Showing 102001 words to 105000 words out of 121208 words
"Na!am! Ranka ya daɗe!"
"Me ke tsakaninka da matarka, kuma uwar 'ya'yanka, mai suna Zaituna Aliyu?"
Fiki-fiki ya fara yi da ido sannan ya ce, "Wallahi ranka ya daɗe, duk matsalolin da ke faruwa ita ce take janyo su."
"Matsaloli! Kamar me da me!?"
Alƙalin ya sake jefo masa wata tambayar cikin ɗaga murya. Mukhtar ya fara rawar murya yana cewa,
"Ita da ƙawarta suka haɗa kai suka yi wa matata ɗan banzan duka har suka tsige mata kitson da ke kanta. Yanzu haka sai da aka yi mata allurai na fito bayan an sake wanke raunin da suka yi mata."
"Idan waccan ta gida ka kira ta da matarka; ita wannan da ke zaune tare da yaranka miye matsayinta a wurinka?"
Tambayar alƙali kenan ga Mukhtar cikin sigar sargafo masa wuya da igiya, ba tare da ya hankalta ba.
"Eee to! Ita ma matata ce! Duk da kullum tana faɗar ita ba matata ce ba!"
"Mace tana saki ne?"
"A'a ranka shi daɗe! Amma ita tuni tana iƙirarin babu aurena a saman kanta."
"Saboda me?"
"Saboda shekara huɗu ba tare da ya haɗa shimfiɗarsa da ni ba!"
Amsar da na cafke kenan ba tare da na jira Mukhtar ya amsa ba. Kafin ya furzo na shi kalaman da ke ƙoƙarin kore maganata da gangan.
"Ko na neme ta, ba ta yarda da ni ranka ya daɗe tsawon shekaru!"
"Ƙarya kake yi baƙin munafuki! Kuma ƙaryarka ta gama shan ƙarya!"
Zancen Ummata kenan, bayan ta yi kukan kura ta cafko wuyan shi. Duka ta shiga kai masa tana ƙarajin faɗin ƙarya yake yi. Da ƙyar aka raba ta da shi bayan ta kai shi ƙasa ta danne wuyan shi da kujerar robar.
Tarin wahala ya dinga yi yana jujjuya wuya bayan an taɓe shi a hannun Umma, ita kuma sai surutai take yi cikin wani yaren da ban taɓa ji ba, daga baya kuma ta dawo fillanci bakinta yana kumfa.
Kasancewar shi ma alƙalin bafulatani ne, tare da shi suka yi ta maganganun da ban san me suke faɗa da fulatanci ba. Don iya sani na ita kanta Ummata ba ta iya yaren ba, amma zar-zar take ta zubo shi ko nunfasawa babu.
Alƙalin ya ce na riƙa ta mu je gida har yaran duka na tafi da su, sannan ya ce da Mukhtar ya je bayan kwana biyu za a nemo mu. Da haka muka fito ɗakin Mukhtar ya wuce ta gabanmu fuuu tamkar ya tashi sama.
Murmushi na ji ya suɓuce mini a lokacin da na tuna murƙusar da ya sha a hannun Umma. Bakin titin kotun muka tsaya har muka samo abin hawa, na miƙar da Ummata daga zaunen da na sa ta yi, a gindin bishiyar dalbejiya domin ta sha iska.
Sai da na saka ta ta zauna, sannan su Ummu Salma suka shiga muka tafi. Zuciyata wasai saboda ganin yarana da ke kusa da ni, duk da wani sashen zuciyar tawa danƙare yake da tunanin halin da Sajida take ciki.
Har ƙofar gidan Kawu Sale aka ajiye mu muka fito. Jakar Umma da ke hannuna na buɗe na biya mana kuɗin sannan muka yi cikin gidan.
Inna kulu da yaranta biyu mata da ke aure suka tarbe mu da gudu, suna ta murnar ganin su Ummu Salma. Tare muka shiga gidan na kai Umma ɗakinta na kwantar sannan na ce da su Inna Kulu,
"Umma ba ta da lafiya."
"Subhanallah! Me ya same ta? Ina kuka je na fita nenan ku ban gan ku ba!" Zancen Inna Kulu kenan da Kawu Sale da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin idonsa a kan Umma.
"Daga babbar kotun jaha muka fito."
"Kotuuuu!!!"
Abin da suka faɗa kenan dukansu suna zaro ido, Kawu Sale ne ya ƙara da cewa,
"Wai ke Habi me ya sa duk abin da za ki yi, ba ki damu da shawara ba? Shi kenan ba za ki bari a bi komai a hankali ba, sai kin fallasa komai a idon duniya kowa ya sani?"
