Showing 111001 words to 114000 words out of 121208 words

Chapter 38 - ABOKIN AIKINA HAUSA NOVEL

24 Nov 2024

6422

gaba da wanke masa toilet ɗin amma na kasa, Ummu Salma ma da nake sakawa tana wanke masa, duk ranar da ta yi aikin ƙyanƙyaminta nake yi ko kusa da ni hana ta zuwa nake yi."

"Tsakani da Allah ko nawa za a ba ni ba zan iya zama da Mukhtar ba!" Umma ta faɗa tana buɗe window ta furzar da yawu tana yatsina fuska. Dariya ta suɓuce mini na ce,
"Ai yanzu ya daina, yana wanke kayansa amma fa wallahi ba koyaushe yake flooshing ba. Saboda ɗabi'ar ta bi jikinsa ba ya iya aikin komai sai ci da kwanciya. Amma shara ma idan ba an yi sa'a ya bar ɗakinsa a buɗe mun share masa ba; sai ya fi ƙarfin wata ɗaya har biyu bai nemi a gyara masa ko ya gyara da kansa ba. Amma babu laifi sharar ma yanzu yana yi da kansa idan ya gaji da zama cikin datti."

"Wannan kuma kin fi shi laifi gaskiya! Don ke ya dace a ce kullum kina share masa ɗakin, ko da ba za ki yi hidimar kashinsa ba!" Umma ta faɗa tana haɗe fuska, sannan ta fitar da hanjin gadon waje ta dawo. Cikin sanyin jiki na ce da ita,
"Ai ke Umma a baya yana barin ɗakin buɗe ya tafiyarsa, amma yanzu kullum rufewa yake yi sai an ci sa'a yake barin shi buɗe ya fita. Ko na ce ya ba da makulli a buɗe ɗakin a share masa, sai ya ce a bar masa kayansa haka nan sai ya tashi."
"To wannan kam daga ke har shi kuna da laifi! Tun da ba makulli ɗaya ba ne sai ki zari wani ki ɓoye. Duk lokacin da ya fita sai ki buɗe ki share masa ɗakin ki mayar ki rufe. Saboda irin Mukhtar ko haƙƙin kansa ma ba ya iya saukewa balle na abokin zamansa. Don wallahi a yadda yaken nan ko dabba aka ba shi kiwo sai ta mutu bai san ta mutu na, saboda rashin kulawa balle ɗan mutum mai buƙatu da yawa. Allah dai ya sauya miki da alheri, amma shi kam ba mijin aure ba ne ga duk macen da ta san ciwon kanta."

Ta ƙare maganar tana goge gumin fuskarta, Inna Kulu ta yi tsaki sannan ta ce, "Ni fa tun inda lamarinsa ya fara ba ni tsoro; da na ji ta ce duk inda za ta je a faɗin garin nan don ta daɗe ba zai neme ta ba. Haka ma idan ta dawo ba zai tambaya ya ji lafiya ba, wannan ai ba aure ba ne kuma rashin sanin ciwon kai ne kawai wallahi. Na ga ni nan tsohuwa ce ba yarinya ba, amma idan fita ta kama ni Sale ya dingà shimfiɗa mini dokoki kenan. Idan ma na yi fitar waya bisa waya a kan na dawo, hankalinsa ba zai kwanta ba har sai ya ga na dawo gidan nan na zauna."

Umma ta riga ni faɗar maganar da nake ƙoƙarin fitarwa a bakina, ta yi hanzarin cewa da ita,
"To ai shi Salenmu na daban ne kowa ma ya sani wallahi."
Inna Kulu tana dariya ta ce,
"Daman can aikinku kenan kuri da nuna kun fi kowa iya zaman aure!"
"Kin dai ga zahiri don ke ma kin san ba kowane namiji ne irin Salenmu ba!"
Umma ta faɗa kanta tsaye, Inna Kulu ta riƙe baki tana kallon ta murmushi a kan fuskarta bakinta ya ƙi rufuwa, saboda ta san gaskiya ce Umma ta faɗa. Don ni kaina rayuwar Kawu Sale tana burge ni matuƙa, musamman da bai haɗa komai da Inna Kulu ba. A gaban kowa yana iya nuna mata ƙauna da kulawa babu ruwansa da sun tsufa, ko 'ya'ya da jikoki ba za su saka shi jin nauyin ɗaura mata ɗankwali ba, ko kuma ya kakkaɓe mata ƙurar hayaƙi a saman kai idan ya ga ta ɓata mata jiki. Nama ma idan ya siyo wani lokaci idan ya ɗauki yanka ɗaya kafin a raba ya ci, to ita ma sai ya ɗauki ɗaya ya kai mata a baki, mu yi ta dariya.
Zancen Inna Kulun ne ya katse mini tunanin rayuwar aurensu mai ɗauke da kulawa tare da fahimtar juna.

