Showing 57001 words to 60000 words out of 89717 words
gyada mata kai yace
"amma fa bance ki ce ma su Hajiya komai
ba, duk da nasan baxa ma ki fada ba," ta
gyada masa kai tace "nasani," snn ta xauna
gaban Aneesah tana kallonta, Aneesah ta
dago kai tana kallonta ita ma, pretty tayi
murmushi tace "Aneesah," ita ma
murmushin tayi bata ce mata komai ba.
Pretty tana kallon Mujaheed tace "yaya tare
kuke a nn?" Mujaheed yace "ko xaki dinga
taya mu kwana ne? Dama gata kullum cikin
tsoro take" tace "ku biyu fa kadae yaya" ya
galla mata harara yace "to me ya faru?" tayi
murmushi ta canxa xancen tace "aa ni
baxan taya ku ba," yace "kira mum kice
mata xaki kwana a nn," ya fadi hkn ne don
ya san bbu ruwan Hajiyar ko kadan baxata
damu ba da yake ita gantalalliya ce, pretty
tayi murmushi ta girgixa kai tace "fushi take
dani ae baxata ma daga kiran ba na sani,"
Mujaheed yace "to shknn, gobe kya xo ki
taya mu kwana amma a wancan gidan ba
wnn ba," hira suka dinga yi har kusan karfe
goma, ita dae Aneesah sae dae tayi
murmushi bata ce masu komai, da xolaya
pretty tace "wllh wnn amaryar yayan nawa
ta cika jin kunya," Mujaheed ya juya yana
kallonta yace "waye yayan naki? Hka yace
maki amaryarsa ce" pretty ta tsaya kallonsa
bata ce komai ba ya dan yi tsaki ya mike
tsaye yace "ynxu xaki koma gida ne ko ko,
don xamu tafi gida ne," pretty bata ce komai
ba ta tashi tsaye snn tace "ehh ynxu xan
wuce," Mujaheed ya juya yana kallon
Aneesah yace "kanwata tashi mu wuce
nasan kin fara jin bacci ynxu," ita dae bata
ce masa komai ba ta mike ya kama
hannunta, pretty na gabansu suka fita gate.
Sae da ya raka pretty har gida snn ya fito
suka yi sallama ita ma ta leka mota tayi ma
Aneesah sallama snn ta shiga da motarta
ciki bayan mai gadi ya bude mata gate, shi
ko yyi reverse suka kama hanyar gida, suna
isa gida yace "dama gidansu Mudatheer
xamu daxu, kinga ynxu dare yyi sae gobe,"
cikin murna Aneesah tace "da gske? Amma
kuma yace min shi dan kano ne ae,"
Mujaheed bae tanka ta ba ya haura sama ta
bi bayansa da sauri, ya juya yana kallonta
bayan sun shiga daki yace "kije ki kwanta
kanwata ni bacci nake ji," ta bata fuska tace
"ni kadae xan kwana?" ya bude baki yana
kallonta yace "to da ke dawa xaki kwana?"
ta marairaice masa tace "ni wllh tsoro nake
ji ynxu," yyi shiru yana kallonta snn yace
"ajinki nawa a islamiyya?" ta wara ido tace
"ni nayi sauka tun yaushe," ya gyada kai ya
matso kusa da ita ya kamo hannunta yace
"iyye, to naji xaki kwana nn amma kwana
xakiyi kina sllh, ni kuma nayi baccina, don
baxan iya bacci kina bacci ba, amma idan
kina ta sllh tsaf xanyi baccina,"
.