Cikin sanyin jiki Inna Kulu ta ce, "Shi ma fa gaskiya ba ya kyautawa. Don ko yaran nan jikina ya ba ni shi ya ɗauke su."
"To idan ma shi ya ɗauke su ai yaransa ne yana da iko da su. Matslarsa ɗaya da bai faɗa suna hannunsa ba tun kafin a fara neman s.."
Kiran da ake yi wa wayata da ke jone jikin cherger ya katse zancen da Kawu Sale yake yi. Da mamaki na bi wayar da kallo saboda ganin ta a ɗakin, don rabon da na saka ta idona tun lokacin da mota ta ture ni na jefar da ita.
"Bayan kun fita ne wani ya aiko da ita ya ce a ajiye miki."
Zancen Inna Kulu kenan a lokacin da na sunkuya zan ɗauki wayar. Ban ce da ita komai saboda ƙoƙarin danna kore da nake yi domin na karɓi kiran, saboda ganin baƙuwar lamba na kwaɗaitu na ji dalilin kiran.
"Aunty ki kwantar da hankalinki ga ni Asibitin Uduth ana ƙara mini ruwa wutar ba ta ƙone ni ba."
Muryar Sajida kenan da na ji cikin muryar kuka, a cikin dodon kunnena.
"Alhamdulillah!"
Ita ce kalmar da na iya ambata sannan na sauke wayar daga kunnena ina sauke ajiyar zuciya. Ina ƙoƙarin mayar da wayar a caji na hango wani saƙon da ya ja hankalina. Babu shiri na dawo na zauna gefen gadon Umma tare da buɗe saƙon, jikina yana rawa ƙirjina yana bugawa da sauri.
"Burinki ya cika an yi mini kishiya kamar yadda kike mini fata. Amma ki sani ko da kin ji saƙon mutuwar Sajida da Aminu ni ce sila, saboda na saka musu wuta dukansu na ƙone su, kuma ko an neme ni; abadan wanda ya san ni ba zai sake saka ni cikin idonsa ba. Na bar ki da girman cin amanar da kika yi mini kuma kika yi wa aurena. Allah ya isa tsakanina da ke Zaituna, Ubangiji ya linka miki azaba da bala'i fiye da wadda kike fuskanta a yanzu. Na tsane ki na tsani duk abin da ya shafe ku daga ke har ci ƙwallon munafukin maci amanar ƙarshe. Allah ya jijjiga rayuwarku duka ya ɗaiɗaita ku duka tare farincikinku, fiye da yadda kuka haɗa kai kuka ci amanata ba tare da na sani ba."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni musibati wa akhlifni khairun minha."
Jiri ya kwashe ni daga zaune na tafi luuu...
😢😢😢😢kuma dai
D. AUTA CE✍🏼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ARBA'IN DA BIYU.*
Wayar ta suɓuce a hannuna tana ƙoƙarin faɗuwa na ji an tare, sannan aka zare ta daga hannuna. Shiru kawai na yi idona a buɗe tangarau ina kallon rufin ɗakin Umma, amma na kasa motsa ko da ƙwayar idon nawa balle hannuna ko wata gaɓa da ke jikina. Sai hawayen da ke bi ta gefe da gefen fuskata yana sauka saman shimfiɗar gadon Ummata.
Sunana Inna Kulu ta fara kira cikin tashin hankali ta iso daidai kaina ta tallabo ni, rikicaa na koma jikinta na kwanta tamkar babu laka a jikina.
"Me ya faru kuma yanzu?...Ke Asabe miƙo mini ruwa."
