Showing 51001 words to 54000 words out of 89717 words
kai ki daki," ta galla masa
harara ta mike ta yi hanyar stairs, yace "ba
sae da safe," ba tare da ta kallesa ba tace
"eh" ta haye sama ta afka daki," yyi
murmushi ya kashe kayan wutan falon ya
wuce dakinsa shima, Aneesah na shiga daki
ta shiga bathroom tayi wanka don bata yi
ba, kusan minti ashirin tayi tana wankan,
snn ta fito daure da towel, tana kkrin dauko
kayan da xata sa taji taku a hankali a stairs,
ta ci gaba da abinda take yi, bata ankaraba
taji an bude kofar dakinta a hankali, ta juya
da sauri xata shige bathroom don a
tunaninta Mujaheed ne, taji ance "ke," ta
juyo a tsorace jin bakon murya taga mai
magana, mutanen daxu na supermarket ne,
ta xaro ido a gigice xata fasa ihu daya ya
nuna mata bindiga, a hnkli yace "kina bude
baki ina harbe kanki yarinya," ta toshe
bakinta jikinta ya dau rawa taji kafarta ya
kasa daukarta ta sulale kasa a hankali
hawaye na bin kuncinta, bala ya karaso
kusa da ita ya tsugunna yana kalln jikinta
yce "hadin kai kawae xaki bani," sallau yace
"kai meye hka da'alla harbeta mu fice dgann
hadin kan me" bala ya galla masa harara yce
"in ga santaleliyar budurwa hka na kasheta
ba tare da na....." yana fadin hka ya daura
hannu kan cinyarta yana shafawa yana
murmushi yace "ban san ki bar duniya a
wahale 'yar budurwa, bna son kwarmato
kawae ki bani hadin kai," cikin rada yake
mata maganar, sallau yyi tsaki yace "ae sae
kayi sauri mu bar nn ko"
.
Aneesah ta girgixa kai a tsorace tana
hawaye tace "don Allah don Annabi don
darajan iyayenku kuyi hkuri ku rufa min
asiri, ni ban san me na maku ba," Bala na
'yar dariyar mugunta murya kasa kasa yace
"baki mana komai ba 'yan mata, aiko mu
kawae aka yi mu kashe ki," ya matso kusa
da ita yana mata kallon sha'awa yace "ni
kuma baxan iya kashe kyakkyawar bby kmr
ki ba tare da naji ddinki ba," ta mike tsaye
da sauri har lkcn hannunta na bakinta tayi
hanyar bathroom, yyi saurin fixgota da karfi
yana huci yace "ke yarinya ki bani hadin kai
kar na murde wuyar ki a nn," ya fara kkrin
cire towel din jikinta ta rike towel din da
karfi tana kuka tace "don Allah kayi hkuri...."
ya toshe bakinta yana huci yace "ke na fa ce
maki ba mu son kwarmato," ta girgixa masa
kai tana hawaye tace "gwara kawae ku
kasheni," sallau yace "da'alla ka bani bindiga
idan baxa kayi abun da ya kawo mu nn ba
ni nayi wnn ae bata lkcn mu kawae kke yi a
nn," bala ya watsa masa wani mugun
harara snn ya fixge towel din jikinta a
fusace tana ganin hka bata san lkcn da ta
kwala wani ihu a gigice da ya raxana su
gaba daya ba lkci daya kuma ta sulale wajen
sumammiya, sallau dake bakin kofa har lkcn
yace "harbeta mu fice bala harbeta mu fice,"
dai dai nn aka bude kofar dakin, Mujaheed
ya shigo, bala ya nuna masa bindiga da
sauri yace "kana karaso wa nn ina harbe
kanka," Mujaheed ya daga hannun sama a
hankali yana kallonsu da daddaya da
daddaya, sallau da tashi bindigar bbu komai
ciki ya shiga kallon bindigar a dan tsorace
yana kallon Mujaheed da ke kallonsa