"Tabbas! Sale mutum ne, don ko ina zan iya bugun ƙirji na ce na yi sa'ar aure. Don duk macen da mijinta bai damu da yawan fitar da take yi ba; gaskiya yana da rangwamen ƙaunarta. Saboda ke kanki macen da kike tambayar fitar kullum yana barin ki babu musu, wallahi watarana sai kin ji wani iri, matuƙar kin san kanki."

Dariya na fashe da ita ina faɗin, "Zancenki haka yake Inna! Saboda ni kaina haushi nake ji a lokacin da nake tambayarsa fita. Wani lokaci ma ba ya bari na kai ƙarshen zancen balle na faɗi abin da zai kai ni; yake cewa da ni sai kin dawo. Watarana ma idan na ji haushi na ce, wai kai ba za ka ce da ni ban zuwa ba, kullum da na faɗa ko bakina ba na rufewa kake cewa sai na dawo. Sai ya ce idan tafiyar ce ba na so na yi zamana kawai, ya fita ya bar ni cike da mamakin murɗaɗɗen halinsa."
"Ai duk macen da ke tambayar fita koyaushe a ce mata tafi, ba ta yi sa'a ba. Gara a dingà nuna miki iko da isa a wasu lokutan. Ta hakan kike gane an damu da ke, kuma ana kishinki."

Shiru kawai na yi a kitchen bayan na gama saka kulolina a buhuhuwa, ina nazarin maganganun Inna Kulu masu ɗauke da zallar gaskiya. Musamman da na tuno faɗan da na ji MD yana yi wa matarsa a waya, a kan yawan fitar da take yi tare da kashedin kada ya dawo ya iske ba ta gidan.

'Kenan dai shi ma yana son matarsa?'

Tambayar da na yi wa kaina kenan, kafin na ɗora Umma ta shigo kitchen ɗin ta sa masu ɗaukar kayan suka ɗauki buhuhuwan. Kallo na ta yi cike da sakin fuska ta ce,
"Sai me kuma ya rage? Duk an fitar da kayan waje har an je kai wasu a dawo."
Murmushin yaƙe na yi, wanda iyakacin shi kan fuskata, sannan na dudduba drowowin babu komai nawa sai na Barira da na bar mata. Na ce da ita,

"Komai na kwashe!"

"To zo mu je waje mu jira shi ya dawo a kwashe mu gabaɗaya"

Bayanta na bi ina ƙoƙarin goge ƙwallar da ta cika mini kurmin ido, saboda kwata-kwata na rasa me ke mini daɗi. Har ga Allah ba na son zama da Mukhtar, amma kuma ba na son rabuwa da gidan. Don na yi sabon da ba na jin daɗin zama ko'ina idan ba shi ba, ko gidan Kawu Sale da nake ban rasa komai ba amma zaman da na yi kwana biyun ba na jin daɗinsa.
Muna ƙoƙarin fitowa falon muka yi kiciɓis da Barira, fuskarta a cure tana yi mana wani irin kallon da na kasa fassara ma'anarsa. Ta gefenta kawai muka raɓa za mu fice gidan, a sama na tsinkayo muryarta tana faɗin,

"Allah dai ya sa ba a haɗa da kayan masu gidan ba!"





To fa! Su waye masu gidan🤭😹







D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*Ina jin daɗin yadda kuke bin alƙalamina sau da ƙafa! Na gode sosai da addu'o'in da kuke yi mini, saboda kyakkyawar Addu'arku gare ni tana faranta mini rai sosai, matuƙa gaya😍 alherin Allah ya kai muku duk inda kuke, kuma a inda kuka kasance. Much luv you all😘*