Tambayar da ta yi mini kenan tare da bai wa 'yarta ta farin umurnin ta kawo mata ruwa. Kaina ta tayar cikin ƙarfin hali tare da ɗora mini kofin ruwan a bakina. Ban musa ba na yi jarumtar buɗe bakin ta zirara mini ruwan ya gangara cikin maƙoshina. Babu shiri na fara tari saboda sarƙenin da ruwan ya yi a maƙogwaro, saboda ya yi gaggawar zuwa inda ba a aike shi ba. Sannu suka fara jera mini daga ita har yaranta da Kawu Manu da ke kaina, kafin tarin ya lafa na samu ƙarfin zubar da ruwan hawayen, wani bayan wani tamkar burgaggen fanfo. Buɗe bakina na yi da ƙyar sannan na ce,
"Rayuwata ba ta da wani amfani, tun da har na kasa hana abin da zai janyo nakasar rayuwakan makusantana. Me ya sa duk wanda ya raɓe ni sai ya samu guzurin baƙinciki da takaici? Me ya sa waɗanda ke kusa da ni ba za su bar ni na ci gaba da rayuwa da baƙincikina ni kaɗai ba? Na yi danasanin sanin Mukhtar a rayuwata balle aurensa. Zama da shi bai yi mini amfani ba, tun da har hakan ya yi silar ruguje zaman amincin da ke tsakanin Maman Taufiƙ da mijinta. Allah ya gani ban haɗa mijinta da Sajida ba, amma ga shi ni take ganin laifi bayan ta juye mini rabin kason zunubinta a kaina. Allah me na yi maka ka jarrabe ni da irin waɗannan tarin matsaloli? Me na yi aka hana mini farinciki rayuwa tun daga ƙurciyata har yanzu da lokaci ya fara gangare mini? Allah ka kashe ni na huta ko da zan rage jin zafin ƙunar da zuciyata ke yi...Allah! Allah! Allah!..."
Na dinga ambaton kiran sunan Allah cikin ƙanƙan da kai, da kai wa maƙura a cikin ƙololuwar damuwar da nake ciki. Abin mamaki hawaye ne shaɓe-shaɓe a kan fuskar Inna Kulu da 'ya'yanta Aunty Asabe da Umaima. Baba Sale ya fice yana girgiza kai fuskarsa a haɗe ba tare da ya ce komai ba.
Kuka nake yi iya ƙarfina yarana ma suna taya ni, Aunty Asabe ta fitar da su tsakar gida tana rarrashin su. Inna Kulu ce ta yi ƙarfin halin faɗin,
"Ki yi shiru Zaituna! Kada ki bari damuwa ta saka ki yin saɓo ba tare da kin sani ba. Ki yi imani da cewa Allah yana son ki kuma yana sane da duk wani halin da kike ciki. Sannan ki ƙara yi masa godiya a kan tarin ni'imomin da ya mallaka miki. Ke musulma ce kuma mumina mai kishin addini da ibada daidai gwargwado. Sannan kina da cikakkiyar lafiya kuma kina da halitta mai kyau, irin wadda ba kowa yake samu ba. Ya arzuta ki da 'ya'ya har guda uku reras, wanɗanda wasu suna can suna nema ido rufe amma ba su samu ba. Mahaifiyarki tana raye kuma koyaushe tana tausaya miki, tana saka miki albarka babu dare babu rana. A duk wani motsinta sunanki ne a bakinta, bayan addu'o'in da kuɗin duniya ba za su iya mallaka miki rabin abin da take roƙar miki ba. Shin ko iya hakan bai sa ki gano Allah ya fifita ki da miliyan ba? Saboda yana son ki kuma yana tare da duk wani mai haƙuri a ko'ina ya jefa ƙafarsa. To ki bar wa Allah ragamarki, domin ya ja ki ya kai ki inda ƙwaƙwalwarki ba ta taɓa tunanin kai wa ba."
Sosai maganganun Inna Kulu sun ratsa jikina, haka ma sun saka ni jin wani sanyi ya tsirga mini a cikin zuciya. Tsoron Allah da tsantsar imani da tawakkali a kan komai ya zauna mini daram a cikin raina. Ajiyar zuciya na shiga saukewa wata bayan wata kafin na fara shesshekar kukan da na ci lokaci bayan lokaci.
"Faɗa mini, me kika gani a cikin wayar wanda ya tayar miki da hankali har haka da yawa?"
Majinar kuka na zuƙe tamkar ƙaramar yarinya, sannan na ce da ita, "Maman Taufiƙ ce ta saka wa Sajida da mijinta wuta. Sannan ta ce ba za a sake jin ɗuriyarta ba a faɗin duniya, kada a neme ta don wani idon sani ba zai taɓa ganin ta ba."
"Subhanallah! Wai me mata suka ɗauki kishi ne? Yanzu irin wannan aika-aikar da ta aikata; kuma ta tsallake ta tsere. Shin a tunaninta don ta yi hakan zai dawo mata da farincikin da ta rasa? Ko kuma zai iya canza wa ƙadddararta suna ne ta dawo kanar ba a yi ba? Kai jama'a! Duniya ina za ki da mu? A kan kishi ka nemi halaka wasu ka halaka kanka a banza!"
Ɗakin ya ɗauki shiru na tsawon lokaci babu wanda ya yi dogon motsi. Umma ta tashi zaune tana ƙare mana kallo ɗaya bayan ɗaya sannan ta tsayar da kallon ta a kaina ta ce,
"Ina Mukhtar ɗin? Ya ba ki takardarki?"