Mujaheed ya tura kofar dakin a hankali ya
shigo yana kalln Aneesah yace "ke fa nake
jira kanwata baki shirya ba har ynxu," bata
ce masa kmai ba kuma bata kallesa ba ya
karaso gefen gadon ya xauna yana kallonta
yace "am tokn Aneesah," ta juya masa baya
tace "bbu inda xa ni," ya xaga yana kallonta
yace "haba kanwata hw many tyms xan baki
hkuri, nace kiyi hkuri kin ki" ta fashe da
kuka tace "ni nace maka ka kyaleni bbu inda
xanje," yyi shiru yana kallnta snn yce "kada
Allah yasa kije din" ya mike ya bar dakin ta
bisa da kallo ta fada kan gadon ta fashe da
wani kukan, throughout ranar bata fito ba
shima bae shiga dakin ba, iyaka lkcn sllh na
yi tayi alwala tayi sllh ta koma ta kwanta, har
sae da yamma snn ya budo kofar dakin ya
shigo ya ajiye mata ledan abinci ya fice, bata
ko juya ba bare ta kalli ledan da ya ajiye
mata, tana xaune kan darduma ta idar da
sllhn Maghrib ya shigo dakin ya xauna kan
gado yana kallnta, ta mike ta dauke
darduman ta linke snn ta xaga xatayi
kwanciyrta kan gado ya riko hannunta,
"haba Aneesah wae me yasa kke min hka
ne, meyasa kka cika taurin kai hka ne," ta
fixge hannunta tana shirin fashewa da
kuka, ya xaunar da ita gefensa yace "don
Allah kiyi hkuri ki ci abinci, nace mki daga
yau...." aka turo kofan dakin pretty ta shigo
suka daga kai suna kallnta, Mujaheed yyi
murmushi yace "sae ynxu bby, tuntuni nake
kiranki baki xo ba har sae da ta huce,"
pretty ta dan yi murmushi tace "Hajiya ce
bata barni na fito ba," ta karaso ciki ta
xauna gefen Aneesah, Aneesah tayi
murmushi tace "ya gidan," pretty tace "lfya
lau," Mujaheed yace "to kuci abincin tare
xan je gun abokina dake nn kusa," pretty
kadae ta amsa masa, Aneesah ta bi sa da
kallo, ya kashe mata ido ta dan yi tsaki ta
hararesa ta kauda kai, yyi dariya ya fice,
pretty ta xamo kasa a hankali hawaye ya
cika idonta, amma in har hka ne Mujaheed
bae ma yayanta adalci ba, ita kuma Aneesah
bata yi masa halacci ba, Aneesah ma ta
sauko kasa ta jawo abincin tace "in xuba
maki," pretty ta girgixa mata kai kawae, ita
ko ta xuba nata ta fara ci. Ranan tare
Aneesah suka kwanta da pretty don
Mujaheed yace dole sae ta kwana sbda
Aneesah, can cikin dare kmr jiya tayi
mafarkin su bala sun sake biyota, bata yi ihu
kmr jiya ba sbda pretty, ta toshe bakinta da
sauri tana kuka, ta mike ta bude kofar dakin
tayi hanyar dakin Mujaheed, ta tura kofar
dakin yana xaune kan gadonsa coffee a
gabansa kan table, ya dago da sauri yana
kallonta ta karaso cikin dakin yace "ya akayi
kanwata bakiyi bacci ba," ta durkushe
gabansa hawaye na ci gaba da xuba a
idonta tana kallonsa tace "yayana ni tsoro
suke bani kullum," ya sauka kasa ya xauna
dan nisa da ita yace "ya isa kanwata ke ce
bakya addu'a," ta girgixa masa kai tace
"wllh ina yi," ya jawo bargon saman gadon
ya shimfida mata nn kasa ya dauko filo ya
ajiye mata yace "to yi kwanciyarki a nn
kanwata" bata yi masa musu ba ta kwanta
ya dauko wani bargon ya lullubata da shi,
tace "yayana meyasa baka yi bacci ba," yace
"tunaninki ne ya hanani bacci kanwata," ta
wara ido tace "ni?" ya gyada mata kai yace
"ina son ki da yawa kanwata," bata ce
komai ba ta gyara kwanciyarta ya matso
kusa da ita yace "baxa ki ce min kina sona
ba," tayi murmushi bata ce komai ba yace "i
luv yhu Aneesah," xata rufe fuskarta da
bargon ya rike yace "kema ki ce min hka
plss" ta girgixa kai tace "baxan iya ba," ya
sake mata bargon a hankali bae ce komai
ba ya koma inda yake ya xauna, can bayan
ya manta yaji tace "i luv yhu 2 yayana," don
farin ciki ma rasa me xae ce mata yyi.