hannunsa a sama, dubura ta fado masa ya
waske ya nuna ma Aneesah bindigar yana
matsawa daga kusa da Mujaheed kmr
akwae bullet ciki, Mujaheed ya karaso cikin
dakin a hankali har lkcin hannunsa na sama
yace "me kuke bukata daga gareni," cikin
tsawa bala na saitin bindigar hannunsa
yace "kana kara taku daya xan harbeka ka
tsaya daga inda kke," Mujaheed yyi fullstop
dae dae kusa da dressin mirror, cikin daga
murya sallau yace ka kwanta kasa kar na
harbeka kar kuma ka dago kanka, Mujaheed
ya sauke hannunsa a hankali yyi kmr xae
kwanta kmr yanda sallau yace yana
durkusawa ya tsuri kwalban humra dake
gaban Madubi da sauri cikin second da bae
wuce shidda ba ya jefi bala dashi, tas kke ji
dae dae goshin bala kwalban ya tarwatse
sae ga jini kmr famfo bala ya fasa ihu ya
dafe kan yana neman faduwa tuni jini ya
bata masa fuska, Mujaheed bae wani bata
lkci ba ya isa kusa dashi da sauri ya murde
hannunsa ya karbe bindigar ya nuna sallau
da shi, sallau da ya shiga karkarwa a tsorace
ya nuna ma Aneesah dake kwance a sume
wajen fankon bindigarsa, Mujaheed yyi
murmushin mugunta ya karaso kusa da shi
sallau yyi karfin halin cewa kana matsowa
ina harbeta wllh, Mujaheed ya buga masa
bindingar da karfi a ka yace harbeta, sallau
ya sake bindigar jikinsa ya dau bari, tun
shigowar Mujaheed ta reaction din sallau ya
gane ba komai cikin bindigar hannunsa, ya
shake sallau da karfi ya buga sa da bango,
bala na ganin haka ya fara kkrin guduwa
daga dakin Mujaheed ya sa kafa ya
kwashesa snn ya rufe kofar dakin, duk sae
da ya sumar da su kmr yanda suka sumar
da Aneesah don dukan fitar hankali yyi
masa. Sae da ya gama dasu snn ya durkushe
gaban Aneesah da sauri ya dago ta yana
kiran sunanta, wayarsa ya dauka da sauri ya
kira wani frnd dinsa likita yace yana
bukatansa urgently, ko minti goma bae cika
ba Doctor din ya shigo gidan don basu da
wani nisa, Mujaheed yace ya hayo sama ya
shigo dakin baby, likitan na bude dakin ya
kasa shiga ya tsaya daga bakin kofa baki
bude ya firffito da ido yana kare ma dakin
kallo, Mujaheed dake rungume da Aneesah
har lkcn yace "da'alla ka shigo ka tsaya daga
bakin kofa," likitan yace "meye hka nake
gani Mujaheed?" Mujaheed yyi tsaki a fusace
yace "ni ka xo ka duba min yarinyar nn
Aminu," da kyar doctorn ya shigo dakin ya
tsallaka su bala ya karaso kusa da Mujahee d
da sauri yace "wacece wnn kuma jaheed ,
me ya faru? Su waye kwance a nn"
Mujaheed yace "ka duba min ita da'alla can,"
Aminu ya shiga dudduba Aneesah yana
kallon Mujaheed yace "ae suma tayi,"
Mujaheed ya daga ta ya daura kan gado
yana kallon Aminu yace "to ae sae ka
farfado da ita ka tsaya kana kallona,"
~25~
Likitan yace "to ina kayan aikin da xan duba
ta da?" Mujaheed ya hararesa yace "dole sae
da kayan aiki kawae ka duba min ita
malam," Aminu ya girgixa kai yana kare ma
su bala dake kwance shememe a tsakar
dakin kallo ya karasa kusa da Aneesah ya
kara dubata snn yace "ka kwantar da
hankalinka yallabae tsorata ce kawae tayi ba
wani abu ba, basu taba ta ba ina ga, wae
