma ta dingà yi mini faɗa cikin kwantar da murya, har ta wanke mini haushin da Ummu Salma ta cusa mini. Saboda kishin ganin ta fi son gidan Mukhtar da gidan Kawu Sale. Haƙuri ta dingà ba ni cikin kuka bayan Umma ta fita, tana roƙon na yi haƙuri na yafe mata.
Fuskata a haɗe na ce da ita, muddin ta sake nuna ba ta son zaman gidan sai ta koma gidan Mukhtar. Kuma daga lokacin da ta koma babu ruwana da ita, kada ta sake zuwa gidan ta bar shi kenan.
Na yi hakan ne saboda tsoron wauta ta sa ta koma gidan ban sani ba. Gudun ta janyo mini gorinsa, ko kuma sabon tashin hankalin da zan shiga sanadin komawar ta hannunsa.
"Gobe dai za mu koma kotun, duk da ya yi sakin yana da kyau mu koma kamar yadda aka umuce mu."
Zancen Umma kenan a lokacin da take ƙoƙarin zama kan gadonta bayan ta fito daga wanka. Ƙirjina na ji ya buga dam-dam! Ina murmushin yaƙe na ce,
"Allah ya kai mu! Amma fa Umma rubutun sakin nan; kamar ba Mukhtar ne ya rubuta shi ba!"
"Saboda me kika ce hakan?" Tambayar da ta jefo mini kenan idonta a kaina ko ƙyaftawa babu, fuskarta a haɗe.
"Rubutun na gani kamar ba nasa ba!"
"To ko ba shi ya rubuta ba kin saku kenan! Babu wanda zai sake mayar da ke gidansa. Idan kuma ke ce ba ki gama fige kazar wa kanki kazar wahalar da ya yanka miki ba; ƙofa a buɗe take kin san hanya kina iya komawa!"
"Innalillahi Umma! Wallahi ba nufina kenan ba! Rubutun ne kawai na gani kamar ba nasa ba!"
"Ummmh!" Bayan hakan ƙanzil ba ta ce da ni ba, illa shirin kwanciya da ta yi ta kwanta tana tofe ɗakin da addu'o'i. Shiru kawai na yi ina nazarin halin Umma, wani lokaci idan ta yi wani abu kamar tana jiran mutum, da ya yi magana ta ga laifinsa.
Haka na kwana ina ta juya abubuwa da yawa a cikin zuciyata har bacci ya ɗauke ni ban tantance ba.
****
Tun da safe na ga shigowar alert a wayata, ganin salary'na ya faranta mini rai sosai. Na tashi da kuzari na share gidan tas sannan na gyara ɗakin Umma ko'ina tsaf-tsaf!
A gurguje na shirya muka fito ni da yaran bayan Najib ya ajiye su; na yi masa transfer'r kuɗin jingar da muka yi da shi duk wata, har da ɗorin wasu canjin don ya ji daɗin ɗawainiyar da yake yi da mu .
Ya ajiye ni yana ta godiya da nufin sha biyu na rana zai dawo ya ɗauke ni, kasancewar ranar jumu'a ce da wuri muke tashi. Fuskata babu yabo babu fallasa na gaisa da mutane, sannan na karɓi makulli a hannun masinjanmu na buɗe na shiga.
Ko zama ban yi ba Inna mai shara ta shigo na fito ofishin bayan mun gaisa a mutunce. Ina zaune saman dogon bencin ƙarfe da ke bakin ofishin saboda baƙi masu zuwa. Kaina duƙe ina latsa waya na ji ƙamshin turaren MD cikin hancina, cikin sauri na ɗago kaina muka yi four eyes da shi ya fito daga ofis ɗinsa.
Murmushin yaƙe na yi masa saboda ƙirjina da ke ta bugawa sanadin ganin shi, ban tashi daga zaunen ba har ya iso inda nake yana shan ƙamshi ya ce,
"Kwanan nan ki gane fashin zuwa aiki. Yana da kyau ki gyara saboda akwai ayukanki sosai da nake bai wa wasu suna yi. Ba na so mutane su hankalta a fara surutun ba ki san aikinki ba, bayan na gama bugun ƙirji a kan jajircewar da kike yi tuƙuru a cikin aikin naki."
