Showing 1 words to 3000 words out of 121208 words

Chapter 1 - ABOKIN AIKINA HAUSA NOVEL

24 Nov 2024

6381

 *ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*LAMBA TA ƊAYA.*

*_True life story_*

Tun da na shiga cikin motar shi, zuciyata ta fara dakan luguden uku-uku. Saboda tsananin tashin hankalin da ya kawo mini ziyara, domin ni kaina na san illar da hakan zai haifar mini. Na yi hanzarin dafe goshina tare da faɗin wash! Saboda mugun saran da na ji a tsakiyar kaina. "Subhanallah! Me ya faru?" Ita ce maganar da ta fito a bakin MD cikin kulawa, tare da damuwar da ta kasa ɓoyuwa a kan fuskar shi. Kafin daga baya ya ci gaba da ce wa "Ki daina saka kanki a damuwar da ke haifar miki da ciwon kan nan naki. Saboda lafiyarki tana da matuƙar amfani a wurina..." ƙarshen maganar shi ba ƙaramin duka ta yi wa zuciyata ba, babu shiri na yi hanzarin kai kallona a kan fuskar shi.. "I, kina da matsayin da ciwonki ya dace mu shiga damuwa sosai a cikin ma'aikatarmu" ba shiri na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, fargabar da ta tokare mini maƙoshi tana ƙoƙarin toshe numfashina ta faɗa. Sannan ya ɗora sharhi a kan maganar shi da ce wa "Dalilin hakan ya sa muke takaicin sabuwar lalurar nan da ta same ki. Wadda take ƙoƙarin kawo mana tawaya a cikin cigaban da muke samu ta ɓangaren jajircewarki. Ki daure ki sha magungunanki kamar yadda likitan ya umurta. Sannan ki samu relief na tsawon kwana uku kafin ki koma wa aikinki. Ubangiji ya ƙara lafiya" "Amin" na amsa cikin maƙoshi saboda har lokacin ban daina jin saran gudumar da ake yi mini a tsakiyar kai ba. A sakamakon somewar wuccin-gadin da na yi ina tsaka da aiki a cikin Offishina.

Har ƙofar gidan ya ajiye ni ba tare da ya damu da matsalar da hakan za ta haifar mana ba daga ni har shi. Na fito motar jiki babu kuzari ina ƙoƙarin yi masa godiya ya miƙo mini ledar magungunan, da ya tsayu kai da fata jikin shi da aljihun shi har na farfaɗo na samu kaina. Na zura hannu da nufin karɓar ledar babu zato muka zabura dukanmu, saboda dukan da muka ji an yi wa gilashin motar shi na gaba. Wanda a lokaci ɗaya ya tarwatse har yana barazanar bugun fuskokinmu. Da sauri na yi baya cike ƙoƙarin janyewa daga jikin motar, shi ma MD ya fito daga motar cikin zafin nama. Ƙirjina ya shiga bugawa a dalilin ido biyun da na yi da curarriyar fuskar Mukhtar. Wanda ke tsaye riƙe da ƙaton ice yana huci tare da aika mini mugun kallon da fitsari ya so suɓuce mini. Kafin na yi wani yunƙuri ya fara ɗaga gandamin icen ya ci gaba da dukan gilasan motar MD babu-ji-babu- gani. Ɗaga icen yake yi yana sauke shi a kan motar iya ƙarfin shi gabaɗaya ya canza mata kamanni. Cikin tsananin tashin hankali na kai kallona ga MD da ke tsaye rungume da hannuwansa a ƙirji, yana ƙare wa Mukhtar kallon da na rasa gane ainahin abin da yake nufi da hakan. Cikin azama na nufi Mukhtar jiri yana kwasa ta da nufin hana shi aika-aikar da yake yi, sai dai kafin na isa wurin shi na yi azamar duƙewa ƙasa saboda hango icen da na yi dishi-dishi a sama yana ƙoƙarin faɗowa kaina. Shirun da na ji ya sa na ɗago kaina na gani da zummar ko dai idanuwana ne bai hango daidai ba. A kiɗime na miƙe jikina ya hau rawa saboda hango Mukhtar a yashe ɗan nesa da ni, icen kuma a hannun MD yana huci cikin matsanancin ɓacin ran da ya bayyana kan shi a kan fuskar shi. Hannu ya shiga nuna Mukhtar da shi cikin wata kausasshiyar murya ya ce "Zan haƙura da rasa komai amma ban da Zaituna. Ka yi duk abin da kake so zan kawar da kai amma kada ka yi gangancin taɓa martabarta balle lafiyarta. Wawa kawai soko wanda bai san darajar aure ba".