yan fashi ne wa in nan koko?" mujaheed
yace "oho," snn ya ciro wayarsa ya kira wani
abokinsa dan sanda yyi masa bayanin
abinda ya faru, dayake dan sandan babba
ne yace to gasu nn xuwa, ya katse wayar
yana kallon Aminu yace "don Allah kaje gida
ka dauka su stesthoscope da allurori ka
farfado min da yarinyar nn Aminu," Aminu
yyi dariya yace "asibiti ma gaba daya xan
dauko," yana fadin hka ya fice daga dakin
yace "ina xuwa," mujaheed ya bi bayansa
yace "ni ban ma je na duba mai gadin nn
ba," suna fita suka tura dakin mai gadi suka
tarar da shi a kwance an xuba masa
cocaine, da sauri Mujaheed ya kullo dakin
kar shima ya shaka yace "Allah sarki," ya
bubbude windows din dakin don warin ya
fita snn ya koma ciki bayan fitar Aminu da
kamr Minti sha biyar 'yan sanda suka shigo
gidan, suka shiga yi ma Mujaheed
tambayoyi yace "ni fa ban san ko suwa ye
ba" nn dae yyi masu bayanin abinda ya
shigo dakin ya tarar yyi defendin din kansa
kuma, suka kwashe su bala da bindigoginsu
suka saka cikin motarsu mujaheed yace ma
su gobe xae xo station din snn suka wuce,
suna barin gidan Aminu ya dawo, yyi mata
allurori, snn ya taimaki Mujaheed suka gyara
dakin, bayan kmr minti ashirin ya duba ta
yace "kaga ynxu bacci take, at anytime xata
iya farkawa ga magunguna nn ka bata idan
ta tashi ni xan koma gida," Mujaheed yace
"haba dae it's too late ka bari gobe mana,"
Aminu yace "aa bbu koma ae da mota
nake," Mujaheed ya rakosa waje ya nuna
masa mai gadi, shima yy masa alluran snn
yace "ka bar kofar dakin a bude gobe xae
dawo hayyacinsa shi kuma," Mujaheed yace
"ok," snn ya rakasa ya shiga mota ya dawo
ciki ya kulle gidan yana mamakin me ya
hana mai gadi kulle gidan da wuri, bae san
tun karfe tara su bala ke labe a anguwar ba,
suna ganin mai gadi ya fito suka shaka
masa cocaine suka shiga da shi dakinsa
suka kulle, snn suka fita daga gidan suka
rufo gate, sae daxun nn suka shigo.
Mujaheed na komawa dakin ya yaye bargon
da ya lullube Aneesah da ya tsura mata ido
yana kallonta daga ita sae inner wears,
tausayinta ya cikasa, ya rumtse ido rufeta ya
koma gefen gado ya xauna ya dafe kansa,
yana xaune wajen har kusan karfe daya ya
ga tana motsi, ya juya da sauri yana kallonta
a hankali ta bude ido tana kare ma dakin
kallo, lkci daya ta fasa ihu, ya mike da sauri
ya karasa gabanta ya riketa yace "menene
kanwata" ta fashe da kuka tana kkrin
mikewa xaune ya rikota yace "haba
Aneesah nine fa yayanki," ta kankamesa
tana kuka tace "na shiga uku yayana," ya
rufe bakinta da sauri yace "sun maki wani
abu ne kanwata," kuka kawae take kmr
ranta xae fita bata ce masa kmai ba,
hankalin Mujaheed ya tashi yace "haba
kanwata kiyi min magana mana, sun maki
wani abu ne," ta girgixa masa kai da kyar
tana kuka tace "wae kasheni suka xo yi," ya
rungumota da sauri yace "bbu wanda xae
kashe min ke kanwata sae lkcn ki yyi, bana
son ki sake wnn kukan" gyada masa kai
kawae take tana hawaye yace "xaki sha tea
na baki maganinki" ta girgixa masa kai da
sauri tace "aa," yace "to ina ke maki ciwo