Washegari da pretty ta fahimce dakinsa
Aneesah ta kwana hkn yasa ta kuka ssae
don tausayin yayanta da irin halin da ya
shiga sbda son Aneesah, taji wani irin
haushin Aneesar da ma Mujaheed, ita kam
bata goyi bayan yayanta ya auri Aneesah ba
kuma, ko sllma bata masu ba ta bar gidan
Yau Monday Aneesah ta tashi da fargaban
xuwa kotu, knn fa yau baffanta da Hajiyarsu
ya Hydar da kowa ma xae ganta, kila ma har
da Amminta, Mujaheed ya shigo dakin yace
"kanwata xaki bata min lkci mana," tace
"yayana jiya da kaje gun ya Hydar me yace
maka?" yyi mata mugun harara yace "ban
sani ba, idan kinga dama kiyi maxa ki
shirya" yana gama fadin hka ya bar mata
dakin, ta bi sa da kallo, idan da sabo ta fara
sabawa da saurin fushin Mujaheed idan ta
kawo masa maganar wani namijin, ko da ya
dawo dakin ta gama shirinta gudun
masifarsa, tace "yayana to ni tsoro nake ji,
bn san me baffa xae min idan ya gan ni ba
da hajiyarsu ya Hydar," yace "duk bbu
abinda suka isa su maki, shi baffan daga
can ma xa a kama sa na sani," Aneesah tace
"to Ammina fa," yace "kila ki ganta yau, xo
muje muyi break" bata yi masa musu ba ya
ja ta suka sauko downstairs suka karya,
karfe tara saura suka bar gida, gabanta ya
dinga faduwa tace "yayana ni fa tsoro nake
ji," yace "kiyi ta addu'a kanwata, snn banda
karya a kotu duk abinda aka tambayeki iya
gskyarki xaki fadi" ta gyada masa kai kmr xa
tayi kuka, ya dinga mata hira don ta
kwantar da hankalinta har suka isa kotun.
.
Mujaheed ya juya yana kallon Aneesah
bayan ya gama parkin yace "kar ki damu
kanwata ba ynxu xaki shigo ba, sae an
nemeki," ta xaro ido tace "wa xae neme ni?"
Mujaheed yace "idan lkcn yyi xaki gani," ya
kunna mata A.c ya sa mata karatun qur'ani,
ya fita daga motar ya kulle, ta bi sa da kallo
har ya shiga kotun, ohh ita fateemah ta ga
lyf, tana ta xaune cikin motar tana bin duk
wanda ta gani da kallo, wata katuwar mota
tayi parkin Hajiya tafito cikin shiga ta
alfarma da kawayenta har hudu kmr ba dan
ta ke kulle a kurkuku ba, motar dake bayan
tasu su meenah da pretty ne a ciki ta bi su
da kallo har suka shiga kotun gaba daya,
bayan shigarsu da kmr minti goma sae ga
motar baffanta da abokansa suka shiga
kotun suna ta surutu, can sae ga Hajiya
zuwaira da nata kawayen, hka Aneesah ta
dinga bin mutane dake ta shiga kotun da
kallo tun daga kan 'yan uwa xuwa kan su
karere, ta san ixuwa ynxu kam kotu ta cika
tam, Abdul ne kadae bata gani ba, can sae
ga motar gidan yari ta shigo haraban kotun
tana kallo aka fito da Hydar, ya rame amma
ba ssae ba, sae dai yyi haske bbu abinda ya
ragu a kyansa, ta bi sa da kallon tausayi
hawaye ya cika idonta har aka shiga da shi
kotun 'yan sanda kusan biyar na biye da shi
a baya, ta fashe da wani matsanancin kukan
da bata san dalilinsa ba. Su oga Baffa sae
surutu ake da abokanansa cikin kotun yana
buga kirji yana fadin irin hukuncin da xa a
yanke ma Hydar idan bae fito masa da
'yarsa ba don ga uwarta can hawan jini ya
kamata ya sa an fita da ita waje tana karban
treatment, Mujaheed da hankalinsa duk
