Showing 15001 words to 18000 words out of 89717 words

Chapter 6 - Aneesa Complete Hausa novel

13 Jul 2024

17489

ranr
ya kai sau uku kuma a kafa, snn dk se da tyi
masu guga da kwalemar dakunansu, krfe
uku suka bar gidn bayan sn ci abncin rana,
sumy ta kawaso mata takalmnta ta wanke
na wankewa na gogewa kuma ta goge tce
mata to, snn suka bar gidn gaba daya har
da Hajiya amma banda pretty, sae bayan
fitarsu pretty tayi mata magana ta kuma
kawo mata maganinta na jiya da Haydar ya
siyo mata tace yace ta bata, ta kuma kama
mta sauran aikin da suka rage a gidan kafin
'yan uwanta su dawo.
.
Yau
Alhamis da kyar Aneesah ta iya xuwa wajen
aiki
don daga ita har Ammi cikin satin duk basu
da lfya
barin ita da nata yafi tsanani daurewa
kawae tayi
ranar taje aiki, tayi masu duk abinda take
masu na
kari don har lkcn basu tashi ba, snn ta shiga
gyaran gida, Haiydar ya sauko yana kallonta
ya
karaso gabanta yace "ya jikin kanwata," ta
dago
tana kallonsa snn ta gaishesa, ya amsa yana
murmushi yace "sarkin aiki, har kin fara" ita
ma
tayi murmushin ba tace komai ba ta ci gaba
da
abinda take, ya xauna yana kallonta har ta
gama
goge gogen da take yi snn ya ja ta xuwa
kitchen
su yi breakfst, tilasta mata ya dinga yi yana
bata
tana ci don ca tayi mashi ta koshi amae take
ji,
bae kyaleta ba sae da ya ga ta kwararo
aman, ya
mike ya riketa da sauri ta dinga yi, ya ja ta
suka
shiga garden, ya taimaka mata ta gyara
jikinta yana
kallonta da tausayi yace "wae don Allah ki
gaya
min me ke damunki Aneesah duk kwanan
nn na
lura yhu re just managin yhur sef, gaya min
ina ke
maki ciwo," ta girgixa masa kai tana
hawaye tace
"kawae bana jin ddi ne, ni ban san idan ke
min
ciwo ba," yace "to muje asibiti kanwata," ta
girgixa
masa kai tace "A'a ni bbu inda xanje," dole
ya fita
siyo mata magani kafin 'yan gidan su sauko
ya
bata ta sha, snn ya kira pretty ta taimaka
mata da
wanke wanke, da mopping kafin masu
bacci su
tashi. Hka Aneesah ta dinga daurewa ranar
a gidan
bayan Haiydar ya fita, pretty ce ma ke dan
taimaka
mata da wasu ayyukan a boye, karfe uku
Haiydar
ya shigo gidan da abokinsa Najeeb, Hajiya
taji ddin
ganinsa sosai don dama tana son hada
Haiydar
dashi ya ja masa kunne ya fita harkan 'ya
yanta,
duk 'yan matan suka fito gaidashi cike da
murna,
ya rungume pretty yana dariya yace "kai,
bbyn
Haiydar hka kika girma," tayi dariya tace "ae
kai
ma ka girma yaya," shima yyi dariyan yana
tambayarta ya karatu, Haiydar da duk
hankalinsa
ya tafi gun Aneesah don ganinta kawae
yake son yi
sanin halin da ya tafi ya bar ta daxun, yace
"ka
kyale min kanwata hka ni dae kar ka cikata
da