Kafin na gama tantance abin da ƙwaƙwalwata take son sanar da ni, tafin Mukhtar ya fara sauka a cikin dodon kunnuwana, sosai ya so ƙara zautar da tunanina ya hautsine mini kuzarin jiki da guntun tunanin da ke cikin kaina. Musamman maganganun da ya fara faɗa waɗanda suka zamo tamkar ɗigar ruwan dalma a jikina. "Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Haka ma rana dubu ta ɓarawo ɗaya tak! Ta mai kaya ce. A yau ka fasa ruɓaɓɓen ƙwan da kuka daɗe kuna ɓoyewa a tsakaninku. Da kanka ka yaye labulen sirrinku, ka fallasa asirinku saboda girman haƙƙin aure da ke bibiyar rayuwarku. To ka sani ka yi kuskure kuma ka yi gangancin shiga gonar da ba taka ba. Kuma ko za ka mutu a kanta wallahi ba zan taɓa sakinta ba balle ka aure ta. Ke kuma sai na nuna miki ba irina ake cin amana a zauna lafiya ba..".

Ƙare maganar shi ta yi daidai da fisgar da ya yi wa hannuna tamkar zai raba shi da gangar jikina, ina tirjiya tare da kai wa hannun shi duka da ɗan ƙarfin da ya rage mini. Amma hakan bai hana shi jefa ni cikin gidan ya wullar tsakiyar ɗakina ba. Ina ji ina gani ya saka mini key ya rufe ni ruf a cikin ɗakin ba tare da ya jira jin komai daga bakina ba. Na fara dukan ƙofar ɗakin ina kuka cikin disasshiyar muryata tare da ƙwala masa kira cikin ƙarfi ina faɗin; ya tsaya ya fahimci yadda abin yake, saɓanin abin da ya zata kuma ya yi tsammani tsakanina da MD. Amma hakan bai sa ya buɗe ni ba balle ya yi lokacin jin ta bakina kamar yadda na sha sanar da shi koyaushe.


ABOKIN AIKINA. Zai zo da zafin shi a cikin wannan shekarar. Free ne ga kowa saboda darussan da ke cikin littafin abin tausayi abin takaici abin koyi ga wasu nagartattun halaye. Abin gudu abin ƙyama daga wasu gurɓatattun halayen da za su zo a cikin littafin ABOKIN AIKINA.

*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA GA DAUGHTER ANUP😘*


*LAMBA TA BIYU.*


Ban san ya rigumar ta ƙare ba, domin shi kan shi tun da ya fita bai dawo gidan ba sai da dare ya ɗauke sawu kamar yadda ya ba. Na ci kuka har idanuwana suka kumbure babu mai rarrashina. Mutum ɗaya ce nake da tabbacin za ta kwantar mini da hankali, sai dai ba zan so ɓata mata farinciki ba kamar yadda nawa ya gurɓace. Ƙarin takaicin kuma yaran duka ba su dawo gidan ba, wanda alamu ya nuna a can za su kwana wurin Ummata. Amma mamakina ba ta kira ta sanar da ni ba kamar yadda ta saba idan sun yi marmarin kwana gidan.