yana gun baffa duk da ba kallonsa yake ba,
ya dinga murmushi yana buga kafa, Hajiya
kam ko a jikinta don tasan tunda Mujaheed
yana nn yau dole sae an yi bail dinn danta,
don Mujaheed ba wasa ba, ba dan ba dan
ba sae tace ma yafi Hydar iya aikinsa don
Hydar slowly yake yin abunsa shi ko sharp
sharp xae yi ya gama, sae taunar cingam
take tana watsa ma Hajiya xuwaira Harara,
ita ma Hajiya xuwairar sae sakar masu
magana take, har alkali ya shigo, kotu tayi
tsit, case daya aka fara yi kafin nasu, kmr
abun arxiki aka fara case dinsu sae Hajiya
taga kmr Mujaheed bae yi serious ba hkn yyi
mugun bata haushi barin ynda taga yyi
shiru yana kallon lawyern baffa dake ta
haukansa, shi ko Mujaheed sae murmushi
yake, don a ganin sa hauka kawae suke
tunda ga Aneesah da suke cewa a fito da
can a mota, Mujaheed ya juya yana kallon
judge din yace "ya mai girma mai shari'a
xan so ka bani ixinin nayi masu tambaya
daya, Alkalin yace "an baka," ya juya yana
kallon lawyern shehu yace "mahafiyar wnn
yarinya nake son gani ynxu,don ita kadae ce
shaidar mu a nn sae wnn yarinya da ake
nema, kafin nace komai" Mujaheed ya dinga
murmushi ganin yanda lawyern ya dinga
xakulo karyar da tayi mugun shigar jama'ar
dake xaune a kotun, sae da Mujaheed ya
bari alkali ya kusan yanke hukunci ganin shi
Mujaheed din bae da kwakkwarar magana
ko shaidar da xae kare Hydar snn yace
"yana rokan alfarmar Alkali ya bari ya fito da
shaida daya da xae nuna ba Wanda ake
xargi da sace yarinyar ba ya sace ta," Alkali
yace "an basa," ya juya yana kallon barrister
umar ya dan matsa kusa da shi yyi masa
magana, barristern ya mike ya fita yan
sanda biyu suka bi sa a baya, Hajiya da
haushin Mujaheed ya cikata sae huci take
ganin yanda yake abu kmr baya son
taimakon dan ta, Hydar ko kansa na kasa
bae bari ya hada ido da kowa ba, shehu sae
murna yake yana hamdala a xuciyarsa
shknn yasan life imprisonment xa a ba
Hydar, xae yi yanda yaga dama da dukiyar
kaninsa ba tare da wani ya xame masa
obstacle na hanasa yin hkn ba, ba a dau lkci
ba Barrister Umar ya shigo Aneesah biye da
shi a baya, da ka ganta kasan a tsorace take,
duk aka bita da kallo, shehu ya mike tsaye
da sauri ya xaro tulelen idonsa yana
kikkiftawa da sauri, hka ma matarsa, Hajiya
kuwa kasa rufe baki tayi don mugun
mamaki ta shiga jijjiga kai tana kallon
Aneesah, Hydar ya bi Aneesah da kallo, har
ta iso gaban kotun alkali ya bada ixinin ta
shiga gun da xatayi take din oath, kanta a
kasa tayi duk yanda aka ce mata, snn
Mujaheed yace "ki fada ma kotu ko ke
wacece," tace "ni sunana Aneesah Mukhtar,"
Mujaheed ya juya yana kallon lawyern shehu
yace "kasan wacece wnn," ya ce "sae ka
fada," Mujaheed yace Ya mai girma mai
sharia wnn ita ce yarinyar da akayi ma
barrister Hydar sharrin sace wa, ynxu ita da
bakinta xata yi maku bayanin wanda ya
dauketa da kuma dalilin da yasa ya dauketa,
snn ina rokan kotu da ta bi ma Barrister
Aliyu hakkinsa a kan sharrin da aka yi masa
da irin abubuwan da yyi pass through kan
hkn.."