surutu," pretty ta dawo jikin yayanta tana
dariya
tayi masa sannu da xuwa, su sumy da
meenah
sae hararta suke suna tabe baki, Hajiya tace
"wae
ina wnn mahaukaciyar yarinyar take ne, ko
uban
me ma take yawan yi a garden ni kam na
kasa
ganewa, bata ji munyi baki bne," meenah ta
tabe
baki tace "bacci take xuwa yi mana, ko da
baki
sani ba," pretty ta mike tsaye da sauri tace
"daxu
dae naga tana shara ne, bari naje na kirata,"
xaune
ta tarda Aneesah ta hade kanta da gwiwa,
ta
durkusa gabnta a hnkli tace "Ana kiranki,"
Aneesah
ta mike da kyar tana ganin jiri pretty tace "ki
bari
yaya ya kai ki Asibiti mana," ta girgixa mata
kai
tayi murmushi kawae suka shiga gidan, a
walakance aka ce ta kawo ma Najeeb lemo,
ta bude
fridge ta ciro lemun da ruwa ta daura da
glass cup
kan faranti ta kawo masa ta durkushe
gabansa
bayan ta gaishesa a hankali, snn ta bude
lemun ta
xuba masa a cup ta dago tana mika masa
gnin
ranar da ta ajiye ma Haiydar xaginta aka
dinga yi,
ido ya tsura mata da mamaki yana kallonta,
gabanta ya shiga faduwa da sauri da sauri
muryar
ta na rawa tace "gashi," ya mika mata
hannu har
lkcn idonsa na cikin nata, ta sake masa juice
din a
tunaninta ya rike, kofin ya fada kansa juice
din
gaba daya suka xube jikinsa, duk wnn
abinda suke
yi kan idon Haiydar da ransa ya gama baci,
Aneesah ta mike a tsorace ta dafe kirji tace
"na
shiga uku wllh ban sani ba," Hajiya ta mike a
fusace tace "kan uban nn ikon Allah kadae
ne xae
sa baxan sumar dake yau ba," tana gama
fadin
hka ta yo kanta, Najeeb ya mike da sauri
yace "ba
laifinta bne mum, nine ban rike kofin ba
ashe,"
cikin fushi hajiyar tace "to ita dabbar ina ce
da
baxa taji ko an rike kofi ko ba a rike ba, hka
fa
ranar tayi ma Aliyu, iskanci ne kawae da
mugunta
irin ta dan kauye, da ka bar ni naci ubanta
kawae
najeeb" najeeb yyi murmushi yana kallon
Aneesar
yace "je ki kawae," ta juya da sauri ta bar
wajen
tana hawaye, Aliyu ya mike ya bar falon
bayan kmr
minti biyar ya sauko ransa a hade yace "mu
je na
dauki abinda xan dauka, Najeeb ya tsaya
kallonsa
da mamaki snn yace "to ina abinda nace
xan karba
idan na xo," ya juya ya haye sama ya dauko
masa,
Hajiya tace "A'a har xaku tafi dama ba
ddewa kaxo
yi ba," Najeeb yace "wllh sauri muke mum,
amma
ran sunday xan dawo idan Allah ya yrda,"
Hajiya
tace "to shkkn don Allah ka fa xo don ina da
magana da kai," yace mata "to" snn yace
yana
xuwa ya dauko abu a mota, ya fita ya xaga
yyi
hanyar garden, tana xaune ta xabga tagumi,
ya
karaso gabanta ya durkushe, ta koma baya
a
tsorace jin ba kamshin turaren Haiydar ba
knn, ya
sakar mata murmsuhi yana kallon cikin
idonta yace
"wllh wllh kina da kyau,
.