ynxu kanwata," bata ce masa komai ba sae
ajiyar xuciyar da take, ya sake tambayarta ta
girgixa masa kai tace "ba ko ina," ya dago
kanta yana kallonta yace "ki kwanta kinji
kanwata," ta kankamesa ta fashe da kuka
tace "wllh ni baxan kwana cikin dakin nn ba
tsoro nake ji don Allah kar ka tafi ka barni,"
yace "haba kanwata, add'ua fa xaki yi ki
kwanta, baxa su sake dawowa ba, nasa an
tafi da su station," cikin kuka tace "wllh
tsoro nake ji ka kaini gun Ammina,"
Mujaheed ya rasa me xae ce mata yyi shiru
yana kallonta, a hankali tace "yayana kar ka
tafi ka barni don Allah ina rokanka," yace "to
naji, kiyi kwanciyarki a kan gado ni sae na
kwanta a kasa," ta rikesa tace "A'a wucewa
xaka yi ka barni yayana," a hankali yace
"shekaranki nawa Aneesah," ta na goge
hawayen fuskarta tace "16" ya mike tsaye ta
rikosa da sauri tana kuka tace "wayyo
yayana wucewa xaka yi," ya girgixa mata kai
yace kaya xan dauko maki ki sa, ita ma ta
mike da sauri ta bisa ya juya yana kallonta
bae ce komai ba ya fito mata da wani gown
mara nauyi ya mika mata tana rike da shi
duk don kar ya fita ya barta ta sa rigan, ya
koma kan gadon tana biye da shi a baya ya
kwantar da ita ta riko hannunsa tana sabon
kuka har wani rawa jikinta yake tace
"wucewa xaka yi ka barni yayana?" ya
girgixa mata kai ya kwanta ta daya side din
yace "kiyi baccinki bbu inda xa ni kinga na
kwanta," ta gyada masa kai ta matso kusa
da shi a hankali ta kwanta tayi lamo a
bayansa tana sauke ajiyar xuciya, ya juyo
yana kallonta da kyar yace "kinga Aneesah
idan baxa ki kwanta a can ba ni xan bar
maki dakinki,"
.
Aneesah ta girgixa masa kai da sauri tace
"A'a kar ka tafi ka barni yayana," a hankali
yace "to koma can," ta koma inda ya nuna
mata tana hawaye ta kwanta, ya juya mata
baya, Mujaheed ya kasa bacci, kuma bae
sake juyawa ba bare ya kalli inda take, a
hankali yaji ta birginowa kusa da shi tayi
lamo a bayansa, ya rumtse idonsa bae dae
ce mata komai ba, har bayan kusan minti
talatin snn ya juyo a hankali yana kallonta ta
takure kanta amma bacci take, ya mike
xaune a hankali kar ta tashi, ya kusan minti
biyar a xaunen daga bisani ya mike ya shige
bathroom dae dae lkcn da agogon dakin ke
struck din 2 o clck ya dauro alwala ya fito, ya
dauki darduma ya shimfida ya fara sallah, ya
kai kusan minti sha biyar yana sllh Aneesah
ta farka a tsorace ta mike xaune da sauri
cikin kuka tace "na shiga uku yayana ina
kke," tayi shiru hankalinta ya kwanta
ganinsa yana sllh, ta bar kan gadon ta dawo
gefensa da sauri ta xauna, can dae ganin ba
gama sllhn xae yi ba, ta tashi ta shiga
bathroom ta wage kofar yanda xata dinga
ganinsa da kyau tayi alwala ta fito ta dauki
hijab dinta ta fara binsa sllhn ita ma, daga
karshe gajiya tayi da binsa ta sallame ta
kwanta kan darduman a bayansa nn da nn
bacci ya kuma dauketa, ba shi ya idar da
sllhn ba sae kusan karfe hudu, ya mike ya
dauko bargo ya lulluba mata snn ya koma
kan darduman ya xauna yana addu'a, daren
ranar dae Mujaheed bae yi bacci ba asuba
tayi xae tafi masallaci ya tuna kar Aneesah ta