@ #dan_gogori_
ANEESAH 🌹🌹🌹
NA KHALEESAT HAYDAR
28➡30
~28~
Aneesah ta fashe da kuka bayan ta gama
bama kotu lbrin yanda akayi baffa ya
dauketa ya kai ta kauye har ixuwa yau da
take bada lbrin, kmr yanda Mujaheed ya
umarceta da tayi, gaba daya jama'ar dake
kotun sae da suka girgixa da jin lbrin da
Aneesah ta bayar, aka juya gaba daya ana
kallon baffa dake ta xufa daga sama xuwa
kasa, har sae da Alkali ya bukaci decorum a
kotu snn ko ina yyi tsit, Alkali ya maida
gilashin idonsa da ya cire duk don jin lbrin
Aneesah snn ya fara rubuce rubucensa a
takarda, Hajiya sae kallon Aneesah take tana
huci, Hajiya Zuwaira ko kasa xaune tayi sae
mutsu mutsu take kan kujera tana kikkifta
ido, Alkali na shirin yanke hukunci Mujaheed
ya dakatar da shi da sauri ta hanyar cewa
"ka gafarceni ya mai girma mai sharia ban
katse maka hanxari ba amma xan so ace
kafin a yanke masa hukunci ya fito da
Mahaifiyar wnn yarinya, don ta fi wata biyar
bata garin nn, kuma shaidu sunce shi ya
dauketa, snn kuma yyi handover din dukiyar
Mahaifinsu dake hannunsa gaba daya" Alkali
ya gyada masa kai ya danyi rubuce
rubucensa snn yace anyi adjourn din case
har xuwa nn da sati biyu, an bada bailn
Hydar snn kuma shehu xae basa million uku
4 d inconvenience he caused him, snn xa a
tsare Shehu gidan yari har xuwa lkcn da
Mahaifiyarta xata bayyana a yanke masa
hukunci kuma ya kasance ya damka masu
dukiyarsu hannu da hannu a bainar
jama'ah, yana kai wa nn ya sallami jama'ah
ya mike ya fita daga kotun, Aneesah ta bi
Mujaheed da kallo tana hawaye, ya juya ya
kashe mata ido, tayi murmushi tana goge
hawayen fuskarta, ba karamin kyau gown
din jikinsa yyi masa ba ya karasa kusa da
Haydar dake kallonsu ya rungumesa yana
murmushi, Hydar ya kirkiro murmushin shi
ma yace "prince ku wuce gida her being
here ix vry risky," Mujaheed yace "tare xamu
wuce da kai ai" Hajiya xuwaira da
kawayenta suka cika kotu da koke kokensu
ganin yanda aka saka ma shehu Handcuff
xa a fita da shi, Mujaheed ya karasa kusa da
Aneesah dake hawaye tana kallon baffan
nata da shi din ma kallonta yake yana wani
mugun murmushi, Mujaheed ya kamo
hannunta yace "bana son unnecessary cry
din nn naki Aneesah," ya ja ta suka bar
wajen, Hydar da frnds dinsa dake taya sa
murna suka bi su a baya, Baffa ya bi
Mujaheed da kallo yana hade hakoransa
'yan sanda suka ja sa suka fice da shi, Hajiya
sae waige waige take tana neman
Mujaheed ta hangosa can yana saka
Aneesah cikin mota ta bisa da gudu tana
bubbuge jama'ah gudun kar ya shiga mota
yasa ta shiga kwala masa kira "Mujaheed
Mujaheed" ya juya yana kallonta, tun kan ta
karaso kusa da shi tana huci tace "ashe
dama kai ma munafuki ne bn sani ba? Ynxu
kana nufin duk kwanakin nn tsinanniyar
yarinyar nn na Gidanku ban sani ba, ynxu
gidan ubanwa xaka kai ta kke saka ta cikin
mota wllh sae dae nima a daureni amma