Aneesah ta koma baya a tsorace ta fara
kkrin mikewa xata bar wajen ya rikota da
sauri ta fixge hannunta a tsorace tace
"meye hka malam wnn wani irin iskanci ne,"
ya wara idonsa ya sake kamo ta da sauri
yace "wats wrong bby yhur temperature is
high," ta buge masa hannu tare da fashewa
da kuka tace "wae meye hka a ina na sanka
ni fa ba 'yar iska bace" yy dariya ya
rungumota gaba daya yace " nima ba dan
iskan bane ba ai, kuma sae kin gaya min
inda ke maki ciwo ko kuma na duba ki
ynxun nn a nn," Haiydar ya shigo garden din
kmr wani xaki tana ganinsa ta fara kkrin
kwace kanta amma ta kasa don kin sakinta
yyi, har Haiydar ya karaso gurinsu Najeeb
bae gansa ba ita ce dae ta gansa, Haiydar ya
fixgota a fusace ya wurgar yana huci yace
"a hkn kike yawan gaya min ke ba 'yar iska
bace," ta fashe da kuka ta hde kanta da
gwiwa, ya juya a fusace yana kallon Najeeb
yace "ka fita gonata malam kar na baka
mamaki, bnxa kawae dan iska," ya juya a
fusace ya bar garden din, najeeb ya bi sa da
kallo yana murmushi, ya karaso gabanta ya
durkusa yace "am srry bby, xan basa
magani ya kawo maki ltr bye," ya mike
shima ya bar garden din, tana jin fitar
motarsu a gidan ta mike da kyar tana goge
hawayen da ya ki tsaya mata ta shiga gidan
kafin hajiya ta fara kwala mata kira tana
nemanta. Har Aneesah ta bar gidan ranar
bata ga Haiydar ba, da kyar ta isa gida ta
tarda jikin Ammi yyi sauki don har ta gyara
gidan tayi masu girki, wanka da Alwala
kadae ta iya yi ta kwanta don kasa sallahn
tayi ammi tace ta sa kaya su tafi Asibiti
amma tace aa don sanin kanta ne kudi
kadan ya rage a hannunsu ynxu kafin
karshen wata a biya su, Ammi ta fita siyo
mata magani a chemist suka shigo tare da
yusuf ya dawo daga makaranta, ya xube
jikinta yace "Antyna baki da lfya har ynxu,"
ta gyada masa kai da kyar, yace "to Anty
idan na girma xan xama Doctor don na
dinga baki magani idan baki da lfya ke da
Ammina" Aneesah ta mike da sauri tace "A'a
lawyer xaka xama yusuf don ka dinga kare
ryt din mutane," ya mike tsaye da sauri yace
"A'a na manta Anty soja xan xama don na
kama baffa na dauresa nae ta dukansa na
sa shi frog jump idan ya sake yi ma Ammi
da ke ihu, kuma xan xama mai kudi na siya
maku gida na dinga baku abinci kullum"
Aneesah ta dinga dariya ta rungumosa tace
"yauwa yusuf dina shi yasa nake son ka,
Allah ya bar mu tare," Ammi ta dinga
murmushi tana kallonsu, nn da nn Aneesah
ta nemi xaxxabinta ta rasa, hka suka dinga
hira yusuf na basu dariya da shirmensa har
dare ya raba snn suka kwanta. Washegari
Aneesah ta tashi da karfinta taji bbu wani
sauran xaxxabi a tattare da ita, ta kama
hanyar gidan aikinta bayan ta ajiye yusuf a
sch, don ca yyi ita xata kai sa ranar baxae bi
su jamia ba, hkn yasa ta fara ajiyesa bakin
gate tayi peck dinsa tayi masa bye bye snn
ta tafi gidan aikinta, har kusan rana bata ga
Haiydar ba, da yake duk 'yan gidan sun tafi
gantali daga ita sae pretty a gida tana tae
mata hira, karfe hudu saura tana wanke
wanke kafin 'yan gidan su dawo pretty na
sama taji wani mugun xaxxabi na neman
rufeta, ta dinga ganin jiri ga ciwon kai da ya
sa ta kasa bude idonta, ta gama wanke
wanken da kyar ta shiga garden ta xauna ta
jingina jikin bango tana mayar da numfashi,
a hka Haiydar ya xo ya sameta a garden din
ya durkusa gabanta ba tare da ya bari sun