Shiru na yi kawai, saboda tunanin da nake yi ai ya san rabin matsalolin da nake ciki. Kuma idan zai yi mini adalci ba zai ga laifina don na yi fashin zuwa aikin ba, saboda ina ƙoƙarin ba da abin da ake so, kafin zuwan matsalolin da suka taushe kuzarina.
"In Sha Allah zan kiyaye!"
Iya abin da na faɗa kenan, sannan na mayar da kaina ina ci gaba da latsar wayata. Takun wucewarsa na ji bayan ƙafafuwansa da na gani a duƙen da nake suna wucewa ta gabana.
Haka kawai na tsinci kaina da wata sabuwar damuwa, saboda yanayin muryarsa da na ji yayin maganar; ya fito mini da damuwar da yake ciki a kan laifin fashin zuwa na aiki. Inna ta fito tana sanar da ni ta kammala, godiya na yi mata sannan na shiga da guntuwar sallama a bakina.
Zaman da na yi a kan kujerata ya tuna mini da file's ɗin da na tura a wadrobe na ajiye, waɗanda ban kammala aikinsu ba a ranar da Najib ya kira ni yana sanar da ni bai ga su Ummu Salma ba.
Abin mamaki ko da na buɗa wurin babu komai, sai jakata da na zo da ita a ranar na gani. Hakan ya sa na tuno lokacin da na fice ofishin da gudu cikin ruɗu waya a kunnena. Murmushi kawai na yi sannan a fili na furta,
"Allah ya raba mu da tashin hankali!"
Amina ce ta faɗo mini a rai, saboda tuno tun ranar ban koma jin ɗuriyarta ba ko a waya. Cikin sauri na fiddo wayata na nemo lambarta na danna mata kira. Sai dai har ta yi ringing ta ƙare ba a ɗauka ba, sai da na sake kira sannan aka ɗauka. Maimakon na ji muryar Amina sai na ji muryar wata babbar mace tana cewa,
"Waye?"
Bakina yana rawa na ce, "Amina nake nema, ni abokiyar aikinta ce kwana biyu ban ji motsinta ba, shi ya sa na kira na ji ko lafiya?"
"Lafiyarta ƙalau! Wayar tana hannuna ne! Kuma ta daina fita yawon gantalin da take zuwa da sunan aiki. Ki faɗa wa shugabanku ya cire sunanta cikin ma'aikatanku don ba za ta sake zuwa yawon tanɓelen ba!."
Tana ƙare faɗar hakan ta katse kiran, ko da na sake bin wayar da kira, da nufin na ba ta haƙuri na ji wayar a kashe.
Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce,
"Ita kuma Amina tata ƙaddarar kenan baƙincikin Suruka! Shin yaushe mata za su huta da matsalolin gidajen aurensu ne? Daga wannan sai wannan!"
Hmmmmm! Mataye Allah ya ƙara mana haƙuri😢
D.AUTA CE✍🏼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ARBA'IN DA SHIDA.*
'Babu rana!' Ita ce amsar da zuciyata ta ba ni kai-tsaye ba tare da jinkiri ba. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na gyara zamana, tare da lulawa duniyar nazarin abubuwan da suka shuɗe a cikin rayuwata. Da waɗanda nake fuskanta a yanzu, bayan tunanin gobena da inda za ta nufa idan aurena da Mukhtar ya ƙare.
Ranar dai kamar MD ya yi fushi da ni, domin kuwa babu aikin da ya ba ni yadda na je haka na fito a lokacin da aka tashi. Zuciyata babu daɗi na fito ofishin ina tunanin na je na same shi ko kuma na share. Saboda ina so na ji laifin da na yi masa, bayan na fashin zuwa aikin da ya sanar da ni.
'Tafiyar ki kawai' shi ne umurnin da wata zuciyar ta ba ni, cike da jin kaina wata saboda ba na son Shan ƙamshin da yake yi mini. Bayan haɗe fuskar da yake yi idan ya gan ni tamkar wata dodanniya.
Adaidaitasahu na samu na nufi gida ban jira Najib ba, saboda zuciyata a cunkushe take da tunanin MD. A kan kalar halin da yake nuna mini, idan yana mini magana tamkar an yi masa dole ba ya so. Motar da na gani a ƙofar gidan Kawu Sale, ta sa na yi hanzarin isa bakin ƙofar ɗakinsa da ke wajen gidan. Saboda ganin baƙin takalmi da kuma muryar Baba Ali da na jiyo suna hira da Kawu Salen.