Ajiyar zuciya na sauke a lokacin da na juya kwanciyata, wadda nake jin suka cikin haƙarƙarina tamkar a kan ƙayoyi nake kwance. Sanin kuka ba zai yi mini ranar komai ba domin ba yau na saba yin irin shi ba, kuma har yanzu bai warkar mini da mikin da ke cikin zuciyata ba balle ya kawo mini waraka, daga ƙangin rayuwar da nake ciki. Wanda a kullum na tuna ina jin kaina tamkar wata marainiyar da ta rasa komai da kowa nata a cikin duniya. Saran da kaina ya yi ya sa na yi hanzarin dafe goshina ina faɗin "Wash! Allah!" Saboda wani zafin da nake ji yana bi cikin jijiyoyin idona, wanda ya haifar mini da zugin da ya hana ni buɗe idanuwan har sai da ciwon ya lafa mini. Shiru na ɗan lokaci ina sauraren azabtuwar da nake fuskanta a cikin kaina har ma da zuciyata da ta karɓi nata kason, tana yi mini wani irin ciwo tamkar za ta tarwatse a cikin ƙirjina.

Daren ranar haka na yi bacci cikin rashin natsuwar zuciya da ciwon da ya ƙi bari na na huta. Da ƙyar na samu ƙarfin halin yin sallah sannan na lallaɓa na koma kan gado na ƙudundune cikin bargo. Daga tunanin da zuciyata ta lula ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba. A cikin baccin na ji muryar Ummata tana faɗa a sama tamkar a mafarki, sai dai buɗe idanuwan da na yi na gan ta tsaye saman kaina fuskarta a haɗe ya tabbatar mini gaske ne ba mafarki ba. Na yi ƙoƙarin tashi zaune cikin disasshiyar muryar da ta gaji da kuka na fara gaishe ta, ba tare da ta amsa ba ta fara feso mini abin da ke cikin bakinta, "Me kike so ki mayar da kanki Zaituna? Har yaushe kika yi girman da za ki fara bin wasu mazan waje bayan da auren wani a kanki. A zatona ko babu igiyar aure kanki za ki tsare mutuncinki ko don ki hana zagin da mutane za su yi mini, a kan riƙon sakainar kashin da ake ganin ni ce na yi silar mayar da ke abin da kika zama yanzu. Shin ba kya ganin rashin zaman lafiyar aurenki zai taɓa mini ɗan guntun mutuncin da ya yi mini saura a idon mutane? Kina buƙatar ki kashe aurenki ki zo mu jeru gida ɗaya ni da ke mu dinga haɗa kafaɗa babu mai aure a cikinmu?. Sau nawa zan ce ki yi haƙuri da halin Mukhtar ko don yaranki? To bari ki ji; Idan ma kin kashe auren gidan wani za ki sake zuwa, kuma bai zama lalle ki samu marar mata ko wanda bai da 'ya'ya ba. Kin ga idan kin ƙi sharar masallaci sai ki je ki yi ta kasuwa, domin kuwa dole ne ki yi wa 'ya'yan wasu bauta bayan kin watsar da naki a wulaƙance..." Kukan da ta fara yi ya ƙara damalmala mini komaina. Ban tsaya rarrashinta ba ni ma na fashe da nawa kukan cikin ƙunar zuciya saboda na kasa furta kalma ɗaya da zan kare kaina, wanda na sani ita kanta shaida ce a kan tsare mutuncin aurena da nake yi duk da bai zama ingantaccen aure kamar sauran aurarraki ba. Daga ni har ita kuka muke yi mun kasa rarrashin juna balle mu samu wanda zai rarrashe mu.