*ARBA'IN DA BIYAR.*

"Ke! Ɗebabbiyar albarka ki shiga taitayinki baƙar almura. Figai-figai da ke amma kin iya haɗa kitifiri da salon makirci kala-kala! To ba kayan masu gida muka haɗa da su ba; rayuwarsu muka kwashe gabaɗaya za mu tafi da ita. Ban da ma kike daƙiƙiya ba ki da ƙwai balle dunge a cikin gidan, amma kike tinƙaho da shi? To buɗe kunnenki da kyau ki ji; da gidan uba ake ado saboda shi ne tabbatacce ba gidan miji ba. Mijin ma irin Mukhtar da ko kansa bai taimaka ba, balle ya taimake ki ku gyara gidan da ke barazanar mutuwa da ƙazanta!"
Zancen Umma kenan tana nuna Barira da hannu cikin ƙololuwar ɓacin rai. Janyo Umma na yi da nufin mu tafi, don ba na so a sake yin wani abu a ce mu ne da laifi. Barira sai kallon banza take aiko mana tun lokacin da Umma ta fara magana, tana wurgo mana hararar sama da ƙasa riƙe da ƙugunta har da murguɗa baki.
Zuciya ta so ingiza ni na kifar da ita, domin ban san lokacin da na saki Umma na isa wurinta ina nuna ta da hannu ba. Amma bakina yana rawa na kasa furta ko kalma ɗaya saboda tunanin kalar dukan da zan yi mata. Duk da bandejin da na gani damɓare a gefen kanta ya nashe da jini.
Umma ta yi hanzarin cewa da ni, "Zo mu je kada ki biye wannan shashashar da ko uwarta ba ta ragawa balle uwar wasu. Ko da yake ma abin a nono aka tsotso, don barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarrafe! Ladi cinnaka ce banza ko Amadu Ƙwambo"
Ƙwafa kawai na yi raina a ɓace na juya, bayan na gama yi mata kashedi da ido tamkar na rufe ta da duka. Muna gaf da fita gidan na tsinkayo muryarta a sama tana faɗin,
"Allah dai ya raba mu da gayyar jaraba a gida. Yanzu mutum ya sakata ya wala babu mai takura shi ko a saka masa ido ana neman tona masa asiri. Wuuuu! Allah ya raka taki gona!"

Raina ya zo wuya na juyo da nufin nuna mata tawa kala, Umma ta yi saurin riƙe ni tana faɗin, "Kada ki ƙarasa gawar da ba taki ba! Na fahimci inda ta dosa abokin mutuwa kawai take nema. Mu tafi kawai kowa halinsa ya cece shi khairan ko sharran!"
Har muka shiga mota Barira ba ta daina jefo mana magana ba, bayan sowar da take yi tana faɗin gaba gaibu. Inna Kulu ta zuro hannu tana faɗin,
"Ke arrr! Tabbatacciya mara ɗa'a! In dai gidan miji ne ke ma ba ki da cikakken garantin zama a cikinsa."
Ina hangen ta ta madubi bayan motar ta juya, har da tiƙar rawa take yi tana dafe kai domin ta nuna mana jin daɗinta a fili. Muna gaf da ficewa layin na hango Taufiƙ cikin sauri na ƙwala masa kira, sannan na ce da mai motar don Allah ya ɗan tsaya.
Da sauri ya iso jikin motar yana gaishe mu fuskarsa babu walwala. Nan take na ji hawaye ya cika mini ido saboda ramar da na gani ta bayyana a kan fuskarsa.

"Ya jikin Baban naka?"

"Da sauƙi!"

"Don Allah ka yi masa sannu da jiki kafin mu zo. Allah ya ƙara lafiya."

"Amin." Ya faɗa sannan ya bar jikin motar hannunsa ɗaya a kai, ban san lokacin da na ce da shi ba,

"Mamarka ta kira ka?"

Hawaye ya sharce sannan ya girgiza kai ya bar wurin hannunsa ɗaya a aljihu, ɗaya yana shafar fuskarsa da jikina ya ba ni kuka ne yake yi. Kuka ya suɓuce mini na ɓalle murfin motar na fito, kiran shi na yi cikin muryar kuka ya waigo ba tare da ya dawo ba. Na yi tattaki da kaina na isa inda yake, hawaye shaɓe-shaɓe a kan fuskata na ce da shi,

"Ba ni lambarka za mu yi waya!"

Ya faɗo mini na yi saving a wayata sannan na ce da shi,
"Mutanen Kano sun san abin da ke faruwa?"
Hawaye ya sharce sannan ya ɗaga mini kai ba tare da ya yi magana ba.
"Ok tom! Ina Bafarawa Estate! Idan akwai wani abu da kake buƙata ka same ni a can. Zan kira ka a waya sai ka yi saving lambata. Allah ya kawo mana sauƙi a cikin al'amurranmu duka."
"Amin" kawai ya ce sannan ya yi gaba, na koma motar muka fice layin zuciyata cike da ƙunci. Don ganin sa ya haifar mini da damuwar da Barira ba ta yi nasarar saka ni cikinta ba.