Har ƙasa na durƙusa bakina a washe na fara gayar da shi, ya amsa mini cike da kulawa na yi masa sannu da zuwa. sannan na gayar da Yaya Manu babban ɗansa da suka zo tare. Na miƙe ina ƙoƙarin juyawa na shiga cikin gidan, Kawu Sale ya yi saurin faɗin,
"Ke muke jira ki dawo mu je kotun fa! Saboda a yi komai a ƙare kowa hankalinsa ya kwanta a huta da an-yi-an-ce."
Dam-dam! Sautin bugun ƙirjina kenan ina dariyar yaƙe na ce, "Ai da an kira ni tun ɗazu Kawu, saboda yau ban yi aiki da yawa ba!"
"Alhaji Ali muka jira ya zo, saboda shi ma bai daɗe da shigowa garin nan ba."
"Allah Sarki!"
Ita ce kalmar da na iya faɗa sannan na yi cikin gidan, Kawu Sale yana faɗin na yi sauri mu fito ni da Umma, kada mu ɓata masa lokaci yau za su komwa Kebbin.
Na jinjina lamarin sosai a zuciyata, saboda tunanin yadda aka yi Baba Alin ya zo garin sanadin matsalar kawai. Domin rabon da ya zo gidan har na manta, duk abin da ake yi ana yi ne a waya. Ko ya kira mu ni da Umma da Kawu Sale, ko kuma mu mu kira shi idan ta kama.
Yarana suka zo da gudu suka faɗa jikina suna faɗin,
"Mama sannu da zuwa!"
Na rungume su kaɗan ina murmushi na yi ɗakin Umma, bayan na yi wa Inna Kulu sannu da gida. Ganin Umma fes cikin shirinta na sabuwar atamfa gal, hakan ya sa na ajiye jakunkunan da ke hannuna ina faɗin,
"Wanga gayu Umma kamar mai zuwa biki?"
Harara ta wurgo mini tana cin abinci ta ce,
"Ki dai shirya ke kaɗai ake jira!"
Na cire hijabina na fice da sauri, jikina kawai na wanke sannan na yi arwala na yi sallah a gurguje. A tsaitsaye na tsakuri abincin da Ummu Salma ta ajiye mini a lokacin da nake sallah, na sauya kaya da ɗan turare kaɗan na goga na fito. Saboda Umma har ta fice waje tare da yaran duka saboda da su za a je, kamar yadda Alƙalin ya ba da umurnin na zo da su tun farko.
Motar muka shiga dukanmu, Baba Ali gaban motar tare da Yaya Manu da ya tuƙo shi. Umma da Kawu da ni har yaran muka zauna bayan motar, Kawu Sale rungume da Haidar Ni na rungume Iman, Umma Salma zaune tsakaninmu ni da Umma.
Kasancewar babu tazara mai yawa a tsakanin Bafarawa Estate da High Cort ɗin. Mintuna kaɗan suka kai mu bakin gate ɗin kotun, Yaya Manu ya shigar da motar harabar kotun bayan an ba shi damar shiga. Wuri ya samu cikin inuwar Durumin da ta yi luf-luf ya yi parking. Muka fito dukanmu muka nufi cikin kotun, ƙirjina yana bugawa da sauri da sauri.
Ba mu jira iso ga kowa ba, muka nufi ofishin Alƙalin Baba Ali gaba muna bayansa. Cike da mamaki kafin mu shiga Alƙalin ya fito ya tarbe mu, sannan ya bai wa Baba Ali hannu suka gaisa cikin fuskar sanayya. Bayan ya gaisa da Kawu Sale mu ma muka gaishe shi ya amsa cikin kulawa.
Ɗakin sulhun muka nufa kai-tsaye tun kafin mu ƙarasa shiga na hango Mukhtar, tare da Yaya Maimuna da ƙannensa biyu maza har da Barira. Zuciyata cike da mamakin me ya kawo Barira a cikin case ɗinmu.
'Mijinta ta yi wa rakiya!'
Amsar da zuciyata ta ba ni kenan, babu shiri na yi murmushi. Saboda daman can na yi niyyar fashe ƙwan Mukhtar a gaban kowa domin a san halin da yake ciki. Shi ma ya san matsayinsa a addinance ko da zai tuba kafin ya mutuwa ta ɗauki ransa, cike da fatar ya samu rabauta a nan duniya da gobe ƙiyama.