hada ido ba yace "har ynxu jikin ne
kanwata," bata ce masa komai ba kanta a
sunkuye, xae yi magana motarsu Hajiya
suka shigo gidan, ya mike da sauri ya shiga
kitchen sae gashi ya fito da ruwa a glass ya
fito da ledar magani ya balla ya durkusa
gabanta yace "gashi ki sha kanwata hope
kinci abinci," ba tace masa komai ba kuma
bata karbi maganin ba, ya dinga rokanta
yana lallabata ta sha maganin amma taki ko
da dagowa ta kallesa sae hawayen da take
tayi, ya mike yyi tsaki ta dalilin kiransa da
yaji Hajiyarsa nayi a falo, bae sake shigowa
garden din ba har karfe biyar saura, ganin
baxa ta iya daurewa bne kuma yasa ta mike
da kyar tana ganin jiri ta shiga falon tace ma
Hajiya tayi hkuri xata tafi gida bata da lafiya,
Hajiyar ta tsaya kallonta don duk wanda
yaga yana yinta yasan bata da lfya, ta tabe
baki xata yi magana pretty tace "momy ki
bar ta ta wuce tun tuni take ta ma mutane
amai kar taje ta sume mana a gida," Hajiyar
tayi tsaki tace "to tashi sae ki gyara min daki
snn ki tafi makira kawae," Haiydar ya mike
yyi waje, ita ko ta shiga ta gyara dakin da
kyar snn ta fito tayi masu sae da safe ta fita,
sumy ta bita a baya, Haiydar na tsaye bakin
gate yana jiranta, tana fitowa kuwa xae yi
magana sae ga sumy, ya juya da sauri yana
danna wayarsa kmr mai shirin kira, ita ko ta
kama hanyar gida tana karanto addu'a a
xuciyarta na Allah ya kai ta lfya ganin
condition dinta, Haiydar ya galla ma sumy
harara a fusace yace "uban me kike nema a
nn," cikin ladabi kar ya maketa tace "kawata
nake jira bata san gidan ba shi yasa na fito,"
yyi tsaki ya juya bae.
~9~
Cikin ikon Allah Aneesah ta isa gida ranar
gabanta na faduwa, amma me, sae taga
mutane fal a kofar gidansu, nn da nn ta
daina ganin jirin da take gani bugun
xuciyarta ya tsananta kuma duk wani ciwo
ta neme shi ta rasa sae bugun xuciyar, ta
karaso da sauri a rude tana tambayar
mutanen me ya faru, bbu wanda ya tanka
mata, a gigice tace "nashiga uku ina
Ammina," nn ma bbu wanda ya bata amsa
sae ma hawaye da taga wasu nayi ba
manyan ba ba yaran ba, haba bata san lkcn
da ta fasa wani raxanannen ihu tayi cikin
gidan da gudu tana kwala ma Amminta kira
a rude, bata damu da kiran da
makwabtansu dake tsakar gidan ke mata
ba, wasu suka bi ta a baya da sauri, da gudu
ta fada dakinsu tana ci gaba da kwala ma
Amminta kira, xaune ta ganta makwabtansu
da dama na xaune gefenta wasu na hawaye
wasu sunyi jigum, nn da nn ganin Amminta
yasa Hankalinta ya kwanta ta xube jikin
Ammin tana maida numfashi har lkcn jikinta
na rawa tana hawaye tace "Ammina me ya
faru," Ammi bata tanka mata ba sae kkrin
boye hawayen da take yi tana shafa kanta
tace "har kin dawo," sae kuma Ammi ta
fashe da kuka, Aneesah ta fara kalle kallen
dakin a tsorace murya can ciki tace "ina
yusuf Ammi," Ammi bata ce mata komai ba
sae kukan da take yi, Aneesah ta shiga jijjiga
Ammin tata a rude tace "Ammi don Allah ina
yusuf ki gaya min," kmr ance ta juya taga
abu a nannade cikin farin kyalle ta karasa da
sauri hannunta na rawa ta bude, me xata
gani, kaninta a kwance ba rai, bata san lkcn
da ta fasa wani irin kara ba daga nn kuma
bata sake sanin me ya faru ba, ta dae farka
can cikin dare ta ganta kwance kan gadon
amminta da makwabtansu har uku a dakin,
Ammi ko na kan darduma a xaune.