kmr yanda tasa dana ya sha wahala nima
sae na wahal da ita," Mujaheed yyi tsaki bai
sake saurararta ba ya shige motarsa da
sauri ganin saura kiris ta iso su yyi reverse
da sauri ya bar haraban kotun, da sauri ita
ma ta shiga tata motar ta bishi da gudu
tana tsine masa, Hydar ya girgixa kai cike da
takaici don yasan xa ayi hkn, ya shiga motar
abokinsa suka bi ta a baya. Kuka Aneesah ta
dinga yi tana ce ma Mujaheed ya ajiyeta
kawae ya tafi, bae ko saurareta ba ya ci
gaba da sharara gudu har yyi ma Hajiyar
nisa ko hangota baya yi, yyi tsaki yace "Allah
ya sauwake," ta madubi ya lura kmr
bakaken motar dake bayansa shi suke bi, ya
canxa hanya ya ga sun biyosa, bae gama
tabbatar da shi suke bi ba sae da yaga wani
na neman shan gabansa, ya taka burki da
karfi, hkn yasa Aneesah ta fasa ihu don ta
xata Hajiyar ce ta riskesu, taga wasu kattin
mutane biyar sun fito suna nuna masa
bindiga wae ya fito ga layi bbu kowa,
Mujaheed ya girgixa kai yace "ya salam," yyi
wani irin reverse ya canxa hanya kmr xasu
tashi sama, mutanen suka shiga tasu
motocin su ma suka bi sa da gudu, tunda
take bata taba ganin tashin hankali irin na
lkcn ba kuka take tana ihu tana rirrikesa
wae ya bude mata motar ta fita, ya rasa da
wanne xae ji kuma hkn da take yi xae iya sa
ya sake motar su lula wani gun daban hkn
ya sa watsa mata mari, ba shiri ta nutsu ta
sulale daga kan kujeran, ya dinga sharara
gudu suna binsa a baya, har cikin ikon Allah
ya samu taxara ssae tsakaninsu shima ta
dalilin wata mota ce da xata juya, yaga wani
guri da ake parkin mota yyi reverse da sauri
ya dawo ya shige tsakanin motocin dake
wajen ya kashe motar ya dafe kansa, yana
ganinsu suka xo suka wuce da gudu, ya
juya yana kallon Aneesah da har lkcn ke
kuka, bae ce mata komai ba, ya ji an kwan
kwasa motar ya xuge glass, mutumin dake
tsaye kan motar yace "biya fa ake malam ba
kyauta bane parkin din," ya ciro dubu biyu
ya mika masa ya ja motarsa mutumin a
tunaninsa gyara parkin din xae yi sae kuma
yaga yyi gaba, Mujaheed bae ce ma Aneesah
komai ba drivin kawae yake a hankali, yana
share xufar dake keto masa da
handkerchief wayarsa tayi ring ya duba ya
ga Mum dinsa ce.
.
Ya daga kiran da sallamarsa, maimakon ta
amsa kawae sae ta hau sa da bala'i, "prince
dama ka komo Nigeria ne don ka dauko ma
ni da ubanka magana ko, wacce yarinyar ce
kke tare da ynxu, har ynxu halin bnxan nn
naka na tare da kai ko, to wllh tun kan raina
bai gama baci ba na kamo hanya ko kuma
na hada ka da ubanka maxa maxa ka rabu
da yarinyar nn, umarni kuma nake baka ba
shawara ba, mutumin bnxa kawae" bae ce
mata komai ba ya tsura ma titi ido har ta
kashe wayarta snn ya juya a hankali yana
kallon Aneesah da ta hade kai da gwiwanta,
yasan Hajiyar Hydar ce ta kirata, ya tada
motar a sanyaye ya bar wajen, yana isa gida
yyi horn mai gadi ya bude gate yyi parkin ya
fito ya