Bayan kowa da ake buƙatar gani a wurin ya hakarta, aka buɗe taro da addu'a sannan aka fara bayanin abin da ya haɗa mu duka.
Wani mai farar takarda a hannunsa, ya fara gabatar da ƙarar da Umma ta kawo kotun, a kan tana buƙatar Mukhtar ya sake ni. Alƙalin ya kira sunan Mukhtar ya jaddada masa abin da Umma take nema a wurin shi. Mukhtar ya gyara zamansa sannan ya ce,
"Ranka shi daɗe! Ba zan iya sakin matata ba! Don haka ina neman alfarmar a yafe mini mu daidaita kanmu. In Sha Allah zan gyara duk abin da ta ce ina yi mata ba tare da ɓata lokaci ba."
Kallon-kallo muka fara yi da juna tsakanin ni, Umma da Kawu Sale har ma da su Yaya Maimuna. Kawu Sale ya ɗaga hannu alamun yana son a ba shi damar yin magana.
Alƙali ya ɗaga masa hannu alamun ya faɗi shaƙƙuwarsa. Kawu Sale ya miƙe yana gyara babbar rigarsa ya ce,
"Ranka ya daɗe Mukhtar ya saki Matarsa jiya. Saboda Yayarsa ta ba mu takardar sakin Zaituna da hannunta ta ce shi ya ce a ba ta. Kuma Alhmdulillah mun duba mun gani saki uku ne a cikin takard...!"
"Wallahi! Wallahi! Ni ban saki matata ba!"
Zancen Mukhtar kenan da ya karaɗe ɗakin bayan ya zabura, jikinsa har ɓari yake yi wurin faɗin maganar tun kafin Kawu Sale ya kai ƙarshen maganarsa. Mamaki ya game fuskokin mutanen wurin, amma ni ko gezau ban yi ba. Saboda daman can na san za a rina; wai an saci zanen mahaukaciya.
"Ina Yayar tasa take a nan?"
Tambayar da Alƙalin ya jefo kenan yana wurga idonsa domin ya hango ta ina zai gan ta. Yaya Maimuna ta miƙe ido wuƙi-wuƙi muryarta tana rawa ta ce,
"A lokacin da yake cikin zafin ciwon da ta yi masa rauni a gabansa. Ya ba mu umurnin mu rubuta mata sakinta uku mu kai mata, bayan ya tabbatar mana da ba zai sake zama da ita ba har abada!"
"To ni dai wallahi ban san na sake ta ba, ban taɓa furta saki a bakina ba ko a hayyacina balle ina cikin zafin ciwo. Kuma ni dukan da ta yi mini a jikina bai zautar da ni ba balle na fita hankalina, na yi irin wannan aika-aikar! Don haka ni ba da yawuna aka ba ta takarda ba, kuma ban san lokacin da suka yi ba. Sannan ba su sanar da ni ba sai yanzu da na ji an faɗa!"
Ɗakin ya yi tsit na ɗan lokaci ana nazarin maganganun Mukhtar. Kafin Alƙalin ya yi gyaran murya ya ce,
"To a shari'ance, wani ba ya sakin matar wani. Ko da Mahaifiyarsa ce ko mahaifinsa, addini bai ba su damar sakin matarsa ba balle Yayarsa. Saboda haka takardar sakin da aka ba ta ba ta saku ba! Har yanzu tana nan matsayinta na matarsa. Don ko da a ce shi ne ya furta sakin da bakinsa ba ya cikin hayyacinsa; to akwai aurensu matuƙar ya dawo hankalinsa ya nuna bai san ya aikata ba. Idan ma ya yi ne da gangan ya ce bai san ya yi ba, shi Allah ya sani kuma zunubin da aka ɗauka cikin auren bayan haka duka a kansa zai hau. Domin mu da zahiri muke aiki, sanin gaibu sai Ubangijin da ya halicci ƙirazanmu!"
"Alhmdulillah!" Ita ce kalmar da Mukhtar ya furta a bayyane cikin ɗaga murya, har da ɗaga hannu sama ya shafa a fuskarsa alamun ya yi nasara.
Umma ta ɗaga hannu aka ba ta damar magana ta miƙe,
"Ranka ya daɗe ni mahaifiyar Zaituna ce!