.
Aneesah ta dauke idonta da sauri daga na
sa ta sunkuyar da kai tana wasa da
yatsunta, cikin tsawa hajiya tace "rainin
wayon naki ne ya tashi shegiya xaki yi ma
mutane shiru ki samu gaba kina kallo da
daddaya da daddaya don uwarki" ta girgixa
kai a raunane tana hawaye tace "kuyi hkuri
hajiya wllh kanina ne ya rasu," cikin halin ko
in kula Hajiya tace "to ni na kashe shi da
xaki ki xuwa min aiki," Aneesah tayi shiru
tana hawayen takaici, Hajiyar ta tabe baki
tace "to ki sani baxan biya ki kudi cikin wnn
watan ba sae karshen sabon watan da
xamu shiga, bace min da gani kar na ji maki
ciwo a nn mayya kawae ba kaninki ba
uwarki da ubanki ma su mutu ina ruwan
wani," Aneesah ta mike tsaye a sanyaye
hawaye na bin kuncinta xata bar falon, cikin
gadara meenah tace "kuma ga kayan wanki
na can ya taru ba kyan gani, dasu xa ki
fara," sumy tace "nima wllh gasu can duk ki
hada yau ki wanke mana ni har da takalma
na, kuma ki cire ma mutane wnn hijabin
jikin naki duk ya janyo ma mutane duhu a
falo," Aneesah dae na tsaye tana hawaye
tana kallon sumyn cike da takaici kuma bata
cire hijab din ba, sumy ta mike a fusace ta
fixge hijab din daga jikinta ta wurgar tana
huci tace "don uwarki ina maki magana
xaki yi min shiru......" ba shiri sumy tayi shiru
ta wara ido baki bude tana kallon gashin
kan Aneesahn da ya xubo har kusan
bayanta ta dalilin fixge mata hijabin da tayi
hade da dankwalin kanta, meenah ta mike
da sauri da mamaki tace "lala attachment ne
a kanki kina matsayin yar aiki ni nasa ke ki
sa," a fusace ta damko gashin Aneesar a
xatonta kari tayi kmr yanda su ma ke yi,
"wllh sae kin cire gashin nn ynxun nn a nn
idan ba hka ba har gashin kanki sae na aske
yau, dama munafuka shi yasa baki son cire
hijab idan kika......" wani wawan marin da
aka dauketa da ne ya sa ta kasa karasawa ta
fasa ihu a gigice ta sake gashin Aneesar
tana kallon wanda ya mareta yayanta ta
gani tsaye kanta yana huci, ya fixgota ya
buga ta da bango snn ya damki nata karin
gashin dake kanta yana huci ya makureta
cikin tsawa yace "uban me ta maki kike
neman birkita mata kwakwalwa nake son ki
gaya min kar na hallakaki a nn," Hajiya ta
mike tana salati a rude tace "me xan gani
hka Aliyu, meye hadinka da 'yar aikin nn
xaka kashe kanwarka kanta," ya wurgar da
meenar a fusace, ya dawo kan Aneesah da
ke durkushe a wajen tana rusa kuka, ya
durkusa gabanta ya dago kanta a hankali
yana kallonta cike da tausayi yace "kiyi
hakuri fateema," Hajiyar ta yo waje da ido
baki bude tana kallonsu a tsorace ta daura
hannu a ka tace "Aliyu," pretty ta mike a
hankali ita ma tana hawaye ta bar falon ta
haye sama, sumy ta mike tsaye ta fashe da
wani wawan dariya tana kallon uwartata
tace "heheho me na gaya maki mummy ba
kin ki yarda dani ba, ni dama nasan da wani
abun a tsakaninsu wllh, kin taba ganin yaya
ya hana 'yar aiki yi mana aiki a gidan nn, ko
kin taba ganin ya ci girkin 'yan aiki, ko 'yar
aiki ta taba shiga dakinsa da sunan gyara
masa ko yi masa guga, yaya bashi da aiki
ynxu sae na xuwa garden, ni dama nasan