tashi ta dinga rusa mashi ihu a gida hkn
yasa yyi sllhn a dakin, snn ya tasheta ita ma
tayi sllh, har gari ya waye bata bar gefen
Mujaheed dake duba wani littafi ba, can ya
juyo yana kallonta yace "kin tashi lfya
kanwata?" ta dan yi murmushi ta sunkuyar
da kanta a hankali tace "ina kwana yayana,"
yyi murmushi ya gyada mata kai ya mike
yace "kije kiyi wanka, nima shi xanje nayi,
da wuri xamu fita yau don sae mun fara
xuwa station," ta marairaice fuska tace "aa
ni yaya kar ka tafi ka barni," yace "to je kiyi
wankan ki fito ina jiranki, baxan tafi ba," ta
mike jikinta a sanyaye ta shiga bathroom ya
bi ta da kallo yana murmushi, bayan kmr
second talatin ta budo kofar ta ga ko yana
nn har lkcn, ta rufe da sauri ganin yana nn,
shi ko yyi murmushi sae da ya ji ta bude tap
snn ya bude kofar dakin a hankali ya fice, ko
da ta fito bata gansa ba ta fashe da kuka ta
fice daga dakin da sauri tayi hanyar dakinsa,
ta jirasa xaune a dakin har ya fito, yana
ganin ta yace "xan fa bata maki rae kanwata
baki shirya ba xaki fito," muryar ta na rawa
tace "tsoro nake ji," ya harareta yace "tsoron
idonki ba," ya rakata ya tsaya daga bakin
kofa ta sa kayan snn ta fito da sauri, tana
xaune ya shirya a dakin, snn suka sauko falo
tare, coffee kawae ya sha ita ko ya tilasta ta
ta ci tea da bread snn suka bar gidan bayan
Mujaheed ya duba mai gadi, a hanya ya
kalleta yace "Aneesah su waye mutanen
jiya," nn da nn hawaye ya cika idonta tace
"nima ban sani ba, amma jiya na gansu a
supermarket, kuma naga kmr suna biyo mu
har muka kai gida snn suka canxa hanya,"
yyi parkin da sauri yace "wat, shine baki
gaya min ba Aneesah," ta fashe da kuka tace
"ni ban san da gske binmu suke ba ashe,"
mujaheed yace "to me suka ce maki?" a
hankali tace "sunce aiko su akayi su
kasheni," Mujaheed ya gyada kai yace xasu
ci ubansu, snn ya ja motar suka bar wajen,
kin shiga station Aneesah tayi tace xata
jirasa a waje, ya shiga shi daya, bae fito
daga station din ba sae kusan karfe tara,
yace "srry kanwata kin gaji da jira ko," ta
girgixa masa ka kawae yyi reverse suka
kama hanyar gidan yari, bae ce mata komai
ba ita ma bata tambayesa ya akayi ba, ko da
suka isa ba su sami ganin haydar a lkcn ba,
aka ce masu sae eleven, suna xaune suna
jiran eleven din yyi Aneesah tace "yayana
tsoro nake ji gabana sae faduwa yake ban
san meyasa ba," ba tare da ya kalleta ba
yace "kiyi ta addu'a," a hankali tace "yaushe
xaka nemo min Ammina yayana," ya juya
yana kallonta yace "vry soon," tace "yayana
amma ba gidan nn xamu kwana ba yau
ko?" yyi murmushi yace "eh" ba tare da ya
kalleta ba, karfe sha daya aka basu ixinin
shiga gun Hydar, Mujaheed ya juya yana
kallonta a sanyaye murya can kasa yace
"tashi muje kanwata," Aneesah ta xaro ido
tace "aa ni baxan shiga ba yayana tsoransa
nake ji, ba kace yarinya ya sace ba,"
Mujaheed yyi murmushi ya kamo hannunta
yace "c'mon sharri aka masa abinda ma xae
ga yarinyar ynxu," bae jira me xata ce ba ya
ja ta tana nonnokewa kmr xa tayi kuka suka
shiga inda Hydar yake.