Murmushin yaƙe kawai na yi mata, sannan na saka hannu na goge ruwan hawayen da ke gangaro mini a kan fuska.
"Ba na son kukan nan! Faɗa mini ya ba ki takardar sakinki ko a'a?"
Abin da ta faɗa kenan fuskarta a haɗe bayan ta ƙure manejin kallonta a kaina. Idonta a kan fuskata na ce,
"Bai ba ni ba! Amma dai zai ba ni idan muka koma."
Zumbur ta miƙe tana zarar ido, na yi hanzarin tashi tsaye na riƙe ta, cikin sigar rarrashi na ce da ita,
"Ki yi haƙuri Umma! In sha Allah komai ya zo ƙarshe a tsakanina da shi. Don kafin mu baro kotun sai da Alƙalin ya sanar da ni; idan muka dawo za a saka shi a sauwaƙe mini ko da ba ya so."
"Yaushe za a koma?" Tambayar da ta yi mini kenana har lokacin idonta a kaina.
"Bayan kwana biyu ya ce mu koma."
Sannan ta koma ta zauna dafe da kanta, wanda alamunta ya nuna mini ciwo yake yi mata. Duba da yadda take yamutsa fuska tana girgiza kan nata idonta a rufe.
Ficewa na yi daga ɗakin jikina babu kuzari, saboda magriba ta gabato amma ko sallar Zuhur ban yi ba balle Asr. Ban bi ta kan yarana da na hango ɗakin Inna Kulu ba, arwala kawai na ɗora na koma na shimfiɗa carpet na fara sallah. Raka'ar ƙarshe ta sallar Asr aka fara kiran magrib. Hattama su na yi duka sannan na buɗe hannuna sama ina roƙon sauƙi da sassauci a wurin Ubangiji.
Na jima a kan sallayar har aka kira Isha ban tashi ba, sannan na ajiye carbin da ke hannuna na gabatar da ita.
Zama na yi ina ta zuba addu'o'i'n da ba zan iya kawo su duka a kaina ba. Saboda tunanin Maman Taufiƙ da inda za ta shiga a faɗin duniya idan ta bar gidan mijinta, kuma ta ƙi komawa gidansu ko wurin wasu 'yan'uwanta.
Inna Kulu ta kawo mini tuwo kuma ta matsa sai da na tsakura. Ina zaune a wurin su Aunty Asabe suka zo yi mini sallama za su tafi gidajensu. Sai da safe muka yi suka tafi suna mini addu'ar samun sauyi a cikin rayuwata.
****
Daren ranar daga ni har Umma kwana rabi da rabi muka yi, saboda duk na motsa sai na ji ta ce, "Lafiya?" Na ce da ita babu komai sannan na gyara kwanciyata.
Da safe bayan mun karya ni da yaran, Umma ta ce su yi zaman su kada su je makaranta. Na ce da ita ta bari su je in sha Allah babu abin da zai faru.
Tare da su muka fito Najib ya ajiye su bakin makarantar. Na fita da kaina muka gaisa da maigadinsu na ce da shi,
"Don Allah Baba kada a bari wani ya sake zuwa ya ɗauke su, idan ba wannan da ya saba zuwa ɗaukar su ba kullum."
"Kada ki damu Hajiya. In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba. Wannan karon ma don ban san yadda tsarin naku yake ba."
Ɗari biyun da Umma ta ba ni na fito da ita a jaka na miƙa masa. Ya karɓa yana ta godiya muka juya. Shiru ya ratsa tsakani bayan barin mu wurin Najib ya ce da ni,
"Don Allah ki yi haƙuri Maman Haidar, ban ji daɗin abin da ya faru ba."
"Kada ka damu! Ai ba laifinka ba ne. Kawai dai ka yi ƙoƙarin zuwa da an tashi ka ɗauke su."
Daga haka na ja bakina na tsuke, bayan na ce da shi ya kai ni Asibitin Uduth. Kaina tsaye na doshi ɓangaren masu wuta, saboda babu inda ban sani ba a cikin asibitin. Domin awo da wasu ciwukanmu ni da yara duka a nan muke zuwa.
Tun da na tunkari doguwar barandar ƙirjina yake bugawa, na ciro wayata na kira layin da Sajida ta kira ni da shi jiya. Wanda ta sanar da ni wutar ba ta ƙone ta ba, kira ɗaya biyu aka ɗauka.
"Hello!"
"Don Allah Sajida nake nema, wadda ta kira ni da wannan layin."
"Sajida!?"
"E, wadda ta ƙone da