da wani abu a kasa amma kika ki yarda dani
da meenah, yau dae gashi kin gane ma
idonki, shiyasa ranan nn ma na fita da sauri
ganin ko bin ta xae yi a bakin gate nayi
masa karya kwata nake jira, ba haushi na ya
dinga ji ba har washegari na hana sa bin
sahibarsa, a bnxa aka ce maki yake rashin
lafiya kwanan nn," ta sake fashewa da
dariya tana tafa hannu tace "kasala don
burst" Aliyu ya yo kanta cikin fushi ya buga
ta da bango da karfi, nn da nn se ga jini da
gudu kmr famfo, daga ita har Hajiya suka
rude Hajiya ta dinga rusa ihu tayi kitchen da
gudu tana cewa "kan wnn matsiyaciyar
xaka kashe min 'ya, wllh wllh wllh sae na
hallaka ta yau," sanin halin uwartasa yasa ya
ja Aneesar dake ta kuka da sauri suka bar
falon, yyi garage ya bude motarsa don
makulli na aljihunsa ya saka ta cikin motar
ya xaga da sauri ya shiga ya tada motar
yana horn ba kakkautawa, sae ga Hajiyar da
gudu ta fito rike da tabarya da wuka, cikin
tsawa ta dinga cewa maigadin kar ya bude
gate din, Aliyu dake jiran ya karasa bude
gate din kawae ya fice ya daka masa tsawa
yace "xan take ka da motar nn baka bude
min gate ba malam," maigadi duk ya rude ya
rasa umarnin wanda xae bi ganin Aliyu ya
yo kansa da motar yasa cikin ihu a gigice ya
dinga cewa xae bude har ya wangala gate
din jikinsa na rawa Aliyu ya fice da gudu ya
bar.
.
Sun yi nisa sosai, kawae tafiya yake ba tare
da ya san inda xa shi ba, Aneesah ko bbu
abin da take sae aikin kuka, ganin kawae
tafiya yake bai da alamar tsayawa yasa cikin
muryar kuka tace "ni ka sauke ni a nn na
wuce gidanmu," sae a snn yyi parkin gefen
titi, ya juyo yana kallonta, ta rufe fuskarta
tana ci gaba da kuka, ya kamo hannunta
yace "ya isa hkan Aneesah kiyi hkuri, bana
son kina kuka, nn" bata ce masa komai ba
amma ta kasa daina hawaye, ya ciro
handkerchief ya goge mata fuskarta yana
kallon gashinta da duk da talaucinsu ba a
haramta mashi gyara ba, don sae kyalli yake
ga tsantsi snn baki wuluk, ta cire hannunsa
daga kan gashin nata da ya dafa a hankali
tace "hijabina," ya gyada mata kai kawae,
snn ya ja motar suka bar wajen, sun danyi
tafiya mai nisa snn taga yyi park yace "fito ki
xabi wanda ki ke so," ta kasa cewa komai
tana kallonsa, ya gyada mata kai ta fito a
sanyaye daga motar suka fara tafiya a
hankali taga duk ido ya dawo kansu barin
ita, da sauri ta fixge hannunta tace "ni
baxan iya ba, ban da dankwali," ya komar
da ita motar snn shi yaje xabo mata Hijab
din, bayan kmr minti goma ya dawo da
katon ledar boutique a hannunsa ya shiga
motar yana kallonta ta sunkuyar da kai, yyi
murmushi ya bude mata ledar yace "gashi ki
xabi wanda xaki sa," a hankali ta jawo wani
milk colour taga yana da tsayi hkn yasa ta
saka shi kawae, tana kallonsa ya gyada mata
kai yyi murmushi snn ya tada motar suka
bar wajen, sae da suka hau kan titi snn a
hankali yace "ina ne gidanku?" ba tare da ta
kallesa ba tace "ka ajiye ni a nn, sae na
wuce," ya girgixa mata kai yace "baxa ki fita
daga motar nn yau ba knn," ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login