"Yaron nan ya ba ni tausayi matuƙa wallahi! Ubangiji ya zama gatansa ya dawo masa da uwarsa kusa."

Zancen Inna Kulu kenan da ya taɓa mini zuciya sosai, saboda mummunar ƙaddara ce kawai ta hau kan Maman Taufiƙ. Ta bar yaronta a gantale bayan ta illata masa Mahaifi balle ya rage masa zafin rashin ta kusa da shi.
Kiran shi na yi tana shiga na ce da shi ni ce, sannan na jaddada masa idan akwai wani abu ya kira ni. Haƙuri na dinga ba shi saboda na ji sautin sharɓen kukan da yake yi a cikin wayar.
Umma da ta cire tagumin da ta yi ta ce,
"Yaro da gatansa an mayar da shi marayan ƙarfi da yaji. Ubangiji ya karkato hankalinta ta dawo gida tun kafin lokaci ya ƙure mata."

"Amin" muka haɗa baki wurin faɗa, sannan shiru ya ratsa tsakani babu wanda ya sake cewa komai tsawon lokaci. Inna Kulu ce ta kawar da shirun da sauke ajiyar zuciya ta ce,
"Allah ya kare mu da tsaka mai wuya. Don duk kishin da zai rufe mana ido mu aikata ba daidai ba; ya zame mana musibar da za mu roƙi Ubangiji ya shiga tsakaninmu da ita! Allah ka dawo da ita hanyar gaskiya ko don yaronta"

"Amin-amin."

Ko da muka isa ƙofar gidan ana shigar da kayan da aka fara kawowa. Ɗaki sukutum aka ware wa kayana, wanda daman can tarkace ne a ciki. Wasu kuma aka saka ƙarƙashin gadon Umma da na Inna Kulun. Wanɗanda zan yi amfani da su kuma na ajiye su kusa.

"Haidar sai tsalle yake yi cike da murnar jin mun dawo gidan gabaɗaya."

Ummu Salma ce kawai na ga damuwa a kan fuskarta, na yi kamar ban gano ta ba. Har sai da ta gaji da ƙuncinta ta same ni a kan sallaya, bayan na gama sallar Isha ina jan carbi ta zauna gefena, cikin sanyin murya ta ce,

"Wai yanzu shi kenan mun bar gidan Abbanmu?"

Wani kallo na yi mata sannan na ce, "Idan kuma kina son zama gidan ki koma can kawai! Amma ni dai na gama zama cikinsa da yardar Allah!"

"Ni ba na so mu bar gidan ne kawai! Amma abin da Abbanmu yake kwata-kwata ba na jin daɗinsa. Shi kenan da gidanmu za mu bar wa wata shi ita kaɗai ta zauna?"

"Ok! Ki ce damuwarki duka tana kan amaryarsa! Kuma tun da shi ya ji ya gani ke miye naki a ciki?"

"Kawai dai haushi nake ji wallahi! A ce saboda ita mun bar gidan Abbanmu!"

"Ba saboda ita muka bar gidan ba! Don ba yau ya fara yi mana cin kashi a cikin gidan ba! Sai dai idan kina so ki ɗora mata laifin da ba nata ba, don kawai kina so ki wanke mahaifinki"

Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, na ci gaba da jan carbina ban sake bi ta kanta ba. Saboda na daɗe da fahimtar ba ta so a faɗi laifin Mukhtar, da an fara zancensa komai take walwala sai fuskarta ta sauya.
Nan take na ji raina ya ɓaci, saboda tunanin da zuciyata ta ɗarsa mini, a kan ta fi son mahaifinta a kaina. Kira na ƙwala mata cikin sauri bayan ta fita ɗakin, ta dawo ta tsugunna gabana, yanayin fuskata da ta gani ta sha jinin jikinta. A fusace na da ita,

"Tattara kayanki gobe idan Allah ya kai mu ki koma gidanku!"

"Don Allah ki yi haƙuri! Wallahi ba da wata manufa na yi maganar ba, kawai dai ba na so ki bar gidan ne saboda wata banza!"
Ta ƙare maganar bayan ta fashe da kuka, cikin ɗaga murya na ce da ita,
"Sai fa kin koma gidan ubanki, tun da na gano kin fi son shi da ni."
Umma ta shigo ɗakin tana faɗin,
"Babu inda za ta je matuƙar ina cikin gidan nan! Ubanta kuma dole ta so shi komai mugun halinsa tana son kayanta a haka. Don babu wanda ya fi mata shi kaf faɗin duniya, saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login