Ita ce ta fara jarumtar tsayar da ruwan hawayen da take yi ta shiga fyace majinar kukan da ta sha, ta janyo ƙafafuwanta ta zauna a bakin gado cikin sigar rarrashi ta ce "Idan ban da tausayin yaran nan da nake yi, me zai sa mu fuskanci baƙincikin rayuwa irin wannan? Ki yi haƙuri Zaituna na san ina sara miki ko babu gaɓa. Amma ki sani ni na san abin da ya sa ba na fatan ki kashe aurenki. Kuma ina roƙon Allah ya hana ki zama bazawara, domin ni kaɗai na san duhun baƙincikin da ke damfare cikin hakan. Ubangiji ya yi miki albarka, yadda kike yi mini biyayya ke ma Allah ya sa 'ya'yanki su yi miki fiye da hakan". Tana ƙare faɗar maganar ta miƙe tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin, na bi bayanta da kallo ina goge hawayen da suka kasa tsayawa cikin kwarmin idona. Kiciɓis suka yi da Mukhtar wanda yake ƙoƙarin shigowa ɗakin fuskarsa a haɗe tamkar bai taɓa dariya ba. Ganin ta ya sa shi sakin fuskar shi kaɗan ya rusuna har ƙasa yana sosa ƙeya cike da girmama ya ce "Umma daman magana nake so mu yi dangane da aikin nan da take zuwa. Ni dai gaskiya ban lamunta da shi ba, idan akwai yiyuwar ta daina zuwa duka a duba mini. Saboda zuwa aikin ne yanzu duk wata matsala take kunno kai tsakanina da ita, amma idan aka jingine shi kamar an yi maganin rabin matsalolin da ke faruwa daga wannan sai wannan". Shiru ya ratsa tsakani idona a kanta ina jiran amsar da za ta ba shi kafin na yi magana, domin na fuskanci nazarin maganganun shi da amsar da za ta bayar take yi. "A gaskiya Mukhtar sai dai ka yi haƙuri da zancen aikin nan, domin ka sani ban da wani iko a kan hana mata zuwa aikin nan. Amma tun da ba ka so kana da ikon da ya fi na kowa a kanta. Ka je ka samu Alhaji Ali domin ka sanar da shi a kai ƙarshen maganar, saboda shigar da kaina cikin maganar yanzu zai sake janyo wata sabuwar rigima tsakanina da shi. Wanda ba na fatar hakan an yi na baya ina fatar kuma ba za a yi maimaici ba". ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi ina aika masa harara da jajayen idanuwana tamkar su fito su manne jikin shi. Saboda tsabar takaicin da yake ba ni ji nake kamar na taso na rufe shi da duka. "Ba sai na je ba, a bar zancen kawai. Umma amma a sanar da ita babu ita babu wannan mayaudarin mutumin. Domin wallahi yanzu haka mutane har sun fara zunɗena a kan na zama mijin ho-ti-ho, saboda ganin yadda na kasa raba ta da mutumin da yake ƙoƙarin keta mata haddin aure..." "Wane aure kake zance? Kai har kana da bakin faɗar kana aurena? Na rantse da Allah darajar Umma kake ci, da tuni na watsa maka fetur na ƙone ka..."

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!" Ita ce kalmar da Ummata ta furta cikin kiɗimewa da tashin hankalin da ya bayyana kan shi cikin fuskarta. "Gara da ta yi gabanki kika gani Umma, haka take yi mini ko a gaban su Haidar. Ba ta jin kunyar faɗa mini magana domin ta wulaƙanta ni a gabansu. Ban san wace irin tsana ce take yi mini ba da ba ta iya ɓoyewa ko a gaban waye..." "Ban ji daɗin maganar nan ba Zaituna, ki san me za ki faɗa wa mijinki saboda gudun shiga matsala da fushin Ubangiji". Nasiha ta shiga yi mini ina sharar hawaye, shi ma tana yi masa faɗan so-kanka a fakaice. Saboda har kullum tana jin nauyin shi da kunyar surukuntakar da ke tsakaninta da shi. Wadda ya dace a ce tuni ta watsar da ita ta huta, ko don kalolin cin amanar da yake yi mini. A gabana suka yi sallama ta fice ya dawo kaina yana ƙare mini kallon wulaƙanci sama da ƙasa, sannan ya yi ƙwafa ya fice tare da buga mini ƙofar ɗakin da ƙarfi kamar zai ɓalla ta.




Shin ya wannan rikicin yake ne? Kun hasko wani abu cikin labarin ko sai mun ƙara nutso a cikin tafiyar?.