.
Haydar ya dago kai yana kallonsu, har lkcn
Aneesah na labe bayan Mujaheed wae ita
tsoro take ji, Hydar ya hade rae yana kallon
Mujaheed ganin ba shi kadae bne don a
xatonsa daya daga gantalallun 'yan matansa
ya taho masa da, Mujaheed ya kyaleta ya
karaso kusa da Haydar ya xauna yana
kallonsa, kasa karasa wa Aneesah tayi ganin
Hydar bayan Mujaheed ya bar ta gun a tsaye,
ji tayi kafarta ya kasa daukar ta ta durkushe
wajen jikinta na rawa, hkn ne dalilin da ya
sa Hydar dago kansa yana kallonta don har
lkcn bae kalle da warce Mujaheed ya shigo
ba, ya mike tsaye a hankali yana kallon
Aneesah da mugun mamaki, Aneesah ta
fashe da kuka tana kallon Mujaheed da ya
tsiri danna waya tace "wayyo Allahna ya
Hydar me kke yi a nn," Hydar ya juya yana
kallon Mujaheed da alamar tambaya, amma
ya kasa cewa komai, ba tare da Mujaheed ya
kallesa ba yace "ita ce Aneesar da kke gaya
min ko," Hydar ya koma ya xauna da kyar
yana ci gaba da kallon Aneesah da mamaki
yace "ina ka samo ta Mujaheed," Mujaheed
ya juya yana kallon Aneesah dake kuka ssae
tana kallon Hydar, bae ce komai ba ya ci
gaba da danna wayarsa, Hydar ya karasa
kusa da Aneesah ya durkushe gabanta yana
kallonta, ta dago kai ita ma tana kallonsa, a
hankali yace "Aneesah," ta girgixa masa kai
ta fashe da wani sabon kukan ta fada
kansa, ya dagota ya girgixa mata kai yace
"No Aneesah," muryarta na rawa tace "ya
Hydar me kke yi a nn dama kai ne yayana ke
fada min," ya tsura mata ido yace "waye
yayanki," ta juya tana kallon Mujaheed da
har lkcn idonsa na kan waya bae ko kalle
inda suke ba, Hydar ma ya juya yana
kallonsa, mujaheed dae bae ce masu kmai
ba, Hydar ya dawo da dubansa ga Aneesar
yace "ina ya kai ki Aneesah?" ta goge
hawayen fuskarta tace "wa?" yace
"baffanki" ta dan yi shiru tana ci gaba da
goge hawayen da yaki tsaya mata tace "can
wani gari ya kai ni," Hydar yace "gun wa?"
ta fashe da kuka tace "ban san su ba, can
wani kauye ya kai ni a kaduna," Hydar yyi
shiru snn yace "Ammi fa?" cikin kuka tace
"ya Hydar ban ga Ammina ba amma yayana
yace xae samo min ita," Hydar yace "gun wa
kike ynxu?" tace "gun yayana," yace "waye
yayanki," ta juya tana kallon Mujaheed, wnn
karon dae Hydar bae kallesa ba, Hydar bae
sake ce mata komai ba ya kauda kansa,
ganin yyi shiru ne ya sa tace "ya Hydar ka
gaya min wa ya kawo ka nn, me kayi?" ba
tare da ya kalleta ba yace "ca akayi na sace
ki," ta fashe da kuka tace "wa yace hka ya
Hydar?" Hydar yace "baffanki," kuka ta shiga
yi ssae, ya dagota ya sa hannu yana share
mata hawayenta yace "kar ki damu
Aneesah, in'sha Allah komai ya xo karshe ki
kwantar da hankalinki," ta gyada masa kai
kawae, ta juya bata sake ganin Mujaheed
ba, ta tsayar da kukanta ta mike tsaye da
sauri tace "ya Hydar ina yayana?" bae ce
mata komai ba ya tsura