D AUTA CE🚶


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*LAMBA TA UKU.*

Ajiyar zuciya na sauke, sannan na yunƙura cikin rashin kuzari na sauko daga gadon. Ina layi na fice ɗakin saboda yunwar da ke ƙwaƙular cikina, kitchen na nufa kai-tsaye don jirin da nake ji ya tabbatar mini da ban samu waraka daga ciwon da ke damuna kwana biyu ba, wanda yake hana ni sukuni a duk lokacin da babu komai a cikina. Turus na yi na ja na tsaya gaban kayan shayinmu. Domin a take na gano Mukhtar ya yi abin da ya saba, saboda kofin da ya yi amfani da shi ma a nan ya bar shi bai ɗauke ba, kamar yadda ya bar gwangwanin madarar a buɗe bai rufe ba, bayan milon da ya barbazar a ƙasan tiles har ya yi danƙo, domin ba na tamtama a kan lokacin da zai zuba ya sha shayin ne ya zubar da shi, saboda halin shi da sani na sakankance komai ba ya yin sa a nutse sai ya yi hargitsi. Sau tari idan zai ci tuwo kafin ya tashi daga cin tuwon nan sai ya zubar da miyar. Idan fura ce kuma da wuya ya gama sha a kofi bai zubar da rabi ba.

Numfashi na ja tare da sauke ajiyar zuciya cikin ƙunar rai, a gurguje na ɗan gyara wurin sannan na ɗora ruwan zafi na haɗa tea. Saboda a yadda nake ji ba zan iya cin komai ba idan ba shi ba. Fitowa ta daga kitchen kenan ina ƙoƙarin komawa ɗaki, na ji muryar maƙociyata tana sallama, hakan ya tabbatar mini da Mukhtar ba ya cikin unguwar, domin a bin da na sani ne ba ta shigowa gidan sai ta tabbatar da ba ya nan, saboda tana cikin mutanen da yake zargin suna kawo mini tsegumin da yake haɗa mu rikici da shi a wasu lokutan. Na amsa mata sallama da disasshiyar muryata irin ta marasa lafiya. Tare muka nemi wurin zama a kan kujerun falon muka zauna, ina kurɓar shayin muka fara gaisawa babu yabo babu fallasa. Yanayin kallon da naga tana yi mini ya tabbatar min da akwai dalilin da ya kawo ta wurina, wanda ba na raba ɗaya biyu a kan rikicin da ya auku ne jiya. Wanda nake da tabbacin zuwa lokacin ya karaɗe ko'ina cikin unguwar da kewaye. Nan take na ji hawaye ya cika idanuwana, na ajiye ɗan sauran shayin da rage kan tebur, saboda zuciyata ta yi duhun da ba zan iya shanye shi ba.
"Ban samu wayarki ba, shi ya sa na kasa haƙuri sai da na yi wanann tattakin. Saboda ba na so Mukhtar ya gan ni ya yi mini abin da raina zai ɓaci a banza..." "Me ke tafe da ke?" Ita ce tambayar da na jefo mata tun kafin ta dire zancenta. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Ban ji daɗin abin da ya faru ba, kuma ban ji daɗin irin zantukan da ake yi a kanki cikin unguwar nan ba" Ta ƙare maganar fuskarta ɗauke da damuwa, shiru na yi na ɗan lokaci sannan cikin muryar kuka na ce "Ban ga laifin duk wanda ya zage ni ba, domin abin zagin ya ji ko kuma ya gani shi ya sa ya zage ni. Idan akwai mai alhakin laifin hakan to ni ce nan. Domin da ban yi biyayyar da nake yi a yanzu ba, da duk hakan bai faru ba. Na sani babu biyayya wurin saɓa wa mahalicci, amma na zaɓi tauye kaina na ci amanar kaina saboda farincikin mahaifiyata. Na sani kuma Allah ma ya sani babu wani abu na assha tsakanina da MD illa gaisuwar mutuncin da muke yi. Amma ban san miye a cikin zuciyar shi dangane da ni ba, domin da ban ji abin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login